Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lvs babi na 5 pp. 60-74
  • Yadda Za Mu Ki Saka Hannu A Harkokin Duniya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Mu Ki Saka Hannu A Harkokin Duniya
  • Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Karanta a “Ƙaunar Allah”
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA GOYI BAYAN MULKIN ALLAH DA AMINCI
  • MU GUJE WA “RUHUN DUNIYA”
  • SAKA TUFAFIN DA SUKE GIRMAMA ALLAH
  • RA’AYIN DA YA DACE GAME DA KUƊI
  • “DUKAN KAYAN KĀRIYA NA YAƘI”
  • KA KASANCE A SHIRYE DON KA BAYYANA IMANINKA
  • Ta Yaya Za Mu Tsayayya Wa Aljanu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Tsakatsaki Na Kirista A Kwanaki Na Ƙarshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ta Yaya Jehobah Yake Kāre Ka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ka Karɓi Ruhun Allah Ba Na Duniya ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
lvs babi na 5 pp. 60-74
Wasu matasa Shaidu

BABI NA 5

Yadda Za Mu Ƙi Saka Hannu A Harkokin Duniya

“Ku ba na duniya ba ne.”​—YOHANNA 15:19.

1. Me ya sa Yesu ya damu a darensa na ƙarshe kafin a kashe shi?

A DAREN Yesu na ƙarshe kafin a kashe shi, ya san cewa zai bar almajiransa, don haka, ya damu da abin da zai faru da su. Saboda haka, ya ce musu: “Ku ba na duniya ba ne.” (Yohanna 15:19) Daga baya, ya yi addu’a dominsu ya ce: “Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.” (Yohanna 17:​15, 16) Me Yesu yake nufi?

2. Mene ne “duniya” da Yesu ya ambata take nufi?

2 Kalmar nan “duniya” da Yesu ya yi amfani da ita tana nufin mutanen da ba su san Allah ba, waɗanda Shaiɗan yake iko da su. (Yohanna 14:30; Afisawa 2:2; Yaƙub 4:4; 1 Yohanna 5:19) Ta yaya za mu kasance “ba na duniya ba”? A wannan babin, za mu tattauna hanyoyi biyar da za mu yi hakan. Na ɗaya, ta kasancewa da aminci ga Mulkin Allah, wato mu ƙi yin siyasa. Na biyu, ta ƙin halayen mutanen duniya. Na uku, ta yin ado da saka kayan da suka dace. Na huɗu, ta kin yawan son abin duniya. Na biyar, ta saka dukan kayan kāriya na yaƙi wanda Allah ya bayar.​—Ka duba Ƙarin Bayani na 16.

KA GOYI BAYAN MULKIN ALLAH DA AMINCI

3. Me ya sa Yesu bai yi siyasa ba?

3 A lokacin da Yesu yake duniya, ya lura cewa mutane suna shan wahala kuma rayuwa ba ta da sauƙi. Ya damu da su kuma ya taimaka musu. Amma ya shiga siyasa ne? A’a. Me ya sa? Domin ya san cewa abin da mutane suke bukata shi ne Mulki ko Gwamnatin Allah. Yesu ne zai zama Sarki a Mulkin Allah, shi ya sa ya yi ta wa’azin Mulkin a lokacin da yake duniya. (Daniyel 7:​13, 14; Luka 4:43; 17:​20, 21) Yesu bai tsaya takara ko ya goyi bayan ’yan siyasa ba. A lokacin da yake gaban Gwamnan Romawa Bilatus Ba-Bunti, ya ce: ‘Mulkina ba irin na duniya ba ne.’ (Yohanna 18:36) Almajiransa ma ba su saka hannu a harkokin siyasa ba. Littafin nan On the Road to Civilization, ya ce Kiristoci na farko “ba su yarda sun yi siyasa ba.” Mu Kiristoci na gaskiya a yau ma ba ma siyasa. Muna goyon bayan Mulkin Allah kuma ba ma saka hannu a harkokin siyasa na duniyar nan.​—Matiyu 24:14.

Wani Mashaidi yana bayyana ma wani abin da ya yi imani da shi

Za ka iya bayyana dalilin da ya sa kake goyon bayan Mulkin Allah?

4. Ta yaya Kiristoci na gaskiya suke goyon bayan Mulkin Allah?

4 Jakadu suna zama a wata ƙasa don su wakilci ƙasarsu, don haka, ba sa saka hannu a harkokin siyasa da ake yi a ƙasar da suke zama. Irin hidimar nan ne Shafaffun Kiristoci da za su yi sarauta tare da Kristi a sama suke yi. Bulus ya rubuta wa Shafaffun Kiristoci wasiƙa, ya ce: “Mu wakilai ne na Almasihu.” (2 Korintiyawa 5:20) Shafaffu suna wakiltar gwamnatin Allah. Don haka, ba sa saka hannu a harkokin siyasa ko gwamnatin duniyar nan. (Filibiyawa 3:20) A maimakon haka, shafaffun sun taimaka wa miliyoyin mutane su san gwamnatin Allah. “Waɗansu tumaki,” da suke sa ran yin rayuwa a sabuwar duniya har abada suna goyon bayan shafaffun. Su ma ba sa saka hannu a harkokin duniyar nan. (Yohanna 10:16; Matiyu 25:​31-40) Babu shakka, Kiristoci na gaskiya ba sa saka hannu a siyasa.​—Karanta Ishaya 2:​2-4.

5. Me ya sa Kiristoci ba sa yaƙi?

5 Kiristoci na gaskiya suna ɗaukan junansu a matsayin iyali ɗaya kuma suna da haɗin kai duk da cewa ƙasashensu da ƙabilunsu sun bambanta. (1 Korintiyawa 1:10) Idan muka saka hannu a yaƙi, za mu yaƙi ’yan’uwanmu Kiristoci da Yesu ya umurce mu mu ƙaunace su. (Yohanna 13:​34, 35; 1 Yohanna 3:​10-12) Ban da haka ma, Yesu ya gaya ma almajiransa su ƙaunaci mutane har da abokan gabansu.​—Matiyu 5:44; 26:52.

6. Yaya bayin Allah suke ɗaukan gwamnatin ’yan Adam?

6 Ko da yake mu Kiristoci na gaskiya ba ma saka hannu a harkokin duniyar nan, muna iya ƙoƙarinmu mu kasance da halayen kirki. Alal misali, muna wa gwamnati biyayya ta wurin bin dokokinta da kuma biyan haraji. Amma a kullum muna tabbata cewa muna “ba Allah abin da yake na Allah.” (Markus 12:17; Romawa 13:​1-7; 1 Korintiyawa 6:​19, 20) “Abin da yake na Allah” shi ne mu ƙaunace shi da yi masa biyayya da kuma bauta masa. Maimakon mu yi wa Allah rashin biyayya, muna a shirye mu rasa ranmu don mu faranta masa rai.​—Luka 4:8; 10:27; karanta Ayyukan Manzanni 5:29; Romawa 14:8.

MU GUJE WA “RUHUN DUNIYA”

7, 8. Mene ne “ruhun duniya” yake nufi kuma ta yaya yake shafan halayen mutane?

7 Idan muna so mu ware kanmu daga harkokin duniya, wajibi ne mu guje wa ‘ruhun duniyar’ nan. Ruhun ya ƙunshi tunani da kuma halaye marasa kyau da Shaiɗan yake sa mutanen da ba sa bauta wa Jehobah su kasance da su. Kiristoci suna guje wa irin waɗannan halayen. Manzo Bulus ya ce, “mu kuwa ba ruhun duniya muka karɓo ba, sai dai Ruhu . . . daga wurin Allah.”​—1 Korintiyawa 2:12; Afisawa 2:​2, 3; ka duba Ƙarin Bayani na 17.

8 Ruhun duniyar nan yana sa mutane su zama masu son kai da girman kai da kuma tawaye. Ruhun yana sa su ganin cewa ba dole ba ne su yi wa Allah biyayya. Shaiɗan yana son mutane su yi abubuwan da suka ga dama ba tare da tunanin mummunar sakamakon da hakan zai jawo ba. Yana son mutane su yarda cewa “sha’awa ta jiki, da kwaɗayin ido” ne suke sa mu ji daɗin rayuwa. (1 Yohanna 2:16; 1 Timoti 6:​9, 10) Shaiɗan yana iya ƙoƙarinsa musamman don ya sa bayin Jehobah su kasance da irin halayensa.​—Yohanna 8:44; Ayyukan Manzanni 13:10; 1 Yohanna 3:8.

9. Ta yaya halayen banza za su iya shafanmu idan ba mu mai da hankali ba?

9 Mutanen da suke da halayen banza suna kewaye da mu kamar iska da muke shaƙa. Idan ba mu yi iya ƙoƙarinmu mu guji halayen ba, za su iya shafan mu. (Karanta Karin Magana 4:23.) Idan ba mu mai da hankali ba, hakan zai faru sa’ad da muka soma bin ra’ayi ko halayen mutanen da ba sa bauta wa Jehobah. (Karin Magana 13:20; 1 Korintiyawa 15:33) Ban da haka ma, za mu iya soma kallon hotunan batsa ko bin ra’ayin ’yan ridda ko kuma goyon bayan wasannin da ake yin gasa.​—Ka duba Ƙarin Bayani na 18.

10. Ta yaya za mu guji bin ra’ayin mutanen duniya?

10 Saboda haka, ta yaya za mu guji bin ra’ayin mutanen duniya? Muna bukatar mu ci gaba da kusantar Jehobah kuma mu bar hikimarsa ta ja-gorance mu. Dole ne mu roƙe shi ya ba mu ruhunsa mai tsarki a kullum kuma mu riƙa yi masa hidima da ƙwazo. Jehobah ya fi kowa iko a sama da ƙasa. Don haka, muna da tabbaci cewa zai taimaka mana mu guji ra’ayin mutanen duniya.​—1 Yohanna 4:4.

SAKA TUFAFIN DA SUKE GIRMAMA ALLAH

11. Wane irin ado ne mutanen duniya suke yi?

11 Muna nuna cewa mu ba na duniya ba ne ta wurin adon da muke yi. Mutanen duniya suna saka tufafi don su ja hankalin mutane kuma su sa su riƙa tunanin lalata ko su sa mutane tawaye. Wasu kuma suna ado don su nuna cewa su masu kuɗi ne. Har ila, wasu ba su damu da irin adon da suke yi ba. Suna iya saka tufafi mara fasali ko masu datti. Saboda haka, bai kamata mu bar irin waɗannan ra’ayoyin su sa mu riƙa adon da bai dace ba.

Wata ’yar’uwa da ta yi ado mai kyau tana nuna bidiyo a wa’azi

Saka tufafi da kuma adon da nake yi yana girmama Jehobah kuwa?

12, 13. Waɗanne ƙa’idodi ne za su taimaka mana sa’ad da muke so mu yi ado ko saka tufafi?

12 Da yake mu bayin Jehobah ne, zai dace tufafinmu ya riƙa kasancewa da tsabta kuma adonmu ya dace da abin da muke yi. Muna yin adon da ya dace, don mu nuna cewa mu “masu bautar Allah ne.”​—1 Timoti 2:​9, 10; Yahuda 21.

13 Yadda muke yin ado zai iya sa mutane su daraja ko kuma su rena Allah da mutanensa. Muna son mu yi “kome saboda ɗaukakar Allah.” (1 Korintiyawa 10:31) Idan muna daraja ra’ayin mutane da kuma yin la’akari da yadda suke ji, hakan zai taimaka mana mu yi adon da ya dace. Don haka, a duk lokacin da muke zaɓan tufafin da za mu saka ko adon da za mu yi, muna bukatar mu tuna cewa zai iya shafan mutanen da ke kewaye da mu.​—1 Korintiyawa 4:9; 2 Korintiyawa 6:​3, 4; 7:1.

14. Me za mu tuna da shi sa’ad da muke zaɓan tufafin da za mu saka zuwa taro ko wa’azi?

14 Yaya muke ado sa’ad da muke zuwa taro ko wa’azi? Muna adon da zai sa mutane su riƙa kallon mu ne? Adonmu ko tufafin da muke sakawa za su iya kunyatar da mutane ne? Shin muna ganin ba ruwan kowa da adon da muke yi? (Filibiyawa 4:5; 1 Bitrus 5:6) Babu shakka, muna son adonmu ya yi kyau, amma abubuwan da za su sa mu zama da daraja su ne ayyuka masu kyau na masu bautar Allah. Waɗannan halayen ne Jehobah ya fi mai da hankali a kai, ba adonmu ba. Halayen suna nuna ainihin yadda muke a “zuciya . . . , wanda yake da muhimmiyar daraja a wurin Allah.”​—1 Bitrus 3:​3, 4.

15. Me ya sa Jehobah bai ba mu jerin dokoki a kan yadda za mu saka tufafi ko mu yi ado ba?

15 Jehobah bai ba mu jerin dokokin da za su nuna mana irin tufafin da za mu saka da waɗanda bai kamata mu saka ba. A maimakon haka, ya ba mu ƙa’idodin da za su taimaka mana mu tsai da shawarwarin da suka dace. (Ibraniyawa 5:14) Yana son shawarwarinmu su nuna cewa muna ƙaunarsa da kuma mutane. (Karanta Markus 12:​30, 31.) Bayin Jehobah a dukan duniya suna saka tufafi dabam-dabam bisa ga al’adarsu da kuma abin da suke so. Tufafi dabam-dabam da muke sakawa suna da kyau.

Wasu matasa Shaidu

RA’AYIN DA YA DACE GAME DA KUƊI

16. Ta yaya ra’ayin mutanen duniya game da kuɗi ya yi dabam da abin da Yesu ya faɗa? Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu?

16 Shaiɗan yana son mutane su gaskata cewa kuɗi ko abin duniya ne abubuwan da za su sa su farin ciki. Amma bayin Jehobah sun san cewa hakan ƙarya ce. Mun tabbata da kalaman Yesu cewa: “Yawan kaya ba shi ne samun rai ba.” (Luka 12:15) Yawan kuɗi ba zai sa mu farin ciki ba. Ba zai sa mu sami abokan kirki da kwanciyar hankali ko kuma rai na har abada ba. Babu shakka, muna bukatar abubuwan mallaka kuma muna son mu sami rai na har abada. Amma Yesu ya gaya mana cewa za mu zama da farin ciki idan mun zama abokan Allah kuma mun saka ibada farko a rayuwa. (Matiyu 5:3; 6:22) Don haka, zai dace ka tambayi kanka: ‘Ra’ayin mutanen duniya game da kuɗi yana shafa na ne? A kullum kuɗi ne nake hirar sa ko tunanin sa?’​—Luka 6:45; 21:​34-36; 2 Yohanna 6.

17. Yaya rayuwarka za ta kasance idan ka guji ra’ayin mutanen duniya game da kuɗi?

17 Rayuwarmu za ta yi kyau idan muka mai da hankali ga hidimar da muke yi wa Jehobah kuma muka ƙi ra’ayin mutanen duniya game da kuɗi. (Matiyu 11:​29, 30) Hakan zai sa mu gamsu da abin da muke da shi kuma mu kasance da kwanciyar hankali. (Matiyu 6:​31, 32; Romawa 15:13) Ban da haka ma, ba za mu damu da abin duniya ainun ba. (Karanta 1 Timoti 6:​9, 10.) Za mu yi farin ciki don bayarwar da muke yi. (Ayyukan Manzanni 20:35) Kuma irin rayuwar da muke yi za ta ba mu zarafin kasancewa tare da ’yan’uwa da abokan arziki. Ƙari ga haka, za mu ji daɗin barci.​—Mai-Wa’azi 5:12.

“DUKAN KAYAN KĀRIYA NA YAƘI”

18. Me Shaiɗan yake ƙoƙari ya yi mana?

18 Shaiɗan yana son mu yi ma Jehobah rashin biyayya, don haka muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don kada hakan ya faru. Muna “kokawa . . . da mugayen ruhohi.” (Afisawa 6:12) Shaiɗan da aljannunsa ba sa so mu yi farin ciki ko mu yi rayuwa har abada. (1 Bitrus 5:8) Waɗannan ruhohi masu iko suna gāba da mu, amma Jehobah zai taimaka mana don mu yi nasara a yaƙin da muke yi!

19. Ta yaya Afisawa 6:​14-18 suka kwatanta ‘kayan kāriyar’ Kirista?

19 A dā, sojojin yaƙi sukan saka kayan kāriya na yaƙi don su kāre kansu a wurin yaƙi. Mu ma ya kamata mu saka “kayan kāriya na yaƙi” da Jehobah ya ba mu. (Afisawa 6:13) Idan muka yi hakan, za mu sami kāriya. Littafin Afisawa 6:​14-18 sun yi magana game da kayan kāriyar nan, sun ce: “Saboda haka fa ku tsaya da ƙarfi, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci ya zama rigar ƙarfenku ta yaƙi. Shirin kai labari mai daɗi na salama, ya zama kamar takalma a ƙafafunku. Ban da haka ma, bari bangaskiya ta zama garkuwarku wadda za ku ɗauka ku kashe kibiyoyi na wutar Mugun nan da ita. Ku ɗauki hular kwano, wato ceto, da kuma takobin Ruhu, wato Kalmar Allah. Kuna yin addu’a kullum ta wurin ikon Ruhu.”

20. Me ya zama dole mu yi idan muna son ‘kayan kāriyar’ su taimaka mana?

20 Idan soja ya manta da ɗaya daga cikin kayan kāriyarsa kuma ya bar wata gaɓar jikinsa a waje, magabtansa za su iya fakon gaɓar nan don su ji masa rauni. Bai kamata mu manta da ɗaya daga cikin “kayan kāriyar” nan ba idan har muna son su kāre mu. Muna bukatar mu saka kayan a kullum kuma mu riƙa tabbata cewa kayan suna cikin yanayi mai kyau. Za mu ci gaba da kokuwa ko yaƙi har sai an hallakar da duniyar Shaiɗan kuma an cire shi da aljanunsa daga duniya. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:17; 20:​1-3) Saboda haka, idan muna fama da sha’awoyin banza ko akwai wani hali marar kyau da muke ƙoƙari mu daina, kada mu fid da rai, mu ci gaba da ƙoƙari!​—1 Korintiyawa 9:27.

21. Ta yaya za mu yi nasara a yaƙin da muke yi?

21 Ba za mu iya yin nasara a kan Shaiɗan da iyawarmu ba. Amma da taimakon Jehobah, za mu yi nasara! Don mu kasance da aminci, muna bukatar mu yi addu’a ga Jehobah, mu yi nazarin Kalmarsa kuma mu riƙa tarayya da ’yan’uwanmu a ikilisiya. (Ibraniyawa 10:​24, 25) Yin waɗannan abubuwan zai taimaka mana mu kasance da aminci a gaban Allah kuma mu kasance a shirye mu gaya wa mutane abin da muka yi imani da shi.

KA KASANCE A SHIRYE DON KA BAYYANA IMANINKA

22, 23. (a) Ta yaya za mu kasance a shirye kullum don mu bayyana wa mutane imaninmu? (b) Me za mu bincika a babi na gaba?

22 Muna bukatar mu kasance a shirye a kowane lokaci don mu gaya wa mutane abin da muka yi imani da shi. (Yohanna 15:19) Shaidun Jehobah ba sa yin wasu abubuwan da yawancin mutane suke yi. Don haka, za ka iya tambayar kanka: ‘Na fahimci dalilin da ya sa ba ma yin waɗannan abubuwan? Na tabbata cewa abin da Littafi Mai Tsarki da kuma bawan nan mai aminci mai hikima suka faɗa gaskiya ne? Ina alfahari da zama Mashaidin Jehobah? (Zabura 34:2; Matiyu 10:​32, 33) Zan iya bayyana wa mutane imanina?’​—Matiyu 24:45; Yohanna 17:17; karanta 1 Bitrus 3:15.

