Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • cl babi na 2 pp. 16-25
  • Za Ka Iya ‘Kusantar Allah’ da Gaske Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya ‘Kusantar Allah’ da Gaske Kuwa?
  • Ka Kusaci Jehobah
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Ya Buɗe Mana Hanya
  • Yadda Jehobah Ya Bayyana Kansa a Kalmarsa
  • “Ɗan Ya So Ya Bayyana” Shi
  • Abin Taimako Wajen Nazari
  • “Ga Shi, Wannan Allahnmu Ne”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Za Ka Iya Zama Aminin Jehobah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Allah da Kuma Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • ‘Zai Kusace Ka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Ka Kusaci Jehobah
cl babi na 2 pp. 16-25
Wata mata tana tunani mai zurfi a kan abin da ta karanta a Baibul.

BABI NA 2

Za Ka Iya ‘Kusantar Allah’ da Gaske Kuwa?

1, 2. (a) Me mutane da yawa za su ji ba zai yiwu ba, amma mene ne Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana? (b) Wace dangantaka ta kusa ce ke tsananin Ibrahim da Allah, kuma me ya sa?

YAYA za ka ji idan Mahaliccin sama da ƙasa ya ce game da kai, “Wannan abokina ne”? Ga mutane da yawa, wannan zai kasance abu ne da ba zai yiwu ba. Yaya kuwa taliki zai ƙulla abota da Jehobah Allah? Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana da gaske cewa za mu iya kusantar Allah.

2 Ibrahim na zamanin dā, ya more irin wannan kusanci. Jehobah ya ce game da wannan kakan, “abokina.” (Ishaya 41:8, NW) Hakika, Jehobah ya ɗauki Ibrahim abokinsa ne. Ibrahim yana da wannan dangantaka ta kusa ne domin “ya ba da gaskiya ga Allah.” (Yakub 2:23) A yau ma, Jehobah yana neman zarafin ƙulla abota da waɗanda suke bauta masa kuma ya nuna musu “ƙauna.” (Maimaitawar Shari’a 10:15) Kalmarsa ta ƙarfafa mu cewa: “Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku.” (Yakub 4:8) A waɗannan kalmomi, mun ga gayyata da kuma alkawari.

3. Wace gayyata ce Jehobah ya ba mu, kuma ta haɗa da wane alkawari?

3 Jehobah ya gayyace mu mu matso kusa da shi. Yana shirye ya karɓe mu mu zama abokanansa. A wannan lokacin kuma ya yi alkawarin cewa idan muka yi ƙoƙarin matsowa kusa da shi, shi ma zai yi haka. Zai kusace mu. Da haka, za mu zama “abokin” Jehobah. (Zabura 25:14) “Aboki” na musamman ne muke gaya wa sirri.

4. Ta yaya za ka kwatanta aboki na kusa, kuma a wace hanya ce Jehobah ya tabbatar shi irin wannan aboki ne ga waɗanda suka kusace shi?

4 Kana da aboki na kusa da za ka gaya wa sirrinka? Irin wannan aboki ne da ya damu da kai. Ka amince da shi, domin ya tabbatar shi amini ne. Farin cikinka zai ƙaru idan ka gaya masa batunka. Kunnensa mai tausayi yana rage zafin baƙin cikinka. Har a lokacin da kamar ba wanda yake fahimtarka, shi yana yi. Haka nan, sa’ad da ka kusaci Allah, za ka zo ga samun Aboki na musamman wanda yake ganinka da tamani da gaske, wanda ya damu da kai da gaske, kuma ya fahimce ka sosai. (Zabura 103:14; 1 Bitrus 5:7) Ka dogara a gare shi sosai, domin ka sani cewa amini ne ga waɗanda suka amince da shi. (Zabura 18:25) Duk da haka, wannan gatar kasancewa kusa da Allah ta yiwu ne domin shi ya sa ta yiwu.

