Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 5/1 pp. 20-25
  • A Ina Za A Sami Ta’aziyya Ta Gaske?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • A Ina Za A Sami Ta’aziyya Ta Gaske?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Bi da Tushen Matsalolin
  • Ta’aziyya ga Mutane da Suke Wahala
  • Ta’aziyya da Aka Yi Tanadinta ta Wurin Kristi
  • Ruhu Mai Tsarki Mai Ta’aziyya
  • Taimako Lokacin Matsi Mai Tsanani
  • Ka Yi Wa Masu Makoki Ta’aziyya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Yadda Allah Yake Karfafa Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Ka “Yi Wa Dukan Masu-makoki Ta’aziyya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Dogara Ga Jehobah, “Allah Na Dukan Ta’aziyya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 5/1 pp. 20-25

A Ina Za A Sami Ta’aziyya Ta Gaske?

“Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Kristi . . . da ke yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.”—2 KORINTHIYAWA 1:3, 4.

1. Waɗanne yanayi za su iya sa mutane su samu bukata mai girma ta ta’aziyya?

CIWO mai naƙasar da mutum zai iya sa ya ji rayuwarsa ba ta da amfani. Girgizar ƙasa, hadari, da kuma yunwa na sa mutane su zama tsiyayyu. Wataƙila yaƙi zai iya haddasa mutuwar wani cikin iyali, halaka gidaje, ko kuma sa mutane su gudu su bar gidajensu. Rashin yin gaskiya kuma na iya sa mutane su ji babu inda za su iya samun sauƙi. Waɗanda irin waɗannan abubuwan sun shafe su suna bukatar ta’aziyya da gaggawa. A ina za a iya same ta?

2. Me ya sa ta’aziyya da Jehovah yake tanadinta ba ta da ta biyunta?

2 Wasu mutane da ƙungiyoyi suna ƙoƙarin su kawo ta’aziyya. Ana fatan a ji kalmomi na alheri. Ba da gudummawar abubuwan jiki na kawo gamsuwa ta ɗan lokaci ne kawai. Amma Jehovah ne kaɗai, Allah na gaskiya zai iya kawar da dukan haɗari kuma ya kawo irin taimakon da ake bukata domin kada irin masifar nan ta sake aukuwa. Littafi Mai Tsarki ya faɗi game da shi: “Albarka ga Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Kristi, Uban jiyejiyenƙai, Allah na dukan ta’aziyya; shi da ke yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu, har da za mu iya ta’azantarda waɗanda ke cikin kowane irin ƙunci, ta wurin ta’aziyya wadda mu da kanmu muka ta’azantu da ita daga wurin Allah.” (2 Korinthiyawa 1:3, 4) Ta yaya Jehovah yake ta’azantar da mu?

Bi da Tushen Matsalolin

3. Ta yaya ta’aziyya da Allah ke bayar ke taɓa tushen matsalolin mutane?

3 Dukan ’yan Adam sun gāji ajizanci domin zunubin Adamu, kuma wannan ya jawo matsaloli da yawa da a ƙarshe suka kai ga mutuwa. (Romawa 5:12) Yanayin ya ƙara muni domin Shaiɗan Iblis ne “mai-mulkin wannan duniya.” (Yohanna 12:31; 1 Yohanna 5:19) Ba kawai Jehovah ya nuna baƙin ciki game da mummunar yanayi da mutane ke fuskanta ba. Ya aika da Ɗansa makaɗaici abin fansa ya yi tanadin ceto, Ya gaya mana cewa za mu iya samun sauƙi daga sakamakon zunubin Adamu idan muka ba da gaskiya ga Ɗansa. (Yohanna 3:16; 1 Yohanna 4:10) Allah kuma ya annabta cewa Yesu Kristi, wanda aka ba wa iko a sama da kuma a duniya, zai halaka Shaiɗan da kuma dukan mugun zamaninsa.—Matta 28:18; 1 Yohanna 3:8; Ru’ya ta Yohanna 6:2; 20:10.

4. (a) Menene Jehovah ya yi tanadinsa don ya ƙarfafa dogararmu cikin alkawuransa na kawo sauƙi? (b) Ta yaya Jehovah yake taimakonmu mu fahimci lokacin da za a samu sauƙin?

4 Domin ya ƙarfafa dogararmu game da alkawuransa, Allah yana da ajiyar tabbaci mai yawa cewa duk abin da ya annabta zai cika. (Joshua 23:14) Ya haɗa a cikin labarin Littafi Mai Tsarki na abin da ya yi ya ceci bayinsa daga yanayin da marar yiwuwa ne a wajen mutum. (Fitowa 14:4-31; 2 Sarakuna 18:13–19:37) Kuma ta wurin Yesu Kristi, Jehovah ya nuna cewa ƙudurinsa ya haɗa da warkar da mutane daga “kowanne irin rashin lafiya,” har ma da tashin matattu. (Matta 9:35; 11:3-6) Yaushe ne dukan wannan zai faru? A amsa wannan, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da kwatancin kwanaki na ƙarshe na wannan tsohon zamani, da ke kasancewa kafin sabuwar sammai na Allah da sabuwar duniya. Kwatancin Yesu ya yi daidai da lokacin da muke ciki.—Matta 24:3-14; 2 Timothawus 3:1-5.

Ta’aziyya ga Mutane da Suke Wahala

5. Yayin da yake ta’azantar da Isra’ila ta dā, menene Jehovah ya jawo hankalinsu a kai?

5 Daga yadda Jehovah ya bi da Isra’ila ta dā, muna koyon yadda ya yi musu ta’aziyya a lokatan wahala. Ya tunasar da su game da irin Allah da yake. Wannan ya ƙarfafa dogararsu ga alkawuransa. Jehovah ya sa annabawansa su yi amfani da bambanci ta sarai da ke tsakaninsa Allah mai rai na gaskiya da kuma gumaka, da ba sa iya taimakon kansu ko kuma masu bauta musu. (Ishaya 41:10; 46:1; Irmiya 10:2-15) Yayin da yake gaya wa Ishaya, “Ku yi ma mutane ta’aziyya, ku ta’azantarda su,” Jehovah ya motsa annabinsa ya yi amfani da misalai da kuma kwatanci na Ayyukansa na halitta domin ya nanata girman Jehovah shi Allah makaɗaici na gaskiya.—Ishaya 40:1-31.

6. Waɗanne nuni wasu lokatai Jehovah yake yi a nuna lokacin da zai yi ceto?

6 A wani lokaci, Jehovah ya yi ta’aziyya ta wurin ambata ainihin lokaci, ko na kusa ko kuma na gaba da daɗewa da za a ceci mutanensa. Lokacin da ceto daga Masar ya jawo kusa, ya gaya wa Isra’ilawa da ake wa hamayya: “Da sauran annoba ɗaya tukuna zan kawo ma Fir’auna, da Masar kuma; daga baya za ya bar ku ku fita daganan.” (Fitowa 11:1) Lokacin da al’ummai uku da suka haɗa kai suka auko wa Yahuda a zamanin Sarki Jehoshaphat, Jehovah ya ce musu zai sa hannu dominsu “gobe.” (2 Labarbaru 20:1-4, 14-17) A wata sassa kuma, Ishaya ya faɗi cetonsu daga Babila kusan shekaru 200 kafin lokacin, aka kuma ba da wasu daki-daki ta wurin Irmiya kusan shekara ɗari kafin ceton. Annabce-annabcen nan da ban ƙarfafa suke ga bayin Allah a lokacin da ceton ya jawo kusa!—Ishaya 44:26–45:3; Irmiya 25:11-14.

7. Sau da yawa me alkawuran ceto ke ƙunsa, kuma yaya hakan ya shafi masu aminci a Isra’ila?

7 Abin lura ne cewa alkawura da ke kawo ta’aziyya ga mutanen Allah sau da yawa suna ɗauke da bayani game da Almasihu. (Ishaya 53:1-12) Bayan tsararraki, wannan ya ba da bege ga mutane masu aminci yayin da suke fuskantar jarabobbi da yawa. Mu karanta a Luka 2:25: “Ga kuma wani mutum cikin Urushalima, sunansa Siman; wannan mutum mai-adalci ne, mai-ibada, yana zuba ido ya ga ta’aziyya [watau, zuwan Almasihu] ta Isra’ila: Ruhu Mai-tsarki kuma yana bisansa.” Siman ya san begen Almasihu da ke rubuce cikin Nassosi, kuma tsammanin cikarsa ya shafi rayuwarsa. Bai dai fahimci yadda hakan zai faru ba, kuma bai rayu ba ya ga ceto da aka annabta ya zama gaskiya, amma ya yi farin ciki da ya san Wanda zai zama ‘ceton’ Allah.—Luka 2:30.

Ta’aziyya da Aka Yi Tanadinta ta Wurin Kristi

8. Ta yaya za a iya gwada taimakon da Yesu ya bayar da abin da mutane da yawa suke tsammanin suke bukata?

8 Yayin da Yesu Kristi yake hidimarsa a duniya, ba kullum ba yake ba da taimako da mutane suke tsammanin suke bukata. Wasu suna son Almasihu da zai ’yantar da su daga karkiyar daular Roma da suke ƙi. Amma Yesu bai gabatar da juyin mulki ba; ya gaya musu su “ba Kaisar abin da ke na Kaisar.” (Matta 22:21) Ƙudurin Allah ya shafi fiye da ’yantar da mutane kawai daga sarautar siyasa. Mutanen suna neman su naɗa Yesu sarki, amma ya ce zai ba da “ransa kuma abin fansar mutane dayawa.” (Matta 20:28; Yohanna 6:15) Bai kai lokacin da zai soma sarauta ba tukuna, Jehovah ne zai ba shi iko ya yi sarauta, ba wani taron ta da zaune tsaye ba.

9. (a) Menene saƙon ta’aziyya da Yesu ya sanar? (b) Ta yaya Yesu ya nuna muhimmancin saƙon ga yanayin da mutanen kansu ke fuskanta? (c) Tushen me hidimar Yesu ta kafa?

9 Ta’aziyya da Yesu ya kawo tana ƙunshe cikin “bishara ta mulkin Allah.” Wannan ne saƙon da Yesu ya sanar duk inda ya je. (Luka 4:43) Ya nanata muhimmancin saƙon wajen matsalolin yau da kullum na mutane ta nuna abin da shi Masarauci Almasihu zai yi wa mutane. Ya ba wa mutane da suke wahala sabon dalili na rayuwa ta mai da musu da ganin gari da iya magana (Matta 12:22; Markus 10:51, 52), ta warkar da naƙasassu (Markus 2:3-12) ta warkar da Isra’ilawa daga cututtuka masu ban ƙyama (Luka 5:12, 13), kuma ta kawo musu sauƙi daga wasu cututtuka. (Markus 5:25-29) Ya kawo sauƙaƙawa mai girma ga iyalai da aka ta da yaransu daga matattu. (Luka 7:11-15; 8:49-56) Ya nuna iyawarsa na tsayar da hadari mai haɗari kuma ya ciyar da babban taro. (Markus 4:37-41; 8:2-9) Bugu kan ƙari, Yesu ya koyar da su ƙa’idar rayuwa wadda za ta taimake su su bi da matsaloli da suke da su kuma haka zai ba su bege domin sarauta ta adalci ƙarƙashin mulkin Almasihu. Yayin da Yesu yake hidimarsa, ba waɗanda suke saurara kuma suke da bangaskiya ya yi wa ta’aziyya kawai ba amma kuma ya kafa tushen ƙarfafa mutane na shekaru dubbai nan gaba.

10. Menene ya yiwu ta wurin hadayar Yesu?

10 Bayan fiye da shekara 60 da Yesu ya ba da ransa na mutum hadaya, kuma aka ta da shi zuwa rayuwa a sama, an hure manzo Yohanna ya rubuta: “ ’Ya’yana ƙanƙanana, waɗannan abu ni ke rubuta muku domin kada ku yi zunubi. Idan kowa ya yi zunubi, muna da Mai-taimako wurin Uba, Yesu Kristi mai-adalci: shi ne kuwa fansar zunubanmu; ba kuwa ta namu kaɗai ba, amma ta duniya duka kuma.” (1 Yohanna 2:1, 2) Domin amfanin kamiltacciyar hadayar Yesu, mun sami ta’aziyya. Mun sani za mu iya samun gafarar zunubai, lamiri mai tsabta, dangantaka yardaje da Allah, da kuma zaton samun rai madawwami.—Yohanna 14:6; Romawa 6:23; Ibraniyawa 9:24-28; 1 Bitrus 3:21.

Ruhu Mai Tsarki Mai Ta’aziyya

11. Wane ƙarin tanadi ne na ta’aziyya Yesu ya yi alkawarinsa kafin mutuwarsa?

11 Lokacin da yake tare da manzanninsa a maraice na ƙarshe kafin mutuwarsa ta hadaya, Yesu ya yi magana game da wani tanadi da Ubansa na samaniya ya yi don ya ta’azantar da su. Yesu ya ce: “In roƙi Uban, shi kuma za ya ba ku wani Mai-taimako [mai ta’aziyya; Helenanci, pa·raʹkle·tos] domin shi zauna tare da ku har abada, shi Ruhu na gaskiya.” Yesu ya tabbatar musu: “Mai-taimako, watau Ruhu Mai-tsarki . . . za ya koya muku abu duka, ya tuna muku kuma dukan abin da na faɗa muku.” (Yohanna 14:16, 17, 26) Ta yaya ne ruhu mai tsarki da gaske ya yi musu ta’aziyya?

12. Ta yaya matsayin ruhu mai tsarki cewa abin taimako ne a tunasar da almajiran Yesu, ya kawo ta’aziyya ga mutane da yawa?

12 Manzannin sun sami koyarwa da yawa daga Yesu. Lallai ba za su taɓa manta da wannan ba, amma za su iya tuna abin da ya faɗi? Za su manta da wasu muhimman koyarwa ne domin tunaninsu na ajizanci? Yesu ya tabbatar da su cewa ruhu mai tsarki zai ‘tuna musu dukan abin da ya gaya musu.’ Saboda haka, bayan shekaru takwas da mutuwar Yesu, Matta ya rubuta Lingila ta farko, da ya rubuta Huɗuba Bisa Dutse na Yesu mai daɗaɗa zuciya, misalansa masu yawa game da Mulkin, da kuma tattaunawar alamar bayyanarsa. Fiye da shekara 50 nan gaba, manzo Yohanna ya iya rubuta labari matabbaci da ke cike da daki-dakin labarin rayuwar Yesu na kwanaki kalilan a duniya. Dubi yadda labaran nan suke da ban ƙarfafa har zuwa zamaninmu!

13. Ta yaya ruhu mai tsarki ya zama mai koyarwa ga Kiristoci na farko?

13 Ban da tuna musu kalmomin, ruhu mai tsarki ya koya wa almajiran kuma ya yi musu ja-gora su samu cikakken fahimin ƙudurin Allah. Yayin da Yesu yake tare da almajiransa, ya gaya musu abubuwa da ba su fahimta ba a lokacin. Bayan haka, ruhu mai tsarki ya motsa, Yohanna, Bitrus, Yaƙub, Yahuda, da kuma Bulus suka rubuta ƙarin bayani na aukuwar ƙudurin Allah. Ta haka, ruhu mai tsarki ya zama mai koyarwa, da ke ba da tabbacin ja-gorar Allah.

14. A waɗanne hanyoyi ne ruhu mai tsarki ke taimakon mutanen Jehovah?

14 Kyauta ta mu’ujiza ta ruhun ma ya taimaka a fahimta cewa Allah ya kawar da tagomashinsa daga wurin Isra’ila ta jiki zuwa ikilisiyar Kirista. (Ibraniyawa 2:4) Bayyanar ’ya’yan ruhun a rayuwan mutane ma muhimmi abu ne a sanin waɗanda suke almajiran Yesu da gaske. (Yohanna 13:35; Galatiyawa 5:22-24) Ruhun kuma ya ƙarfafa waɗanda suke cikin ikilisiyar su kasance da gaba gaɗi kuma shaidu marasa tsoro.—Ayukan Manzanni 4:31.

Taimako Lokacin Matsi Mai Tsanani

15. (a) Waɗanne matsi Kiristoci na dā da na yanzu suka fuskanta? (b) Me ya sa waɗanda suke ba da ƙarfafa, wasu lokatai suke bukatar samun ƙarfafa su ma?

15 Dukan waɗanda suka ba da kansu ga Jehovah da suke aminci gare shi suna fuskantar tsanani. (2 Timothawus 3:12) Amma, Kiristoci da yawa sun sha matsi mafi tsanani. A zamanin yau, taron banza sun fitine wasu kuma jefa su cikin sansanin fursuna, kurkuku, da kuma sansanin aiki cikin yanayi mafi muni. Gwamnati ta zama masu tsanantawa ƙwarai, kuma ta yarda wa mutane masu taka doka su yi abin da suka ga dama. Ban da haka, Kiristoci sun fuskanci matsalolin rashin lafiya ko kuma tarzomar iyali. Wani Kirista da ya ƙware da yake taimaka wa ’yan’uwa masu bi su sha kan matsaloli masu wuya ma zai iya shan matsi. A irin waɗannan yanayi, wanda yake ba da ƙarfafar ma zai bukace ta shi ma.

16. Yayin da Dauda ke cikin matsi, ta yaya ya samu taimako?

16 Yayin da Sarki Saul yake neman Dauda ya kashe shi, Dauda ya juya ga Allah Mai taimakonsa: “Ka ji addu’ata, ya Allah,” ya yi roƙo. “Cikin inuwar fukafukanka zan fake.” (Zabura 54:2, 4; 57:1) Dauda ya samu taimako kuwa? Hakika. A wannan lokaci, Jehovah ya yi amfani da Gad annabi da Abiathar firist su yi wa Dauda ja-gora, kuma Ya yi amfani da Jonathan ɗan Saul ya ƙarfafa wannan saurayin. (1 Samu’ila 22:1, 5; 23:9-13, 16-18) Jehovah ya kuma ƙyale Filistiyawa su kai wa ƙasar hari, suna janye hankalin Saul daga ƙorar da yake yi.—1 Samu’ila 23:27, 28.

17. Lokacin da yake cikin matsi, ina ne Yesu ya nemi taimako?

17 Yesu Kristi ma ya sha matsi ƙwarai da ƙarshen rayuwarsa a duniya ta jawo kusa. Ya sani sarai yadda halinsa zai shafi sunan Ubansa na samaniya da kuma abin da zai nufa ga dukan ’yan Adam a nan gaba. Ya yi addu’a da naciya, “cikin raɗaɗi.” Allah ya sa Yesu ya sami taimako da yake bukata a lokacin nan mai wuya.—Luka 22:41-44.

18. Wace ta’aziyya Allah ya ba wa Kiristoci na farko da aka tsananta musu?

18 An tsananta wa Kiristoci sosai bayan da aka kafa ikilisiya ta ƙarni na farko har da aka kore duka daga Urushalima sai manzannin kawai aka bari. An fitar da maza da mata daga gidajensu. Wace ta’aziyya Allah ya yi musu? Tabbaci daga Kalmarsa cewa suna da “dukiya mafiya kyau, matabbaciya kuwa,” gadō ne na dindindin cikin sammai tare da Kristi. (Ibraniyawa 10:34; Afisawa 1:18-20) Yayin da suka ci gaba da wa’azi, sun ga tabbacin cewa ruhun Allah na tare da su, kuma abin da ya faru musu ya daɗa ba su dalilin farin ciki.—Matta 5:11, 12; Ayukan Manzanni 8:1-40.

19. Ko da yake Bulus ya sha tsanani ƙwarai, yaya ya ji game da ta’aziyya da Allah ya bayar?

19 A ƙarshe, Saul (Bulus) wanda shi kansa matsananci ne, ya zama wanda ake tsananta masa domin ya zama Kirista. A tsibirin Ƙubrus, da akwai wani maye da yake neman ya hana hidimar Bulus ta yin amfani da ha’inci da kuma karkatawa. A Galatiya, aka jejjefe Bulus da duwatsu kuma ƙyale shi ya mutu. (Ayukan Manzanni 13:8-10; 14:19) A Makidoniya aka yi masa dūka da sanda. (Ayukan Manzanni 16:22, 23) Bayan da taron banza suka hau masa a Afisus, ya rubuta: “Muka nauwaita ƙwarai, har ya fi ƙarfinmu, har ranmu muka fidda zuciya a ciki: labudda kuwa, mu da kanmu muna da hukuncin mutuwa a cikin ranmu.” (2 Korinthiyawa 1:8, 9) Amma kuma a cikin wasiƙar, Bulus ya rubuta waɗannan kalmomin ta’aziyya da aka yi ƙaulinsu a sakin layi na 2 na wannan talifin.—2 Korinthiyawa 1:3, 4.

20. Menene za mu yi la’akari da shi cikin talifi na gaba?

20 Ta yaya za ka sa hannu a ba da irin ta’aziyyar nan? Da akwai mutane da yawa a zamaninmu da suke bukatarta da suke baƙin ciki, ƙila domin masifa da ta sami mutane dubbai ko kuma saboda ƙunci da ke wahalar da su. A cikin talifi na gaba, za mu yi la’akari da yadda za mu ba da ta’aziyya a kowanne yanayin nan.

Ka Tuna?

• Me ya sa ta’aziyya daga wurin Allah ke da muhimmanci mai girma?

• Wace ta’aziyya aka bayar ta wurin Kristi?

• Ta yaya ne ruhu mai tsarki ya zama mai ta’aziyya?

• Ka ba da misalan ta’aziyya da Allah ya bayar lokacin da bayinsa ke cikin matsi ƙwarai.

[Hotuna a shafi na 21]

Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa Jehovah ya kawo ta’aziyya ta wurin ceton mutanensa

[Hotuna a shafi na 22]

Yesu ya yi tanadin ta’aziyya ta wurin koyarwa, ta warkarwa, da kuma ta wurin ta da matattu

[Hoto a shafi na 24]

Yesu ya samu taimako daga sama

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba