Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 5/15 pp. 3-7
  • Ta Yaya Ya Kamata Mu Bi Da Mutane?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Ya Kamata Mu Bi Da Mutane?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kasance Mai Tawali’u
  • Masu Jin Ƙai Suna Samun Farin Ciki!
  • Abin da ya sa “Masu-Sada Zumunta” Suke Farin Ciki
  • “Ku Bari Haskenku Shi Haskaka”
  • Ka “Sulhuntu da Ɗan’uwanka Tukuna”
  • Ka Daraja Mutane A Koyaushe
  • Yadda Zantattukan Yesu Ke Kawo Albarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Bayin Jehovah Masu Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • “Ku Bari Haskenku Shi Haskaka”
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • “Bari Ku Zama Masu Haske” Don Ku Daukaka Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 5/15 pp. 3-7

Ta Yaya Ya Kamata Mu Bi Da Mutane?

“Kamar yadda ku ke so mutane su yi maku, ku yi masu hakanan kuma.”—LUKA 6:31.

1, 2. (a) Menene Huɗuba a kan Dutse? (b) Menene za mu tattauna a wannan talifin da na gaba?

YESU KRISTI Babban Malami ne da gaske. Sa’ad da abokan gabansa na addini suka aika mutane su kama shi, dogarawan suka koma ban da shi kuma suka ce: “Babu mutumin da ya taɓa yin magana haka.” (Yoh. 7:32, 45, 46) Ɗaya a cikin jawabai mafi daɗi da Yesu ya ba da shi ne Huɗuba a kan Dutse. An rubuta shi a surori 5 zuwa 7 ta Linjilar Matta, kuma an rubuta irin wannan bayanin a Luka 6:20-49.a

2 Wataƙila furci da aka fi sani a cikin wannan huɗuba shi ne wanda sau da yawa ake kiransa Ƙa’idar Ja-gora. Ya yi maganar yadda za mu bi da mutane. Yesu ya ce: “Kamar yadda ku ke so mutane su yi maku, ku yi masu hakanan kuma.” (Luka 6:31) Kuma ya yi wa mutane nagarin abubuwa! Yesu ya warkar da marasa lafiya ya kuma ta da matattu. Mutane sun sami albarka musamman sa’ad da suka yi na’am da bisharar da ya gaya musu. (Ka karanta Luka 7:20-22.) Mu Shaidun Jehobah, muna farin cikin yin irin wannan aikin wa’azin Mulki. (Mat. 24:14; 28:19, 20) A cikin wannan talifin da na gaba, za mu tattauna maganar Yesu game da wannan aikin da kuma wasu bayanai a cikin Huɗuba a kan Dutse da suka shafi yadda ya kamata mu bi da mutane.

Ka Kasance Mai Tawali’u

3. Ta yaya za ka ba da ma’anar tawali’u?

3 Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-tawali’u: gama su za su gāji duniya.” (Mat. 5:5) A cikin Nassosi, tawali’u ba ragonci ba ne. Sauƙin hali ne da muke nunawa don muna bin farillan Allah. Muna nuna wannan halin a yadda muke bi da mutane. Alal misali, ba ma “sāka ma kowanne mutum mugunta da mugunta.”—Rom. 12:17-19.

4. Me ya sa masu tawali’u suke farin ciki?

4 Masu tawali’u suna farin ciki domin “za su gāji duniya.” Da yake Yesu “mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya,” an naɗa shi “magajin abu duka” saboda haka shi ne magajin duniya na musamman. (Mat. 11:29; Ibran. 1:2; Zab. 2:8) An annabta cewa Almasihu “ɗan mutum” zai samu waɗanda za su yi sarauta da shi a Mulkin samaniya. (Dan. 7:13, 14, 21, 22, 27) Da yake su “masu-tarayyan gādo [ne] da Kristi” shafaffu 144,000 masu tawali’u za su yi tarayyan gado da Yesu a duniya. (Rom. 8:16, 17; R. Yoh. 14:1) Za a albarkaci masu tawali’u da rai madawwami a duniya a ƙarƙashin Mulkin.—Zab. 37:11.

5. Ta yaya tawali’u irin na Kristi yake shafanmu?

5 Idan ba mu da tausayi, mutane ba za su so yin sha’ani da mu ba kuma hakan zai sa su guje mu. Amma kasancewa da tawali’u irin ta Kristi, zai sa mu zama masu fara’a kuma mu zama waɗanda za su riƙa ƙarfafa mutane a ruhaniya a cikin ikilisiya. Tawali’u yana cikin ’yar ruhu da ikon Allah ke sa mu nuna idan muka ‘rayu kuma muka yi tafiya bisa ga ruhu.’ (Ka karanta Galatiyawa 5:22-25.) Babu shakka za mu so a haɗa mu cikin masu tawali’u da ruhu mai tsarki na Jehobah ke yi wa ja-gora!

Masu Jin Ƙai Suna Samun Farin Ciki!

6. “Masu jinƙai” suna da waɗanne halaye masu kyau?

6 A cikin Huɗubarsa a kan Dutse, Yesu ya ce: “Masu-[farin ciki] ne masu-jinƙai: gama su za su sami jinƙai.” (Mat. 5:7) “Masu-jinƙai” suna nuna juyayi kuma suna jin tausayin talakawa. Yesu ya yi mu’ujizar da ta kawo sauƙi ga masu shan wahala domin ya ji “tausayi” ko kuma ya yi ‘juyayinsu.’ (Mat. 14:14; 20:34) Ya kamata tausayi da yin la’akari su motsa mu mu zama masu jin ƙai.—Yaƙ. 2:13.

7. Tausayi ya motsa Yesu ya yi menene?

7 Sa’ad da taron jama’a suka sadu da Yesu a kan hanyarsa ta zuwa inda zai huta, “ya ji juyayinsu, gama kamar tumaki su ke waɗanda ba su da makiyayi.” Saboda haka, “ya fara koya masu abu dayawa.” (Mar. 6:34) Mu ma za mu yi farin ciki sa’ad da muka gaya wa mutane saƙon Mulki da kuma jin ƙai da Allah yake nunawa!

8. Me ya sa masu jin ƙai suke farin ciki?

8 Masu jin ƙai suna farin ciki domin suna ‘samun jin ƙai.’ Sa’ad da muka yi wa mutane jin ƙai, su ma za su yi mana hakan. (Luka 6:38) Bugu da ƙari, Yesu ya ce: “Idan kuna gafarta ma mutane laifofinsu, Ubanku na sama kuma za ya gafarta muku.” (Mat. 6:14) Masu jin ƙai ne kawai za su sami farin cikin da ke tattare da gafartawar Allah da kuma amincewarsa.

Abin da ya sa “Masu-Sada Zumunta” Suke Farin Ciki

9. Menene za mu yi idan mu masu son zaman lafiya ne?

9 Da yake ambata wani dalilin yin farin ciki, Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-sada zumunta [son zaman lafiya]: gama za a ce da su ’ya’yan Allah.” (Mat. 5:9) Kalmar Helenanci da aka fassara ‘zumunci’ a zahiri tana nufin “masu son zaman lafiya.” Idan mu masu son zaman lafiya ne, ba za mu amince ba ko kuma mu sa hannu a yin wani abu kamar tsegumi, da ke “raba abokan gaske.” (Mis. 16:28) Ta furcinmu da ayyukanmu, za mu zauna lafiya da mutanen da suke cikin ikilisiyar Kirista da kuma waɗanda ba sa ciki. (Ibran. 12:14) Za mu yi iya ƙoƙarinmu mu kasance da salama da Jehobah Allah.—Ka karanta 1 Bitrus 3:10-12.

10. Me ya sa “masu-sada zamunta [“son zaman lafiya”]” suke farin ciki?

10 Yesu ya ce “masu-sada zumunta [son zaman lafiya]” suna farin ciki, “gama za a ce da su ’ya’yan Allah.” Domin sun ba da gaskiya ga Yesu a matsayin Almasihu, Kiristoci shafaffu sun sami ‘ikon zama ’ya’yan Allah.’ (Yoh. 1:12; 1 Bit. 2:24) “Waɗansu tumaki” na Yesu masu zumunci kuma fa? Yesu zai zama musu “Uba madawwami” a lokacin Sarautarsa ta Shekara Dubu tare da masu yin sarauta da shi a sama. (Yoh. 10:14, 16; Isha. 9:6; R. Yoh. 20:6) A ƙarshen Sarautarsa ta Shekara Dubu, irin waɗannan masu son zaman lafiya za su zama cikakkun ’ya’yan Allah na duniya.—1 Kor. 15:27, 28.

11. Ta yaya za mu bi da mutane idan muka bar “hikima mai-fitowa daga bisa” ta yi mana ja-gora?

11 Don mu more dangantaka na kud da kud da Jehobah, “Allah kuwa na salama,” dole ne mu yi koyi da halayensa, har da zaman lafiya. (Filib. 4:9) Idan muka bar “hikima mai-fitowa daga bisa” ta yi mana ja-gora, za mu bi da mutane cikin salama. (Yaƙ. 3:17) Hakika, za mu zama masu salama masu farin ciki.

“Ku Bari Haskenku Shi Haskaka”

12. (a) Menene Yesu ya ce game da haske na ruhaniya? (b) Ta yaya za mu bar haskenmu ya haskaka?

12 Muna bi da mutane a hanya mafi kyau sa’ad da muka taimaka musu su sami haske na ruhaniya daga wajen Allah. (Zab. 43:3) Yesu ya gaya wa almajiransa cewa su ne “hasken duniya” kuma ya aririce su su sa haskensu ya haskaka domin mutane su ga ‘ayyukansu masu kyau’ ko kuma nagarin abubuwan da suka yi wa mutane. Wannan zai sa gaskiya ta ruhaniya ta haskaka a “gaban mutane,” ko don amfanin ’yan adam. (Ka karanta Matta 5:14-16.) A yau, muna barin haskenmu ya haskaka ta wajen yi wa maƙwabtanmu nagarin abubuwa da kuma sa hannu a aikin wa’azin bishara da ake yi a “cikin duniya duka,” wato, “ga al’ummai duka.” (Mat. 26:13; Mar. 13:10) Gata ce mu sa hannu a wannan aikin!

13. Da menene aka san mu?

13 “Birnin da ke kafe bisa tudu ba shi ɓoyuwa,” in ji Yesu. Za a iya ganin birnin da ke kan dutse da wuri. Hakazalika, mutane suna gane mu ta ayyukanmu masu kyau a matsayin masu shelar Mulki da kuma halaye kamar su kasancewa da daidai kima da ɗabi’a mai kyau.—Tit. 2:1-14.

14. (a) Yaya za ka kwatanta fitila na ƙarni na farko? (b) Me ya sa ba za mu ɓoye fitila ta ruhaniya a ƙarkashin “akushi” ba?

14 Yesu ya yi maganar kunna fitila da kuma ɗora ta a kan maɗorinta, ba a ƙarƙashin masaki ba, domin ta ba duk mutanen gidan haske. Fitilar da ake yawan amfani da ita a ƙarni na farko ita ce a-ci-bal-bal ɗin da aka yi da yumɓu. Da yake sau da yawa ana ɗaura ta ne a kan maɗaurin katako ko na ƙarfe, fitilar tana “haskaka ma dukan waɗanda ke cikin gida.” Mutane ba za su kunna fitila su ɗaura ta a ƙarƙashin “akushi” ba, wato, wanda ya fi babban mudu girma. Yesu ba ya son almajiransa su ɓoye fitilarsu ta ruhaniya a ƙarƙashin akushi na alama. Saboda haka, dole ne mu bar haskenmu ya haskaka, kada mu bari hamayya ta sa mu ɓoye gaskiyar da muke da ita.

15. Ta yaya ‘ayyukanmu masu kyau’ suke shafan wasu mutane?

15 Bayan da ya ambata fitila mai haske ne Yesu ya gaya wa almajiransa: “Hakanan ku kuma ku bari haskenku shi haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu-kyau, su girmama Ubanku wanda ke cikin sama.” Domin ‘ayyukanmu masu kyau’ wasu suna “girmama” Allah ta wurin zama bayinsa. Ya kamata hakan ya motsa mu mu ci gaba da haskakawa “kamar haskoki a cikin duniya”!—Filib. 2:15.

16. Zama “hasken duniya” na bukatar mu yi menene?

16 Zama “hasken duniya” yana bukatar mu sa hannu a wa’azin Mulki da aikin almajirantarwa. Amma muna bukatar mu yi wani abu kuma. Manzo Bulus ya rubuta: “Ku yi tafiya kamar ’ya’yan haske (gama amfanin haske yana cikin dukan nagarta da adalci da gaskiya.)” (Afis. 5:8, 9) Muna bukatar mu yi abubuwan da suka jitu da mizanan Allah masu girma a kowane lokaci. Hakika, dole ne mu yi biyayya da gargaɗin manzo Bitrus: “Kuna al’amura na dacewa wurin Al’ummai; domin, yayinda su ke kushenku kamar ma’aikatan mugunta, ta wurin nagargarun ayyukanku da su ke dubawa su ɗaukaka Allah cikin ranar ziyara.” (1 Bit. 2:12) Amma menene za a yi idan matsala ta taso tsakanin ’yan’uwa masu bi?

Ka “Sulhuntu da Ɗan’uwanka Tukuna”

17-19. (a) Wace ‘baiwa’ ce aka ambata a Matta 5:23, 24? (b) Menene muhimmancin yin sulhu da ɗan’uwa, kuma ta yaya Yesu ya nuna hakan?

17 A cikin Huɗubarsa na kan Dutse, Yesu ya gargaɗi almajiransa game da jin haushi da kuma riƙe ɗan’uwa a zuciya. Maimakon haka, suna bukatar su yi sulhu da wuri da ɗan’uwan da suka yi wa laifi. (Ka karanta Matta 5:21-25.) Ka lura sosai da wannan gargaɗin da Yesu ya yi. Idan ka kawo kyautarka kan bagadi kuma ka tuna cewa kana da matsala da ɗan’uwanka, menene za ka yi? Za ka bar kyautarka a gaban bagadin kuma ka je ka sulhunta da ɗan’uwanka. Bayan ka yi hakan, za ka iya komawa ka ba da kyautarka.

18 Sau da yawa ‘baiwar’ hadaya ce da mutum zai iya yi a haikalin Jehobah. Hadayu na dabbobi suna da muhimmanci sosai, domin Allah ya ba Isra’ilawa umurni a cikin Dokar Musa su riƙa yin hakan a bautarsu. Amma idan ka tuna cewa kana da wata matsala da ɗan’uwanka, magance wannan matsalar ya fi miƙa baiwarka muhimmanci. “Sai ka bar baiwarka can a gaban bagadi, ka yi tafiyarka,” in ji Yesu. Ka “sulhuntu da ɗan’uwanka tukuna, kāna ka zo ka miƙa baiwarka.” Za ka sulhunta da ɗan’uwaka tukuna kafin ka yi abin da aka kafa a cikin Doka.

19 Yesu bai ambata irin hadaya da kuma laifin ba. Saboda haka, mutum ba zai miƙa kowace irin hadaya ba idan ya tuna cewa yana da wata matsala da ɗan’uwansa. Idan hadayar dabba mai rai ce, za a bar ta “a gaban bagadi” na hadayar ƙonawa a farfajiyar haikali na firist. Bayan ya magance matsalar, wanda ya yi laifin zai koma ya miƙa hadayar.

20. Me ya sa ya kamata mu magance matsala da sauri idan mun yi fushi da wani ɗan’uwa?

20 A ra’ayin Allah, dangantakarmu da ’yan’uwanmu sashe ne mai muhimmanci na bauta ta gaskiya. Hadayun dabba ba su da amfani ga Jehobah idan waɗanda suke miƙa su ba sa bi da ɗan’uwansu yadda ya kamata. (Mik. 6:6-8) Shi ya sa Yesu ya aririce almajiransa su “shirya da abokin husuman[su] da sauri.” (Mat. 5:25) Bulus ma ya rubuta makamancin hakan yana cewa: “Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi: kada rana ta faɗi kuna kan fushinku: kada kuwa ku ba Shaiɗan dama.” (Afis. 4:26, 27) Ko da wani ya ba mu haushi, ya kamata mu magance matsalar da sauri don kada fushinmu ya kai faɗuwar rana kuma Iblis ya yi amfani da wanann zarafin.—Luka 17:3, 4.

Ka Daraja Mutane A Koyaushe

21, 22. (a) Ta yaya za mu iya bin umurnin da Yesu ya bayar da muka tattauna? (b) Menene za mu bincika a talifi na gaba?

21 Ya kamata yadda muka maimaita wasu kalaman Yesu a cikin Huɗubarsa na kan Dutse ya taimake mu mu bi da mutane cikin alheri da daraja. Ko da yake dukanmu ajizai ne, za mu iya bin umurnin da Yesu ya bayar domin ba ya bukatar abin da ba za mu iya yi ba, kuma Ubanmu na samaniya ma ba ya hakan. Da addu’a, ƙoƙari, da kuma taimakon Jehobah Allah, za mu iya kasancewa masu tawali’u, jin ƙai da kuma salama. Za mu iya haskaka haske na ruhaniya da ke haska ɗaukakar Jehobah. Ƙari ga haka, za mu sulhunta da ɗan’uwanmu idan bukata ta kama.

22 Bauta da Jehobah yake amince da ita ta haɗa da bi da maƙwabcinmu yadda ya dace. (Mar. 12:31) A talifinmu na gaba, za mu bincika wasu kalamai a cikin Huɗuba a kan Dutse da ya kamata su taimake mu mu ci gaba da nuna nagarta ga wasu. Bayan mun yi bimbini a kan darussan da aka ambata a baya da aka samu daga jawabin Yesu na musamman, muna iya tambayar kanmu, ‘Ina bi da mutane yadda ya kamata?’

[Hasiya]

a A nazarinka za ka amfana sosai idan ka karanta waɗannan ayoyin kafin a tattauna wannan talifin da na gaba.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene ake nufi da mutum ya zama mai tawali’u?

• Me ya sa “masu-jinƙai” suke farin ciki?

• Ta yaya za mu bar haskenmu ya haskaka?

• Me ya sa ya kamata mu yi saurin ‘sulhuntawa da ɗan’uwanmu?

[Hoto a shafi na 4]

Yin shelar saƙon Mulki hanya ce mai muhimmanci na barin haskenmu ya haskaka

[Hoto a shafi na 5]

Ya kamata Kiristoci su zama masu halin kirki

[Hoto a shafi na 6]

Ka yi iya ƙoƙarinka ka yi sulhu da ɗan’uwanka

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba