TALIFIN NAZARI NA 41
WAƘA TA 108 Ƙauna ta Gaskiya Daga Allah
Ƙaunar Jehobah Za Ta Kasance Har Abada
“ Ku yi godiya ga Yahweh, gama shi mai alheri ne, ƙaunarsa marar canjawa ta har abada ce!”—ZAB. 136:1.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu tattauna yadda gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da ƙaunar Jehobah, za ta taimaka mana mu guji yin sanyin gwiwa idan muka fuskanci matsala.
1-2. Wane yanayi ne ꞌyanꞌuwa da yawa suke fama da shi?
A CE wani jirgin ruwa yana tsakiyar teku sai aka soma iska mai tsanani, kuma iskar ta soma kaɗa shi nan da can. Idan wani a jirgin bai jefa ƙugiya da ke riƙe jirgin ruwa ba, jirgin zai je duk inda iskar ta kai shi. Amma ƙugiyar za ta sa jirgin ya tsaya wuri ɗaya yayin da ake iskar.
2 Idan kana fama da wata matsala, yanayinka zai iya zama kamar na jirgin ruwa da ke tsakiyar teku saꞌad da ake iska mai tsanani, kuma za ka iya soma yin tunani iri-iri. Wata rana za ka ji kamar Jehobah yana ƙaunar ka kuma yana taimaka maka, wata rana kuma ka ji kamar bai san da zamanka ba. (Zab. 10:1; 13:1) Mai yiwuwa wani abokinka ya zo ya ƙarfafa ka, sai ka ji ka ɗan sami sauƙi. (K. Mag. 17:17; 25:11) Amma ba da daɗewa ba sai ka soma shakka kuma. Wataƙila za ka soma ganin kamar Jehobah ba ya ƙaunar ka, ko kuma ba ka da wani amfani a wurinsa. Amma, kamar yadda ƙugiya take taimaka wa jirgin ruwa ya tsaya daram saꞌad da ake iska, me zai taimaka mana mu tsaya daram saꞌad da muke fuskantar matsaloli? Ta yaya za mu kasance da tabbaci, kuma mu ci-gaba da zama da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu kuma zai taimaka mana?
3. Bisa ga Zabura 31:7 da 136:1, mene ne furucin nan “ƙauna marar canjawa” yake nufi, kuma me ya sa za mu iya cewa Jehobah ne ya fi nuna irin wannan ƙaunar? (Ka kuma duba hoton.)
3 Wani abin da zai taimaka mana mu tsaya daram saꞌad da muke fama da matsaloli shi ne, tuna cewa ƙaunar Jehobah marar canjawa ce. (Karanta Zabura 31:7; 136:1.) Furucin nan “ƙauna marar canjawa” yana nufin ci-gaba da nuna wa mutum ƙauna da aminci ba tare da dainawa ba. Babu wanda ya kai Jehobah nuna irin wannan ƙaunar. Littafi Mai Tsarki ya ce, shi “mai yawan ƙauna marar canjawa” ce. (Fit. 34:6, 7) Littafi Mai Tsarki ya kuma ce, Jehobah “mai yawan ƙauna marar canjawa” ce “ga dukan masu kira gare” shi. (Zab. 86:5) Abin da nassosin nan suke nufi shi ne, Jehobah ba ya taɓa barin bayinsa masu aminci! Idan mun tuna cewa ƙaunar Jehobah ba ta canjawa, hakan zai sa mu tsaya daram saꞌad da muke fuskantar matsaloli.—Zab. 23:4.
Kamar yadda ƙugiya take sa jirgin ruwa ya tsaya wuri ɗaya saꞌad da ake iska mai ƙarfi. Haka ma idan muka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mu, za mu tsaya daram saꞌad da muke fuskantar matsaloli (Ka duba sakin layi na 3)
LITTAFI MAI TSARKI YA KOYAR CEWA JEHOBAH YANA ƘAUNAR MU
4. Ka ba da misalin wasu koyarwa da ke cikin Littafi Mai Tsarki, kuma ka bayyana dalilin da ya sa muka yi imani da su.
4 Idan muka tuna cewa, ɗaya daga cikin abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya koyar shi ne, Jehobah yana ƙaunar mu. Hakan zai sa mu ƙara tabbata cewa yana ƙaunar mu. Saꞌad da ka soma koyan gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, waɗanne abubuwa ne ka koya? Babu shakka, ka koyi cewa sunan Allah Jehobah ne, da cewa Yesu ne Ɗan Allah makaɗaici. Ƙari ga haka, ka koyi cewa waɗanda suka mutu ba su san kome ba, da kuma cewa duniya za ta zama aljanna kuma mutane za su yi rayuwa a ciki har abada. (Zab. 83:18; M. Wa. 9:5; Yoh. 3:16; R. Yar. 21:3, 4) Bayan ka gane cewa waɗannan koyarwar gaskiya ne, babu wanda ya iya ruɗin ka kuma. Me ya sa? Domin ka gane cewa abin da ka koya gaskiya ne ba tatsuniya ba. Idan muna shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu ko kuma bai damu da yanayin da muke ciki ba, me zai taimaka mana? Bari mu gani.
5. Ka bayyana yadda mutum zai iya guje wa koyarwar ƙarya.
5 Saꞌad da ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki, me ya taimaka maka ka guji koyarwar ƙarya? Mai yiwuwa ka gwada abin da ka koya daga Littafi Mai Tsarki da abin da ka sani a dā. Alal misali, a ce kafin ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki ka yi imani cewa Yesu ne Allah Maɗaukaki. Amma da ka ci-gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki sai ka soma tambayar kanka, ‘anya hakan gaskiya ne kuwa? Da ka bincika Littafi Mai Tsarki game da batun, sai ka gano cewa hakan ba gaskiya ba ne. Nan da nan ka bar koyarwar ƙaryar kuma ka gaskata da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa: Yesu ne “Ɗan fari gaban dukan halitta” kuma shi ne “makaɗaicin Ɗan Allah.” (Kol. 1:15; Yoh. 3:18) Gaskiyar ita ce, yana da wuya mutum ya daina amincewa da koyarwar ƙarya. (2 Kor. 10:4, 5) Amma da zarar ka gane gaskiya, ba ka sake komawa gidan jiya ba.—Filib. 3:13.
6. Me ya sa za mu iya kasance da tabbaci cewa ‘ƙaunar Jehobah marar canjawa ta har abada ce’?
6 Kamar yadda muka guje wa koyarwar ƙarya, kuma muka amince da gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. Haka ma za mu yi a batun ƙaunar Allah. Idan kana fama da wata matsala kuma ka soma shakka cewa Jehobah yana ƙaunar ka. Zai dace ka tambayi kanka, ‘anya yadda nake tunani ya jitu da raꞌayin Allah kuwa?’ Idan kana shakka ko Jehobah yana ƙaunar ka ko aꞌa, ka yi tunani a kan nassin da aka ɗauko jigon talifin nan, wato Zabura 136:1. Me ya sa Jehobah ya ce “ƙaunarsa marar canjawa ce”? Me ya sa zaburar nan ta maimaita cewa, “ƙaunarsa marar canjawa ta har abada ce” har sau 26? Kamar yadda muka tattauna, ɗaya daga cikin gaskiyar da Littafi Mai Tsarki ya koyar shi ne cewa, Jehobah yana ƙaunar bayinsa. Wannan gaskiyar na kama da wasu abubuwan da muka koya daga Littafi Mai Tsarki da muka yi imani da su. Yin tunani cewa Jehobah ba ya ƙaunar mu, ko ba mu da wani amfani a wurin sa, bai dace ba. Tamkar ƙarya ce. Kuma zai dace mu guji irin tunanin nan, kamar yadda muke guje wa koyarwar ƙarya!
7. Ka ba da misalin wasu nassosin da suka tabbatar mana cewa Jehobah yana ƙaunar mu.
7 Littafi Mai Tsarki na ɗauke da bayanai da yawa da suka ƙara nuna mana cewa Jehobah yana ƙaunar mu. Alal misali, Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “Kuna da daraja fiye da ƙananan tsuntsaye da yawa.” (Mat. 10:31) Jehobah da kansa ya gaya wa kowane bawansa cewa: “Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, zan riƙe ka da hannun damana mai nasara.” (Isha. 41:10) Shin, ka lura cewa sun yi magana da tabbaci? Yesu bai ce ‘wataƙila kun fi ƙananan tsuntsaye daraja ba,’ kuma Jehobah bai ce ‘wataƙila zan taimake ka ba.’ A maimakon haka, sun ce: “Kuna da daraja fiye da ƙananan tsuntsaye” da kuma “Zan . . . taimake ka.” Idan ka soma shakka cewa Jehobah yana ƙaunar ka saꞌad da kake fama da wata matsala, irin nassosin nan za su taimaka maka, amma ba shi ke nan ba. Za su kuma tabbatar maka cewa Jehobah yana ƙaunar ka. Abin da nassosin nan suka faɗa gaskiya ne ba tatsuniya ba. Idan ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka daina shakka, kuma ka yi tunani a kan irin nassosin nan, za ka iya faɗan abin da ke 1 Yohanna 4:16 da ƙarfin zuciya cewa: “Mun sani mun kuma ba da gaskiya ga ƙaunar da Allah yake nuna mana.”a
8. Mene ne za ka iya yi idan a wasu lokuta kana ji kamar Jehobah ba ya ƙaunar ka?
8 Amma me za ka yi idan har ila a wasu lokuta kana ji kamar Jehobah ba ya ƙaunar ka? Ka gwada yadda kake ji da abin da ka sani game da Jehobah. Yadda muke ji zai iya canjawa, amma gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki game da yadda Jehobah yake ƙaunar mu, ba ta canjawa. Idan muna shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu, hakan ya nuna ba mu yarda cewa halinsa na musamman shi ne ƙauna ba.—1 Yoh. 4:8.
KA YI TUNANI A KAN YADDA JEHOBAH YAKE ƘAUNAR KA
9-10. Mene ne Yesu yake magana a kai saꞌad da ya ce “Uban da kansa yana ƙaunar ku”? (Yohanna 16:26, 27) (Ka kuma duba hoton.)
9 Za mu ƙara koya game da yadda Jehobah yake ƙaunar mu, ta wajen yin tunani a kan abin da Yesu ya faɗa wa mabiyansa. Ya ce: “Uban da kansa yana ƙaunar ku.” (Karanta Yohanna 16:26, 27.) Yesu bai faɗi hakan don kawai ya sa mabiyansa su ji daɗi ba. Idan muka karanta ayoyin da aka ambata kafin ayoyi 26 da 27, za mu ga cewa ba game da yadda mabiyansa suke ji ne kawai Yesu yake magana ba. A maimakon haka, yana magana ne a kan wani batu dabam wato, adduꞌa.
10 Yesu ya gama magana ne game da yadda almajiransa za su yi adduꞌa a cikin sunansa, ba a gare shi ba. (Yoh. 16:23, 24) Yana da muhimmanci su san hakan. Mai yiwuwa bayan da aka ta da shi daga mutuwa, almajiransa za su so su yi adduꞌa a gare shi. Da yake Yesu abokinsu ne kuma yana ƙaunar su, za su iya gani kamar hakan zai sa ya ji roƙonsu. Kuma ya roƙi Jehobah ya taimaka musu. Amma Yesu ya ce kada su yi irin wannan tunanin. Me ya sa? Domin ya gaya musu cewa: “Uban da kansa yana ƙaunar ku.” Wannan ɗaya ne daga cikin gaskiyar da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da adduꞌa. Ka yi tunani a kan abin da hakan yake nufi. Nazarin Littafi Mai Tsarki ya taimaka maka ka san kuma ka ƙaunaci Yesu. (Yoh. 14:21) Amma kamar mabiyansa a ƙarni na farko, za ka iya yin adduꞌa ga Jehobah da tabbaci cewa zai ji ka. Domin shi “da kansa yana ƙaunar” ka. Kana nuna ka ba da gaskiya ga hakan a duk lokacin da ka yi adduꞌa ga Jehobah.—1 Yoh. 5:14.
Za ka iya yin adduꞌa ga Jehobah da tabbacin cewa shi da “kansa yana ƙaunar” ka (Ka duba sakin layi na 9-10)b
KA SAN ABIN DA YAKE SA KA SHAKKA
11. Me ya sa Shaiɗan zai ji daɗi idan muka soma shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu?
11 Me yake sa mu yi shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu? Za ka iya cewa Shaiɗan ne yake sa hakan. Hakan ma gaskiya ne. Shaiɗan yana neman yadda zai “cinye” mu, kuma yin hakan zai yi masa sauƙi idan muka soma shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu. (1 Bit. 5:8) Jehobah yana ƙaunar mu sosai shi ya sa ya ba da fansa. Amma Shaiɗan zai so mu ga kamar mu masu zunubi ne sosai kuma ba za mu iya amfana daga fansar ba. (Ibran. 2:9) Amma waye ne zai ji daɗi idan muka gaskata da wannan ƙaryar? Shaiɗan ne. Kuma waye ne zai ji daɗi idan muka yi sanyin gwiwa kuma muka daina bauta wa Jehobah? Shaiɗan ne har ila. Shaiɗan yana so mu ga kamar Jehobah ba ya ƙaunar mu, alhali shi ne Jehobah ba ya ƙauna kwata-kwata. Duk da haka, ɗaya daga cikin “dabarun Shaiɗan” shi ne, yana ƙoƙari ya sa mu ga kamar Jehobah ba ya ƙaunar mu kuma zai halaka mu. (Afis. 6:11) Idan mun gane abin da Shaiɗan maƙiyinmu yake so ya yi, hakan zai sa mu ƙuduri niyyar cewa ba za mu ba shi dama ba.—Yak. 4:7.
12-13. Ta yaya zunubin da muka gāda zai iya sa mu soma shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu?
12 Akwai wani abu kuma da yake sa mu soma shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu. Me ke nan? Zunubin da muka gāda. (Zab. 51:5; Rom. 5:12) Zunubi ya ɓata dangantaka da ke tsakanin ꞌyanꞌadam da Mahaliccinsu. Ya kuma ɓata tunaninmu, da zuciyarmu, da kuma lafiyar jikinmu.
13 Zunubi ya shafe mu ba kaɗan ba. Domin yana sa mu damu, mu yi shakka, mu ji tsoro, kuma mu ji kunya. Idan mutum ya yi zunubi, zai iya samun kansa a cikin irin waɗannan yanayoyin. Amma ko da mutum bai yi zunubi ba, zai iya jin hakan da yake mu ajizai ne. Gaskiyar ita ce, ba haka ne Jehobah ya halicci ꞌyanꞌadam tun farko ba. (Rom. 8:20, 21) Kamar yadda motar da ta yi faci ba za ta iya tafiya da kyau ba, haka mu ma ba za mu iya yin rayuwa yadda ya kamata ba domin ajizancinmu. Shi ya sa ba abin mamaki ba ne cewa, a wasu lokuta muna shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu. Idan hakan ya faru, mu tuna cewa Jehobah, ‘Allah ne mai girma, mai ban tsoro, mai kiyaye yarjejeniya ne, mai ƙauna marar canjawa ga waɗanda suke ƙaunar sa, suke kuma kiyaye umarnansa.’—Neh. 1:5.
14. Ta yaya yin tunani game da fansar Yesu zai taimaka mana mu daina shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu? (Romawa 5:8) (Ka kuma duba akwatin “Ka Kiyaye Kanka Daga ‘Ruɗu na Zunubi’”)
14 A wasu lokuta, za mu iya ji kamar ba mu cancanci Jehobah ya ƙaunace mu ba. Gaskiyar ita ce ba mu cancanta ba. Duk da haka, ya ƙaunace mu shi ya sa muke matuƙar godiya. Babu abin da za mu iya yi da zai sa mu cancanci Jehobah ya ƙaunace mu. Duk da haka, Jehobah ya ba da fansa don ya iya gafarta mana zunubanmu. Hakan ya nuna cewa yana ƙaunar mu. (1 Yoh. 4:10) Ka kuma tuna cewa Yesu ya zo ne don ya ceci masu zunubi, ba marasa zunubi ba. (Karanta Romawa 5:8.) Babu waninmu da zai iya yin abu babu kuskure. Kuma Jehobah ma ya san da hakan. Idan mun gane cewa zunubin da muka gāda zai iya sa mu soma shakka cewa Jehobah yana ƙaunar mu, hakan zai sa mu ƙuduri niyyar cewa ba za mu taɓa barin hakan ya faru ba.—Rom. 7:24, 25.
KA KASANCE DA AMINCI
15-16. Idan muka ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci, wane tabbaci ne muke da shi kuma me ya sa? (2 Samaꞌila 22:26)
15 Jehobah yana so mu yi zaɓin da ya dace ta wurin “manne masa.” (M. Sha. 30:19, 20) Idan muka yi hakan, babu shakka Jehobah zai amince da mu har abada. (Karanta 2 Samaꞌila 22:26.) Muddin mun riƙe amincinmu ga Jehobah, muna da tabbaci cewa zai taimaka mana ko da a wane irin yanayi ne muka sami kanmu.
16 Kamar yadda muka tattauna, muna da dalilan da za su sa mu tsaya daram saꞌad da muke fuskantar matsaloli. Mun san cewa Jehobah yana ƙaunar mu kuma yana taimaka mana. Abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar ke nan. A duk lokacin da muka soma shakka cewa yana ƙaunar mu, zai dace mu yi tunani a kan gaskiyar da muka sani game da Jehobah, maimakon yadda muke ji. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, bari mu kasance da tabbaci cewa ƙaunar da Jehobah yake mana, marar canjawa ce har abada.
WAƘA TA 159 Mu Ɗaukaka Jehobah
a Wasu misalai su ne, Maimaitawar Shariꞌa 31:8, da Zabura 94:14, da kuma Ishaya 49:15.
b BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa yana roƙan Jehobah ya taimaka masa ya iya kula da matarsa da ba ta da lafiya, ya tsai da shawarwari masu kyau game da kuɗi, kuma ya iya koya wa ꞌyarsa yadda za ta ƙaunaci Jehobah.