DARASI NA 34
Me Za Mu Yi don Mu Nuna Muna Ƙaunar Jehobah?
Shin ka daɗa kusantar Allah tun da ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki? Za ka so ka ci gaba da ƙarfafa dangantakarka da shi? Idan haka ne, ka tuna cewa yayin da kake daɗa ƙaunar Jehobah, zai ƙaunace ka sosai kuma zai kula da kai. Me za ka yi don ka nuna kana ƙaunar sa?
1. Me za mu yi don mu nuna wa Jehobah muna ƙaunar sa?
Za mu nuna muna ƙaunar Jehobah ta wajen yi masa biyayya. (Karanta 1 Yohanna 5:3.) Jehobah ba ya tilasta wa kowa ya yi masa biyayya. Maimakon haka, yana ba kowannenmu dama mu zaɓi ko za mu yi masa biyayya ko a’a. Me ya sa? Domin Jehobah yana so mu yi masa ‘biyayya da dukan zuciyarmu.’ (Romawa 6:17) Hakan yana nufin cewa Jehobah yana so ka yi masa biyayya domin kana ƙaunar sa. An shirya Sashe na 3 da na 4 na wannan littafin don ka nuna kana ƙaunar Jehobah, ta wajen yin abin da zai faranta ransa da kuma guji yin abin da zai ɓata masa rai.
2. Me ya sa zai iya yi mana wuya mu ƙaunaci Jehobah?
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai adalci yakan sami wahaloli da yawa.” (Zabura 34:19) Dukanmu ajizai ne kuma muna iya fama da rashin kuɗi ko rashin adalci ko wasu matsaloli. Zai iya yi mana wuya mu yi abin da Jehobah yake so sa’ad da muke cikin matsala. Kuma za mu iya ɗauka cewa yin rashin biyayya ne zai fi sauƙi. Amma idan ka yi abin da Jehobah ya ce, hakan ya nuna cewa kana ƙaunar sa fiye da kome, kana da aminci a gare shi, kuma shi zai kasance da aminci a gare ka. Ba zai taɓa barin ka ba.—Karanta Zabura 4:3.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu ga dalilin da ya sa yin biyayya ga Jehobah yake da muhimmanci, da abin da zai taimaka maka ka kasance da aminci a gare shi.
3. Wani batu da ya shafe ka
A cikin littafin Ayuba, Shaiɗan ya zargi Ayuba da dukan mutane da suke so su bauta wa Jehobah. Ku karanta Ayuba 1:1, 6–2:10, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Mene ne Shaiɗan ya ce ya sa Ayuba yake yi wa Jehobah biyayya?—Ka duba Ayuba 1:9-11.
Mene ne Shaiɗan ya ce game da dukan ’yan Adam, har da kai?—Ka duba Ayuba 2:4.
Ku karanta Ayuba 27:5b, sai ku tattauna tambayar nan:
Ta yaya Ayuba ya nuna yana ƙaunar Jehobah sosai?
Ayuba ya nuna yana ƙaunar Jehobah ta wajen kasancewa da aminci a gare shi
Za mu nuna muna ƙaunar Jehobah ta wajen kasancewa da aminci a gare shi
4. Ka sa Jehobah farin ciki
Ku karanta Karin Magana 27:11, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Yaya Jehobah zai ji sa’ad da ka zama mai hikima kuma ka yi masa biyayya? Me ya sa?
5. Za ka iya kasancewa da aminci ga Jehobah
Ƙaunarmu ga Jehobah ce take sa mu gaya wa mutane game da shi. Kuma hakan za ta sa mu kasance da aminci a gare shi ko da muna cikin matsala. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.
Ya taɓa yi maka wuya ka gaya wa mutane game da Jehobah?
A bidiyon, mene ne ya taimaka wa Grayson ya daina jin tsoro?
Zai yi mana sauƙi mu kasance da aminci ga Jehobah idan muna son abin da yake so kuma muka tsani abin da ya tsana. Ku karanta Zabura 97:10, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Kamar yadda ka koya, waɗanne abubuwa ne Jehobah yake so? Waɗanne abubuwa ne Jehobah ya tsana?
Ta yaya za ka riƙa son yin abin da ya dace kuma ka ƙi yin mugunta?
6. Muna amfana idan muka yi wa Jehobah biyayya
Yi wa Jehobah biyayya zai amfane mu. Ku karanta Ishaya 48:17, 18, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Kana ganin Jehobah ya san abin da ya fi dacewa da mu? Me ya sa?
Ta yaya ka amfana tun lokacin da ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma koya game da Jehobah?
WASU SUN CE: “Ba za mu iya sa Allah farin ciki ba.”
Wane nassi ne za ka karanta wa mutumin don ka nuna cewa ayyukanmu suna iya sa Jehobah farin ciki ko baƙin ciki?
TAƘAITAWA
Za ka iya nuna cewa kana ƙaunar Jehobah ta wajen yi masa biyayya da kuma kasancewa da aminci a gare shi ko da kana fuskantar matsaloli.
Bita
Mene ne ka koya daga labarin Ayuba?
Ta yaya za ka nuna kana ƙaunar Jehobah?
Mene ne zai taimaka maka ka kasance da aminci ga Jehobah?
KA BINCIKA
Ku kalli bidiyon nan don ku koyi yadda mutum zai iya kasancewa da aminci ga Jehobah da kuma ikilisiya.
Ku karanta ƙasidar nan don ku ga yadda Shaiɗan ya zargi ’yan Adam.
“Ayuba Ya Riƙe Amincinsa” (Littafi Mai Tsarki—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa? sashe na 6)
Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda yara ma za su iya nuna cewa suna ƙaunar Jehobah.
Ta yaya matasa za su kasance da aminci idan tsaransu suka matsa musu su yi abin da bai dace ba? Ku kalli bidiyon nan don ku ga amsar.