Jehobah Ya Buɗe Mana Hanya

5. Mene ne Jehobah ya yi domin ya sa ya yiwu mu kusace shi?

5 Idan Jehobah bai taimaka mana ba, mu masu zunubi ba za mu taɓa kusantar sa ba. (Zabura 5:4) Manzo Bulus ya rubuta cewa: “Amma Allah ya tabbatar mana yawan ƙaunarsa, da yake tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu saboda mu.” (Romawa 5:8) Hakika, Jehobah ya shirya Yesu ya “ba da ransa domin ceton mutane da yawa.” (Matiyu 20:28) Bangaskiyarmu ga hadayar fansa ta sa ya yiwu mu kusaci Allah. Tun da Allah ne ya “fara ƙaunace mu,” ya kafa mana tushen shiga dangantaka da shi.—1 Yohanna 4:19.

6, 7. (a) Ta yaya muka sani cewa Jehobah ba Allah ba ne ɓoyayye kuma wanda ba za a san shi ba? (b) A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya bayyana kansa?

6 Jehobah ya sake yin wani abu: Ya bayyana mana kansa. A kowacce dangantaka, kusanta ta dangana ne bisa sanin mutumin da kuma son halayensa da hanyoyinsa. Idan Jehobah Allah ne da yake ɓoye, wanda ba za a iya saninsa ba, ba za mu taɓa kusantarsa ba. Duk da haka, bai ɓoye kansa ba, yana so mu san shi. (Ishaya 45:19) Bugu da ƙari, abin da ya bayyana game da kansa yana samuwa ga kowa, har ga mu waɗanda ba a ɗauke mu kome ba a duniya.—Matiyu 11:25.

Hotuna: Wasu hanyoyi da Jehobah yake bayyana mana kansa. 1. Fure da malam-bude-littafi. 2. Rana da teku. 3. Budadden Baibul.

Jehobah ya bayyana kansa ta wajen abin da ya halitta da kuma rubutacciyar Kalmarsa

7 Ta yaya Jehobah ya bayyana kansa gare mu? Abin da ya halitta sun nuna wasu ɓangaren mutuntakarsa, wato yawan ikonsa, zurfin hikimarsa, yawaitar ƙaunarsa. (Romawa 1:20) Amma bayyana kansa da Jehobah ya yi bai tsaya daga abin da ya halitta ba. Babban Mai Magana, ya yi tanadin rubutaccen wahayi game da kansa a cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki.

Yadda Jehobah Ya Bayyana Kansa a Kalmarsa

8. Me ya sa za a iya cewa Littafi Mai Tsarki kansa tabbaci ne na ƙaunar Jehobah gare mu?

8 Littafi Mai Tsarki kansa tabbaci ne na ƙaunar Jehobah gare mu. A cikin Kalmarsa, ya bayyana kansa a kalmomin da za mu fahimta. Hakan ya tabbatar da cewa ba kawai yana ƙaunar mu ba amma yana so mu san shi kuma mu ƙaunace shi. Abin da muka karanta a wannan littafi mai tamani ya taimake mu mu kusace shi. (Zabura 1:1-3) Bari mu tattauna wasu hanyoyi masu daɗaɗa zuciya da Jehobah ya bayyana kansa a cikin Kalmarsa.

9. Waɗanne ne wasu misalai na furuci na kai tsaye a cikin Littafi Mai Tsarki da suka nuna halayen Allah?

9 Nassosi suna ɗauke da furuci da yawa na kai tsaye da suke lissafa halayen Allah. Ka lura da wasu misalai. “Yahweh yana ƙaunar shari’ar gaskiya.” (Zabura 37:28) “Ikon [Allah] ya yi yawa.” (Ayuba 37:23) Jehobah ya ce: “Ni mai ƙauna marar canjawa ne.” (Irmiya 3:12) Shi “mai zuciyar hikima ne.” (Ayuba 9:4 ) Shi “Allah mai jinƙai ne, mai alheri, marar saurin fushi, mai yawan ƙauna marar canjawa, cike da aminci kuma.” (Fitowa 34:6) “Kai, ya Ubangiji, mai alheri ne kuma mai yin gafara.” (Zabura 86:5) Kuma, kamar yadda aka faɗa a babi na baya, hali ɗaya ya fi shahara: “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Yayin da kake bimbini bisa waɗannan halaye, ba ka sha’awar kusantar wannan Allah da ba shi da na biyunsa?

10, 11. (a) Don ya taimake mu mu ga mutuntakarsa sosai, mene ne Jehobah ya haɗa cikin Kalmarsa? (b) Wane misali ne na Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu ƙaga ikon Allah yana aiki?

10 Ƙari ga gaya mana halayensa, Jehobah cikin ƙauna ya haɗa cikin Kalmarsa takamammun misalai na waɗannan halaye. Irin wannan labaran suna zana hoton zuci da suke taimaka mana mu ga ɓangarori na mutuntakarsa sosai. Wannan kuma yana sa mu kusace shi. Ga wani misali.

Littafi Mai Tsarki yana taimaka mana mu kusaci Jehobah

11 Wani abu ne ka karanta cewa Allah yana da “girman iko.” (Ishaya 40:26) Wani ne kuma dabam ka karanta game da yadda ya ceci Isra’ilawa a Jar Teku kuma ya ciyar da al’ummar a daji na shekara 40. Za ka iya zana hoton zuci na mafaɗacin ruwa yana tsagewa biyu. Za ka iya tunanin al’ummar, wataƙila duka 3,000,000 suna tafiya a kan busashiyar ƙasa a daɓen tekun, dasƙararren ruwa yana tsaye kamar ganuwa a gefen hagu da na dama. (Fitowa 14:21; 15:8) Za ka ga tabbacin kāriyar Allah a cikin daji. Ruwa ya tumbatso daga dutse. Abinci, da ya yi kama da fararen iri suka bayyana a ƙasa. (Fitowa 16:31; Littafin Ƙidaya 20:11) A nan Jehobah bai nuna kawai cewa yana da iko ba amma yana amfani da shi domin mutanensa. Ba ƙarfafa ba ce mu sani cewa addu’o’inmu suna zuwa wajen Allah mai iko wanda “shi ne wurin ɓuyanmu da ƙarfinmu, taimakonmu na kurkusa lokacin wahala”?—Zabura 46:1.

12. Ta yaya Jehobah yake taimaka mana mu “fahimce” shi a kalmomin da za mu iya fahimta?

12 Jehobah, wanda ruhu ne, ya taimaka mana sosai mu san shi. Da yake mutane ne, iyakarmu duniya ta zahiri ne saboda ba ma iya ganin duniya ta ruhaniya. Don haka idan Allah zai kwatanta mana kansa a kalmomi na ruhu zai kasance ne kamar kana ƙoƙari ne ka kwatanta siffarka, kamar su launin idanunka ko kuma tawadar Allah ga wanda aka haife shi makaho. Maimakon haka, Jehobah ya taimaka mana mu “fahimce” shi a kalmomin da za mu fahimta. A wasu lokatai, ya yi amfani da misalai da kuma kwatanci, ya kwatanta kansa da abubuwa da muka sani. Ya kwatanta kansa ma kamar yana da wasu gaɓoɓi na mutane.a

13. Wane hoton zuci ne Ishaya 40:11 ta zana, kuma ta yaya wannan ya shafe ka?

13 Ka lura da kwatancin Jehobah da ke cikin Ishaya 40:11: “Yana ciyar da tumakinsa kamar yadda makiyayi yake yi. Yana tara ’yan tumakin a hannuwansa, ya rungume su a ƙirjinsa.” A nan an kwatanta Jehobah da makiyayi wanda yake ɗaukan ’ya’yan tumaki da “hannuwansa.” Wannan ya nuna iyawar Jehobah ya kāre kuma ya tallafa wa mutanensa, har da marasa ƙarfi. Za mu samu kwanciyar rai cikin hannunsa mai ƙarfi, idan muna da aminci a gare sa, ba zai taɓa yasar da mu ba. (Romawa 8:38, 39) Makiyayi Mafi Girma yana ɗaukan ɗan rago a “ƙirjinsa.” Furuci da ke nufin wata kalmasa da ke kwancewa a saman riga, inda wani lokaci makiyayi yake ɗaukan ɗan rago sabon haihuwa. Saboda haka an tabbatar mana cewa Jehobah yana ƙaunarmu kuma ya damu da mu. Daidai ne mu so mu kusace shi.

“Ɗan Ya So Ya Bayyana” Shi

14. Me ya sa za a iya cewa Jehobah ya bayyana sirrinsa sosai ta wajen Yesu?

14 A cikin Kalmarsa, Jehobah ya bayyana sirrinsa sosai ta wajen Ɗansa da yake ƙauna, Yesu. Babu wani wanda zai nuna tunanin Allah da kuma yadda yake ji sosai ko kuma ya bayyana Shi fiye da yadda Yesu ya yi. Ban da haka, Ɗan farin yana tare da Ubansa kafin a halicci wasu halittun ruhu da na sararin sama da ake gani. (Kolosiyawa 1:15) Yesu ya san Jehobah ƙwarai. Shi ya sa ya ce: “Ba wanda ya san ko wane ne Ɗan sai dai Uban kaɗai, ko kuma ya san ko wane ne Uban sai dai shi Ɗan, da kuma wanda Ɗan ya so ya bayyana masa.” (Luka 10:22) A lokacin da yake duniya, Yesu ya bayyana Ubansa a hanyoyi biyu masu muhimmanci.

15, 16. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya bayyana Ubansa?

15 Na farko, koyarwar Yesu ta taimake mu mu san Ubansa. Yesu ya kwatanta Jehobah a kalmomin da za su taɓa zukatanmu. Alal misali, wajen bayyana Allah mai jinƙai wanda yake marabtar masu zunubi da suka tuba. Yesu ya kwatanta Jehobah da uba mai gafartawa wanda ya motsa da ganin ɗansa almubazzari yana komowa sai ya sheƙa da gudu, ya rungumi ɗansa, ya yi ta yi masa sumba. (Luka 15:11-24) Yesu kuma ya kwatanta Jehobah cewa Allah ne wanda yake “jawo” mutane masu zukatan kirki domin yana ƙaunar kowannensu. (Yohanna 6:44) Ya sani idan ƙaramin gwarare ya faɗi ƙasa. Yesu ya ce: “Kada ku ji tsoro. Ai, kun fi ɗan tsuntsu daraja sau barkatai.” (Matiyu 10:29, 31) Babu shakka muna da tabbacin muna so mu kusaci irin wannan Allah mai kula.

16 Na biyu, misalin Yesu ya nuna yadda Jehobah yake. Yesu ya yi koyi da Ubansa sarai har ya ce: “Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban.” (Yohanna 14:9) Saboda haka, sa’ad da muke karatun Linjila game da Yesu, wato juyayin da ya yi da kuma hanyar da ya bi da wasu, a wata hanya muna ganin hoto ne mai rai na Ubansa. Babu yadda Jehobah zai bayyana mana halayensa fiye da haka kuma. Me ya sa?

17. Ka ba da misalin abin da Jehobah ya yi domin ya taimake mu mu fahimci yadda yake.

17 Alal misali: A ce kana so ka bayyana abin da kirki yake nufi. Za ka iya bayyana shi da kalmomi. Amma idan za ka iya nuna wani yana yin abin kirki kuma ka ce, “Wannan shi ne misalin abin kirki,” sai kalmar “kirki” ta ƙara ma’ana kuma ta kasance da sauƙin fahimta. Jehobah ya yi abu kusan haka ya taimake mu mu fahimci yadda yake. Haɗe da bayyana kansa cikin kalmomi, ya yi mana tanadin rayayyen misali na Ɗansa. A wurin Yesu, ana ganin halayen Allah sosai. Ta cikin kwatancin Yesu na Lingila, Jehobah yana cewa ne: “Wannan haka nake.” Yaya hurarren tarihi ya kwatanta Yesu lokacin da yake duniya?

18. Ta yaya Yesu ya nuna iko, shari’a, da kuma hikima?

18 Halaye huɗu na musamman na Allah, Yesu ya nuna su da kyau. Yana da iko bisa cututtuka, yunwa, har da mutuwa. Duk da haka, ba kamar mutane ba masu son kai waɗanda suke ɓarna da ikonsu, shi bai taɓa yin amfani da ikonsa na yin mu’ujiza domin kansa ba ko kuma domin ya cuci wasu. (Matiyu 4:2-4) Yana ƙaunar shari’ar gaskiya. Zuciyarsa ta cika da fushi da ya ga ’yan kasuwa suna yi wa mutane ha’inci. (Matiyu 21:12, 13) Ya bi da matalauta da kuma waɗanda ake wahalar da su babu wariya, ya taimaki waɗannan su sami “huta a zuciyarsu.” (Matiyu 11:4, 5, 28-30) A koyarwar Yesu ‘wanda ya fi Sulemanu girma’ da akwai hikima wadda babu irin ta. (Matiyu 12:42) Amma Yesu bai taɓa fahariya ba domin hikimarsa. Kalmominsa sun taɓa zukatan talakawa, domin koyarwarsa a bayyane take, tana da sauƙi, kuma tana yiwuwa.

19, 20. (a) Ta yaya Yesu misali ne mafi kyau na ƙauna? (b) Yayin da muke karatu, muke bimbini game da misalin Yesu, me za mu tuna da shi?

19 Yesu fitaccen misali ne na ƙauna. A cikin dukan hidimarsa, ya nuna ƙauna a hanyarta dabam dabam, haɗe da juyayi da kuma tausayi. Ba ya kallon wahalar wasu, ba tare da ya tausaya musu ba. Sau da yawa, wannan tausayin ya motsa shi ga aikatawa. (Matiyu 14:14) Ko da yake ya warkar da marasa lafiya kuma ya ciyar da mayunwata, Yesu ya nuna tausayi a hanya mafi muhimmanci. Ya taimake wasu su ƙaunaci gaskiyar Mulkin Allah, kuma su karɓe ta, wadda za ta kawo wa ’yan Adam albarka ta dindindin. (Markus 6:34; Luka 4:43) Fiye da kome, Yesu ya nuna ƙauna ta sadaukar da kai ta wajen ba da kansa da son rai domin wasu.—Yohanna 15:13.

20 Abin mamaki ne cewa mutane na dukan tsararraki da kuma kowacce ƙabila suna so su matso kusa da wannan mutum wanda yake da ƙauna da kuma juyayi? (Markus 10:13-16) Ko da yake, yayin da muke karatu game da shi kuma muke yin bimbini a kan misalin Yesu, bari mu riƙe a zuciyarmu cewa a cikin Ɗansa muna ganin kamanin Ubansa sosai.—Ibraniyawa 1:3.

Abin Taimako Wajen Nazari

21, 22. Mene ne yake ƙunshe cikin neman Jehobah, kuma ta yaya littafin nan zai taimaka mana wajen yin haka?

21 Ta wajen bayyana kansa sosai a cikin Kalmarsa, Jehobah ya nuna mana cewa yana so mu kusace shi. Amma, bai tilasta mana mu ƙulla dangantaka da shi ba. Hakkinmu ne mu nemi Jehobah “tun yana samuwa.” (Ishaya 55:6) Neman Jehobah ya ƙunshi sanin halayensa da kuma hanyoyinsa kamar yadda aka bayyana su cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan abin taimako wajen nazari da kake karantawa an shirya ne domin ya taimake ka wajen yin haka.

22 Za ka lura cewa wannan littafin an raba shi kashi kashi da suka yi daidai da halaye huɗu na musamman na Jehobah: iko, shari’a, hikima, da kuma ƙauna. Kowanne kashi ya fara ne da taƙaitaccen bayani game da wannan halin. Babobi na gaba sun tattauna yadda Jehobah ya nuna waɗannan halaye a ɓangarori dabam dabam. Kowanne sashe yana ɗauke da babi da yake nuna yadda Yesu ya ba da misalin wannan halin, da wani babi kuma wanda yake bincika yadda mu za mu nuna wannan halin a rayuwarmu.

23, 24. (a) Ka bayyana amfanin akwatin nan “Tambayoyi don Bimbini.” (b) Ta yaya bimbini yake taimaka mana mu kusaci Allah?

23 Daga wannan babin, akwai fasali na musamman da ke da jigo “Tambayoyi don Bimbini.” Alal misali, ka duba akwati da ke shafi na 24. Nassosin da kuma tambayoyin ba a tsara su domin maimaita abin da ke cikin babin ba. Maimakon haka, manufarsu shi ne su taimake ka ka yi bimbini a kan wasu abubuwa masu muhimmanci na wannan batu. Ta yaya za ka yi amfani da wannan da kyau? Ka dubi kowanne cikin ayoyin da aka rubuta, kuma ka karanta ayoyin a hankali. Sa’an nan ka bincika tambaya da take kan kowacce aya. Ka yi bimbini a kan amsoshin. Kana iya ƙara bincike. Ka yi wa kanka ƙarin tambayoyi: ‘Mene ne wannan yake gaya mini game da Jehobah? Ta yaya ya shafi rayuwata? Ta yaya zan yi amfani da shi in taimake wasu?’

24 Irin wannan bimbinin zai taimake mu mu kusaci Jehobah sosai. Me ya sa? Littafi Mai Tsarki ya haɗa bimbini da zuciya. (Zabura 19:14) Sa’ad da muka yi bimbini a nuna godiya ga abin da muka koya game da Allah, sanin zai shiga zuciyarmu ta alama, a inda zai taɓa tunaninmu, ya motsa mu, kuma a ƙarshe ya motsa mu ga aikatawa. Ƙaunarmu ga Allah za ta ƙaru, kuma wannan ƙaunar za ta motsa mu mu so yin abin da zai faranta masa rai tun da Abokinmu ne da muke ƙauna. (1 Yohanna 5:3) Don mu shiga irin wannan dangantakar, dole ne mu san halayen Jehobah da kuma hanyoyinsa. Da farko, bari mu tattauna ɓangaren mutuntakar Allah da ya ba da dalili wanda zai sa mu kusace shi, wato tsarkakarsa.

a Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya yi maganar fuskar Allah, idanunsa, kunnuwansa, hancinsa, bakinsa, hannunsa, da kuma ƙafafuwansa. (Zabura 18:15; 27:8; 44:3; Ishaya 60:13; Matiyu 4:4; 1 Bitrus 3:12) Irin wannan furuci na kwatanci kada a ɗauke shi a zahiri, kamar yadda ba za mu ɗauki kwatanta Jehobah da “Dutse” ko kuma “garkuwa” a zahiri ba.—Maimaitawar Shari’a 32:4; Zabura 84:11.

Tambayoyi don Bimbini

  • Zabura 15:1-5 Mene ne Jehobah yake bukata daga waɗanda suke so su zama abokanansa?

  • Zabura 34:1-18 Jehobah yana kusa da su wa, kuma waɗannan za su kasance da wane tabbaci game da shi?

  • Zabura 145:18-21 Waɗanne ayyuka ne za mu yi su sa mu kusaci Jehobah?

  • 2 Korintiyawa 6:14–7:1 Waɗanne halaye ne suke da muhimmanci idan muna so mu kasance da dangantaka ta kusa da Jehobah?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba