Littafi Mai Tsarki Zai Sa Ka Sami Farin Ciki
KO DA yake ba littafin kiwon lafiya ba ne, Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da yadda sosuwar zuciya, mai kyau da marar kyau, za ta iya shafar hankali da kuma lafiyar mutum. “Kasancewa da murna yakan ba ka lafiya,” in ji Littafi Mai Tsarki, “zama da baƙin rai dukan lokaci mutuwar tsaye ce.” Mun kuma karanta: “Idan ba ka da ƙarfi a lokacin hargitsi, hakika ka tabbata marar ƙarfi.” (Karin Magana 17:22; 24:10) Mutuwar zuci tana iya gajiyar da mu, ta sa mu ji mun raunana kuma muna cikin haɗari amma ba mu da muradin mu yi canji ko kuma mu nemi taimako.
Mutuwar zuci tana iya kuma shafan mutum a ruhaniya. Mutane da suke jin ba su da wani amfani, sau da yawa suna jin ba za su iya samun dangantaka mai kyau da Allah ba kuma ba zai yi musu albarka ba. Simone, da aka ambata a talifi na baya, ta yi shakka cewa “tana cikin mutane da Allah zai yarda da su.” Amma, idan muka bincika Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, za mu ga cewa Allah yana yarda da waɗanda suke ƙoƙari su faranta masa rai.
Allah Yana Kula da Gaske
Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Jehobah “yana kusa da waɗanda suka karai, yakan ceci waɗanda suka fid da zuciya.” Allah ba ya ‘ƙin zuciya mai ladabi da biyayya,’ amma ya yi alkawarin “farfaɗo da zukatan masu tuba.”—Zabura 34:18; 51:17; Ishaya 57:15.
Da wani lokaci da Ɗan Allah, Yesu, ya ga dole ne ya jawo hankalin almajiransa ga gaskiyar cewa Allah yana ganin mutuncin bayinsa. Ta wajen ba da wani kwatanci, ya faɗi cewa Allah yana lura sa’ad da gwara ta faɗi ƙasa—abin da yawancin mutane ba za su ɗauke shi da muhimmanci ba. Ya kuma nanata cewa Allah yana sane da kome game da mutane, har gashin kansu an kiɗaye. Yesu ya kammala kwatancinsa da cewa: “Kada ku ji tsoro. Ai, martabarku ta fi ta gwara masu yawa.” (Matiyu 10:29-31)a Yesu ya nuna cewa ko yaya mutane za su ji game da kansu, mutane masu bangaskiya suna da martaba a gaban Allah. Hakika, manzo Bitrus ya tuna mana cewa “Allah ba ya tara, amma a kowace al’umma duk mai tsoronsa, mai kuma aikata adalci, abin karɓuwa ne a gare shi.”—Ayyukan Manzanni 10:34, 35.
Ka Kasance da Ra’ayi da ya Dace
Kalmar Allah ta aririce mu mu kasance da daidaituwa game da yadda muke ɗaukan kanmu. An huri manzo Bulus ya rubuta: “Albarkacin alherin da aka yi mini, ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi.”—Romawa 12:3.
Hakika, bai kamata mu ɗauki kanmu da muhimmanci fiye da yadda ya kamata ba, ko kuma mu faɗa tunanin cewa ba mu isa kome ba. Maimakon haka, makasudinmu ya kamata ya kasance koyon ɗaukan kanmu yadda ya dace, yadda za mu riƙa tuna ƙarfinmu da kuma inda muka raunana. Wata mace Kirista ta faɗi wannan: “Ba ni ce uwar mugunta ba; kuma ba ni ce sarauniyar adalci ba. Ina da kyawawa da munanan hali, kamar yadda kowa yake da su.”
Hakika, cim ma wannan madaidaicin ra’ayi yana da wuya. Zai bukaci ƙoƙari ƙwarai a kawar da rashin jin daɗi da ake yi da wataƙila ya fara shekaru da yawa da suka gabata. Duk da haka, da taimakon Allah za mu iya canja halayenmu da kuma yadda muke ɗaukan rayuwa. Hakika, abin da Kalmar Allah ta aririce mu mu yi ke nan. Mun karanta: “Ku yar da halinku na dā, wanda dā kuke ciki, wanda yake lalacewa saboda sha’awoyinsa na yaudara, ku kuma sabunta ra’ayin hankalinku, ku ɗauki sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah da hakikanin adalci da tsarki.”—Afisawa 4:22-24.
Ta wajen yin ƙoƙari mu sake ‘ra’ayin hankalinmu,’ wato, abin da ke motsa mu a ciki, za mu iya canja halinmu daga wanda ba shi da kyau zuwa mai kyau. Lena, da aka ambata a talifi na baya, ta fahimci cewa idan ba ta kawar da tunanin cewa babu wanda zai ƙaunace ta ko kuma ya taimake ta ba, babu abin da zai canja yadda take ji game da kanta. Waɗanne shawarwari ne masu kyau daga Littafi Mai Tsarki suka taimaki Lena, Simone, da kuma wasu da suka sake halayensu?
Mizanan Littafi Mai Tsarki da Suke Kawo Farin Ciki
“Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji, zai kuwa taimake ka.” (Zabura 55:22) Na farko kuma mafi muhimmanci, addu’a za ta iya taimakonmu mu sami farin ciki. Simone ta ce: “Duk lokacin da na ji mutuwar zuci, sai na juya ga Jehobah na nemi taimakonsa. Ban taɓa kasancewa a yanayin da ban ji na sami ƙarfi da ja-gora daga wurinsa ba.” Sa’ad da mai zabura ya aririce mu mu gabatar da wahalarmu ga Jehobah, yana tuna mana ne cewa Jehobah yana kula da mu kuma yana ɗaukanmu mutane ne da suka cancanci taimakonsa. A daren bikin Ƙetarewa a shekara ta 33 A.Z., almajiran Yesu sun yi baƙin ciki domin abin da Yesu ya ce game da tafiyarsa. Yesu ya aririce su su yi wa Uba addu’a, sai kuma ya daɗa cewa: “Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”—Yahaya 16:23, 24.
“Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (Ayyukan Manzanni 20:35) Kamar yadda Yesu ya koyar, bayarwa mabuɗi ne na samun farin ciki a rayuwa. Bin wannan gaskiya ta Littafi Mai Tsarki tana sa mu mai da hankali a kan bukatun wasu maimakon namu kurakurai. Sa’ad da muka taimaki wasu kuma muka ga yadda suke godiya saboda abin da muka yi, za mu ga darajar kanmu. Lena ta tabbata cewa saka hannu cikin shelar bisharar mulki na Littafi Mai Tsarki a kai a kai ga maƙwabtanta ya taimake ta a hanyoyi biyu. “Na farko, ya ba ni farin ciki da gamsuwa da Yesu ya yi magana a kai,” in ji ta. “Na biyu, ina samun amsa mai kyau daga wasu, da ya taimake ni na sami farin ciki.”Ta wajen ba da kanmu, za mu shaidi gaskiyar Karin Magana 11:25: “Ka taimaki waɗansu, su kuma za su taimake ka.”
“Wahaltaccen mutum a koyaushe, fama yake yi a zamansa, amma masu farin ciki suna zama da daɗin rai.” (Karin Magana 15:15) Dukanmu muna da zaɓin ɗaukan kanmu da yanayinmu yadda muke so. Muna iya zama kamar wahaltaccen mutum da ba ya jin daɗin kome, ko kuma mu zaɓi mu yi tunanin abubuwa masu kyau, mu sami “daɗin rai,” kuma mu yi farin ciki kamar dai muna liyafa. Simone ta ce: “Na yi ƙoƙari in kasance da farin ciki kamar yadda ya dace. Na shagala cikin nazari na kai da kuma hidima, kuma na nace cikin addu’a. Na kuma yi ƙoƙari in kasance tsakanin mutane masu farin ciki, kamar yadda nake ƙoƙarin in taimaki wasu.” Irin wannan yanayin zuciya yana kai wa ga farin ciki na gaske, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukanku adalai, ku yi murna, ku yi farin ciki, saboda abin da Ubangiji ya yi! Dukanku da ke yi masa biyayya, ku yi sowa ta farin ciki!”—Zabura 32:11.
“A koyaushe abokai sukan nuna ƙaunarsu, ’yan’uwa kuma, ai, don su ɗauki nawayar juna suke.” (Karin Magana 17:17) Faɗin damuwarmu ga wanda muke ƙauna ko kuma wani amini zai iya taimaka mana mu magance rashin jin daɗi, kafin ya lulluɓe mu. Magana da wasu za ta iya taimakonmu mu ga abubuwa yadda ya dace. Simone ta ce: “Furta yadda kake ji zai taimaka sosai.” “Kana bukatar ka faɗa wa wani yadda kake ji. Sau da yawa furta yadda kake ji kawai kake bukata.” Yin haka zai taimake ka ka fahimci gaskiyar Karin Magana da ya ce: “Damuwa takan hana wa mutum farin ciki, amma kalmomin alheri za su sa shi ya yi murna.”—Karin Magana 12:25.
Abin da Za Ka Iya Yi
Mun yi la’akari da kaɗan cikin mizanai da yawa masu ban sha’awa na Littafi Mai Tsarki da za su iya taimakonmu mu magance rashin jin daɗi kuma mu sami farin ciki. Idan kana cikin waɗanda suke fama da jin ba su cancanta ba, muna ƙarfafa ka ka bincika Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. Ka koyi ka daidaita yadda kake ji game da kanka da kuma game da dangantakarka da Allah. Muna masu sa rai cewa da ja-gorar Kalmar Allah, za ka iya samun farin ciki a dukan abin da kake yi.
[Hasiya]
a An tattauna wannan Nassosi sosai a shafuffuka na 18 zuwa 19.