“Fiye Da Kome Kuma, Ku Himmantu Ga Ƙaunar Juna Gaya”
“Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato . . . Fiye da kome kuma ku himmantu ga ƙaunar juna gaya.” —1 BITRUS 4:7, 8.
YESU ya san cewa ’yan sa’o’i na ƙarshe da yake tare da almajiransa suna da tamani. Ya san abin da yake jiransu. Suna da babban aiki da za su yi, amma za a ƙi su kuma a tsananta musu yadda aka yi masa. (Yahaya 15:18-20) Ya tunasar da su fiye da sau ɗaya a dare na ƙarshe da suke tare, su “ƙaunaci juna.”—Yahaya 13:34, 35; 15:12, 13, 17.
2 Manzo Bitrus da yake wajen a daren ya fahimci abin da ake nufi. Shekaru daga baya, ba da daɗewa ba da yake rubutu game da halakar Urushalima, Bitrus ya nanata muhimmancin ƙauna. Ya yi wa Kiristoci gargaɗi: “Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato . . . Fiye da kome kuma ku himmantu ga ƙaunar juna gaya.” (1 Bitrus 4:7, 8) Kalmomin Bitrus suna da ma’ana mai kyau ga waɗanda suke zama cikin “kwanaki na ƙarshe” na wannan zamani. (2 Timoti 3:1) Menene ‘himmantuwa ga ƙauna gaya’? Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da irin wannan ƙauna ga mutane? Ta yaya za mu nuna muna da irin wannan ƙauna?
Me Take Nufi a—‘Himmantu ga Ƙauna Gaya’?
3 Mutane da yawa suna jin cewa ƙauna halin mutum ne kawai. Amma Bitrus ba magana yake game da kowacce irin ƙauna kawai ba; yana magana ne game da ƙauna mafi girma. Kalmar nan ‘ƙauna’ da aka ambata a 1 Bitrus 4:8 an fassara ta ne daga kalmar Helenancin nan a·gaʹpe. Wannan tana nufin ƙauna ce marar son kai ko kuma wadda ƙa’ida ke mata ja-gora. Wata majiya ta ce: “Nuna ƙauna ta agape ba tsotsuwar zuciya ba ce kawai amma son rai ne da ke sa mutum ya yi wani abu.” Saboda mun gāji son kai, muna bukatar tunasarwa mu yi ƙaunar juna, muna yin haka a hanyoyi da ƙa’idodin ibada suke sarrafawa.—Farawa 8:21; Romawa 5:12.
4 Wannan ba ya nufin cewa za mu ƙaunaci mutane don kawai muna da hakkin mu ƙaunace su ba. A·gaʹpe tana daɗaɗa rai da jiye-jiye. Bitrus ya ce dole mu ‘himmantu ga [a zahiri, “miƙa”] ƙaunar juna gaya.’a (Kingdom Interlinear) Duk da haka, irin wannan ƙauna tana bukatar ƙoƙari. Wani masani ya ce game da kalmar Helenanci da aka fassara “himmantu . . . gaya”: “Tana da ra’ayi na ɗan wasa da yake iyakacin ƙoƙarinsa ya kai ƙarshen tsere.”
5 Saboda haka, ƙaunar da za mu nuna ba sai tana da sauƙin yi kawai ba ko a nuna ta wa mutane kalilan ba. Ƙauna ta Kirista tana bukatar muna yawaita ƙaunarmu har sa’ad da yake da wuya a yi haka ma. (2 Korantiyawa 6:11-13) A bayyane yake cewa wannan irin ƙauna dole a koye ta kuma a yi ƙoƙari, yadda ɗan wasa yake koyo kuma yake ƙoƙarin ya kasance da fasaha. Yana da muhimmanci mu kasance da irin wannan ƙaunar ga mutane. Me ya sa? Aƙalla saboda dalilai uku.
Me Ya Sa Za Mu Yi Ƙaunar Juna?
6 Da farko, “domin ƙauna ta Allah ce.” (1 Yahaya 4:7) Jehovah wanda shi ne Tushen wannan hali mafi kyau, shi ya fara ƙaunar mu. Manzo Yahaya ya ce: “Ta haka aka bayyana ƙaunar Allah gare mu, da Allah ya aiko da Ɗansa makaɗaici a duniya, domin mu sami rai madawwami ta wurinsa.” (1 Yahaya 4:9) An “aiko” da Ɗan Allah ya zama mutum, ya cika hidimarsa, ya mutu a kan gungumen azaba—dukan wannan domin “mu sami rai madawwami” ne. Me ya kamata mu yi game da wannan nuna ƙauna da Allah ya yi? Yahaya ya ce: “Tun da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ai, mu ma ya kamata mu ƙaunaci juna.” (1 Yahaya 4:11) Ka lura cewa Yahaya ya rubuta, ‘Tun da yake Allah ya ƙaunace mu’—ba kai kawai ba amma mu. Ma’anar ita ce: Idan Allah yana ƙaunar ’yan’uwanmu da muke bauta tare, to ya kamata mu ma mu ƙaunace su.
7 Na biyu, yanzu ya fi muhimmanci mu ƙaunaci juna don mu taimaki ’yan’uwanmu mabukata saboda “ƙarshen dukan abubuwa ya gabato.” (1 Bitrus 4:7) Muna cikin zamanin da “za a sha wuya ƙwarai.” (2 Timoti 3:1) Yanayin duniya, bala’i, da kuma hamayya tana kawo mana wahala. Cikin yanayi mai wuya, muna bukatar mu matsa kurkusa da juna. Ƙauna mai himmantuwa tana haɗa mu kuma tana motsa mu mu “kula da juna.”—1 Korantiyawa 12:25, 26.
8 Na uku, muna bukatar mu ƙaunaci juna saboda ba ma son ‘mu bar wa Iblis wata ƙofa’ da zai same mu. (Afisawa 4:27) Yana da sauƙi Shaiɗan ya so ya yi amfani da ajizancin ’yan’uwa masu bi—kumamancinsu, laifofi, da kuma kurakure—abin cikas. Wata magana da aka yi da garaje ko wani hali zai sa mu daina zuwan ikilisiya ne? (Karin Magana 12:18) Sai dai idan ba ma ƙaunar juna! Irin wannan ƙauna na taimakonmu mu kasance da salama kuma da haɗin kai mu bauta wa Allah “da zuciya ɗaya.”—Zafaniya 3:9.
Yadda Za Ka Nuna Cewa Kana Ƙaunar Mutane
9 Dole a fara nuna ƙauna a gida. Yesu ya ce za a san mabiyansa na gaskiya ta wurin ƙauna da suke yi wa juna. (Yahaya 13:34, 35) Dole a nuna ƙauna ba a cikin ikilisiya kawai ba amma har cikin iyali ma—tsakanin abokan aure, kuma tsakanin iyaye da yara. Bai isa ba kawai mutum ya ji yana ƙaunar waɗanda suke cikin iyali; muna bukatar mu nuna ta a hanyoyi masu kyau.
10 Ta yaya abokan aure za su ƙaunaci juna? Maigida da yake ƙaunar matarsa da gaske zai gaya mata kuma ya nuna haka—cewa yana ƙaunarta a fili da kuma a ɓoye. Yana girmama mutuncinta kuma yana kula da juyayinta, ra’ayinta, da kuma tsotsuwar zuciyarta. (1 Bitrus 3:7) Yana lura da lafiyarta gaba da nasa, kuma yana iyakacin ƙoƙarinsa don ya lura da bukatunta na jiki, ruhaniya, da kuma tsotsuwar zuciyarta. (Afisawa 5:25, 28) Mata da take ƙaunar mijinta da gaske tana “ladabta” masa ko idan bai yi abin da take tsammaninsa ya yi ba. (Afisawa 5:22, 33) Tana goyon bayan abokin aurenta kuma tana masa biyayya, ba ta matsa masa lamba, amma tana haɗa kai da shi a kasance da daidaici a batun abubuwa na ruhaniya.—Farawa 2:18; Matiyu 6:33.
11 Iyaye, ta yaya za ku yi ƙaunar yaranku? Niyyarku ku yi aiki tuƙuru don ku yi musu tanadin abin duniya tabbaci ne cewa kuna ƙaunarsu. (1 Timoti 5:8) Amma ba abinci, sutura, da mafaka kawai yara suke bukata ba. Domin su yi girma su koyi ƙauna kuma su bauta wa Allah na gaskiya, suna bukatar koyarwa ta ruhaniya. (Karin Magana 22:6) Wannan yana nufin sayan lokaci don yin nazarin Littafi Mai Tsarki, sa hannu a hidimar fage, da kuma halartar taron Kirista. (Maimaitawar Shari’a 6:4-7) Domin mutum ya ci gaba da yin waɗannan ayyuka, yana bukatar sadaukarwa, musamman a wannan zamani mai wuya. Damuwarku da ƙoƙarce-ƙoƙarcenku ku lura da bukatun ruhaniya na yaranku ƙaunarku ce gare su, domin ta haka kuna nuna damuwarku game da lafiyarsu ta har abada.—Yahaya 17:3.
12 Muhimmin abu ne iyaye su yi ƙaunar yaransu ta wurin lura da bukatarsu ta tsotsuwar zuciya. Yana da sauƙi a ruɗi yara; zukatansu marasa hikima na bukatar a dinga tabbatar da su ta wurin ƙaunarku. Ku gaya musu kuna ƙaunarsu, kuma ku nuna musu soyayya, domin wannan na tabbatar da su cewa ana son su kuma suna da daraja. Ku yaba musu da gaske kuma ku daɗaɗa musu, domin wannan zai nuna kuna ganin ƙoƙarce-ƙoƙarcensu kuma ku daraja su. Ku yi musu horo cikin ƙauna, domin wannan gyara yana nuna kun damu da mutuntakarsu ta nan gaba. (Afisawa 6:4) Irin wannan nuna ƙauna yana taimaka a sami iyali mai farin ciki, da ke da haɗin kai kuma da suke a shirye su yi tsayayya da matsi na waɗannan kwanaki na ƙarshe.
13 Ƙauna tana motsa mu mu ƙyale kasawar wasu. Ka tuna cewa sa’ad da yake ariritar masu karatun rubutunsa su “himmantu ga ƙaunar juna gaya,” Bitrus ya ba da dalilin da ya sa yake da muhimmanci: “Domin ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa.” (1 Bitrus 4:8) Tana yafe laifofi ba ya nufin manyan laifofi. Ana yin ƙarar irin waɗannan batutuwa ga waɗanda suka cancanta cikin ikilisiya. (Littafin Firistoci 5:1; Karin Magana 29:24) Rashin ƙauna ne—kuma ba daidai da Nassi ba ne—a ƙyale masu laifi su ci gaba da ɓata wa marasa laifi rai ko kuma damunsu.—1 Korantiyawa 5:9-13.
14 Yawancin lokaci, kurakure da laifofin ’yan’uwanmu masu bi ƙanana ne. Dukanmu a wasu lokatai muna kuskure wajen magana ko a yin wasu ayyuka, muna ɓata wa juna rai. (Yakubu 3:2) Ya kamata mu yi saurin yaɗa kasawar wasu ne? Irin wannan mataki zai iya kawo jayayya cikin ikilisiya. (Afisawa 4:1-3) Idan ƙauna tana sarrafa abin da muke yi, ba za mu ‘sa laifi’ wa ’yan’uwanmu masu bauta ba. (Zabura 50:20) Kamar yadda shafa fenti a bango yake rufe tabo da ke bangon, haka ma ƙauna take rufe ajizancin mutane.—Karin Magana 17:9.
15 Ƙauna za ta sa mu taimaka wa waɗanda suke da bukata da gaske. Sa’ad da yanayi cikin kwanaki na ƙarshe yake ci gaba da suƙuƙucewa, da akwai lokatai da ’yan’uwa masu bi za su bukaci taimakon abinci ko sutura. (1 Yahaya 3:17, 18) Alal misali, idan waɗanda suke cikin ikilisiyarmu ba su da kuɗi ko sun yi rashin aiki fa? To, za mu iya ba da taimakon kaya yadda yanayinmu ya kai. (Karin Magana 3:27, 28; Yakubu 2:14-17) Gidan wata tsohuwa yana bukatar gyara ne? To, ƙila za mu iya ɗaukan mataki don mu taimaka da wasu gyare-gyare.—Yakubu 1:27.
16 Nuna ƙauna wa mutane ba ga waɗanda suke a inda muke zama ne kawai ba. A wasu lokatai muna iya jin rahoton wasu bayin Allah da suke wasu ƙasashe suna shan wuyan hadari, girgizar ƙasa, ko kuma faɗace-faɗace. Suna bukatar abinci ƙwarai, sutura, da wasu abubuwa. Babu zancen daga wace ƙasa suka fito ba. Muna ‘ƙaunar ’yan’uwa.’ (1 Bitrus 2:17) Saboda haka, kamar ikilisiyoyi na ƙarni na farko, muna ɗokin mu ba da gudummawa yadda aka shirya. (Ayyukan Manzanni 11:27-30; Romawa 15:26) Idan muka nuna ƙauna a waɗannan hanyoyi, za ta ƙarfafa ƙulluwarmu cikin waɗannan kwanaki na ƙarshe.—Kolosiyawa 3:14.
17 Ƙauna tana motsa mu mu gaya wa mutane bisharar Mulkin Allah. Ka yi la’akari da misalin Yesu. Me ya sa ya yi wa’azi kuma ya koyar? Ya ‘ji tausayi’ domin yanayin ruhaniya na taron. (Markus 6:34) Makiyayan addinin ƙarya sun yi banza da su kuma sun ruɗe su, su ya kamata su koya musu gaskiya ta ruhaniya da kuma bege. Saboda haka, ƙauna daga zuci da kuma juyayi ya motsa Yesu ya ta’azantar da mutanen ta wurin “bisharar Mulkin Allah.”—Luka 4:16-21, 43.
18 Haka ma a yau an yashe mutane da yawa kuma an ruɗe su a hanya ta ruhaniya ba tare da bege ba. Idan mun yi kamar Yesu, muna damuwa da bukatun ruhaniya na waɗanda ba su san Allah na gaskiya ba tukuna, ƙauna da juyayi za su motsa mu mu gaya wa mutane bisharar Mulkin Allah. (Matiyu 6:9, 10; 24:14) Domin ƙaramin lokacin da ya rage, ya fi gaggawa yanzu a yi wa’azin saƙon nan na ceton rai.—1 Timoti 4:16.
“Ƙarshen Dukan Abubuwa Ya Gabato”
19 Ka tuna Bitrus ya soma gargaɗinsa cewa ku ƙaunaci juna ta waɗannan kalmomin: “Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato.” (1 Bitrus 4:7) Ba da daɗewa ba wannan duniyar za ta bar wuri wa sabuwar duniyar Allah ta adalci. (2 Bitrus 3:13) Saboda haka, yanzu ba lokaci ba ne na rashin himma ba. Yesu ya yi mana gargaɗi: “Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranan nan ta mamaye ku kamar tarko.”—Luka 21:34, 35.
20 Saboda haka, mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu “zauna a faɗake,” mu zauna da fahimtar yanayin lokaci da muke ciki. (Matiyu 24:42) Bari mu tsare kanmu daga kowane irin gwajin Shaiɗan da zai iya raba mana hankali. Bari kada mu yarda rashin ƙauna na wannan duniya ta hana mu nuna ƙauna ga mutane. Fiye da kome, bari mu daɗa kusaci Allah na gaskiya, Jehovah wanda Mulkin Almasihu ba da daɗewa ba zai cika maɗaukakin ƙudurinsa game da wannan duniya.—Wahayin Yahaya 21:4, 5.
[Hasiya]
a A 1 Bitrus 4:8, wasu fassarar Littafi Mai Tsarki suka ce dole mu yi ƙaunar juna “da gaske,” kuma “sosai.”
TAMBAYOYI DON NAZARI
• Wane gargaɗi na ƙarshe Yesu ya yi wa almajiransa, kuma me ya nuna cewa Bitrus ya fahimci darasin? (Sakin layi na 1-2)
• Mecece ‘ƙauna mai himma gaya’? (Sakin layi na 3-5)
• Me ya sa za mu ƙaunaci juna? (Sakin layi na 6-8)
• Ta yaya za ka nuna cewa kana ƙaunar mutane? (Sakin layi na 9-18)
• Me ya sa wannan ba lokaci na rashin ƙwazo ba, kuma me ya kamata mu ƙudura mu yi? (Sakin layi 19-20)
[Hoto a shafi na 29]
Iyali da take da haɗin kai za ta iya jimre wa matsi a waɗannan kwanaki na ƙarshe
[Hoto a shafi na 30]
Ƙauna tana motsa mu mu taimaka wa mabukata
[Hoto a shafi na 31]
Gaya wa mutane bisharar Mulkin Allah nuna ƙauna ce