Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwyp talifi na 108
  • Yana da Muhimmanci Mutum Ya Sami Dimbin Abokai a Shafin Sada Zumunta?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yana da Muhimmanci Mutum Ya Sami Dimbin Abokai a Shafin Sada Zumunta?
  • Tambayoyin Matasa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Me ya sa yake da hadari?
  • Mutane suna karya don su nuna cewa su shahararru ne
  • Yawan mabiya da masu son abin da ka saka yana da muhimmanci ne?
  • Dandalinmu na Intane—Ku Yi Amfani da Shi Wajen Yin Nazari da Iyalinku ko Kuma Ku Kaɗai
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Su Waye Ne Abokanka a Dandalin Sada Zumunta?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Abin da Ya Kamata in Sani Game da Tura Hotuna Zuwa Dandalin Yada Zumunta
    Tambayoyin Matasa
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
Dubi Ƙari
Tambayoyin Matasa
ijwyp talifi na 108
Wata yarinya tana kallon wayarta tana murmushi. Mutane 85 ne suka nuna cewa suna son abin da ta saka.

TAMBAYOYIN MATASA

Yana da Muhimmanci Mutum Ya Sami Dimbin Abokai a Shafin Sada Zumunta?

Wata matashiya mai suna Elaine ta ce: “Da na ga cewa ’yan makarantarmu suna da daruruwan mabiya a shafin sada zumunta, sai na ce wa kaina, ‘Lallai su shahararru ne!’ A gaskiya, na dan yi kishin su.”

Ka taba jin haka? Idan amsarka e ce, wannan talifin zai taimaka maka kada ka fada a tarkon neman suna ta shafin zumunta.

  • Me ya sa yake da hadari?

  • Mutane suna karya don su nuna cewa su shahararru ne

  • Yawan mabiya da masu son abin da ka saka yana da muhimmanci ne?

  • Kar ka nuna girman kai da wayo

Me ya sa yake da hadari?

A Karin Magana 22:​1, Littafi Mai Tsarki ya ce “gwamma suna mai kyau da samun dukiya.” Don haka ba laifi ba ne mutum ya so ya sami suna mai kyau ko ma a ce mutane su so shi.

Amma a wasu lokuta, neman a so ka zai iya sa ka kasa yin farin ciki idan ba a so ka ba. Neman yin suna yana da hadari kuwa? Wata matashiya ’yar shekara 16 mai suna Onya ta amince da hakan. Ga abin da ta ce:

“Na taba ganin ’yan makarantarmu suna yin wasa da ransu don kawai suna so su yi suna. Har wasu sukan yi tsalle daga gidan sama su fado a kasa.”

Garin kokarin jawo hankalin tsararsu, wasu sukan yi bidiyon wasan banza da suke yi kuma su saka shi a intane. Alal misali, wasu matasa sun taba saka wani bidiyo da ke nuna su suna cin sabulun wanki mai hadarin gaske, abin da bai kamata a ce mutum ya yi ba!

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku yi kome da . . . girman kai.”​—Filibiyawa 2:3.

Ka yi tunani a kan wannan:

  • Kana bala’in son mutane su san da kai a dandalin sada zumunta?

  • Za ka iya sa ranka ko lafiyarka a cikin hadari don kawai ka burge tsararka kuma ka sa su so ka?

    Abin da tsararka suka ce

    Leianna.

    Wata mai suna Leianna ta ce: “Neman yin suna yakan zama babban matsala idan mutum ya soma yin kome don ya sa a san da shi. Suna ganin kamar idan suka yi wani irin magana, ko suka saka wani irin kaya, ko suka yi wani abin a-zo-a-gani, ko da a dandalin sada zumunta ne, zai jawo hankalin mutane. Za ka yi da-na-sani idan ka yi abin da ka san cewa bai dace ba don kawai ka zama shahararre.”

Mutane suna karya don su nuna cewa su shahararru ne

Ba a kowane lokaci ba ne masu neman suna suke sa ransu a cikin hadari. Wata ’yar shekara 22 mai suna Erica ta fadi wani abu kuma da mutane suke yi, ta ce:

“Mutane sukan saka hotuna da yawa da za su sa a dauka cewa suna da abokai da yawa da suke shakatawa tare a kowane lokaci. Hakan zai sa mutane su ga kamar su shahararru ne.”

Wata ’yar shekara 15 mai suna Cara ta ce mutane sukan yi karya don a ga kamar sun yi suna sosai. Ta ce:

“Na taba ganin mutane sun saka hotuna da suka yi kamar suna wurin fati, alhali kuwa, a gida suke.”

Matthew, wani dan shekara 22, ya fadi yadda ya taba yin hakan, ya ce:

“Na taba saka wani hoto ya nuna cewa a Dutsen Everest na dauke shi, alhali ban taba zuwa wani wuri a Asiya ba!”

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Nufinmu shi ne mu yi gaskiya a cikin ayyukanmu duka.”​—Ibraniyawa 13:​18, New World Translation.

