Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 7/1 pp. 24-29
  • Ka Sa Hannu A Farin Cikin Bayarwa!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sa Hannu A Farin Cikin Bayarwa!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Bayarwa Tana Kawo Farin Ciki
  • Samun Abokai na Har Abada
  • Yin Ajiyar Dukiya a Sama
  • Neman Waɗanda Suke Son Gaskiya
  • Yin Iyakacin Ƙoƙarinka
  • Farin Ciki​—Hali Ne da Muke Koya Daga Wurin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Ka Yi Farin Ciki Tare Da Allah Mai Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ka Yi Farin Ciki A Aikin Almajirantarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Kada Ka Gaji!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 7/1 pp. 24-29

Ka Sa Hannu A Farin Cikin Bayarwa!

“Bayarwa ta fi karɓa albarka.”—AYUKAN MANZANNI 20:35.

1. Ta yaya ne Jehovah ya nuna farin cikin bayarwa?

FARIN CIKIN sanin gaskiya da kuma albarka da take kawowa, kyauta ce daga wurin Allah. Waɗanda sun riga sun san Jehovah suna da dalilai da yawa na yin farin ciki. Amma, yayin da akwai farin ciki a karɓan kyauta, da akwai farin ciki ma a bayar da kyauta. Jehovah shi ne Mai Bayar da “kowacce kyakkyawar baiwa,” kuma shi ne ‘Allah mai farin ciki.’ (Yaƙub 1:17; 1 Timothawus 1:11) Yana koyarwa da kyau ga duk wanda ke saurara kuma yana jin daɗin biyayyar waɗanda yake koyar da su, kamar yadda iyaye suke farin ciki yayin da yaransu suka saurari umurnansu na ƙauna.—Misalai 27:11.

2. (a) Menene Yesu ya faɗa game da bayarwa? (b) Wane farin ciki ne muke samu yayin da mun koya wa wasu gaskiyar Littafi Mai Tsarki?

2 Hakazalika, yayin da yake duniya Yesu ya yi farin cikin ganin mutane suna karɓan koyarwarsa. Manzo Bulus ya ɗauko abin da Yesu ya faɗa cewa: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (Ayukan Manzanni 20:35) Farin ciki da muke samu yayin da muka koya wa wasu gaskiyar Littafi Mai Tsarki ba kawai na ganin wani ya yarda da imaninmu na addini ba ne. Fiye da haka, farin ciki na sanin cewa muna bayar da wani abu da gaske kuma mai daraja ne. Ta bayar da abin da ke da daraja ta ruhaniya, za mu iya taimakon mutane su amfani kansu a yanzu da kuma duk cikin dawwama.—1 Timothawus 4:8.

Bayarwa Tana Kawo Farin Ciki

3. (a) Yaya ne manzanni Bulus da Yohanna suka nuna farin cikinsu a taimaka wa wasu a ruhaniya? (b) Me ya sa bayar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki wa ’ya’yanmu nuna ƙauna ce?

3 Hakika, kamar yadda Jehovah da Yesu suke farin ciki a bayar da kyauta ta ruhaniya, haka ma Kiristoci suke. Manzo Bulus ya sami farin ciki a samun sani da yake da shi da ya taimake wasu su koyi gaskiyar Kalmar Allah. Ya rubuta zuwa ga ikilisiyar Tassaluniki: “Menene begenmu, da farinzuciyarmu, da rawanin fahariyarmu? Ba ku ne ba, a gaban Ubangijinmu Yesu cikin zuwansa? Gama ku ne fahariyarmu da farinzuciyarmu.” (1 Tassalunikawa 2:19, 20) Hakanan ma manzo Yohanna, da yake ambata game da yaransa na ruhaniya, ya ce: “Ba ni da wani farinciki wanda ya fi wannan, in ji ’ya’yana suna tafiya cikin gaskiya.” (3 Yohanna 4) Ka yi tunanin farin cikin da za mu samu wajen taimakon yaranmu su zama ’ya’yanmu na ruhaniya! Yin renon yara cikin “horon Ubangiji da kuma gargaɗinsa” nuna ƙauna ce daga wajen iyaye. (Afisawa 6:4) Ta haka iyaye suna nuna cewa sun damu da madawwamin yanayin ƙananan ’ya’yansu. Yayin da waɗannan suka bi daidai, iyaye sukan sami farin ciki sosai da kuma gamsuwa.

4. Wane labari ne ya nuna farin cikin bayarwa ta ruhaniya?

4 Dell, mai hidima ce ta cikakken lokaci uwar ’ya’ya biyar. Ta ce: “Zan iya faɗa daidai abin da manzo Yohanna ya faɗa domin godiyata cewa yarana huɗu suna ‘tafiya cikin gaskiya.’ Na sani yana kawo girma da daraja ga Jehovah yayin da iyalai sun haɗa kai cikin bauta ta gaskiya, domin haka na gamsu sosai a ganin albarkarsa a kan ƙoƙarce-ƙoƙarcena na shuka gaskiyar cikin yarana. Zato mai kyau na rai mara matuƙa cikin Aljanna da iyalina yana sa ni bege kuma motsa ni na jimre wahala da kuma abubuwan tangarɗa.” Abin baƙin ciki kuwa, aka yi wa ’yar Dell yankan zumunci daga ikilisiyar domin bin tafarkin da ba na Kirista ba. Duk da haka, Dell tana aiki sosai don ta ci gaba da hali mai kyau. “Ina fata cewa wata rana ’yata za ta yi sauƙin kai kuma ta juya wurin Jehovah da gaske,” in ji ta. “Amma godiya nake yi ga Jehovah da yake yawancin yarana suna bauta masa da aminci. Farin ciki da nake yi dalilin ƙarfi ne gare ni.”—Nehemiah 8:10.

Samun Abokai na Har Abada

5. Yayin da muke bayar da kanmu cikin aikin almajirantarwa, sanin menene ke gamsar da mu?

5 Yesu ya umurci mabiyansa su almajirantar kuma su koya musu game da Jehovah da kuma farillansa. (Matta 28:19, 20) Jehovah da Yesu cikin ƙauna sun taimaki mutane su koyi hanyar gaskiya. Saboda haka, yayin da muka bayar da kanmu a aikin almajirantarwa, muna samun gamsarwa na sanin cewa muna yin koyi da misalin Jehovah da kuma na Yesu, yadda Kiristoci na farko suka yi. (1 Korinthiyawa 11:1) Yayin da muka haɗa kai da Allah Mai Iko Duka da Ɗansa da yake ƙauna, rayuwarmu na kasancewa da ma’ana. Albarka ce ƙwarai a lissafa mu tsakanin “abokan aiki” na Allah! (1 Korinthiyawa 3:9) Kuma ba abin farin ciki ne ba cewa mala’iku ma suna sa hannu cikin wannan aikin wa’azin bishara?—Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7.

6. Yayin da muka sa hannu cikin bayarwa ta ruhaniya, su wa za su zama abokanmu?

6 Hakika, ta sa hannu cikin aikin bayarwa a ruhaniya, za mu zama ba abokan aiki da Allah kawai ba—za mu iya shiga abokantaka ta har abada da shi. Domin bangaskiyarsa, aka kira Ibrahim abokin Jehovah. (Yaƙub 2:23) Yayin da muke fama mu yi nufin Allah, mu ma za mu iya zama abokan Allah. Idan muka yi hakan, za mu kuma zama abokan Yesu. Ya gaya wa almajiransa: “Na ce da ku abokai; gama dukan abin da na ji daga wurin Ubana, na sanar muku da su.” (Yohanna 15:15) Mutane da yawa suna farin ciki a ce su abokan wasu manyan mutane ko na gwamnati, amma za a iya kiranmu abokan manyan mutane biyu na dukan sararin samaniya!

7. (a) Ta yaya wata mata ta sami abokiya ta gaske? (b) Ka taɓa shaida irin wannan?

7 Ƙari ga haka, yayin da muka taimake mutane su san Allah, sukan zama abokanmu kuma, wannan na kawo farin ciki na musamman gare mu. Joan, da take zama a Amurka, ta fara nazarin Littafi Mai Tsarki da wata mata da ake kira Thelma. Ko da yake Thelma ta sha hamayya daga iyalinta a nazarin da take yi, ta nace kuma ta yi baftisma bayan shekara guda. Joan ta rubuta: “Tarayyarmu bai ƙare wajen ba; maimako ya ci gaba zuwa abokantaka da ta kai shekara 35 yanzu. Sau da yawa muna zuwa hidima tare da kuma manyan taro. A ƙarshe, na ƙaura zuwa sabon gida mai nisan mil 500. Amma Thelma ta ci gaba da rubuta mini wasiƙu na ƙauna masu daɗaɗa rai, tana cewa tana tunanina sosai kuma ta gode mini domin ni abokiyarta ce abin kwaikwayo, kuma domin na koya mata gaskiya daga Littafi Mai Tsarki. Samun abuya ta kurkusa mai kyau albarka ce mai girma na ƙoƙarin da na yi na taimake ta ta koya game da Jehovah.

