Me Ya Sa Za A Kiyaye Jibin Maraice Na Ubangiji?
“Daga wurin Ubangiji na karɓo wannan da na bayar a gareku.”—1 KORINTHIYAWA 11:23.
1, 2. Menene Yesu ya yi a daren Faska ta 33 A.Z.?
ƊA MAKAƊAICI na Jehovah yana wurin. Maza 11 da suka ‘lizimce shi a cikin jarabarsa’ ma suna wurin. (Luka 22:28) A daren Jumma’a ne, 31 ga Maris, 33 A.Z., wata ya haskaka Urushalima. Bai daɗe ba da Yesu Kristi da manzanninsa suka gama bikin Faska. An riga an sallami Yahuda Iskariyoti marar aminci, amma lokaci bai yi ba tukuna domin sauran su watse. Me ya sa? Domin Yesu yana so ya yi wani abu mai muhimmanci ƙwarai. Me ke nan?
2 Da yake marubucin Lingila Matta yana wajen, bari ya gaya mana ko menene ne. Ya rubuta: “Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya, ya karya; ya ba almajiran, ya ce, Ku karɓa, ku ci; wannan jikina ne. Kuma ya ɗauki ƙoƙo, ya yi godiya, ya ba su kuma, ya ce, Dukanku ku sha daga cikinsa; gama wannan jinina ne na alkawari, wanda an zubar domin mutane dayawa zuwa gafarar zunubai.” (Matta 26:26-28) Wannan biki ne da za a yi sa sau ɗaya kawai? Menene manufarsa? Yana da wata ma’ana ce a gare mu a yau?
‘Ku Yi ta Yin Wannan’
3. Me ya sa abin da Yesu ya yi a daren 14 ga Nisan, 33 A.Z., ke da muhimmanci?
3 Abin da Yesu Kristi ya yi a daren 14 ga Nisan, 33 A.Z., ba wani tsautsayi ne ba kawai a rayuwarsa. Manzo Bulus ya tattauna wannan sa’ad da yake rubutu zuwa ga Kiristoci shafaffu a Koranti, inda suke bin tafarkin har bayan shekara 20. Ko da yake Bulus ba ya tare da Yesu da manzanni 11 ɗin a 33 A.Z., babu shakka ya koyi abin da ya faru a sa’ar daga wasu manzanni. Bugu kan ƙari, Bulus ya sami tabbacin bikin nan ta wurin hurarren wahayi. Bulus ya ce: “Daga wurin Ubangiji na karɓo wannan da na bayar a gareku, cewa, Ubangiji Yesu a cikin daren da aka bashe shi ya ɗauki gurasa; sa’anda ya yi godiya, ya kakkarya, ya ce, Wannan jikina ne, wanda shi ke dominku: ku yi wannan abin tunawa da ni. Hakanan kuma ya ɗauki ƙoƙon bayan jibi, ya ce, Wannan ƙoƙo sabon alkawari ne cikin jinina: ku yi wannan, loton da ku ke sha duka, abin tunawa da ni.”—1 Korinthiyawa 11:23-25.
4. Me ya sa Kiristoci ya kamata su kiyaye Jibin Maraice na Ubangiji?
4 Marubucin Lingila Luka ya tabbatar da cewa Yesu ya ba da umurni: “Ku yi wannan abin tunawa da ni.” (Luka 22:19) Waɗannan kalmomi ma an fassara su: “Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.” (Littafi Mai Tsarki Duk da Afokirifa) Sau da yawa ana kiran wannan bikin, Tuna Mutuwar Kristi. Bulus ya kira shi Jibin Maraice na Ubangiji—ya dace a kira shi hakan, da yake an kafa shi da daddare ne. (1 Korinthiyawa 11:20) An umurci Kiristoci su kiyaye Jibin Maraice na Ubangiji. To, me ya sa aka kafa wannan bikin?
Abin da Ya Sa Aka Kafa Shi
5, 6. (a) Wane dalili ne ya sa Yesu ya kafa bikin Tuna Mutuwarsa? (b) Ka ba da wani dalilin da ya sa aka kafa Jibin Maraice na Ubangiji.
5 Dalili ɗaya da ya sa aka kafa bikin Tuna Mutuwarsa ya shafi abu ɗaya da mutuwar Yesu ta cika. Ya mutu domin yana ɗaukaka ikon mallaka na Ubansa na samaniya. Ta haka, Kristi ya tabbatar Shaiɗan Iblis maƙaryaci ne, wanda ya tuhumi mutane cewa suna bauta wa Allah ne domin son kai. (Ayuba 2:1-5) Mutuwar da Yesu ya yi cikin aminci ta fallasa ƙaryar wannan tuhumar kuma ta faranta wa Jehovah zuciya.—Misalai 27:11.
6 Wani dalilin da ya sa aka kafa Jibin Maraice na Ubangiji shi ne domin ya tunasar da mu cewa ta wurin mutuwarsa ta mutum kamiltacce, marar zunubi, Yesu ya ‘ba da ransa abin fansa ga mutane da yawa.’ (Matta 20:28) Lokacin da mutum na farko ya yi wa Allah zunubi, ya ɓatar da kamiltaccen rai da dukan albarkarsa. Amma Yesu ya ce: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yohanna 3:16) Hakika, “hakkin zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai na har abada ce cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.” (Romawa 6:23) Kiyaye Jibin Maraice na Ubangiji na tunasar da mu ƙauna mai yawa da Jehovah tare da Ɗansa suka nuna game da mutuwar Yesu ta hadaya. Lallai muna bukatar nuna godiya ga wannan ƙaunar!
Yaushe Ya Kamata a Yi Shi?
7. Ta yaya Kiristoci shafaffu suka ci daga isharar bikin Tuna Mutuwarsa ‘kowanne lokaci’?
7 Game da Jibin Maraice na Ubangiji, Bulus ya ce: “Kowanne lokacin da ku ke cin wannan gurasa, kuna kuwa shan ƙoƙon, kuna shelar mutuwar Ubangiji har ya zo.” (1 Korinthiyawa 11:26) Kiristoci shafaffu ɗai-ɗai za su ci gaba da cin isharar Abin Tunawa har mutuwarsu. Ta haka, a gaban Jehovah Allah, da kuma duniyar za su ci gaba da yin shelar bangaskiyarsu ga tanadin da Allah ya yi na hadayar fansar Yesu.
8. Har yaushe rukunin shafaffu za su kiyaye Jibin Maraice na Ubangiji?
8 Har yaushe rukunin Kiristoci shafaffu za su kiyaye bikin Tuna Mutuwar Kristi? “Har ya zo,” in ji Bulus, watau, yana nufin cewa za a ci gaba da wannan bikin har dawowar Yesu ya karɓi mabiyansa shafaffu zuwa sama ta wurin tashin matattu a ‘[bayyanuwarsa, NW ].’ (1 Tassalunikawa 4:14-17) Wannan ya yi daidai da kalmomin Yesu wa manzanni 11 masu aminci: “Kadan na tafi na shirya muku wuri kuma, sai in sake dawowa, in karɓe ku wurin kaina; domin wurin da ni ke, ku zauna kuma.”—Yohanna 14:3.
9. Menene kalmomin Yesu da ke Markus 14:25 ke nufi?
9 Lokacin da Yesu ya kafa bikin Tuna Mutuwarsa, ya yi nuni ga ƙoƙon giya kuma ya gaya wa manzanninsa masu aminci: “Ba ni ƙara sha ruwan ’ya’yan kuringar inabi ba, har wancan rana da zan sha shi sabo cikin mulkin Allah.” (Markus 14:25) Tun da yake Yesu ba zai sha ruwan inabi na zahiri ba a sama, lallai yana maganar wartsakewa da ake samu daga ruwan inabi ne. (Zabura 104:15; Mai-Wa’azi 10:19) Kasancewa tare a Mulkin zai zama abin farin ciki ne da shi da mabiyansa suke da tsammaninsa ƙwarai.—Romawa 8:23; 2 Korinthiyawa 5:2.
10. Sau nawa ya kamata a yi bikin Tuna Mutuwar?
10 Ya kamata ne a yi bikin mutuwar Yesu kowanne wata, mako, ko kuma kowacce rana? A’a. Yesu ya kafa Jibin Maraice na Ubangiji kuma an kashe shi a ranar Faska, wadda ake kiyayewa ‘abin tuna’ da ceton Isra’ila daga bauta a ƙasar Masar a shekara ta 1513 K.Z. (Fitowa 12:14) Ana yin Faskar sau ɗaya ne a shekara, a ranar 14 ga watan Nisan na Yahudawa. (Fitowa 12:1-6; Leviticus 23:5) Wannan ya nuna cewa ya kamata a yi bikin mutuwar Yesu kowanne lokaci kamar Faska—shekara shekara—ba kowanne wata, mako, ko kuma kowacce rana ba.
11, 12. Menene tarihi ya nuna game da biki na farko na Tuna Mutuwar?
11 Saboda haka, ya dace a yi bikin Tuna Mutuwarsa shekara shekara a ranar 14 ga Nisan. Wata majiya ta ce: “Ana kiran Kiristoci da suke Asiya Ƙarama Fourteenthers [masu bin ranar 14 ga Nisan] domin al’adarsu ta yin bikin pascha [Jibin Maraice na Ubangiji] da ba ta canzawa daga ranar 14 ga Nisan . . . Ranar za ta iya kasancewa ranar Jumma’a ko kuma kowacce cikin ranakun mako.”—The New Schaff-Herzog Encyclopedia of Religious Knowledge, Littafi na IV, shafi na 44.
12 Da yake zance game da abin da ake yi a ƙarni na biyu A.Z., ɗan tarihin J. L. von Mosheim ya ce waɗannan Fourteenthers suna kiyaye bikin Tuna Mutuwar a ranar 14 ga Nisan domin “suna bin misalin Kristi shi ne ikon doka.” Wani ɗan tarihi ya ce: “Yadda aka yi amfani da Fourteenthers wa cocin Asiya haka ne ma wa cocin Urushalima. A ƙarni na biyu waɗannan cocin a lokacin Faskarsu a ranar 14 ga Nisan suna bikin fansa da mutuwar Kristi ta kafa.”—Studia Patristica, Littafi na V, 1962, shafi na 8.
Manufar Gurasar
13. Wace irin gurasa ce Yesu ya yi amfani da ita a kafa Jibin Maraice na Ubangiji?
13 Yayin da Yesu ya kafa bikin Tuna Mutuwarsa, “ya ɗauki gurasa, sa’anda ya sa albarka, ya karya, ya ba [manzannin].” (Markus 14:22) Gurasar da ake da ita a lokacin, wadda aka yi amfani da ita ce a bikin Faska. (Fitowa 13:6-10) Domin marar yisti ne, kamar waina take marar ƙwari da za a iya rarrabawa. Lokacin da Yesu ya yi tanadin gurasa wa dubbai ta wurin mu’ujiza, ita ma mai sauƙin rabuwa ce da za a iya rarrabawa. (Matta 14:19; 15:36) Saboda haka, raba gurasar bikin Tuna Mutuwarsa ba ta da wata ma’ana ta ruhaniya.
14. (a) Me ya sa ya dace gurasar Jibin ta zama marar yisti? (b) Wace irin gurasa za a saya ko kuma a gasa don a yi amfani da ita a Jibin Maraice na Ubangiji?
14 Game da gurasa da aka yi amfani da ita a kafa bikin Tuna Mutuwarsa, Yesu ya ce: “Wannan jikina ne, wanda shi ke dominku.” (1 Korinthiyawa 11:24; Markus 14:22) Daidai ne da gurasar ba ta da yisti. Me ya sa? Domin yisti zai iya nufin mummuna, mugunta, ko kuma zunubi. (1 Korinthiyawa 5:6-8) Gurasar tana wakiltar kamiltaccen jikin Yesu, marar zunubi da aka ba da hadayarsa don fansa. (Ibraniyawa 7:26; 10:5-10) Shaidun Jehovah suna tunawa da wannan kuma suna bin tafarkin da Yesu ya kafa na yin amfani da gurasa marar yisti a bikin Tuna Mutuwarsa. A wasu lokatai, sukan yi amfani da matzos na Yahudawa da ba shi da ƙarin abubuwan ɗanɗano, kamar su albasa ko ƙwai. Idan ba haka ba, za a iya gasa gurasa marar yisti da garin dawa (ko alkama, idan akwai) da aka dama da ruwa. Ya kamata a yanke ƙullun kada ya yi tauri ainun sai a gasa da ɗan mai cikin kasko.
Manufar Ruwan Inabi
15. Menene ke cikin ƙoƙon da Kristi ya yi amfani da shi a kafa Tuna Mutuwarsa?
15 Bayan zagaya da gurasar marar yisti, Yesu ya ɗauki ƙoƙon, “ya yi godiya, ya ba [manzannin]: dukansu suka sha daga cikinsa.” Yesu ya yi bayani: “Wannan jinina ne na alkawari, wanda an zubar domin mutane dayawa.” (Markus 14:23, 24) Menene ke cikin ƙoƙon? Ruwan inabi ne, ba ruwan ’ya’yan inabi mai zaki ba. Sa’ad da Nassosi sun yi nuni ga ruwan inabi, ba ruwan ’ya’yan inabi mai zaki ba ake nufi. Alal misali, ruwan inabi, ba ruwan ’ya’yan inabi mai zaki ne zai fashe “tsofaffin salkuna” ba, yadda Yesu ya ce. Maƙiyan Kristi kuma sun tuhume shi cewa “mai-zarin sha” ne. Hakan tuhuma ce marar ma’ana idan ruwan inabi ɗin ruwan ’ya’yan inabi mai zaki ne. (Matta 9:17; 11:19) Ruwan inabi aka yi amfani da ita a lokacin Faska, kuma Kristi ya yi amfani da ita a kafa bikin Tuna Mutuwarsa.
16, 17. Wace irin ruwan inabi ne ya dace don bikin Tuna Mutuwar Yesu, kuma me ya sa?
16 Jan ruwan inabi ne kawai ya dace ya zama isharar abin da ke cikin ƙoƙon ke wakilta, watau, jinin Yesu da aka zubar. Shi kansa ya ce: “Wannan jinina ne na alkawari, wanda an zubar domin mutane dayawa.” Sai kuma manzo Bitrus ya rubuta: “[Kiristoci shafaffu] kun sani aka fanshe ku, ba da abubuwa masu-lalacewa ba, da su azurfa ko kuwa zinariya, daga cikin irin zamanku na banza abin gadō daga ubanninku; amma da jini mai-daraja, kamar na ɗan rago marar-aibi, marar-cikas, watau jinin Kristi.”—1 Bitrus 1:18, 19.
17 Babu shakka cewa jan ruwan inabi ne Yesu ya yi amfani da ita lokacin da yake kafa Tuna Mutuwarsa. Amma wasu jan ruwan inabi na zamanin nan ba su dace ba domin suna da abubuwa da ake sakawa ciki su daɗa ɗanɗanonta kamar su jiƙo da sauransu. Jinin Yesu cikakke ne da ba ya bukatar a daɗa wani abu a ciki. Saboda haka, irin waɗannan ruwan inabi da aka sa wasu abubuwan ɗanɗano ciki ba za su dace ba. Ya kamata a zuba ruwan inabi marar zaki da ba a daɗa masa kome ba a cikin ƙoƙon bikin Tuna Mutuwar.
18. Me ya sa Yesu bai yi mu’ujiza game da gurasa da giyar Tuna Mutuwar ba?
18 Sa’ad da Yesu yake kafa jibin, bai yi wata mu’ujiza ba, ya canza isharar zuwa jikinsa da jininsa na zahiri. Cin naman mutum da shan jininsa zai zama nyam-nyamci da dokar Allah ta haramta. (Farawa 9:3, 4; Leviticus 17:10) A maraicen, Yesu yana da jikinsa da dukan jininsa. Ya ba da jikinsa kamiltaccen hadaya, da jininsa da aka zubar washegari da rana a ranar 14 ga Nisan na Yahudawa. Saboda haka, gurasa da giyar bikin Tuna Mutuwarsa ishara ce, da ke wakilta jikin Kristi da jininsa.a
Bikin Tuna Mutuwarsa —Jibin Tarayya Ne
19. Me ya sa za a iya yin amfani da kofi da faranti fiye da ɗaya a bikin Jibin Maraice na Ubangiji?
19 Sa’ad da Yesu ya kafa bikin Tuna Mutuwarsa, ya ce manzanninsa masu aminci su sha daga ƙoƙo ɗaya. Lingilar Matta ta ce: “[Yesu] ya ɗauki ƙoƙo, ya yi godiya, ya ba su kuma, ya ce, Dukanku ku sha daga cikinsa.” (Matta 26:27) Yin amfani da “ƙoƙo” ɗaya kawai ba da yawa ba, ba wata matsala ba tun da mutanen 11 ne kawai da hakika suna zama kewaye da tebur ɗaya ne kuma ƙoƙo ɗaya zai isa, daga wannan zuwa wancan. A wannan shekarar, miliyoyi za su taru a ikilisiyoyi 94,000 na Shaidun Jehovah domin bikin Jibin Maraice na Ubangiji a dukan duniya. Da yake mutane da yawa ne za su halarci wannan bikin a dare ɗaya, ba zai isa a yi amfani da ƙoƙo ɗaya ba. Ana bin ƙa’ida ɗaya ne a manyan ikilisiyoyi ta yin amfani da ƙoƙo da yawa don zagaya da wannan isharar a gaban jama’a a ɗan lokaci. Haka ma za a iya amfani da fiye da faranti ɗaya wajen zagayawa da gurasar. Babu wani abu cikin Nassosi da ya nuna cewa ƙoƙon ko kuma moɗa sai an yi mata wani zane. Amma, ƙoƙon da farantin ya kamata su dace da darajar bikin. Zai fi kyau idan ba a cika moɗar maƙil da giyar ba don kada ta dinga zuba yayin da ake zagayawa da ita.
20, 21. Me ya sa za mu iya ce Abin Tunawa jibin tarayya ne?
20 Ko da yake za a iya amfani da fiye da faranti ɗaya na gurasa da moɗa ɗaya na giyar, bikin Tuna Mutuwarsa jibin tarayya ne. A Isra’ila ta dā, mutum zai iya kawo jibin tarayya ta kawo dabba zuwa wuri mai tsarki na Allah, inda ake yanka. Za a ƙone ɓarinsa a kan bagadi, wani ɓari kuma domin firist da yake hidima wani kuma domin ’ya’yan Haruna firistoci da mai kawo hadayar tare da iyalinsa su ma su ci daga jibin. (Leviticus 3:1-16; 7:28-36) Bikin Tuna Mutuwarsa ma jibin tarayya ne domin ana tarayya ciki.
21 Jehovah yana wajen wannan jibin tarayya da yake shi ne Mawallafinsa. Yesu ne hadayar, Kiristoci shafaffu suna ci daga isharar da yake suna ciki. Ci daga tebur na Jehovah yana nufin cewa masu cin suna zaman zumunci da shi. Domin haka, Bulus ya rubuta: “Ƙoƙon albarka wanda mu ke albarkatasa, ba zumunta ta jinin Kristi ba ne? Dunƙulen gurasa da mu ke karkarye, ba zumuntar jikin Kristi ba ne? da shi ke fa mu, da mu ke dayawa, dunƙule ɗaya ne, jiki ɗaya ne: gama mu duka muna tarayya daga cikin dunƙule ɗaya.”—1 Korinthiyawa 10:16, 17.
22. Waɗanne tambayoyi ne game da bikin Tuna Mutuwar Yesu har ila za a tattauna?
22 Jibin Maraice na Ubangiji ne kawai bikin addini na shekara shekara da Shaidun Jehovah suke yi. Wannan ya dace domin Yesu ya umurci mabiyansa: “Ku yi wannan a tunawa da ni.” A bikin Tuna Mutuwarsa, muna bikin mutuwar Yesu, mutuwar da ta ɗaukaka ikon mallaka na Jehovah. Yadda mun riga mun lura, a wannan jibin tarayya, gurasar tana nufin jikin Kristi da aka ba da hadaya, giyar kuma jininsa da aka zubar. Amma, mutane kalilan ne suke ci daga gurasa suke sha daga giyar. Me ya sa? Bikin Tuna Mutuwarsa yana da ma’ana kuwa ga miliyoyin da ba sa ci? Hakika, me ya kamata Jibin Maraice na Ubangiji ya nufa a gare ka?
[Hasiya]
a Dubi Littafi na 2, shafi na 271, na Insight on the Scriptures, da Shaidun Jehovah suka buga.
Menene Amsarka?
• Me ya sa Yesu ya kafa Jibin Maraice na Ubangiji?
• Yaya za a yi bikin Tuna Mutuwar Yesu?
• Mecece manufar gurasa marar yisti na Tuna Mutuwar?
• Mecece giyar bikin Tuna Mutuwar take wakilta?
[Hoto a shafi na 11]
Yesu ya kafa Jibin Maraice na Ubangiji