WAƘA TA 20
Ka Ba da Ɗanka Mai Daraja
Hoto
(1 Yohanna 4:9)
1. Jehobah Ubanmu,
Da ba mu da bege.
Amma Ɗanka Yesu
Ya ba mu bege!
Za mu bauta maka
Da dukan ƙarfinmu.
Za mu yi shelar sa
Don nufinka ke nan.
(AMSHI)
Muna rera yabo
Don ka ba da Ɗanka.
Za mu riƙa godiya,
Domin Ɗanka ya fanshe mu.
2. Jehobah, jinƙanka,
Na sa mu ƙaunar ka.
Muna son sunanka
Da alherinka.
Amma fansar Yesu
Ce alheri babba.
Ya mutu dominmu.
Kai ne ka aiko shi.
(AMSHI)
Muna rera yabo
Don ka ba da Ɗanka.
Za mu riƙa godiya,
Domin Ɗanka ya fanshe mu.
(KAMMALAWA)
Jehobah Ubanmu, duk muna godiya.
Yabon ka muke yi domin ka aiko Ɗanka.
(Ka kuma duba Yoh. 3:16; 15:13.)