8. Wane hali mai kyau ne zai taimake mu cikin hidima?

8 Zaton samun wani da yake son ya koyi gaskiya zai taimake mu mu jimre ko idan yawancin mutane da muka sadu da su ba sa so ko kuma kaɗan kawai suke son Kalmar Jehovah. Irin rashin son nan yakan zama kalubale wa bangaskiyarmu da kuma jimrewa. Amma, hali mai kyau zai taimake mu. Fausto, wanda ya fito daga Guatemala, ya ce: “Yayin da na yi wa wasu wa’azi, nakan yi tunanin daɗinsa idan mutumin da na yi magana da shi ya zama ɗan’uwa ko ’yar’uwa a ruhaniya. Ina tunanin cewa aƙalla zan iske wani da a ƙarshe zai amince da gaskiyar Kalmar Allah. Wannan tunanin ya sa na ci gaba kuma yana kawo mini farin ciki.”

Yin Ajiyar Dukiya a Sama

9. Menene Yesu ya faɗa game da dukiya a sama, kuma me za mu iya koya daga wannan?

9 Almajirantarwa, ko yaranmu ne ko wasu, ba shi da sauƙi. Yana iya cin lokaci, haƙuri, da kuma naciya. Ka tuna cewa, mutane da yawa za su so su yi aiki tuƙuru don su tara abin duniya, abubuwan da ba sa kawo musu farin ciki kuma da ba sa dawwama. Yesu ya gaya wa masu sauraronsa cewa ya fi kyau su yi aiki don abubuwa na ruhaniya. Ya ce: “Kada ku ajiye wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa ke cinyewa, inda ɓarayi kuma ke hudawa suna sata: amma ku ajiye wa kanku dukiya cikin sama, inda asu da tsatsa ba su cinyewa, ɓarayi kuma ba su hudawa su yi sata ba.” (Matta 6:19, 20) Ta biɗan abubuwa na ruhaniya—da ya ƙunshi sa hannu cikin muhimmin aikin almajirantarwa—za mu samu gamsuwa ta sanin cewa muna yin nufin Allah kuma cewa zai albarkace mu. Manzo Bulus ya rubuta: “Allah ba mara-adalci ba ne da za shi manta da aikinku da ƙauna wadda kuka nuna ga sunansa.”—Ibraniyawa 6:10.

10. (a) Me ya sa Yesu yake da dukiya ta ruhaniya? (b) Ta yaya Yesu ya ba da kansa, da wane babban amfani ga wasu?

10 Idan muka yi aiki sosai don mu almajirantar, muna ajiyar “dukiya a sama,” cikin jituwa da abin da Yesu ya faɗa. Wannan yana kawo mana farin cikin bayarwa. Idan muna bayarwa cikin ƙauna, za mu azurta kanmu. Yesu kansa ya yi hidima cikin aminci ga Jehovah na biliyoyin shekaru. Ka yi tunanin dukiya da ya yi ajiyarsa a sama! Duk da haka, Yesu bai biɗi abin da yake so wa kansa ba. Manzo Bulus ya rubuta: “[Yesu] ya bada kansa domin zunubanmu, domin shi tsamo mu daga cikin wannan mugunyar duniya ta yanzu, bisa ga nufin Allahnmu Ubanmu.” (Galatiyawa 1:4, tafiyar tsutsa tamu ce.) Ba kawai cewa Yesu ya ba da kansa cikin ƙauna a hidimarsa ba amma ya ba da ransa fansa domin wasu su sami zarafi su yi ajiyar dukiya a sama.

11. Me ya sa kyauta ta ruhaniya ta fi kyautar abin duniya amfani?

11 Ta koya wa mutane game da Allah, muna taimakonsu su ga yadda su kansu za su iya ajiyar dukiya ta ruhaniya da ba ta lalacewa. Wace kyauta ce mai girma za ka iya bayarwa? Idan ka ba wa abokinka agogo mai tsada, mota, ko kuma gida, hakika abokin nan zai yi godiya kuma ya yi murna, kuma za ka samu farin cikin bayarwa. Amma me zai faru ga kyautar shekara 20 nan gaba? Shekara 200? Shekara 2,000? A wata sassa kuma, idan ka bayar da kanka ka taimaki mutum ya bauta wa Jehovah, shi ko ita za ta iya amfana daga kyautar nan har abada.

Neman Waɗanda Suke Son Gaskiya

12. Ta yaya mutane da yawa suka ba da kansu su taimake wasu a ruhaniya?

12 Don a sa hannu a farin cikin bayarwa ta ruhaniya, mutanen Jehovah sun kai dukan ƙusurwoyin duniya. Dubbai sun bar gida da iyalai don su shiga aikin wa’azi na ƙasar waje a ƙasashen da sukan koyi sabon yare da al’adu. Wasu sun ƙaura zuwa wuraren da akwai bukata matuƙa na masu shelar Mulki a ƙasashensu. Har ila kuma wasu sun koyi sabon yare, suna samun zarafi na yin wa’azi a yanki na jama’a da suka ƙaura. Alal misali, bayan sun yi renon yara biyu da suke hidima yanzu a hedkwatar Shaidun Jehovah, wata mata da mijinta a New Jersey, U.S.A., suka fara aikin majagaba kuma suka koyi yaren Sinawa. Cikin shekara uku, sun tafiyar da nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane 74 da suke yaren Sinawa da suke wani kwaleji. Za ka iya yaɗa hidimarka a wata hanya don ka ƙara samun farin ciki cikin aikin almajirantarwan nan?

13. Menene za ka iya yi idan kana son hidimarka ta ba da ’ya’ya sosai?

13 Wataƙila kana son ka tafiyar da nazarin Littafi Mai Tsarki amma ba ka iya haka ba tukuna. A wasu ƙasashe yana da wuya a sami waɗanda suke son saƙon. Wataƙila mutanen da ka sadu da su ba sa son Littafi Mai Tsarki. Idan haka ne, ƙila kana bukatar ka daɗa ambata muradinka cikin addu’a, da sanin cewa Jehovah da Yesu Kristi suna son aikin kuma za su yi maka ja-gora zuwa wajen mutum mai kama da tunkiya. Ka biɗi shawarwari daga waɗanda suke cikin ikilisiyarka da suka manyanta ko waɗanda hidimarsu ke ba da ’ya’ya sosai. Ka yi amfani da koyarwa da shawarwari da ake bayar a taron Kirista. Amfani daga shawarar masu kula masu ziyara da matansu. Ban da haka ma, kada ka fid da rai. Mutum mai hikima ya rubuta: “Da safe sai ka shuka irinka, da yamma kuma kada ka ja hannunka; gama ba ka san wanda za ya yi albarka ba.” (Mai-Wa’azi 11:6) A yanzu haka, ka tuna da mutane masu aminci kamar su Nuhu da Irmiya. Ko da yake kalilan ne suka yi na’am ga wa’azinsu, hidimarsu ta yi nasara. Mafi muhimmanci ma, ya faranta wa Jehovah rai.

Yin Iyakacin Ƙoƙarinka

14. Yaya Jehovah yake ɗaukan waɗanda suka tsufa cikin hidimarsa?

14 Wataƙila yanayinka bai ba ka zarafin yin yadda za ka so ka yi cikin hidima ba. Alal misali tsufa zai iya rage abin da za ka iya yi cikin hidimar Jehovah. Amma, ka tuna da abin da mutum mai hikima ya rubuta: “Furfura rawanin daraja ce, idan an iske ta cikin hanyar adalci.” (Misalai 16:31) Ga Jehovah, rayuwa da aka yi cikin hidimarsa tana faranta masa rai ƙwarai. Ban da haka kuma Nassosi suka ce: “Har tsufarku kuma, ni [Jehovah] ne shi, har zuwa furfuranku kuma ni zan ɗauke ku: ni na yi, ni kuwa zan ɗauka; i, ni zan ɗauka, ni kuma zan yiwo ceto.” (Ishaya 46:4) Ubanmu mai ƙauna na samaniya ya yi alkawarin zai kiyaye kuma ya toƙara wa masu aminci nasa.

15. Ka gaskata cewa Jehovah ya san yanayinka? Me ya sa?

15 Wataƙila kana jurewa da wani ciwo, hamayya daga abokin aure mara bi, hakkin iyali mai nauyi ƙwarai, ko wasu matsaloli masu wuya. Jehovah ya san iyawarmu da yanayinmu, yana ƙaunarmu kuma don ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu na gaske don mu bauta masa. Wannan gaskiya ne ko idan abin da muke yi kalilan ne idan aka gwada da na wasu. (Galatiyawa 6:4) Jehovah ya san mu ajizai ne, ya san abin da yake tsammani daga gare mu. (Zabura 147:11) Idan muka yi iyakacin ƙoƙarinmu, za mu tabbata cewa muna da tamani a gaban Allah cewa ba zai manta da ayyukanmu na bangaskiya ba.—Luka 21:1-4.

16. A wace hanya ce dukan ikilisiya take da hannu wajen almajirantarwa?

16 Ka tuna kuma cewa aikin almajirantarwar ba aikin mutum ɗaya ba ne. Babu wani mutum da shi kaɗai ne ya almajirantar, kamar a ce wai ɗigon ruwa zai girmar da tsiro ba. Hakika, wani Mashaidi ya iya sami wani da yake so kuma ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Amma muddin sabon mutumin ya zo Majami’ar Mulki, dukan ikilisiyar ce take taimakonsa ko taimakonta ta fahimci gaskiyar. Yadda ’yan’uwanci ke da daɗaɗa rai yana nuna rinjayar ruhun Allah. (1 Korinthiyawa 14:24, 25) Yara ƙanana da kuma matasa suna yin kalami mai ban sha’awa, wannan yana nuna wa sabon mutumin cewa yaranmu dabam suke da matasa na duniya. Marasa lafiya, marasa ƙarfi, da tsofaffi cikin ikilisiyar suna koyar wa sababbi abin da jimrewa ta ƙunsa. Duk da shekarunmu ko iyawarmu, dukanmu muna da muhimmin aiki a taimakon sababbi yayin da ƙaunarsu ga gaskiyar Littafi Mai Tsarki take zurfi kuma sun ci gaba zuwa baftisma. Kowacce sa’a da muka yi cikin hidima, kowacce koma ziyara, kowanne taɗi da muka yi da sabon mutum a Majami’ar Mulki kamar babu wani amfani, amma yana cikin aiki mai girma da Jehovah yake yi.

17, 18. (a) Ban da sa hannu cikin aikin almajirantarwa, ta yaya za mu sa hannu a farin cikin bayarwa? (b) Ta sa hannu a farin cikin bayarwa, wanene muke koyi da shi?

17 Babu shakka, ban da sa hannu cikin muhimmin aikin almajirantarwa, mu Kiristoci ma muna samun farin ciki na bayarwa a wasu hanyoyi. Za mu iya yin ajiyar kuɗi don mu bayar kuma mu toƙara wa bauta mai tsarki kuma mu taimaka wa waɗanda suke bukata. (Luka 16:9; 1 Korinthiyawa 16:1, 2) Za mu iya neman zarafi don mu nuna halin karɓan baƙi wajen wasu. (Romawa 12:13) Za mu yi ƙoƙari mu “aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda su ke cikin iyalin imani.” (Galatiyawa 6:10) Kuma, a hanya mai sauƙi na muhimmanci, za mu iya bai wa wasu ta—wasiƙa, kira ta tarho, ba da kyauta, taimakawa, furcin ƙarfafawa.

18 Ta bayarwa, muna nuna cewa muna koyi da Ubanmu na sama. Muna kuma nuna ƙaunarmu na ’yan’uwanci, alamar sanin Kiristoci na gaskiya. (Yohanna 13:35) Tuna da waɗannan abubuwa zai taimake mu mu sa hannu a farin cikin bayarwa.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Ta yaya Jehovah da Yesu suka kafa misali na bayarwa a ruhaniya?

• Ta yaya za mu iya samun madawwaman abokai?

• Waɗanne matakai za mu iya ɗauka don mu sa hidimarmu ta yi nasara?

• Ta yaya duka cikin ikilisiya za su samu farin cikin bayarwa?

[Hotuna a shafi na 25]

Yayin da yara suka bi renon da aka yi musu, iyaye suna samun farin ciki mai yawa da kuma gamsarwa

[Hoto a shafi na 27]

A almajirantarwa, za mu iya samun abokai na gaske

[Hoto a shafi na 28]

Jehovah yana taimakonmu a lokacin tsufa

[Hotuna a shafi na 29]

A muhimman hanyoyi masu sauƙi muna samun farin ciki a bayarwa

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba