An Fallasa Tushen Mugunta!
AƘARNI na farko, Yahudawa da yawa suna jiran zuwan Almasihu da aka yi alkawarinsa. (Yohanna 6:14) Da Yesu ya zo duniya, ya kawo ta’aziyya da ƙarin fahimi na Kalmar Allah. Ya warkar da masu ciwo, ya ciyar da mayunwata, ya tsawata wa iskar sai ta lafa ta yi tsit, kuma ya ta da matattu. (Matta 8:26; 14:14-21; 15:30, 31; Markus 5:38-43) Ya faɗi zantuttukan Jehobah kuma ya yi alkawarin rai madawwami. (Yohanna 3:34) Ta wurin abin da ya faɗa kuma ya yi, Yesu ya nuna sarai cewa shi ne Almasihu, wanda zai ’yantar da ’yan adam daga zunubi da dukan sakamakonsa na mugunta.
Ya kamata shugabannin addini na Yahudawa su zama mutanen farko da za su marabci Yesu, su saurare shi, kuma su amince da ja-gorarsa da farin ciki. Amma ba su yi hakan ba. Maimakon haka, sun tsane shi, sun tsananta masa, kuma suka ƙulla su kashe shi!—Markus 14:1; 15:1-3, 10-15.
Ya dace da Yesu ya hukunta waɗannan mutanen. (Matta 23:33-35) Amma, ya fahimci cewa da akwai wani da yake da alhakin muguntar da ke zuciyarsu. Ya ce musu: “Ku na ubanku Shaiɗan ne, ƙyashe ƙyashe na ubanku kuma kuna da nufi ku yi. Shi mai-kisan kai ne tun daga farko, ba ya tsaya a kan gaskiya ba, domin babu gaskiya a cikinsa. Sa’anda ya ke yin ƙarya, don kansa ya ke yi: gama maƙaryaci ne shi, da uban ƙarya kuma.” (Yohanna 8:44) Ko da yake Yesu ya fahimci cewa ’yan adam suna iya yin ayyukan mugunta, ya faɗi ainihin tushen mugunta, wato, Shaiɗan Iblis.
Sa’ad da ya ce Shaiɗan “ba ya tsaya a kan gaskiya ba,” Yesu ya nuna cewa wannan ruhun a dā bawan Allah ne mai aminci amma ya bijire daga wannan tafarki na gaskiya. Me ya sa Shaiɗan ya yi wa Jehobah tawaye? Domin ya yi tunanin neman girma a zuciyarsa kuma ya yi ƙyashin bauta da ya kamata a yi wa Allah shi kaɗai.a—Matta 4:8, 9.
An ga tawayen Shaiɗan a lambun Adnin sa’ad da ya ruɗi Hauwa’u ta ci ’ya’yan itace da aka hana su. Ta wurin ƙarya ta farko da kuma tsegumin Jehobah da ya yi, Shaiɗan ya mai da kansa “uban ƙarya.” Ƙari ga haka, ta wurin sa Adamu da Hauwa’u su yi rashin biyayya, ya sa zunubi ya yi sarauta a kansu, ya kai su ga mutuwa da mutuwar tsararraki ta gaba. Da haka, Shaiɗan ya mai da kansa “mai-kisan kai,” hakika, mai kisan kai da ya fi kowane!—Farawa 3:1-6; Romawa 5:12.
Mugun tasirin Shaiɗan ya kai har ga duniya ta ruhu, inda ya rinjayi wasu mala’iku su bi shi su yi tawaye. (2 Bitrus 2:4) Kamar Shaiɗan, waɗannan mugayen ruhohi sun soma son ’yan adam a hanyar da ba ta dace ba. Amma, nasu sha’awa na lalata ne ya kawo mugun sakamako mai lahani.
Duniya ta Cika da Mugunta
Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Lokacin da mutane suka soma yawaita a duniya, aka haifa masu ’ya’ya mata kuma, sai ’ya’yan Allah suka ga yan mata na mutane kyawawa ne; suka ɗauko wa kansu mata dukan waɗanda suka zaɓa.” (Farawa 6:1, 2) Su waye ne waɗannan “’ya’yan Allah”? Halittu na ruhu ne, ba ’yan adam ba. (Ayuba 1:6; 2:1) Ta yaya muka sani? Don ’yan adam sun yi wajen shekaru 1,500 suna aure, saboda haka ba a bukata a ambata ta a hanya ta musamman. Saboda haka, da labarin ya ce “ya’yan Allah” da suka canja kamaninsu kuma suka ɗauki “yan mata na mutane” suka yi jima’i da su, yana nuna sarai cewa abin da suka yi bai dace ba.
’Ya’yan da suka haifa sun nuna cewa irin wannan nasaba bai dace ba. Ana kiransu Nefilawa, sun yi girma sun zama ƙattai. Mugaye ne masu cin zalin mutane. Hakika, ‘Nefilin’ na nufin “mai ƙayarwa,” ko “waɗanda suke ƙayar da wasu.” An kwatanta waɗannan azzalumai da “ƙarfafan mutane waɗanda ke na dā, mutane masusuna.”—Farawa 6:4.
Ƙattan da ubansu mugaye ne sosai. “Duniya kuwa ta ɓāci a gaban Allah . . . kuma ta cika da zalunci,” in ji Farawa 6:11. Hakika, ’yan adam sun bi hanyoyin mugunta na sababbin halittun da ke tsakaninsu.
Ta yaya ne Ƙattan da kuma ubaninsu suka kasance da mugun tasiri sosai bisa ’yan adam? Ta wurin yin abin da zai motsa hali da sha’awoyin zunubi na ’yan adam. Menene sakamakon haka? “Dukan masu-rai sun ɓata tafarkinsu a duniya.” A ƙarshe, Jehobah ya halaka wancan duniyar da Rigyawa ta dukan duniya, ya bar Nuhu adali da iyalinsa. (Farawa 6:5, 12-22) Amma mala’ikun suka koma duniyar ruhu cikin kunya. Da yake su lalatattun aljannu ne, sun ci gaba da yin hamayya da Allah da iyalinsa na mala’iku masu aminci. Kamar dai tun daga lokacin ne Allah ya hana waɗannan miyagun ruhohi su canja zuwa kamanin ’yan adam. (Yahuda 6) Duk da haka, suna da iko sosai a harkokin ’yan adam.
An Fallasa Mugun Sosai!
An bayyana yawan mugun tasirin Shaiɗan a 1 Yohanna 5:19, wadda ta ce: ‘Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.’ Iblis yana ja-gorar ’yan adam zuwa ƙarin wahala. Hakika, ya ƙudurta fiye da dā ya yi ɓarna. Me ya sa? Domin an kawar da shi da aljannu daga sama bayan an kafa Mulkin Allah a shekara ta 1914. Littafi Mai Tsarki ya annabta game da wannan: “Kaiton duniya . . . domin Shaiɗan ya sauko wajenku, hasala mai-girma kuwa gareshi, domin ya sani sauran zarafinsa kaɗan ne.” (Ru’ya ta Yohanna 12:7-12) To, ta yaya Shaiɗan yake nuna ikonsa bisa ’yan adam a yau?
Shaiɗan yana haka musamman ta wajen gabatar da halin da ke ja-gorar yadda mutane suke tunani da kuma ayyuka. Ya dace da Afisawa 2:2 ta kira Iblis “sarkin ikon sararin sama, ruhun [ko halin] da ke aikawa yanzu a cikin ’ya’yan kangara.” Maimakon ya ƙarfafa tsoron Allah da yin nagarta, wannan “ruhun” na kawo tawaye ga Allah da mizanansa. Ta hakan Shaiɗan da aljannunsa suna gabatar da kuma ɗaukaka mugunta da ’yan adam suke yi.
“Ka Kiyaye Zuciyarka”
Ɗaya cikin wannan “ruhun” shi ne hotunan batsa, wanda ke ta da sha’awar lalata da bai dace ba kuma ya sa halin da ba daidai ba ya kasance da ban sha’awa. (1 Tassalunikawa 4:3-5) Fyaɗe, wulakanci, yin jima’i da dabba, da yin lalata da yara, suna cikin abubuwa da ake gani a hotunan batsa. Ko da yake kamar ba ta da lahani, hotunan batsa na yi wa waɗanda suke kallonsu ko karanta su lahani ta wajen zama jininsu, kuma tana mai da su masu biyan bukatunsu na jima’i ta wajen kallonsu.b Mugun abu ne da ke ɓata dangantakar mutum da ’yan adam da kuma Allah. Batsa na nuna mugun hali na aljannu da suka gabatar da ita, wato, ’yan tawaye da sha’awoyinsu na jima’i ya soma kafin Rigyawa na zamanin Nuhu.
Da dalili mai kyau ne Sulemanu mutum mai hikima ya ba da gargaɗi: “Ka kiyaye zuciyarka gaba da dukan abin da ka ke kiyayewa: gama daga cikinta mafitan rai su ke.” (Misalai 4:23) Kiyaye zuciyarka daga tarkon batsa yana nufin canja tashan talabijin ko kuma kashe kwamfuta sa’ad da irin waɗannan hotuna suka fito, kumayana da muhimmanci ka aikata nan da nan! Ka ɗauki kanka a matsayin soja da yake ƙoƙarin ya kauce wa harbi. Shaiɗan yana son ya harbi zuciyarka ta alama, inda motsawarka da sha’awoyinka suke kuma yana son ya ɓata shi.
Kana bukatar ka kāre zuciyarka daga son mugunta, domin Iblis ya san cewa Jehobah yana ƙin masu-son zalunci’.’ (Zabura 11:5) Ba sai Shaiɗan ya sa ka yi ayyukan mugunta kafin ka zama maƙiyin Allah ba; zai sa ka so mugunta. Ba tsautsayi ba ne sau da yawa ana gabatar da mugunta, yawanci masu ɗauke da jigon rukunin asiri a wasan talabijin. Ƙattan sun riga sun mutu, amma halayensu har ila yana ko’ina! Nishaɗin da ka zaɓa yana nuna cewa kana tsayayya da ƙullin Shaiɗan?—2 Korinthiyawa 2:11.
Yadda Za Mu Tsayayya wa Mugun Tasirin Shaiɗan
Zai iya kasance da wuya a bi da ikon mugunta. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa waɗanda suke ƙoƙarin su faranta wa Allah rai suna kokawa da “rundunai masu-ruhaniya na mugunta,” da kuma nasu jiki na ajizanci. Don mu ci nasara a wannan kokawar kuma mu samu tagomashin Allah, muna bukatar mu yi amfani da tanadin da Allah yake yi.—Afisawa 6:12; Romawa 7:21-25.
Wannan tanadin ya ƙunshi ruhu mai tsarki na Allah, ikon da ya fi ƙarfi a sararin samaniya. Manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci a ƙarni na farko: “Ba ruhun duniya muka karɓa ba, amma ruhun da ke daga wurin Allah.” (1 Korinthiyawa 2:12) Waɗanda ruhun Allah ke yi musu ja-gora suna son abin da Allah ke so kuma suna ƙin abin da Allah ya ƙi. (Amos 5:15) Ta yaya mutum zai sami ruhu mai tsarki? Musamman ta wurin addu’a, da nazarin Littafi Mai Tsarki, don ta ruhu mai tsarki ne aka rubuta shi, da kuma tarayya mai kyau da waɗanda suke ƙaunar Allah da gaske.—Luka 11:13; 2 Timothawus 3:16; Ibraniyawa 10:24, 25.
Ta wurin yin amfani da waɗannan tanadodi na Allah, za ka soma yafa “dukan makamai na Allah,” wanda shi ne kariya kaɗai da muke da shi a kan “dabarun Shaiɗan.” (Afisawa 6:11-18) Ya fi gaggawa yanzu mu yi amfani da waɗannan tanadodi. Ta yaya?
Ƙarshen Mugunta Ya Kusa!
Mai zabura ya ce: “Lokacin da masu-mugunta suna tsiro kamar ciyawa, Sa’anda dukan masu-aikin mugunta suna yabanya: Domin su hallaka ke nan har abada.” (Zabura 92:7) Hakika, yadda yake a zamanin Nuhu, ƙaruwar mugunta ya tabbatar da cewa hukuncin Allah ya kusa ba kawai ga mugaye ba amma kuma ga Shaiɗan da aljannunsa, waɗanda za a saka cikin yanayin rashin aiki kafin a halaka su gaba ɗaya. (2 Timothawus 3:1-5; Ru’ya ta Yohanna 20:1-3, 7-10) Wanene zai zartar da wannan hukunci? Yesu Kristi ne, wanda muka karanta game da shi: “Dalilin bayyanuwar Ɗan Allah ke nan, shi halaka ayyukan Shaiɗan.”—1 Yohanna 3:8.
Kana son ka ga ƙarshen mugunta? Idan haka ne, alkawuran da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su ƙarfafa ka. Babu wani littafin kuma da ya fallasa Shaiɗan wanda shi ne tushen mugunta, kuma babu wani littafin da ya nuna yadda za a kawar da shi da dukan miyagun ayyukansa. Muna aririce ka ka sami cikakken sani na Littafi Mai Tsarki don ka karē kanka daga mugun tasirin Shaiɗan yanzu kuma ka sami begen rayuwa a duniyar da babu mugunta.—Zabura 37:9, 10.
[Hasiya]
a Ba a san ainihin sunan mala’ikan da ya zama Shaiɗan ba. Sunayen nan “Shaiɗan” da “Iblis” suna nufin “Maƙaryaci” da “Ɗan Hamayya.” A wasu hanyoyi, tafarkin Shaiɗan ya yi daidai da na sarkin Tyre na dā. (Ezekiel 28:12-19) Dukansu sun soma da kyau amma daga baya suka soma nuna girman kai.
b Ka duba talifofi “Pornography—Harmless or Harmful” a cikin Awake na 22 ga Yuli, 2003 da Shaidun Jehobah suka wallafa.
[Box/Hoto a shafi na 6]
Labaran dā da ke da Kashin Gaskiya
An sami labarai game da shahararru da ake ɗaukansu alla, gwarzaye, da rigyawa a cikin tatsuniyoyi na dā a dukan duniya. Alal misali, labarin Gilgamesh na Akkadiyawa ya ambaci rigyawa, jirgin ruwa, da waɗanda suka tsira. An kwatanta Gilgamesh an ce shi kansa jarabbabe ne, mugun alla ne, wanda rabi alla ne, rabi mutum. Tsatsuniyar mutanen Aztec ta yi maganar duniya ta dā da gwarzaye suke ciki da kuma rigyawa mai girma. Tatsuniyar mutanen Jamus na arewa ta kwatanta zamanin gwarzaye da wani mutum mai hikima da ake kira Bergelmir wanda ya gina babban jirgi kuma ya ceci kansa da matarsa. Waɗannan labaran sun tabbatar da gaskiyar Littafi Mai Tsarki cewa dukan ’yan adam sun fito daga waɗanda suka tsira daga rigyawar da ta halaka muguwar duniya ta dā.
[Picture]
Dutsen da aka rubuta labarin Gilgamesh
[Inda aka Dauko]
Jami’ar ma’adana, Jami’ar Pennsylvania (neg. # 22065)
[Hoto a shafi na 5]
Mutane a yau suna nuna halayen Ƙattai
[Hoto a shafi na 7]
Cikakken sani yana karē mu daga tasirin mugunta