“Ku Zauna A Faɗake”—Lokacin Hukunci Ya Yi!
Bayanin da ke cikin wannan talifin ya fito ne daga mujallar nan Ka Zauna A Faɗake! da aka fito da ita a taron gunduma da aka yi a dukan duniya a shekara ta 2004 da 2005.
“Ku zauna a faɗake . . . don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba.”—Matiyu 24:42.
1, 2. Da menene Yesu ya kwatanta zuwansa?
MENENE za ka yi idan ka sani cewa ɓarawo ya shiga gidan maƙwabcinka yana sata? Domin ka kāre ƙaunatattunka da kuma dukiyarka, za ka kasance a faɗake. Ɓarawo ba ya aiko da wasiƙa don ya sanar da lokacin da zai zo. Akasarin haka, ya kan zo ne a ɓoye kuma a lokacin da ba a yi tsammani ba.
2 Sau da yawa, Yesu ya yi amfani da ɓarawo a misalinsa. (Luka 10:30; Yahaya 10:10) Game da abubuwan da za su auku a zamani na ƙarshe waɗanda za su faru kafin zuwansa domin ya zartar da hukunci, Yesu ya ba da wannan gargaɗin: “Ku zauna a faɗake fa, don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba. Amma dai ku sani, da maigida zai san ko a wane lokaci ne da dare ɓarawo zai zo, da ya zauna a faɗake ya hana a shigar masa gida.” (Matiyu 24:42, 43) Saboda haka, Yesu ya kamanta zuwansa da ta ɓarawo, wato, babu zato.
3, 4. (a) Menene bin gargaɗin Yesu game da zuwansa ya ƙunsa? (b) Waɗanne tambayoyi ne suka taso?
3 Misalin ya yi daidai, domin babu wanda ya san lokacin da Yesu zai zo. A dā, a cikin wannan annabcin, Yesu ya ce: “Amma fa wannan rana da wannan sa’a ba wanda ya sani, ko mala’ikun da ke sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.” (Matiyu 24:36) Saboda haka, Yesu ya umurci masu sauraronsa: “Ku zauna a kan shiri.” (Matiyu 24:44) Waɗanda suke bin gargaɗin Yesu za su kasance a shirye, suna riƙe da tasarrufi mai kyau, ko da wane lokaci ne zai zo a matsayin mai Zartar da Hukuncin Jehobah.
4 Amma akwai tambayoyi masu muhimmanci da suka taso: Gargaɗin da Yesu ya bayar domin mutanen duniya ne kawai, ko kuwa Kiristoci na gaskiya suna bukatar su “zauna a faɗake”? Me ya sa yake da gaggawa a “zauna a faɗake,” kuma menene wannan ya ƙunsa?
Su Waye ne Aka Yi wa Gargaɗi?
5. Ta yaya ne muka sani cewa gargaɗin nan “ku zauna a faɗake” yana nuni ne ga Kiristoci na gaskiya?
5 Hakika, gaskiya ne cewa zuwan Ubangiji zai yi kama da zuwan ɓarawo ga mutanen duniya, waɗanda suka rufe kunnuwansu ga gargaɗi game da bala’in da zai zo. (2 Bitrus 3:3-7) Amma, Kiristoci na gaskiya fa? Manzo Bulus ya rubuta wa ’yan’uwa masu bi: “Ku da kanku kun sani sarai, ranar Ubangiji za ta zo ne kamar ɓarawo da dare.” (1 Tasalonikawa 5:2) Ba ma shakka a zukatanmu cewa “ranar Ubangiji za ta zo.” Amma hakan ya rage bukatar mu zauna a faɗake ne? Ka lura Yesu yana gaya wa almajiransa ne cewa: ‘A lokacin da ba ku zata ba, Ɗan Mutum zai zo.’ (Matiyu 24:44) Da farko, da yake ariritar manzanninsa su ci gaba da biɗar Mulki, Yesu ya yi musu gargaɗi: ‘Ku ma sai ku zauna a kan shiri, don a lokacin da ba ku zata ba Ɗan Mutum zai zo.’ (Luka 12:31, 40) Wannan ya nuna cewa Yesu yana yi wa mabiyansa gargaɗi su “zauna a faɗake.”
6. Me ya sa muke bukatan mu “zauna a faɗake”?
6 Me ya sa muke bukatar mu “zauna a faɗake” kuma mu “zauna a kan shiri”? Yesu ya yi bayani: “Za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. Za a ga mata biyu suna niƙe, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.” (Matiyu 24:40, 41) Waɗanda suka kasance a shirye ne za a “ɗau,” ko kuwa za su tsira, a lokacin da aka halaka wannan duniya mai fajirci. Za a “bar” sauran ga halaka domin suna biɗar hanyar rayuwa ta son kai. Wataƙila waɗannan za su haɗa da waɗanda a dā sun san gaskiya amma ba su zauna a faɗake ba.
7. Menene rashin sanin sa’ad da ƙarshe za ta zo zai sa mu yi?
7 Rashin sanin ainihin ranar da tsohon zamanin nan zai kai ƙarshe yana ba mu zarafin nuna cewa muna bauta wa Allah da tsarkakken nufi. Me ya sa muka faɗi haka? Ana ganin cewa ƙarshen zai daɗe kafin ya zo. Abin baƙin ciki, wasu Kiristoci da suke jin haka sun yi sanyin gwiwa a hidimarsu ga Jehobah. Amma dai, ta wurin keɓe kai, mun riga mun miƙa kanmu babu tantama ga Jehobah domin mu bauta masa. Waɗanda suka san Jehobah sun sani cewa kasancewa da himma ta nan da nan kafin ƙarshe ba za ta burge shi ba. Ya san abin da ke cikin zuciya.—1 Sama’ila 16:7.
8. Ta yaya ƙauna ga Jehobah ke motsa mu mu zauna a faɗake?
8 Domin muna ƙaunar Jehobah da gaske, muna samun farin ciki wajen yin nufinsa. (Zabura 40:8; Matiyu 26:39) Muna son mu bauta wa Jehobah har abada. Wannan bege ba a banza ba ne domin dole ne mu jira wasu albarkatai na ɗan lokaci fiye da yadda muka zata. Fiye da haka, muna zaune a faɗake ne domin muna ɗokin abin da ranar Jehobah za ta yi wajen cika nufinsa. Muradinmu na son faranta wa Allah zuciya na motsa mu mu aikata umurnin Kalmarsa kuma mu mai da Mulkinsa abu na farko a rayuwarmu. (Matiyu 6:33; 1 Yahaya 5:3) Bari mu tattauna yadda zama a faɗake ya kamata ya rinjayi shawarar da muke ɗauka da kuma hanyar da muke rayuwarmu a koyaushe.
Ina Rayuwarka ta Nufa?
9. Me ya sa da bukata ta gaggawa ga mutanen duniya su zauna a faɗake kuma su fahimci muhimmancin lokacinmu?
9 Yawancin mutane a yau sun fahimci cewa matsaloli masu tsanani da abubuwa masu ban mamaki sun zama labarun yau da kullum, kuma wataƙila ba sa jin daɗin inda rayuwarsu ta nufa. Amma sun san ainihin ma’anar yanayin duniya? Sun fahimci cewa muna zaune ne a “ƙarewar zamani”? (Matiyu 24:3) Sun fahimci cewa halin son kai, mugunta, da halin rashin ibada suna nuna cewa muna zaune a “zamanin ƙarshe”? (2 Timoti 3:1-5) Cikin gaggawa suna bukata su zauna a faɗake don su fahimci muhimmancin waɗannan abubuwa kuma su yi la’akari da inda rayuwarsu ta nufa.
10. Menene ya kamata mu yi don mu tabbata cewa muna zaune a faɗake?
10 Mu kuma fa? Kowace rana muna tsai da shawarwari da suka shafi aikinmu, lafiyar jikinmu, iyalinmu, da bautarmu. Mun san abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa, kuma muna ƙoƙarin mu aikata su. Saboda haka, yana da kyau mu tambayi kanmu: ‘Na ƙyale alhini na rayuwa ya ɗauke mini hankali? Ina yarda wa ussan ilimi na duniya, da tunaninsa, ya gaya mini abin da zan zaɓa?’ (Luka 21:34-36; Kolosiyawa 2:8) Ya kamata mu ci gaba da nuna cewa mun dogara ga Jehobah da dukan zuciyarmu, kada mu dogara ga abin da muke tsammanin cewa mun sani. (Karin Magana 3:5) Ta haka, za mu “riƙi rai madawwamin nan,” wato rai madawwami a sabuwar duniya ta Allah.—1 Timoti 6:12, 19.
11-13. Menene za mu iya koya daga misalan abin da ya faru (a) a zamanin Nuhu? (b) a zamanin Lutu?
11 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalai na gargaɗi masu yawa da za su taimaka mana mu zauna a faɗake. Yi la’akari da abin da ya faru a zamanin Nuhu. Kafin wannan lokacin, Allah ya tabbatar cewa an ba da gargaɗi. Ban da Nuhu da iyalinsa, mutane ba su lura ba. (2 Bitrus 2:5) Game da wannan, Yesu ya ce: “Kamar yadda aka yi a zamanin Nuhu, haka dawowar Ɗan Mutum za ta zama. Kamar a kwanakin nan ne gabannin Ruwan Tsufana, ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi, ba su farga ba har Ruwan Tsufana ya zo ya share su. Haka komowar Ɗan Mutum za ta zama.” (Matiyu 24:37-39) Menene za mu iya koya daga wannan? Idan waninmu ya ƙyale abubuwan rayuwa na yau da kullum, ko bukatun rayuwa su sha kan ayyuka na ruhaniya da Allah ke ƙarfafa mu mu sa shi farko, to lallai muna bukatar mu yi tunanin yanayinmu sosai.—Romawa 14:17.
12 Ka yi tunani game da zamanin Lutu. Birnin Saduma, inda Lutu da iyalinsa suka zauna, yana da ni’ima, amma cike yake da lalata mai yawa. Jehobah ya aiki mala’ikunsa su halaka birnin. Mala’ikun sun umurci Lutu da iyalinsa su gudu daga Saduma kuma kada su waiwaya. Sun bar birnin domin ƙarfafa daga mala’ikun. Amma, matar Lutu ta kasa yin watsi da tunanin gidanta da ke Saduma. Don rashin biyayya, ta waiwaya, kuma ta yi hasarar ranta. (Farawa 19:15-26) A hanyar annabci, Yesu ya yi gargaɗi: “Ku tuna fa da matar Lutu.” Muna bin wannan gargaɗin kuwa?—Luka 17:32.
13 Waɗanda suka saurari gargaɗin Allah sun tsira. Haka yake da Nuhu da iyalinsa da kuma Lutu da ’ya’yansa mata biyu. (2 Bitrus 2:9) Sa’ad da muke bin gargaɗin da ke cikin waɗannan misalan, muna samun ƙarfafa ta wajen saƙon ceto da ke ciki don masu ƙaunar adalci. Wannan na cika zuciyarmu da tabbataccen bege game da cikar alkawarin Allah na “sababbin sammai da sabuwar ƙasa, inda adalci zai yi zamansa.”—2 Bitrus 3:13.
‘Lokacin Hukunci’ ya Yi!
14, 15. (a) Menene ‘lokacin’ hukunci ya ƙunsa? (b) Menene ‘jin tsoron Allah da kuma ɗaukaka shi’ ya ƙunsa?
14 Yayin da muka zauna a faɗake, menene za mu yi tsammaninsa? Littafin Wahayin Yahaya ya yi nuni sarai ga tsarin abubuwa da za su kai ga cikar nufin Allah. Idan muna son mu zauna a faɗake, dole ne mu aikata a kan abin da ya ce. Wannan annabcin ya yi nuni sarai ga abubuwan da za su auku a “ranar Ubangiji,” wadda ta soma tun lokacin da aka ɗora Kristi a kan gadon sarauta a sama a shekara ta 1914. (Wahayin Yahaya 1:10) Wahayin Yahaya ya mai da hankalinmu ga wani mala’ika wanda yake bayyana “madawwamiyar bishara.” Da murya mai ƙarfi ya ce: “Ku ji tsoron Allah, ku ɗaukaka shi, domin lokacinsa na yin hukunci ya yi.” (Wahayin Yahaya 14:6, 7) Wannan ‘lokacin’ na hukunci ɗan lokaci ne; ya haɗa da lokacin da za a yi shela kuma a zartar da hukuncin da aka nuna a wannan annabcin. Muna zaune a wannan lokacin.
15 Yanzu, kafin a kammala lokacin hukuncin, an aririce mu: “Ku ji tsoron Allah, ku ɗaukaka shi.” Menene wannan ya ƙunsa? Tsoron Allah ya kamata ya motsa mu mu guje wa yin abu marar kyau. (Karin Magana 8:13) Idan muna ɗaukaka Allah, za mu yi ladabi mu saurare shi. Ba za mu shagala a yin wasu abubuwa kuma mu yi banza da karatun Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, a kai a kai ba. Ba za mu rena umurninsa ta ƙin halartar taron Kirista ba. (Ibraniyawa 10:24, 25) Za mu so gatarmu na yin shelar bisharar Mulkin Almasihu na Allah kuma za mu yi haka da himma. Za mu dogara ga Jehobah a kowane lokaci da dukan zuciyarmu. (Zabura 62:8) Sanin cewa Jehobah ne Mamallakin Dukan Halitta, muna daraja shi ta wajen ba da kanmu a gare shi domin shi ne Mamallakin ranmu. Kana tsoron Allah kuwa da gaske kuma kana ɗaukaka shi a dukan waɗannan hanyoyin?
16. Me ya sa za mu iya cewa hukuncin Babila Mai Girma da aka ambata a Wahayin Yahaya 14:8 ta riga ta cika?
16 Wahayin Yahaya sura 14 ta ci gaba da kwatanta abubuwa da za su auku a lokacin hukuncin. Babila Mai Girma, daular duniya na addinin ƙarya ce aka fara ambata: “Sai wani mala’ika na biyu ya biyo, yana cewa, “Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi!” (Wahayin Yahaya 14:8) Hakika, bisa ga ra’ayin Allah, Babila Mai Girma ta riga ta faɗi. A shekara ta 1919, an ceci shafaffun bayin Jehobah daga koyarwa da ayyukan Babila, waɗanda suka rinjayi mutane da al’ummai na shekaru dubbai. (Wahayin Yahaya 17:1, 15) Tun daga lokacin suna iya ba da kansu ga yaɗa bauta ta gaskiya. Tun daga lokacin ana wa’azin bishara na mulkin Allah a dukan duniya.—Matiyu 24:14.
17. Menene fitowa daga cikin Babila Mai Girma ta ƙunsa?
17 Amma ba ƙarshen hukuncin Allah bisa Babila Mai Girma ba ke nan. Jim kaɗan, halaka na ƙarshe za ta zo kanta. (Wahayin Yahaya 18:21) Da kyakkyawan dalili, Littafi Mai Tsarki ya umurci mutane a ko’ina: “Ku fito daga cikinta [Babila Mai Girma], . . . kada zunubanta su shafe ku.” (Wahayin Yahaya 18:4, 5) Ta yaya muka fito daga Babila Mai girma? Wannan ya ƙunshi fiye da ɗaukan matakin yanke zumunci da addinan ƙarya. Tasirin Babila Mai Girma tana cikin yawancin sanannun bukukuwa da al’adu, cikin halin kome daidai na duniya game da jima’i, cikin gabatar da nishaɗi da ya shafi sihiri, da sauransu. Domin mu zauna a faɗake, yana da muhimmanci mu nuna ta wajen halayenmu da muradin zuciyarmu, cewa lallai ba ma cikin Babila Mai Girma a kowace hanya.
18. Domin abin da aka kwatanta a Wahayin Yahaya 14:9, 10, menene Kiristoci da suke mai da hankali za su kauce wa?
18 A Wahayin Yahaya 14:9, 10, an sake kwatanta wani fanni na ‘lokacin hukunci.’ Wani mala’ika ya ce: “Duk mai yi wa dabban nan da siffarta sujada, wanda kuma ya yarda a yi masa alama a goshinsa, ko a hannunsa, zai ci karo da azabar Allah tsantsa ta tsananin fushinsa.” Me ya sa? Domin “dabban nan da siffarta” alamun sarautar ’yan adam ce da ba ta yarda da ikon mallakar Jehobah ba. Kiristoci da suke zaune a faɗake suna mai da hankali kada a shaida su ta halayensu ko ayyukansu, kamar masu bauta ga waɗanda ba su yarda da mafificin ikon mallakar Allah na gaskiya, Jehobah ba. Kiristoci sun sani cewa an riga an kafa Mulkin Allah a sama, wanda zai farfashe kuma ya kawo ƙarshen mulkin ’yan adam, kuma zai dawwama har abada.—Daniyel 2:44.
Kada Ka Manta Cewa Yanzu Lokaci ne na Gaggawa!
19, 20. (a) Yayin da muke ƙara nitsewa cikin wannan zamani na ƙarshe, menene muke da tabbacin cewa Shaiɗan zai yi ƙoƙarin yi?
19 Yayin da muke ƙara nitsewa cikin zamanin ƙarshe, matsi da gwaji za su ƙara tsanani. Yayin da muke zaune a cikin wannan tsohon zamanin da kuma wahalar ajizancinmu, za mu fuskanci abubuwa kamar su rashin lafiya, tsufa, rashin wani ƙaunatacce, ɓacin rai sa’ad da muka fuskanci ƙiyayya domin ƙoƙarinmu na yin wa’azin Kalmar Allah, da wasu abubuwa da yawa. Kada ka manta cewa Shaiɗan zai so ya yi amfani da matsin da muke fuskanta don mu daina yin wa’azin bishara ko kuwa mu daina bin mizanan Allah. (Afisawa 6:11-13) Wannan ba lokaci ba ne da za mu yi hasarar azancinmu na gaggawa game da lokacin da muke zaune a ciki!
20 Yesu ya sani cewa za mu fuskanci matsi mai yawa da za su iya sa mu kasala, shi ya sa ya yi mana gargaɗi: “Ku zauna a faɗake . . . don ba ku san ranar da Ubangijinku zai dawo ba.” (Matiyu 24:42) Bari mu kasance a faɗake domin lokacin da muke ciki. Bari mu kula da dabarun da Shaiɗan zai iya amfani da su da za su rage mana kuzari ko mu kasala. Bari mu ƙudurta cewa za mu yi wa’azin bisharar Mulkin Allah da ƙarin himma da kuma ƙuduri. Ko yaya dai, bari mu kasance da azancinmu na gaggawa yayin da muke bin gargaɗin Yesu: “Ku zauna a faɗake.” Idan muka yi haka, za mu ɗaukaka Jehobah kuma za mu kasance cikin waɗanda za su more madawwamin albarkarsa.
Yaya Za Ka Amsa?
• Ta yaya muka sani cewa gargaɗin Yesu mu “zauna a faɗake” ga Kiristoci na gaskiya?
• Waɗanne misalai na gargaɗi da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne za su iya taimaka mana mu “zauna a faɗake”?
• Menene lokacin hukunci, kuma menene aka umurce mu mu yi kafin a kammala lokacin?
(b) Menene ya kamata mu ƙuduri anniyar yi?
[Hoto a shafi na 19]
Yesu ya kwatanta zuwansa da na ɓarawo
[Hoto a shafi na 20]
Halakar Babila Mai Girma ta yi kusa
[Hotuna a shafi na 21]
Bari mu ƙuduri anniyar yin wa’azi da himma da kuma ƙwazo