WAƘA TA 98
Nassosi Hurarre Ne Daga Allah
Hoto
(2 Timotawus 3:16, 17)
1. Kalmar Allah na taimaka,
Tana sa mu ga haske.
In muna bin umurninta,
Za mu ceci rayukanmu.
2. Ya yi tanadin Kalmarsa,
Don mu san umurninsa.
Tana ƙarfafa mutane,
Tana horar da mu sosai.
3. Kalmar Allah ta sa mu san,
Cewa Yana da ƙauna.
Karanta ta a koyaushe
Zai sa mu riƙe aminci.
(Ka kuma duba Zab. 119:105; Mis. 4:13.)