WAƘA TA 8
Jehobah Ne Mafakarmu
Hoto
(Zabura 91)
1. Jehobah mafakarmu
Da Madogararmu.
A cikin inuwarsa
Ne za mu kasance.
Mu dogara ga ikonsa,
Domin shi ne zai kāre mu.
Jehobah ne ƙarfinmu,
Kuma shi mai aminci ne.
2. Ko dubbai sun bar Allah,
Sun ƙi bauta masa.
Shaidunsa da ke son sa,
Ba za su bar shi ba.
Kar hakan ya tsorata mu,
Ba za mu sha wahala ba.
Bala’i za ya ƙare,
Don Jehobah na kāre mu.
3. Allah zai kiyaye mu,
Daga tarkon Shaiɗan,
Da kuma barazana,
Har da masifarsa.
Ba abubuwan fargaba,
Za mu je inda muke so.
Jehobah mafakarmu,
Zai kiyaye mu koyaushe.
(Ka kuma duba Zab. 97:10; 121:3, 5; Isha. 52:12.)