23 A wasu lokuta muna iya fahimtar abin da za mu yi don kada mu saka hannu a harkokin duniyar nan. Amma a wasu lokuta, ba za mu iya sanin abin da za mu yi ba. Shaiɗan yana son ya yaudare mu a hanyoyi da yawa. Wani abu da yake amfani da shi, shi ne nishaɗi. Ta yaya za mu zaɓi nishaɗin da ya dace? Za mu bincika hakan a babi na gaba.

ƘA’IDODIN LITTAFI MAI TSARKI

1 KIRISTOCI SUNA GOYON BAYAN MULKIN ALLAH

‘Mulkina ba irin na duniya ba ne.’ ​—Yohanna 18:36

Ta yaya za mu nuna cewa ba ma saka hannu a harkokin duniyar nan amma muna goyon bayan Mulkin Allah?

  • Ishaya 2:​2-4; Yohanna 6:15; 1 Bitrus 3:15

    Ba ma yaƙi balle mu yi siyasa.

  • Fitowa 20:​4, 5; 1 Yohanna 5:21

    Ba ma yi wa kowace irin siffa sujada. Alal misali, ba ma sara wa tutar ƙasa.

  • Matiyu 26:52

    Yaƙi yana jawo kashe-kashe. Muna jiran lokacin da Jehobah zai kawo ƙarshen matsalolin duniya gabaki ɗaya.

  • Yohanna 13:​34, 35; 1 Yohanna 3:​10-12

    Duka bayin Jehobah ko daga wace ƙasa ko ƙabila ko yare muka fito, dukanmu ’yan’uwan juna ne. Ba za mu taɓa yin faɗa da juna ba.

2 KIRISTOCI “BA NA DUNIYA BA NE”

“Su ba na duniya ba ne, kamar yadda ni ma ba na duniya ba ne.”​—Yohanna 17:16

Me ya sa muke bukatar mu ƙi saka hannu a harkokin duniyar Shaiɗan?

  • 1 Yohanna 5:19

    Kalmar nan “duniya” tana nufin mutanen da ba su san Allah ba, waɗanda Shaiɗan yake iko da su.

  • Yaƙub 4:4

    Muna so mu zama abokan Jehobah. Kuma muna so mu yi koyi da Yesu a furucinmu da halinmu da kuma ayyukanmu.

3 KIRISTOCI SUNA ƘIN HALAYEN MUTANEN DUNIYA

“Kiyaye zuciyarka da dukan iyakacin ƙoƙari.”​—Karin Magana 4:23

Ta yaya za mu ƙi halayen mutanen duniya?

  • Afisawa 2:2; 1 Yohanna 2:16

    Shaiɗan yana son kai da fahariya da kuma taurin kai. Yana so mutane su gaskata cewa ba sai sun yi biyayya ga Allah ba.

  • 1 Korintiyawa 10:31

    Muna nuna cewa mu ba na duniya ba ne ta wurin abin da muke faɗa da kuma yi. Muna hakan a shawarwarin da muke yankewa a rayuwarmu.

  • 1 Korintiyawa 2:12; 1 Yohanna 4:4

    Idan muna so mu guji halayen duniyar Shaiɗan, muna bukatar mu ci gaba da zama aminan Jehobah kuma mu riƙa tunanin abubuwan da suka dace.

4 KUƊI BA ZAI KĀRE MU KO YA SA MU SAMI KWANCIYAR HANKALI BA

“Yawan kaya ba shi ne samun rai ba.” ​—Luka 12:15

Me zai taimaka mana mu kasance da ra’ayin Jehobah game da kayan duniya?

  • Ayyukan Manzanni 20:35; 1 Timoti 6:​9, 10

    Shaiɗan yana so mu ɗauka cewa jin daɗi da arziki za su sa mu sami kwanciyar hankali. Amma Yesu ya gaya mana cewa za mu sami kwanciyar hankali idan mun zama aminan Jehobah kuma muna taimaka wa mutane.

  • Matiyu 6:​31, 32; Markus 12:​30, 31; Luka 21:​34-36

    Rayuwarmu za ta zama da amfani idan muka mai da hankali ga hidimar da muke yi wa Jehobah. Za mu yi wadar zuci da abin da muke da shi kuma za mu sami kwanciyar hankali.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba