Kana bin “Hanya Mafificiya” Ta Ƙauna?
“ALLAH ƙauna ne.” Waɗannan kalmomi na manzo Yohanna sun nuna halin Allah na musamman. (1 Yoh. 4:8) Ƙaunar Allah ce ga ’yan adam ta sa ya yiwu mu kusace shi kuma mu ƙulla dangantaka na kud da kud da shi. A wace hanya ce kuma ƙaunar Allah take shafan mu? An faɗi cewa: “Abin da muke ƙauna yana iya shafan halinmu.” Hakan gaskiya ne. Amma, gaskiya ne kuma cewa wanda muke ƙauna da kuma waɗanda suke ƙaunarmu suna shafan halinmu. Da yake an halicce mu cikin surar Allah, muna iya yin koyi da ƙaunarsa a rayuwarmu. (Far. 1:27) Shi ya sa, manzo Yohanna ya rubuta cewa muna ƙaunar Allah “domin ya fara ƙaunace mu.”—1 Yoh. 4:19.
Kalmomi Huɗu da Za a Kwatanta Ƙauna
Manzo Bulus ya kira ƙauna “hanya mafificiya.” (1 Kor. 12:31) Me ya sa ya kwatanta ƙauna a wannan hanya? Wace irin ƙauna ce Bulus yake maganarta? Don mu sani, bari mu bincika ma’anar kalmar nan “ƙauna” sosai.
Helenawa na dā suna da kalmomi huɗu da suka yi amfani da su a hanyoyi dabam dabam don su kwatanta ƙauna, kamar stor·geʹ, eʹros, phi·liʹa, da kuma a·gaʹpe. A cikin waɗannan, a·gaʹpe, ce kalmar da aka yi amfani da ita aka kwatanta Allah wanda “ƙauna ne.”a Game da wannan ƙaunar, Farfesa William Barclay a littafinsa New Testament Words ya ce: “Agapē ƙauna ce da take fitowa daga zuciya: ba motsin rai kaɗai ba ce da ke tasowa farat ɗaya a zuciyarmu; ƙa’ida ce da muke bi a rayuwa. Agapē ƙauna ce da ke fitowa daga abin da muke sha’awarsa.” A cikin wannan mahalli, a·gaʹpe ƙauna ce da ƙa’ida ke yi mata ja-gora amma sau da yawa tana nuna motsin rai mai ƙarfi. Tun da yake akwai ƙa’idodi masu kyau da mararsa kyau, a bayyane yake cewa ya kamata ƙa’idodi masu kyau da Jehobah Allah da kansa ya kafa a cikin Littafi Mai Tsarki su yi wa Kiristoci ja-gora. Sa’ad da muka gwada yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta ƙaunar a·gaʹpe da wasu kalmomi da aka yi amfani da su cikin Littafi Mai Tsarki don a kwatanta ƙauna, za mu fi fahimtar ƙauna da ya kamata mu nuna.
Ƙauna Cikin Iyali
Abin farin ciki ne mutum ya kasance cikin iyali inda ake nuna ƙauna da kuma haɗin kai! Stor·geʹ kalmar Helenanci ce da sau da yawa aka yi amfani da ita don a nuna soyayya da ke tsakanin waɗanda suke cikin iyali ɗaya. Kiristoci suna ƙoƙari su nuna ƙauna ga waɗanda suke cikin iyalinsu. Bulus ya annabta cewa a kwanaki na ƙarshe, mutane gabaki ɗaya za su zama “marasa-ƙauna irin na tabi’a.”b—2 Tim. 3:1, 3.
Abin baƙin ciki, babu irin ƙauna da ya kamata ta kasance tsakanin waɗanda suke cikin iyali a duniya ta yau. Me ya sa mata da yawa suke zubar da ciki? Me ya sa iyalai da yawa ba sa damuwa da iyayensu da suka tsufa? Me ya sa kashe aure ya ci gaba da ƙaruwa? Amsar ita ce, rashin ƙauna irin ta tabi’a.
Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa “zuciya ta fi komi rikici.” (Irm. 17:9) Ƙauna cikin iyali tana shafan zuciyarmu da yadda muke ji. Yana da kyau da Bulus ya yi amfani da a·gaʹpe don ya kwatanta ƙauna da miji yake nuna wa matarsa. Bulus ya gwada wannan ƙaunar ga ƙaunar da Kristi yake nuna wa ikilisiya. (Afis. 5:28, 29) Wannan ƙauna tana bisa ƙa’idodin da Jehobah wanda ya kafa iyali ya tsara.
Nuna ƙauna ta gaske ga waɗanda suke cikin iyalinmu tana motsa mu mu kula da iyayenmu tsofaffi kuma tana motsa mu mu ɗauki hakkin kula da yaranmu. Tana kuma motsa iyaye su ba yaransu horo cikin ƙauna sa’ad da ya dace kuma tana hana iyaye aikatawa bisa motsin rai, wanda sau da yawa yake sa su nuna halin kome daidai game da yara.—Afis. 6:1-4.
Soyayya Tsakanin Namiji da Mace da kuma Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki
Soyayya da ke tsakanin ma’aurata kyauta ce daga Allah. (Mis. 5:15-17) Amma, marubutan Littafi Mai Tsarki da aka hure ba su yi amfani da kalmar nan eʹros, da ke nufin ƙauna tsakanin namiji da tamace ba. Me ya sa? Shekaru da suka shige, Hasumiyar Tsaro ta ce: “A yau dukan duniya kamar tana yin irin kuskure da Helenawa na dā suka yi. Sun bauta wa Eros a matsayin alla, sun yi bauta a bagadinsa kuma sun miƙa masa hadayu. . . . Amma tarihi ya nuna cewa irin wannan bauta ta ƙaunar jima’i tana kawo rashin mutunci, masha’a da kuma rabuwa. Wataƙila shi ya sa marubutan Littafi Mai Tsarki ba su yi amfani da kalmar nan ba.” Don mu guji ƙulla dangantaka da ke bisa kyaun siffa, dole ne a kame soyayya da ƙa’idodi na Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, ka tambayi kanka, ‘Ina daidaita soyayya na da ƙauna ta gaske ga mijina ko matata?’
‘A lokacin’ da sha’awar jima’i take yin ƙarfi sosai, matasa da suka manne wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su kasance da tsabtar ɗabi’a. (1 Kor. 7:36; Kol. 3:5) Mun ɗauki aure a matsayin kyauta ce mai tsarki daga Jehobah. Yesu ya ce game da ma’aurata: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Mat. 19:6) Maimakon mu kasance tare muddin muna son juna, muna ɗaukan aure a matsayin alkawari mai muhimmanci. Sa’ad da matsala ta taso a aure, ba ma neman hanya mai sauƙi na fita amma muna ƙoƙari mu nuna halaye na Allah don mu sa rayuwar iyalinmu ta kasance na farin ciki. Irin wannan ƙoƙarce-ƙoƙarce za su kawo farin ciki na dindindin.—Afis. 5:33; Ibran. 13:4.
Ƙauna Tsakanin Abokai
Ba za a ji daɗin rayuwa ba idan babu abokai! Wani karin magana a cikin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Akwai masoyi wanda ya fi ɗan-uwa mannewa.” (Mis. 18:24) Jehobah yana son mu samu aminai. An san abokantaka na kud da kud da ke tsakanin Dauda da Jonathan. (1 Sam. 18:1) Kuma Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu yana ‘ƙaunar’ manzo Yohanna. (Yoh. 20:2) Kalmar Helenanci ta “ƙauna” ko kuma “abokantaka” ita ce phi·liʹa. Ba laifi ba ne mutum ya samu amini a cikin ikilisiya. Amma, an ƙarfafa mu a 2 Bitrus 1:7 mu nuna ƙauna (a·gaʹpe) ga “son ’yan’uwa” (wato phi·la·del·phiʹa, kalmomi biyu da aka haɗa, wato, phiʹlos, kalmar Helenanci da ke nufin “aboki,” da a·del·phos,ʹ wato kalmar Helenanci da ke nufin “’yan’uwa”). Domin mu ci gaba da more abokantaka, muna bukatar mu yi amfani da wannan gargaɗin. Yana da kyau mu tambayi kanmu, ‘Ina daidaita yadda nake ji game da abokantaka da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?’
Kalmar Allah tana taimaka mana mu guji nuna son kai a yadda muke sha’ani da abokanmu. Bai kamata mu yi amfani da mizanai biyu ba: mizani mai sauƙi ga abokanmu kuma mai wuya ga mutanen da ba abokanmu ba. Bugu da ƙari, ba ma yin amfani da daɗin baki don mu sami abokai. Mafi muhimmanci, yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki na ba mu fahimin da muke bukata don mu mai da hankali wajen zaɓan abokai kuma mu guji ‘zama da miyagu da ke ɓata halaye na kirki.’—1 Kor. 15:33.
Gami na Ƙauna na Musamman!
Hakika, ba inda za a iya samun irin gami da ke haɗa kan Kiristoci! Manzo Bulus ya rubuta: “Bari ƙaunan da ba na ganin ido ba ya zauna tare da ku. . . . Ku yi zaman daɗin soyayya da junanku cikin ƙaunar ’yan’uwa.” (Rom. 12:9, 10) Babu shakka, Kiristoci suna nuna ‘ƙauna (a·gaʹpe) da ba na ganin ido ba.’ Wannan ƙaunar ba motsin rai kawai da ke cika zuciyarmu ba ce. Maimakon haka, tana bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Amma, Bulus ya kuma yi maganar “ƙaunar ’yan’uwa” (phi·la·del·phiʹa) da “soyayya” (phi·loʹstor·gos, an haɗa phiʹlos da stor·geʹ). Wani masani ya ce “ƙaunar ’yan’uwa” “ƙauna ce ta soyayya, yin alheri, tausayi da kuma ba da taimako.” Idan aka haɗa da a·gaʹpe, tana kawo abokantaka na kud da kud tsakanin masu bauta wa Jehobah. (1 Tas. 4:9, 10) Ɗayan furcin da aka fassara “daɗin soyayya,” ya fito sau ɗaya a cikin Littafi Mai Tsarki kuma yana nuni ga dangantaka na kusa, kamar a cikin iyali.c
Gamin da ya haɗa Kiristoci na gaskiya ya ƙunshi ƙauna cikin iyali da ƙauna ga abokai na gaskiya, da dukan dangantaka da ke bisa ƙa’idodi na Littafi Mai Tsarki. Ikilisiyar Kirista ba rukuni ba ne inda mutane da suka fito daga wuri ɗaya suke taruwa, amma iyali ce mai haɗin kai wajen bauta wa Jehobah Allah. Muna kiran masu bi ɗan’uwa da ’yar’uwa, kuma muna ɗaukansu hakan. Suna cikin iyalinmu ta ruhaniya, muna ƙaunarsu a matsayin abokai, kuma muna bi da su bisa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Bari dukanmu mu ci gaba da daɗa sa a kasance da gamin ƙauna da ke haɗa kanmu da kuma nuna cewa muna cikin ikilisiyar Kirista na gaskiya.—Yoh. 13:35.
[Hasiya]
a Wani lokaci a kan yi amfani da kalmar nan a·gaʹpe a hanyoyi marar kyau.—Yoh. 3:19; 12:43; 2 Tim. 4:10; 1 Yoh. 2:15-17.
b Furcin nan “marasa-ƙauna irin na tabi’a” fassara ce na irin stor·geʹ da take nufin “rashi.” Ka duba Romawa 1:31.
c A cikin New World Translation, an fassara wasu kalmomin Helenanci zuwa “daɗin soyayya.” Saboda haka, a wannan juyin “daɗin soyayya” ya fito a Romawa 12:10 da Filibiyawa 1:8 da kuma Tasalonikawa 2:8.
[Bayanin da ke shafi na 12]
Yaya za ka sa a daɗa kasance da gamin ƙauna da ke haɗa kanmu?