Ka Ta’azantu, Kuma Ka Ta’azantar da Wasu
Da yake mu ajizai ne, dukanmu mun taɓa yin ciwo, wasu ma masu tsanani sosai. Amma, mene ne zai taimaka mana mu jimre idan muna fuskantar irin wannan yanayin?
Ta’aziyar da iyalinmu da abokanmu da kuma ’yan’uwanmu suke mana, za ta taimaka mana.
Za a iya gwada kalaman abokinmu da ruwan sanyi da ke wartsake mutum. (Mis. 16:24; 18:24; 25:11) Amma, Kiristoci na gaskiya ba su fi damun kansu da samun ta’aziya ba. Suna ƙoƙari su ‘ta’azantar da waɗanda ke cikin kowane irin ƙunci, ta wurin ta’aziyya wadda su ma da kansu suka ta’azantu da ita daga wurin Allah.’ (2 Kor. 1:4; Luk 6:31) Wani mai kula da gunduma a ƙasar Meziko, mai suna Antonio ya shaida hakan.
Antonio ya cika da baƙin ciki sosai sa’ad da aka sanar da shi cewa yana da wani irin ciwon daji na jini. Ko da yake hakan ya sa shi baƙin ciki sosai, amma ya kame kansa. Ta yaya? Ya tuna waƙoƙin ƙungiyar Jehobah kuma ya rera su, domin ya ji kalmomin kuma ya yi bimbini a kansu. Yin addu’a da ƙarfi da kuma karanta Littafi Mai Tsarki ma ya ta’azantar da shi sosai.
Yanzu, Antonio ya fahimci cewa abin da ya taimaka masa sosai shi ne ’yan’uwansa Kiristoci. Ya ce: “Sa’ad da ni da matata muke sanyin gwiwa, muna gayyatar wani danginmu da dattijo ne a cikin ikilisiya ya zo ya yi mana addu’a. Hakan yana ta’azantar da kuma kwantar da hankalinmu. Muna matuƙar godiya ga yadda danginmu da kuma ’yan’uwanmu a cikin ikilisiya suka taimaka mana. Ba da daɗewa ba, mun shawo kan wannan baƙin cikin.” Ya yi farin ciki sosai domin yana da abokai masu ƙauna da kuma kula.
Wani abu kuma da ke taimaka mana sa’ad da muke baƙin ciki, shi ne ruhu mai tsarki da aka mana alkawarin sa. Manzo Bitrus ya ce ruhu mai tsarki na Allah “kyauta” ne. (A. M. 2:38) Shafe mutane da yawa da ruhun a ranar Fentakos na shekara ta 33 da aka yi, ya nuna cewa hakan gaskiya ne. Ko da yake Bitrus yana magana game da shafaffu, amma hakan ya shafi dukanmu. Jehobah yana ba mu wannan kyautar a yalwace. Zai dace mu roƙe shi ya ba mu ruhunsa.—Isha. 40:28-31.
KA ƘAUNACI WAƊANDA SUKE SHAN WAHALA
Manzo Bulus ya jimre da wahala da yawa, kuma an ma kusa kashe shi a wasu lokatai. (2 Kor. 1:8-10) Duk da haka, bai yi fargaba ba. Ya samu ta’aziya domin ya san cewa Allah yana tare da shi. Ya ce: “Albarka ga Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Kristi, Uban jiyejiyenƙai, Allah na dukan ta’aziyya; shi da ke yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.” (2 Kor. 1:3, 4) Bulus bai ƙyale matsalolinsa su shawo kansa ba. Maimakon haka, matsalolin da ya jimre sun taimaka masa ya kasance da jin ƙai, domin ya samu ya ta’azantar da wasu idan bukata ta taso.
Bayan Antonio ya warke, sai ya koma hidimarsa na mai kula mai ziyara. Kafin wannan lokacin, Antonio yana kula da ’yan’uwa sosai, amma bayan wannan matsalar da ya fuskanta, sai shi da matarsa suka daɗa ƙwazo sosai don su ziyarci marasa lafiya kuma su ƙarfafa su. Alal misali, bayan Antonio ya ziyarci wani ɗan’uwa da ke ciwo mai tsanani, sai ya samu labari cewa ba ya son ya halarci taro. Antonio ya ce: “Ba wai ya daina ƙaunar Jehobah ko kuma ’yan’uwa ba, amma ciwon ya sa shi baƙin ciki sosai har ya daina daraja kansa.”
Antonio ya gayyaci wannan ɗan’uwan ya yi addu’a a wani liyafa da aka yi, kuma hakan ya ƙarfafa shi sosai. Ko da yake ɗan’uwan ya ji wani iri, amma ya yi addu’ar. Antonio ya ce: “Ya yi addu’a mai kyau sosai, kuma bayan haka, ya ji kamar ba shi ba ne. Ya sake soma ji yana da daraja.”
Babu shakka, dukanmu mun taɓa jimre da wata matsala. Amma Bitrus ya ce, hakan zai iya ƙarfafa mu mu iya ta’azantar da wasu sa’ad da suke cikin matsala. Saboda haka, kada mu yi kunne uwar shegu sa’ad da ’yan’uwanmu suke shan wahala. Amma, zai dace mu yi koyi da Allahnmu Jehobah, ta wajen ta’azantar da mutane.