Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/1 pp. 4-6
  • Annabci Game da Almasihu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Annabci Game da Almasihu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Annabce-Annabcen da Suka Cika
  • Sun Jira Zuwan Almasihu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Annabce-annabce Game da Almasihu Sun Nuna Cewa Yesu Ne Almasihu Kuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Sun Samu Almasihu!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Yesu Kristi—Almasihu da Aka Yi Alkawarinsa
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/1 pp. 4-6

Annabci Game da Almasihu

DA SHIKE suna sane da abin da Ishaya da sauran annabawa suka rubuta game da Almasihu, Yahudawa sun yi ɗokin zuwansa. A zamanin Yesu, Yahudawa da yawa ‘suna cikin sauraron’ zuwan Almasihu da ya yi kusa. (Luka 3:15) Abin muhimmanci, annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suna ɗauke da wasu aukuwa masu ban mamaki na rayuwar Almasihu. Babu ɗan adam da ya isa ya annabta irin waɗannan abubuwa ko kuma ya sa su faru a lokacin da Yesu yake duniya.

Cikakken Bayani Game da Haihuwar Almasihu. Ishaya ya annabta cewa budurwa ce za ta haifi Almasihu ko Kristi. Bayan da ya bayyana mu’ujiza game da haihuwar Yesu, manzo Matta ya rubuta: “Dukan wannan fa ya zama domin a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabi, cewa, Duba, budurwa za ta yi juna biyu, za ta haifi ɗa.” (Matta 1:22, 23; Ishaya 7:14) Ishaya ya annabta kuma cewa Kristi zai fito daga zuriyar Dauda, musamman ya ambata Yassa, uban Dauda. Hakika, Yesu ya fito kai tsaye daga zuriyar Dauda. (Matta 1:6, 16; Luka 3:23, 31, 32) Ta haka, kafin haihuwar Yesu, mala’ika Jibra’ilu ya gaya wa uwar Yesu, Maryamu: ‘Ubangiji Allah kuma za ya ba shi kursiyi na ubansa Dauda’— Luka 1:32, 33; Ishaya 11:1-5, 10; Romawa 15:12.

Cikakken Bayani Game da Rayuwar Almasihu. A majami’ar Nazarat, sa’ad da Yesu ya girma, kalmomin da ya karanta da babbar murya daga annabcin Ishaya sun ƙunshi waɗannan: “Ruhun Ubangiji yana bisa gareni, gama ya shafe ni da zan yi shelar bishara ga talakawa.” Ta wajen nuna cewa wannan annabcin yana magana game da shi, Yesu ya ce: “Yau an cika wannan nassi a cikin kunnuwanku.” (Luka 4:17-21; Ishaya 61:1, 2) Ishaya ya annabta cewa Yesu zai bi da waɗanda suke bukatar warkarwa cikin alheri da tawali’u. Matta ya rubuta: “Mutane kuwa dayawa suka bi shi: har ya warkadda su duka, ya kuwa dokace su kada su bayana shi: domin a cika abin da aka faɗi ta bakin Ishaya annabi,. . . Ba za shi yi husuma ba, ba kuwa za shi tada murya ba . . . Rarraunan kara ba za ya karye ta ba.” —Matta 8:16, 17; 12:10-21; Ishaya 42:1-4; 53:4, 5.

Cikakken Bayani Game da Wahalar da Almasihu Zai Sha. Ishaya ya annabta cewa mutane da yawa a Isra’ila ba za su karɓi Almasihu ba amma za ya zama “dutsen tuntube” a garesu. (1 Bitrus 2:6-8; Ishaya 8:14, 15) Hakika, duk da mu’ujizan da Yesu ya yi, mutanen “ba su bada gaskiya gareshi ba, domin magana wadda annabi Ishaya ya faɗi ta cika, Ubangiji, wa ya gaskanta abin da aka ji wurinmu?” (Yohanna 12:37, 38; Ishaya 53:1) Wani dalili kuma da ya sa Yahudawa suka kasance da rashin bangaskiya shi ne imanin da suke da shi cewa Almasihu zai ceci al’ummar daga sarautar Roma kuma ya maida mulki ga zuriyar Dauda a nan duniya. Domin Yesu ya sha wuya kuma ya mutu, Yahudawa da yawa ba su karɓe shi a matsayin Almasihu ba. Amma, Ishaya ya annabta cewa Almasihu zai sha wuya kafin ya zama Sarki.

A littafin Ishaya, Almasihu ya annabta: “Na bada bayana ga masu-bugu . . . ban ɓoye fuskata daga kumya da zubda miyau ba.” Matta ya rubuta abin da ya faru sa’ad da ake gwada Yesu: “Suka tufa miyau a fuskatasa, suka mammare shi: waɗansu kuma suka buge shi da tafin hannuwansu.” (Ishaya 50:6; Matta 26:67) Ishaya ya ce: “Aka wulakance shi, duk da haka ya yi tawali’u, ba ya buɗe bakinsa ba.” Saboda haka, yayin da Bilatus ya yi wa Yesu tambaya game da zargin da Yahudawa suka yi masa, Yesu “ko da magana ɗaya ba ya amsa masa ba: har mai-mulkin ya yi mamaki ƙwarai.”—Ishaya 53:7; Matta 27:12-14; Ayukan Manzanni 8:28, 32-35.

Cikakken Bayani Game da Mutuwar Almasihu. Annabcin Ishaya ya ci gaba da cika a lokacin mutuwar Yesu da kuma bayan mutuwarsa. Ishaya ya annabta: “Tare da masu-mugunta aka yi masa kabari, tare da mawadaci ya ke cikin mutuwarsa kuma.” (Ishaya 53:9) Ta yaya wannan annabci da kamar dai yana da saɓani zai cika? Sa’ad da Yesu ya mutu, an rataye shi tsakanin ’yan fashi biyu. (Matta 27:38) Daga baya attajiri Yusufu na Arimathiya ya ajiye shi a sabon kabari da aka tauna daga dutse. (Matta 27:57-60) A ƙarshe, mutuwar Yesu ta cika wani sashe mai muhimmanci na annabcin Ishaya. Yayin da yake magana game da Almasihu, Ishaya ya ce: “Bawana mai-adilci za ya baratadda masu-yawa; za ya ɗauki kura-kuransu kuma.” Hakika, mutuwar Yesu ta yi tanadin fansa domin a ɗauke nauyin zunubi daga mutane masu aminci. —Ishaya 53:8, 11; Romawa 4:25.

Annabce-Annabcen da Suka Cika

Domin su kafa tabbaci bisa Nassi game da wanda zai zama Almasihu, manzannin da Yesu kansa sun yi ƙauli sosai daga annabcin Ishaya fiye da kowane littafi na Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, ba littafin Ishaya kaɗai ne ya annabta abin da zai faru a gaba ba. Wasu annabce-annabce da suke cikin Nassosin Ibrananci sun cika a kan Yesu, mulkinsa, da kuma abubuwa masu kyau da mulkinsa zai cim ma a nan gaba.a (Ayukan Manzanni 28:23; Ru’ya ta Yohanna 19:10) Da tabbacin cewa waɗannan annabce-annabcen za su cika kuwa? Yesu ya gaya wa Yahudawa da suke sauraronsa: “Kada ku zace na zo domin in warware Attaurat da Annabawa [wato Nassosin Ibrananci]: ban zo domin in warware ba, amma domin in cicika. Gaskiya fa ni ke faɗa maku, Har sama da duniya su shuɗe, ko wasali ɗaya ko ɗigo ɗaya ba za ya shuɗe daga Attaurat ba, sai dukan abu ya cika.” —Matta 5:17, 18.

Bisa ga abubuwan da suka faru a zamaninsa Yesu ya bayyana cikar annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da kuma waɗanda za su faru a nan gaba. (Daniel 9:27; Matta 15:7-9; 24:15) Bugu da ƙari, Yesu da almajiransa sun annabta abubuwa da za su faru bayan zamaninsu da kuma waɗanda muke gani a yau. Talifi na gaba zai tattauna waɗannan da wasu annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da za su cika a nan gaba.

[Hasiya]

a Domin Ƙarin bayani game da annabce-annabce da suka cika a rayuwar Yesu, ka duba Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shafi na 200, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Hoto a shafi na 4]

“Budurwa za ta . . .haifi ɗa”

[Hoto a shafi na 5]

“Ban ɓoye fuskata daga kumya . . . ba.”

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba