Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 11/1 pp. 20-25
  • Bayin Jehovah Masu Farin Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bayin Jehovah Masu Farin Ciki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sanin Talaucinmu na Ruhaniya
  • Yadda Masu Nadama Za Su Yi Farin Ciki
  • Farin ciki ya Tabbata ga Masu Tawali’u
  • Farin Ciki ta Tabbata ga Masu Ƙwaɗaita ga Adalci
  • Farin Ciki ta Tabbata ga Majiya Tausayi
  • Masu Tsarkakkiyar Zuciya Masu Ƙulla Zumunci
  • Yadda Zantattukan Yesu Ke Kawo Albarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Wadanda Ke Bauta wa Allah Suna Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Yadda Za a Samu Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ta Yaya Ya Kamata Mu Bi Da Mutane?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 11/1 pp. 20-25

Bayin Jehovah Masu Farin Ciki

“Albarka [farin ciki] tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu.”—Matiyu 5:3.

1. Menene farin ciki na gaskiya, kuma menene yake nunawa?

FARIN ciki abu ne mai muhimmanci ga mutanen Jehovah. Mai Zabura Dauda ya ce: “Masu farin ciki ne jama’ar da Allahnsu shi ne Ubangiji! (Zabura 144:15) Farin ciki jin lafiya ke nan. Cikakken farin ciki, ana jinsa a can cikin zuciya, yana tasowa daga fahimtar cewa Jehovah ya yi mana albarka. (Karin Magana 10:22) Irin wannan farin ciki yana nuna dangantakarmu ta kusa da Ubanmu na samaniya da kuma fahimtar muna yin nufinsa. (Zabura 112:1; 119:1, 2) Abin farin ciki, Yesu ya lissafa dalilai tara, domin waɗannan za a iya cewa da mu masu farin ciki. Bincika irin wannan abin da aka kira farin ciki, ko albarka, a wannan talifi da kuma mai zuwa zai taimake mu mu ga yadda za mu yi farin ciki idan muka bauta wa ‘Allah mai farin ciki’ Jehovah da aminci.—1 Timoti 1:11.

Sanin Talaucinmu na Ruhaniya

2. A wane lokaci ne Yesu ya yi maganar farin ciki, kuma menene kalmominsa na farko?

2 A shekara ta 31 A.Z., Yesu ya gabatar da huɗubarsa mafificiya a tarihi. Ana kiransa Huɗuba a kan Dutse domin Yesu ya yi ta ne a gefen dutse yana kallon Tekun Galili. Lingila ta Matiyu ta ce: “Da Yesu ya ga taro masu yawa sai ya hau dutse. Da ya zauna almajiransa kuma suka zo gunsa. Sai ya buɗe baki ya koya musu. ‘Albarka [farin ciki] tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu, domin Mulkin Sama nasu ne.’ ” Idan aka fassara kalmomin farko na Yesu a zahiri za su kasance: “Farin ciki ta tabbata ga matalauta na ruhu,” ko “Farin ciki ta tabbata ga masu barar ruhu.”—Matiyu 5:1-3; Kingdom Interlinear; hasiya.

3. Ta yaya kasancewa masu tawali’u yake ƙara farin ciki?

3 A huɗubarsa a gefen dutse, Yesu ya nuna cewa mutum zai kasance mai farin ciki matuƙa, idan ya fahimci bukatarsa ta ruhaniya. Kiristoci masu tawali’u, da cikakken sanin yanayinsu na zunubi, suna roƙon gafara daga Jehovah bisa hadayar fansa ta Kristi. (1 Yahaya 1:9) Saboda haka suna samun farin ciki da kwanciyar hankali. “Mai farin ciki ne mutumin da aka gafarta masa zunubansa, mai farin ciki ne kuma wanda aka gafarta masa laifofinsa.”—Zabura 32:1; 119:165.

4. (a) A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna mun fahimci bukatar mu ta ruhaniya da kuma ta wasu? (b) Menene yake ƙara mana farin ciki sa’ad da muka fahimci bukatarmu ta ruhaniya?

4 Fahimtar bukatarmu ta ruhaniya za ta motsa mu mu yi karatun Littafi Mai Tsarki kullum, domin mu amfana daga abinci na ruhaniya da “amintaccen bawan nan mai hikima” yake rabawa “a kan kari,” da kuma halartar taron Kirista a kai a kai. (Matiyu 24:45; Zabura 1:1, 2; 119:111; Ibraniyawa 10:25) Ƙaunar maƙwabta takan sa mu fahimci bukata ta ruhaniya na wasu kuma ta motsa mu mu zama masu ƙwazo wajen wa’azi da koyarwa da bishara ta Mulki. (Markus 13:10; Romawa 1:14-16) Sanar da wasu gaskiya ta Littafi Mai tsarki yana sa mu farin ciki. (Ayyukan Manzanni 20:20, 35) Farin cikinmu yana zurfafa sa’ad da muka yi bimbini bisa bege mai ban sha’awa na Mulki da kuma albarkatai da Mulkin zai kawo. Ga “ɗan ƙaramin garke” na Kiristoci shafaffu, wannan begen Mulkin yana nufin rai marar mutuwa a samaniya cikin Sarauta a gwamnatin Kristi. (Luka 12:32; 1 Korantiyawa 15:50, 54) Ga “waɗansu tumaki” kuma yana nufin rai madawwami a aljanna ta duniya a ƙarƙashin sarautar wannan gwamnatin.—Yahaya 10:16; Zabura 37:11; Matiyu 25:34, 46.

Yadda Masu Nadama Za Su Yi Farin Ciki

5. (a) Me ake nufi da “masu nadama”? (b) Ta yaya ake sanyaya zukatan irin waɗannan da suke nadama?

5 Kalmomin farin ciki na gaba da Yesu ya furta kamar dai ba su jitu ba da juna. Ya ce: “Albarka [farin ciki] tā tabbata ga masu nadama, domin za a sanyaya musu rai.” (Matiyu 5:4) Ta yaya mutum zai yi nadama kuma a ce yana farin ciki? Domin mu fahimci ma’anar furcin nan na Yesu, muna bukatar mu fahimci irin nadamar da ake magana a kai. Almajiri Yakubu ya yi bayani cewa matsayinmu na zunubi ya kamata ya kasance dalilin nadama. Ya rubuta: “Ku tsarkake al’amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukatanku, ya ku masu zuciya biyu. Ku yi nadama, ku yi baƙin ciki, ku yi ta kuka. Dariyarku tā zama baƙin ciki, murnarku tā koma ɓacin zuciya. Ku ƙasƙantar da kanku ga Ubangiji, shi kuwa zai ɗaukaka ku.” (Yakubu 4:8-10) Waɗanda suke baƙin ciki domin zunubansu ana sanyaya musu zuciya sa’ad da suka fahimci cewa za a gafarta musu zunubansu idan suka ba da gaskiya ga hadayar fansa ta Kristi kuma suka yi tuba ta gaskiya suka yi nufin Jehovah. (Yahaya 3:16; 2 Korantiyawa 7:9, 10) Saboda haka za su iya kasancewa da kyakkyawar dangantaka da Jehovah kuma su yi begen rayuwa har abada su bauta masa kuma su yabe shi. Wannan yana ba su farin ciki mai yawa ƙwarai.—Romawa 4:7, 8.

6. A wace hanya ce wasu suke nadama, kuma ta yaya ake sanyaya musu zuciya?

6 Furcin Yesu ya haɗa da waɗanda suke nadama domin mummunar yanayi da ya kasance a duniya. Yesu ya nuna cewa annabcin Ishaya 61:1, 2, dominsa ne, ya ce: “Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, in warkar da waɗanda suka karai a zuci, . . . in ta’azantar da masu [nadama] makoki.” Wannan aikin na shafaffu Kiristoci ne da har yanzu suke duniya, da suke yin sa tare da taimakon abokanansu, “waɗansu tumaki.” Dukansu suna saka hannu cikin aikin saka shaida a goshin “mutanen da ke ajiyar zuciya, suna damuwa saboda dukan abubuwa masu banƙyama waɗanda ake aikatawa a birnin [Urushalima mai riyya, da yake kwatanta Kiristendam].” (Ezekiyel 9:4) Irin waɗannan da suke damuwa ana sanyaya musu zuciya da “bisharan nan ta Mulki.” (Matiyu 24:14) Suna farin ciki sun fahimci cewa mugun zamanin nan na Shaiɗan ba zai kai labari ba, sabuwar duniya ta adalci ta Jehovah za ta sauya shi.

Farin ciki ya Tabbata ga Masu Tawali’u

7. Menene wannan kalmar “tawali’u” ba ta nufi?

7 Ya ci gaba da Huɗubarsa a kan Dutse yana cewa: “Albarka [farin ciki] tā tabbata ga masu tawali’u, domin za su gaji duniya.” (Matiyu 5:5) Wani lokaci ana ɗaukan tawali’u ragonci ne. Amma, ba haka abin yake ba. Wani masanin Littafi Mai Tsarki da yake bayani game da ma’anar kalmar da aka fassara “tawali’u,” ya rubuta: “Mafificin hali na mutum [mai tawali’u] shi ne yana da kame kai. Ba laushin hali ba ne na ragonci, ko na rashin abin yi. Ƙarfi ne cikin kamewa.” Yesu ya ce game da kansa: “Ni mai tawali’u ne, marar girmankai.” (Matiyu 11:29) Duk da haka, Yesu ya kāre mizanan adalci da gaba gaɗi.—Matiyu 21:12, 13; 23:13-33.

8. Tawali’u ya danganci me, kuma me ya sa muke bukatar wannan hali a dangantakarmu da wasu?

8 Saboda haka, tawali’u ya danganci kame kai. Hakika, manzo Bulus ya jera tawali’u da kame kai sa’ad da ya jera “albarkar Ruhu.” (Galatiyawa 5:22, 23) Dole ne sai da taimakon ruhu mai tsarki za a koyi tawali’u. Hali ne na lumana na Kiristoci da yake sa zaman lumana da waɗanda ba Kiristoci ba da kuma waɗanda suke cikin ikilisiya. Bulus ya rubuta: “Ku ɗau halin tausayi, da kirki, da tawali’u, da salihanci, da haƙuri, . . . kuna jure wa juna, sai [ku] yafe wa juna.”—Kolosiyawa 3:12, 13.

9. (a) Me ya sa kasancewarmu masu tawali’u bai tsaya ga dangantakarmu da wasu mutane ba kawai? (b) Ta yaya masu tawali’u za su “gāji duniya”?

9 Tawali’u bai tsaya a dangantakarmu da mutane ba kawai. Idan muka miƙa kai ga ikon mallaka na Jehovah, muna nuna cewa muna da tawali’u. Babban misali a wannan Yesu Kristi ne, wanda sa’ad da yake nan duniya ya nuna tawali’u da kuma miƙa kai ga nufin Ubansa. (Yahaya 5:19, 30) Da farko Yesu zai gaji duniya, domin shi ne aka naɗa Sarkinta. (Zabura 2:6-8; Daniyel 7:13, 14) Ya raba wannan gādo da 144,000 “abokan gādo” da aka zaɓa “cikin mutane” domin su “mallaki duniya.” (Romawa 8:17; Wahayin Yahaya 5:9, 10; 14:1, 3, 4; Daniyel 7:27) Kristi da abokan sarautarsa za su shugabanci miliyoyin mutane maza da mata masu kama da tumaki, waɗanda zabura za ta cika a kansu: “Masu ladabi za su zauna lafiya a ƙasar, su ji daɗin cikakkiyar salama.”—Zabura 37:11; Matiyu 25:33, 34, 46.

Farin Ciki ta Tabbata ga Masu Ƙwaɗaita ga Adalci

10. A wace hanya ce waɗanda suke ‘ƙwaɗayi da ƙishi na adalci’ za a biya musu muradi?

10 Farin ciki na gaba da Yesu ya furta sa’ad da yake magana a kan dutsen Galili shi ne: “Albarka [farin ciki] tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.” (Matiyu 5:6) Ga Kiristoci, Jehovah ne ya kafa mizanin adalci. Saboda haka, waɗanda suke ƙwaɗayi kuma jin ƙishi na adalci wato suna ƙwaɗayi da kuma ƙishin ja-gorar Allah ce. Irin waɗannan suna sane da zunubinsu da kuma ajizancinsu kuma suna son su sami matsayi mai kyau a gaban Jehovah. Masu farin ciki ne matuƙa idan suka koyi daga Kalmar Allah cewa idan suka tuba suka nemi gafara bisa hadayar fansa ta Kristi, za su sami matsayin adalci a gaban Allah!—Ayyukan Manzanni 2:38; 10:43; 13:38, 39; Romawa 5:19.

11, 12. (a) Ta yaya Kiristoci shafaffu suka kai ga adalci? (b) Ta yaya za a biya wa abokanan shafaffu muradin ƙishirunwasu na adalci?

11 Yesu ya ce irin waɗannan za su yi farin ciki, tun da za a “biyu musu muradi.” (Matiyu 5:6) Kiristoci shafaffu da aka kira su “yi mallaka” tare da Kristi a samaniya sun “kuɓuta zuwa rai.” (Romawa 5:1, 9, 16-18) Jehovah ya ɗauke su ’ya’yansa na ruhaniya. Sun zama abokan gadō da Kristi, an kira su su zama sarakuna da firistoci a gwamnatin Mulkin sama.—Yahaya 3:3; 1 Bitrus 2:9.

12 Abokanan shafaffun har yanzu ba su kuɓuta zuwa rai ba tukuna. Amma Jehovah yana ɗaukansu masu adalci domin bangaskiyarsu a jinin Kristi. (Yakubu 2:22-25; Wahayin Yahaya 7:9, 10) Ana ɗaukansu abokanan Jehovah masu adalci da za a cece su a lokacin “matsananciyar wahala.” (Wahayin Yahaya 7:14) Za a biya musu muradinsu na ƙishiruwansu na adalci, sa’ad da suka kasance suna cikin sabuwar ƙasa, inda “adalci zai yi zamansa” a ƙarƙashin “sababbin samai.”—2 Bitrus 3:13; Zabura 37:29.

Farin Ciki ta Tabbata ga Majiya Tausayi

13, 14. A waɗanne hanyoyi ne na zahiri za mu iya nuna cewa mu masu tausayi ne, kuma ta yaya za mu amfana?

13 Yesu ya ci gaba da Huɗubarsa a kan Dutse, yana cewa: “Albarka [farin ciki] tā tabbata ga majiya tausayi, domin su ma za a ji tausayinsu.” (Matiyu 5:7) A hanyar shari’a, an fahimci tausayi da ahuwa daga alƙali wanda ya sauƙaƙa hukunci da shari’a ta tanada ga mai laifi. Amma kamar yadda aka yi amfani da ita a Littafi Mai Tsarki, kalmar ainihi da aka fassara “tausayi” yawanci tana nufin yin alheri ko kuma juyayi da yake sa a yi taimako ga gajiyayyu. Saboda haka, waɗanda suke da tausayi masu juyayi ne ƙwarai. Almarar Yesu ta maƙwabci Basamariye, ya ba da misali mai kyau na mutumin da ya ji “tausayin” wanda yake cikin bukata.—Luka 10:29-37.

14 Domin mu more farin ciki da ke zuwa daga tausayi, muna bukatar mu duƙufa cikin ayyukan alheri domin waɗanda suke cikin bukata. (Galatiyawa 6:10) Yesu ya yi juyayin mutane da ya gani. “Ya kuma ji tausayinsu, domin kamar tumaki suke ba makiyayi. Ya fara koya musu abubuwa da yawa.” (Markus 6:34) Yesu ya fahimci cewa babbar bukatar ’yan adam ruhaniya ce. Mu ma za mu iya nuna cewa mu masu tausayi ne da jinƙai ta wajen ba mutane abin da suke matuƙar bukata—“bisharan nan ta Mulki.” (Matiyu 24:14) Za mu iya ba da taimako na zahiri ga ’yan’uwanmu Kiristoci da suka tsufa, gwauraye, da marayu, kuma mu “ƙarfafa masu rarraunar zuciya.” (1 Tasalonikawa 5:14; Karin Magana 12:25; Yakubu 1:27) Wannan zai sa mu farin ciki kuma ya sa mu sami jinƙan Jehovah.—Ayyukan Manzanni 20:35; Yakubu 2:13.

Masu Tsarkakkiyar Zuciya Masu Ƙulla Zumunci

15. Ta yaya za mu kasance masu tsarkakkiyar zuciya kuma masu ƙulla zumunci?

15 Yesu ya furta farin ciki na shida da bakwai yana cewa: “Albarka [farin ciki] tā tabbata ga masu tsarkakakkiyar zuciya, domin za su ga Allah. Albarka [farin ciki] tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su ’ya’yan Allah.” (Matiyu 5:8, 9) Tsarkakkiyar zuciya tana da tsabta ta ɗabi’a kuma ba ta da aibi a ruhaniya kuma ta jitu wajen bautar Jehovah. (1 Tarihi 28:9; Zabura 86:11) Kalmar asali da aka fassara masu “ƙulla zumunci” tana nufin masu “zaman lumana.” Masu zumunci suna zaman lumana da ’yan’uwa Kiristoci da kuma, in mai yiwuwa ne a gare su, suna zaman lumana da maƙwabtansu. (Romawa 12:17-21) Sun ‘himmantu ga zaman lafiya, suna kuma dimance ta.’—1 Bitrus 3:11.

16, 17. (a) Me ya sa aka kira shafaffu “ ’ya’yan Allah,” kuma ta yaya suka “ga Allah”? (b) Ta yaya “waɗansu tumaki” suka “ga Allah”? (c) Ta yaya kuma a yaushe, “waɗansu tumaki” za su zama cikakkun “ ’ya’yan Allah”?

16 Ga masu ƙulla zumunci masu tsarkakkiyar zuciya, an yi musu alkawarin cewa “za a ce da su ’ya’yan Allah” kuma “za su ga Allah.” Kiristoci shafaffu ta wajen ruhu Allah ya ce da su “ ’ya’ya” sa’ad da ma suke duniya. (Romawa 8:14-17) Sa’ad da aka ta da su daga matattu su kasance tare da Kristi a samaniya, za su yi bauta a gaban Jehovah kuma hakika za su gan shi.—1 Yahaya 3:1, 2; Wahayin Yahaya 4:9-11.

17 “Waɗansu Tumaki” masu ƙulla zumunta suna bauta wa Jehovah a ƙarƙashin Makiyayi Mai Kyau, Kristi Yesu, wanda ya zama ‘Ubansu Madawwami.’ (Yahaya 10:14, 16; Ishaya 9:6) Waɗanda suka yi nasara a gwaji na ƙarshe bayan Sarautar Alif ta Kristi za su zama ’ya’yan Jehovah a nan duniya kuma za su “sami ’yancin nan na ɗaukaka na ’ya’yan Allah.” (Romawa 8:21; Wahayin Yahaya 20:7, 9) Domin suna sauraron wannan, suna kiran Jehovah Uba, tun da sun keɓe masa rayukansu, sun fahimci cewa shi ya ba su rai. (Ishaya 64:8) Kamar Ayuba da Musa na zamanin dā, su ma za su “ga Allah” da idanun bangaskiya. (Ayuba 42:5; Ibraniyawa 11:27) Da ‘idanun zuciyarsu’ da kuma cikaken sanin Allah, sun fahimci halayen Jehovah masu ban sha’awa suna yin ƙoƙarin koyi da shi ta wajen yin nufinsa.—Afisawa 1:18; Romawa 1:19, 20; 3 Yahaya 11.

18. A farin ciki guda bakwai da Yesu ya ambata, su waye suke samun farin ciki na gaske a yau?

18 Mun ga cewa waɗanda suka san bukatarsu ta ruhaniya, waɗanda suke nadama, masu tawali’u, waɗanda suke kwaɗayi da kishiruwa na adalci, masu tausayi, masu tsarkakkiyar zuciya, da kuma masu ƙulla zumanci suna samun farin ciki na gaske wajen bauta wa Jehovah. Duk da haka, waɗannan a kullum suna fuskantar hamayya, har ma da tsanantawa. Shin wannan yana mai da farin cikinsu ciki ne? Za a amsa wannan tambayar a talifi na gaba.

Domin Bita

• Wane farin ciki waɗanda suka san bukatarsu ta ruhaniya suke samu?

• A wace hanya ake sanyaya zukatan waɗanda suke nadama?

• Ta yaya za mu nuna tawali’u?

• Me ya sa ya kamata mu zama masu tausayi, masu tsarkakkun zukata, masu ƙulla zumunci?

[Hoto a shafi na 22]

‘Farin ciki ta tabbata ga waɗanda suka san bukatarsu ta ruhaniya’

[Hotuna a shafi na 22]

‘Farin ciki ta tabbata ga masu tausayi’

[Hoto a shafi na 22]

‘Farin ciki ta tabbata ga masu kwaɗayi da ƙishiruwan adalci’

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba