Ka Bar Zantattukan Yesu Su Shafi Halinka
“Wanda Allah ya aiko, zantattukan Allah ya ke faɗi.”—YOH. 3:34.
1, 2. Me ya sa za mu faɗi cewa Huɗuba a kan Dutse daga “zantattukan Allah” ne?
YESU ya koyar da darussa masu kyau a cikin Huɗuba a kan Dutse. Hakan ba abin mamaki ba ne, domin Jehobah ne Tushen koyarwar Kristi! Da yake magana game da Yesu, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Shi wanda Allah ya aiko, zantattukan Allah ya ke faɗi.”—Yoh. 3:34-36.
2 Ko da yake wataƙila Huɗuba a kan Dutse ba ta kai minti talatin ba, tana ɗauke da nassosi da aka yi ƙaulinsu daga littattafai takwas na Nassosin Ibrananci. Saboda haka, tushensa ainihi daga “zantattukan Allah” ne. Bari yanzu mu ga yadda za mu yi amfani da wasu cikin zantattuka da yawa masu tamani da ke cikin wannan huɗuba na Ɗan Allah ƙaunatacce.
Ka “Sulhuntu da Ɗan’uwanka Tukuna”
3. Bayan ya yi wa almajiransa kashedi game da sakamakon yin fushi, wane umurni ne Yesu ya bayar?
3 A matsayin Kiristoci, muna farin ciki, kuma mu masu salama ne domin muna da ruhu mai tsarki na Allah, kuma ɗiyar ruhu ya ƙunshi farin ciki da salama. (Gal. 5:22, 23) Yesu ba ya son almajiransa su yi rashin salamarsu da kuma farin ciki, saboda haka, ya yi musu kashedi game da sakamakon ci gaba da yin fushi, wanda yana iya jawo mutuwa. (Karanta Matta 5:21, 22) Ya faɗi cewa: “Idan fa kana cikin miƙa baiwarka a wurin bagadi, can ka tuna ɗan’uwanka yana da wani abu game da kai, sai ka bar baiwarka can a gaban bagadi, ka yi tafiyarka, a sulhuntu da ɗan’uwanka tukuna, kāna ka zo ka miƙa baiwarka.”—Mat. 5:23, 24.
4, 5. (a) Wace “baiwa” ce aka yi maganarta a kalamin Yesu da ke rubuce a Matta 5:23, 24? (b) Yaya sulhuntawa da ɗan’uwa da aka yi masa laifi yake da muhimmanci?
4 “Baiwa” da Yesu ya ambata tana nufin kowace hadaya da aka miƙa a haikali a Urushalima. Alal misali, hadayun dabba suna da muhimmanci domin sashen bauta ne da mutanen Jehobah suke yi masa a lokacin. Amma, Yesu ya nanata abin da ya fi muhimmanci, wato, sulhuntawa da ɗan’uwa da aka yi masa laifi kafin a miƙa wa Allah baiwa.
5 Saboda haka, wane darassi za mu iya koya daga wannan furci na Yesu? Babu shakka, yadda muke bi da mutane yana shafan dangantakarmu da Jehobah. (1 Yoh. 4:20) Hakika, hadayun da ake miƙa wa Allah a dā ba su da amfani idan wanda yake miƙa su ba ya bi da ’yan’uwansa ’yan adam yadda ya kamata.—Karanta Mikah 6:6-8.
Tawali’u Yana da Muhimmanci
6, 7. Me ya sa muke bukatar mu kasance da tawali’u sa’ad da muke ƙoƙarin yin sulhu da ɗan’uwan da muka yi wa laifi?
6 Yin sulhu da ɗan’uwan da muka yi wa laifi zai iya gwada tawali’unmu. Masu tawali’u ba sa gardama ko jayayya da ’yan’uwa masu bi don su nuna cewa ba su yi laifi ba. Hakan zai jawo yanayin da ba shi da kyau, makamancin wanda ya faru tsakanin Kiristoci da ke Koranti na dā. Game da wannan yanayin, manzo Bulus ya yi wannan bayani mai sa tunani: “Ya zama abin hasara a gareku ƙwarai, da ku ke kai juna ƙara a gaban shari’a. Ba gwamma a yi haƙuri da zalunci ba?”—1 Kor. 6:7.
7 Yesu bai ce mu je mu sami ɗan’uwanmu don mu tabbatar masa cewa shi ne ya yi mana laifi ba. Ya kamata muradinmu ya zama na shiryawa. Don mu yi sulhu, dole ne mu furta yadda muke ji. Muna kuma bukatar mu yarda cewa mun ɓata wa ɗan’uwan rai. Idan mun yi kuskure, ya kamata mu nemi gafara cikin tawali’u.
“Idan Idonka na Dama Yana sa Ka Yi Tuntuɓe”
8. Ka ɗan bayyana kalaman Yesu da ke rubuce a Matta 5:29, 30.
8 A Huɗubarsa a kan Dutse, Yesu ya ba da shawara mai kyau a kan ɗabi’a. Ya san cewa gaɓoɓin jikinmu ajizai za su iya kasancewa da mummunar rinjaya a gare mu. Saboda haka, Yesu ya ce: “Kuma idan idonka na dama yana sa ka yi tuntuɓe, ka cire shi, ka yar: gama gara gareka gaɓanka ɗaya ya lalace, da a jefa jikinka ɗungum cikin Jahannama. Kuma idan hannunka na dama yana sa ka yi tuntuɓe, ka yanke shi, ka yas: gama gara gareka gaɓanka ɗaya shi lalace, da jikinka ya shiga ɗungum cikin Jahannama.”—Mat. 5:29, 30.
9. Ta yaya ‘idonmu’ ko ‘hannunmu’ za su sa mu “tuntuɓe”?
9 ‘Ido’ da Yesu yake maganarsa yana nufin iko ko kuma iya mai da hankalinmu a kan wani abu, kuma ‘hannu’ na nufin abin da muke yi da hannunmu. Idan ba mu mai da hankali ba, waɗannan gaɓoɓin jiki za su sa mu yi “tuntuɓe” kuma mu daina “tafiya tare da Allah.” (Far. 5:22; 6:9) Sa’ad da muka fuskanci gwaji na yi wa Jehobah rashin biyayya, muna bukatar mu ɗauki tsattsauran mataki, wato, mu ƙwaƙule idonmu ko kuma mu yanke hannunmu a alamance.
10, 11. Menene zai taimake mu mu guji lalata?
10 Ta yaya za mu iya hana idonmu mai da hankali ga abubuwa na lalata? Ayuba mutum mai jin tsoron Allah ya ce: “Na yi wa’adi da idanuna; yaya fa zan yi sha’awar budurwa?” (Ayu. 31:1) Ayuba mutum ne mai aure da ya ƙudurta cewa ba zai taka dokokin Allah na ɗabi’a ba. Hakan ya kamata ya zama halinmu ko da muna da aure ko a’a. Don mu guji lalata, muna bukatar ruhu mai tsarki na Allah wanda yake sa waɗanda suke ƙaunar Allah su kame kansu kuma ya yi mana ja-gora.—Gal. 5:22-25.
11 Don mu guji lalata, yana da kyau mu tambayi kanmu, ‘Ina barin idanuna su sa na soma sha’awar abubuwa na lalata da ke cikin littattafai, a talabijin, ko kuma Intane?’ Bari mu tuna waɗannan kalmomin almajiri Yaƙub: “Kowane mutum yakan jarabtu in mugun burinsa ya ruɗe shi, ya kuma yaudare shi. Mugun buri kuma in ya yi ciki, yakan haifi zunubi. Zunubi kuma in ya balaga, yakan jawo mutuwa.” (Yaƙ. 1:14, 15) Hakika, idan wanda ya keɓe kansa ga Allah ya ci gaba da “duba” wata kishiyar jinsi da nufin yin lalata, yana bukatar ya yi canje-canje masu muhimmanci da suka yi daidai da ƙwaƙule idonsa ya jefar.—Karanta Matta 5:27, 28.
12. Wane gargaɗi da Bulus ya bayar zai taimake mu mu yaƙi sha’awoyi na lalata?
12 Domin yin amfani da hannunmu yadda bai dace ba zai iya sa mu keta mizanan Jehobah na ɗabi’a, dole ne mu ƙudurta kasancewa da tsabta na ɗabi’a. Saboda haka, ya kamata mu yi biyayya ga gargaɗin Bulus: “Ku matarda gaɓaɓuwanku fa waɗanda ke a duniya; fasikanci, ƙazanta, kwaɗayi, mugun guri, da sha’awa, watau bautar gumaka ke nan.” (Kol. 3:5) Kalmar nan “matarda” ta nanata mataki mai muhimmanci da za mu ɗauka don mu yaƙi sha’awoyi na lalata.
13, 14. Me ya sa yake da muhimmanci mu guji tunani da ayyuka na lalata?
13 Don ya ceci ransa, mutum zai so a yanke masa ƙafarsa. ‘Jefar’ da idonmu da kuma hannunmu a alamance yana da muhimmanci don mu guji tunanin lalata da ayyuka da za su sa mu yi hasarar tagomashin Jehobah. Kasancewa da tsabta na hankali, na ɗabi’a da kuma na ruhaniya ce kawai hanyar da za mu tsira daga halaka na har abada da wutar Jahannama ke wakilta.
14 Domin zunubin da muka gāda da kuma ajizanci, kasancewa da tsabta na ɗabi’a yana bukatar ƙoƙari sosai. Bulus ya ce: “Ina dandaƙin jikina, ina kai shi cikin bauta: domin kada ya zama bayanda na yi ma waɗansu wa’azi, ni da kaina a yashe ni.” (1 Kor. 9:27) Saboda haka, bari mu ƙuduri aniya mu yi amfani da gargaɗin Yesu a kan ɗabi’a, kada mu aikata a hanyoyin da suka nuna rashin godiya ga hadayarsa ta fansa.—Mat. 20:28; Ibran. 6:4-6.
Ku Riƙa ‘Bayarwa’
15, 16. (a) Ta yaya Yesu ya kafa misali wajen bayarwa? (b) Menene kalmomin Yesu da ke rubuce a Luk 6:38 suke nufi?
15 Zantattukan Yesu da kuma misalinsa mafi kyau suna ɗaukaka halin bayarwa. Yesu ya nuna karimci ta wajen zuwa duniya don amfanin ’yan adam ajizai. (Karanta 2 Korinthiyawa 8:9.) Yesu da yardan ransa ya bar ɗaukaka na samaniya don ya zama ɗan adam kuma ya ba da ransa don ’yan adam masu zunubi, wasu cikinsu za su samu arziki a sama a matsayin abokansa na sarauta a Mulkin. (Rom. 8:16, 17) Kuma Yesu ya ƙarfafa nuna karimci sa’ad da ya ce:
16 “Ku bayar, za a ba ku, mudu mai-kyau, danƙararre, girgizajje, mai-zuba, za su bayar cikin ƙirjinku. Gama da mudun da ku ke aunawa, da shi za a auna muku.” (Luk 6:38) ‘Zubawa a ƙirji’ na nuni ne ga al’ada da ake bi a kasuwoyi na ƙasashen dā a gabashin duniya, a lokacin masu sayar da kaya suna zuba kaya a cikin kalmasa da ke saman rigar mai ciniki da aka ɗinka kamar zabira don ɗaukan kaya. Halin karimci yana iya sa a dawo mana da mudu mai yawa, wataƙila sa’ad da muke cikin bukata.—M. Wa. 11:2.
17. Ta yaya Jehobah ya kafa misali mafi kyau wajen bayarwa, wace irin bayarwa ce za ta sa mu farin ciki?
17 Jehobah yana ƙaunar waɗanda suke bayarwa da daɗin rai kuma yana saka musu. Shi da kansa ya kafa misali mafi kyau ta wajen ba da Ɗansa makaɗaici “domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yoh. 3:16) Bulus ya rubuta: “Wanda ya ke shuka da yalwa, da yalwa kuma zai girbe. Kowane mutum shi aika bisa yadda ya annita a zuciyarsa; ba da cicijewa ba, ba kuwa kamar ta dole ba: gama Allah yana son mai-bayarwa da daɗin rai.” (2 Kor. 9:6, 7) Ba da lokacinmu, ƙarfinmu, da dukiyarmu don mu ɗaukaka bauta ta gaskiya zai kawo mana farin ciki da sakamako mai kyau.—Karanta Misalai 19:17; Luka 16:9.
“Kada Ka Busa Ƙafo a Gabanka”
18. A wane yanayi ne ba za mu sami “lada” ba daga Ubanmu na samaniya?
18 “Ku yi lura kada ku yi adilcinku a gaban mutane, domin su gani: im ba haka ba ne, ba ku da lada a wurin Ubanku wanda ke cikin sama ba.” (Mat. 6:1) Ta wajen ambata ‘adalci,’ Yesu yana nufin halin da ya jitu da nufin Allah. Ba ya nufin cewa kada a yi ayyuka na ibada a fili, gama ya gaya wa almajiransa su “bari hasken[su] shi haskaka a gaban mutane.” (Mat. 5:14-16) Amma ba za mu samu “lada” daga Ubanmu na samaniya ba idan muna yin abubuwa domin mutane “su gani” kuma su so mu, kamar ’yan wasa da suke wasa a saman fage na gidan wasan kwaikwayo. Idan muna da irin wannan muradi, ba za mu more dangantaka na kud da kud da Allah ko kuma albarka na dindindin na sarautar Mulki ba.
19, 20. (a) Menene Yesu yake nufi sa’ad da ya ce kada a ‘busa ƙaho’ sa’ad da ake ba da “sadaka”? (b) Ta yaya ba za mu bar hannunmu na hagu ya san abin da na dama yake yi ba?
19 Idan muna da halin da ya dace, za mu bi umurnin Yesu: “Sa’anda fa ka ke yin sadaka, kada ka busa ƙaho a gabanka, kamar yadda masu-riya ke yi cikin majami’u da hanyoyi, domin su sami daraja a wurin mutane. Gaskiya ina ce muku, sun rigaya sun karɓi ladarsu.” (Mat. 6:2) “Sadaka” na nufin abubuwa da ka ba da don ka tallafa wa mabukata. (Karanta Ishaya 58:6, 7.) Yesu da manzanninsa suna da kuɗin da suke amfani da shi wajen taimaka wa talakawa. (Yoh. 12:5-8; 13:29) Tun da yake ba a busa ƙaho a zahiri kafin a ba da sadaka, Yesu ya yi amfani da zugugu sa’ad da ya ce bai kamata mu “busa ƙaho” ba sa’ad da muke ba da “sadaka.” Bai kamata mu sanar da mutane ba sa’ad da muke ba da irin wannan sadaka kamar yadda Farisawa na Yahudawa suka yi. Yesu ya kira su masu riya domin suna sanar da sadakarsu a “cikin majami’u da hanyoyi.” Waɗannan masu riya “sun rigaya sun karɓi ladarsu.” Samun yabo daga ’yan adam da kuma zama a gaban kujera tare da sanannun malamai a cikin majami’a ne kawai ladan da za su samu, gama Jehobah ba zai ba su kome ba. (Mat. 23:6) Amma, ta yaya almajiran Kristi za su aikata? Yesu ya gaya wa su da mu cewa:
20 “Amma sa’anda ka ke yin sadaka, kada ka bar hannunka na hagu ya san abin da hannunka na dama ke yi: domin sadakarka ta kasance a ɓoye: Ubanka kuwa wanda ya ke gani daga cikin ɓoye za ya sāka maka.” (Mat. 6:3, 4) Hannayenmu suna aiki tare. Saboda haka, hana hannun hagu sanin abin da na dama yake yi yana nufin cewa kada mu sanar da ayyukanmu na sadaka, har ga waɗanda suka yi kusa da mu kamar yadda hannunmu na hagu yake da hannunmu na dama.
21. Cewa wanda “ya ke gani daga cikin ɓoye” zai ba mu lada ya ƙunshi menene?
21 Idan ba mu yi fahariya game da sadaka da muka bayar ba, ‘sadakarmu’ za ta kasance a ɓoye. Sa’an nan Ubanmu, “wanda ya ke gani daga cikin ɓoye” zai sāka mana. Da yake yana sama kuma ’yan adam ba sa ganinsa, Ubanmu na samaniya ya kasance a “ɓoye” ga mutane. (Yoh. 1:18) Lada daga wanda “ya ke gani daga cikin ɓoye” ya haɗa da dangantaka na kud da kud da Jehobah, gafarta mana zunubanmu, da kuma rai madawwami da zai ba mu. (Mis. 3:32; Yoh. 17:3; Afis. 1:7) Hakan ya fi samun yabo daga ’yan adam kyau!
Zantattuka Masu Tamani da za a Bi
22, 23. Me ya sa za mu daraja zantattukan Yesu?
22 Babu shakka, Huɗuba bisa Dutse tana ɗauke da zantattuka masu tamani da za su kawo mana farin ciki a wannan duniya ta wahala. Hakika, za mu yi farin ciki idan muka yi amfani da zantattukan Yesu kuma muka sa su shafi halinmu da hanyar rayuwarmu.
23 Duk wanda ya ‘ji’ kuma ya “aikata” abin da Yesu ya koyar zai samu albarka. (Karanta Matta 7, 24, 25.) Saboda haka, bari mu ƙuduri aniya mu bi gargaɗin Yesu. Za a ƙara tattauna zantattukansa cikin Huɗuba na kan Dutse a talifi na gaba.
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa yake da muhimmanci ka sulhunta da ɗan’uwa da ka yi wa laifi?
• Ta yaya za mu guji ‘idonmu na dama’ ya sa mu tuntuɓe?
• Menene ya kamata ya zama halinmu game da bayarwa?
[Hotunan da ke shafi na 11]
Yana da kyau “ka sulhunta” da ɗan’uwa mai bi da ka yi masa laifi
[Hotunan da ke shafi na 13]
Jehobah yana ba da lada ga waɗanda suke bayarwa da daɗin rai