Ka yi tunani a kan wannan:

  • Idan kana amfani da dandalin sada zumunta, kana yin karya don ka sa a san da kai?

  • Kalamai da hotuna da kake sakawa suna nuna ainihin halinka da kuma imaninka?

    Abin da tsararku suka ce

    Hannah.

    Wata mai suna Hannah ta ce, “Wasu sukan yi iya kokarinsu su ga cewa mutane da yawa sun nuna cewa suna son abin da suka saka. Amma za ka so a sanka a matsayin wanda yake maganar banza ko yake sa kayan da bai kamata ba ko mai yin burga da abin da yake da shi? Ko za ka so a san ka a matsayin wanda yake da hankali kuma yana kyautata ma mutane? Idan mutane sun so abin da ka saka a dandalin sada zumunta, za ka yi murna, amma ka tabbata abubuwan kirki ne.”

Yawan mabiya da masu son abin da ka saka yana da muhimmanci ne?

Mutane da dama suna ganin idan kana so ka yi suna a intane, ka samo mabiya da yawa da masu son abin da kake sakawa a shafinka. Matthew wanda aka ambata dazu ya ce ra’ayinsa ke nan a dā. Ya ce:

“Nakan tambayi mutane, ‘mabiya nawa kake da su a shafinka?’ ko ‘Mene ne adadi mafi girma na mutanen da suka so abin da ka saka a shafinka?’ Don in sami mabiya da yawa, nakan bi mutane barkatai da ban ma san su ba, da fatan su ma za su bi ni. Na zama mai bala’in so a san da ni kuma dandalin sada zumunta ya dada zuga ni.”

Hotuna: 1. Wata matashiya tana murmushi da ta ga yawan mutane da suka nuna cewa suna son abin da ta saka a shafinta. 2. Yarinyar tana cin kayan kwadayi cike a kwano. 3. Yarinyar ta dora hannu a ciki tana damuwa.

Neman suna a intane kamar kayan kwadayi yake, za ka ji dadinsa na dan lokaci amma ba zai cika ma ciki ba

Maria, wata ’yar shekara 25, ta lura cewa wasu mutane suna ganin yawan mabiya da mutanen da ke son abin da suka saka ne yake nuna ko suna da daraja ko a’a. Ta ce:

“Idan yarinya ta saka hotonta kuma mutane da yawa ba su danna alamar cewa suna son hoton ba, sai ta dauka cewa ba ta da kyau. Mutane da suke son saka hotonsu a intane sukan ji hakan. Amma ba gaskiya ba ne. Gaskiyar ita ce, suna ba wa kansu wahala ne kawai.”

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada mu zama masu girman kai ko masu tā da hankalin juna ko masu kishin juna.”​—Galatiyawa 5:26.

Ka yi tunani a kan wannan:

  • Yin amfani da dandalin sada zumunta yana sa ka rika gwada kanka da wasu?

  • Ka fi so ka sami mabiya da yawa maimakon ka kulla abota da mutanen kirki?

    Abin da tsararka suka ce

    Joshua.

    Wani mai suna Joshua ya ce: “Idan kana so a san da kai sosai a dandalin sada zumunta, dole ka zama mutumin da ke jan hankalin mutane, kuma a yawancin lokuta sai ka zama kamar su kafin su san da kai. Hakan zai iya sa ka dami kanka a kan ra’ayinsu game da kai da abin da za ka yi don ka gamsar da su. Kowa yana so a so shi, amma idan mutum ya mai da hankali ainun ga neman suna, hakan zai iya jawo masa matsala.”

Kar ka nuna girman kai da wayo

Ka taba ganin mutanen da suke yin burga amma sai su yi kamar ba abin da suke so su yi ke nan ba?

  • “Tun da na sayi sabuwar motata gal a leda, mutane suna ta damu na wai in dauke su a ciki!”

  • “Ba na son yadda mutane suke ta yaba min don na samu na rage jiki!”

Masu irin maganganun nan sukan yi kamar ba sa so abin da ake musu don su nuna cewa su masu tawali’u ne, amma burga suke yi.

Gargadi: Irin wannan halin yakan ba mutane haushi don sukan gane cewa burga mutumin yake yi. Yin burga da wayo ne ya fi bata wa mutane rai domin ya nuna cewa mutumin yana wasa da hankalinsu.

Idan za ka saka hoto ko ka yi wani kalami a dandalin sada zumunta, ka guji nuna girman kai da wayo. Maimakon haka, ka bi shawarar Littafi Mai Tsarki da ta ce: “Bari wani ya yabe ka, ba kai da kanka ba.”​—Karin Magana 27:2.

Bita: Ta yaya za ka guji tarkon neman suna a dandalin sada zumunta?

  • Ka tabbata abin da kake sakawa a dandalin sada zumunta ya jitu da halinka da dabi’unka.

  • Ka tabbata abin da kake sakawa game da kanka gaskiya ne.

  • Kar ka dami kanka da yawan mabiya ko yawan mutane da suke son abin da ka saka.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba