BABI NA 26
Allah “Mai Yin Gafara”
1-3. (a) Wane kaya mai nauyi ne mai Zabura Dauda ya ɗauka, kuma ta yaya ya samu lallami ga wahalar zuciyarsa? (b) Idan muka yi zunubi, wane nauyi ne za mu ɗauka domin wannan, amma mene ne Jehobah ya tabbatar mana?
“ZUNUBAINA sun sha kaina” haka mai Zabura Dauda ya rubuta. “Kamar kaya mai nauyi sun fi ƙarfina. Na gaji kakaf, an kuma tattake ni ƙwarai.” (Zabura 38:4, 8) Dauda ya san yadda lamiri mai laifi yake da nauyi. Amma ya samu lallami ga wahalar zuciyarsa. Ya fahimci cewa ko da yake Jehobah yana ƙin zunubi, ba ya ƙin mai zunubi idan wannan ya tuba da gaske ne kuma ya guje wa tafarkin zunubi. Da cikakkiyar bangaskiya cewa Jehobah yana shirye ya yi jinƙai ga wanda ya tuba, Dauda ya ce: “Ya Ubangiji, mai alheri ne kuma mai yin gafara.”—Zabura 86:5.
2 Sa’ad da muka yi zunubi, mu ma za mu ɗauki nauyin lamiri mai ciwo. Wannan yin nadama tana da kyau. Za ta sa mu yi ƙoƙarin gyara halinmu. Amma, da akwai haɗarin nauyaya domin zunubi. Zuciyarmu mai hukunci za ta iya nacewa cewa Jehobah ba zai gafarta mana ba, ko yaya muka tuba. Idan muka ‘nitse’ cikin baƙin cikin laifi, Shaiɗan zai yi ƙoƙari ya sa mu fid da rai, ta jin cewa Jehobah yana ganinmu marasa amfani, waɗanda ba su cancanci bauta masa ba.—2 Korintiyawa 2:5-11.
3 Haka ne Jehobah yake ɗaukan al’amura? A’a! Gafartawa ɓangare ne na ƙauna mai girma ta Jehobah. A cikin Kalmarsa, ya tabbatar mana cewa idan muka nuna tuba ta gaskiya daga zuciyarmu, a shirye yake ya gafarta. (Karin Magana 28:13) Domin mu guje wa jin cewa gafarar Jehobah aba ce da ba za mu taɓa samu ba, bari mu bincika abin da ya sa yake gafartawa da kuma yadda yake gafartawa.
Dalilin da Ya Sa Jehobah “Mai Gafara” Ne
4. Mene ne Jehobah yake tuna game da yanayinmu, kuma ta yaya wannan yake shafar yadda yake bi da mu?
4 Jehobah yana sane da kasawarmu. “Ya san abin da aka yi mu da shi, yana kuma tuna cewa mu ƙurar ƙasa ne,” in ji Zabura 103:14. Ba ya manta cewa mu halittu ne daga turɓaya, masu kumamanci, domin ajizanci. Furucin nan ya san “abin da aka yi mu da shi” yana tuna mana cewa Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Jehobah da maginin tukwane mu kuma an kwatanta mu da tukwanen yumɓu da ya gina. (Irmiya 18:2-6) Maginin Tukwane Mai Girma yana sauƙaƙa yadda yake bi da mu bisa ga kumamancinmu na zunubi da yadda muka amsa kuma da yadda muka ƙi bin ja-gorarsa.
5. Yaya littafin Romawa ya kwatanta ikon danƙewa na zunubi?
5 Jehobah ya fahimci yadda zunubi yake da tasiri. Kalmarsa ta kwatanta zunubi da cewa iko ne mai ƙarfi da ya danƙe mutum. Yaya ƙarfin danƙewarsa? A cikin littafin Romawa, manzo Bulus ya yi bayani: Muna “ƙarƙashin ikon zunubi” kamar sojoji a ƙarƙashin kwamandansu (Romawa 3:9); zunubi ya yi ‘mulki’ bisa ’yan Adam kamar sarki (Romawa 5:21); yana “zama,” cikinmu (Romawa 7:17, 20); “ƙa’idar” sa tana aiki a cikinmu kullayaumi, wato, yana ƙoƙarin ya ja-goranci tafarkinmu. (Romawa 7:23, 25) Lalle zunubi ya danƙe jikinmu ajizi!—Romawa 7:21, 24.
6, 7. (a) Yaya Jehobah yake ganin waɗanda suke biɗan jinƙansa da zuciya mai nadama? (b) Me ya sa ba za mu ɗauki jinƙan Allah dalilin zunubi ba?
6 Jehobah ya sani cewa cikakkiyar biyayya ba za ta yiwu ba, ko yaya muke so mu kasance da cikakkiyar biyayya a gare shi. Ya tabbatar mana cikin ƙauna cewa sa’ad da muka nemi jinƙansa da zuciya mai nadama, zai gafarta mana. Zabura 51:17 ta ce: “Ya Allah, hadaya ta gaske a wurinka, ita ce halin sauƙin kai, halin sauƙin kai da zuciya mai tuba ba za ka ƙi ba, ya Allah.” Jehobah ba zai taɓa ƙin, ko kuma ya kori, mutum mai ‘sauƙin kai’ domin nauyin alhakin laifi ba.
7 Wannan yana nufi ne cewa za mu ɗauki jinƙan Allah banza, dalilin yin zunubi? A’a! Ba motsin rai ba ne yake rinjayar Jehobah. Jinƙansa yana da iyaka. Ba zai taɓa gafarta wa waɗanda suke zunubi domin taurin zuciya ba, ba sa nuna tuba. (Ibraniyawa 10:26) A wani ɓangare kuma, idan ya ga zuciya da take nadama, yana shirye ya gafarta. Bari yanzu mu ga wasu kalmomi da aka yi amfani da su a cikin Littafi Mai Tsarki wajen kwatanta wannan ɓangare na ban sha’awa na ƙaunar Jehobah.
Jehobah Yana Gafartawa Gabaki Ɗaya Kuwa?
8. Mene ne Jehobah yake yi sa’ad da yake gafarta mana zunubanmu, kuma wane tabbaci ne wannan yake ba mu?
8 Dauda da ya tuba ya ce: “Na furta zunubaina gare ka ban ɓoye laifofina ba. . . . Ka kuwa gafarta mini laifofina.” (Zabura 32:5) Kalmar nan “gafarta” ta fassara kalmar Ibrananci da ainihi take nufi “ɗaga” ko kuma “ɗauka.” Amfani da ita a nan tana nuna ɗauke “alhakin laifi, saɓo, zunubi.” Wato, Jehobah ya ɗaga zunubin Dauda ne, ya kawar da su. Wannan babu shakka ya sauƙaƙa alhakin laifin da Dauda yake ɗauke da shi. (Zabura 32:3) Mu ma za mu iya kasancewa da cikakken tabbaci ga Allah wanda yake ɗaukan zunubin waɗanda suka nemi gafararsa bisa bangaskiyarsu ga hadayar fansa ta Yesu.—Matiyu 20:28.
9. Yaya nisan yadda Jehobah yake kawar da zunubinmu daga gare mu yake?
9 Dauda ya yi amfani da wani furuci ya kwatanta gafartawa ta Jehobah: “Kamar yadda gabas take nesa da yamma, haka ne ya sa zunuban gangancinmu sun yi nesa da mu.” (Zabura 103:12) Yaya nisan gabas daga yamma yake? Nisan gabas daga yamma ba ta da iyaka; waje biyun ba za su taɓa haɗuwa ba. Wani manazarci ya lura cewa wannan furucin yana nufin “yadda nisan ya yiwu; nisan da za mu iya tunaninsa.” Hurarrun kalmomin Dauda sun gaya mana cewa sa’ad da Jehobah ya gafarta, yana kawar da zunubanmu da nisa yadda ba za mu yi tsammani ba daga gare mu.
‘[Zunubanku] . . . za su yi fari kamar [dusar ƙanƙara]’
10. Sa’ad da Jehobah ya gafarta mana zunubanmu, me ya sa bai kamata mu ji cewa muna ɗauke da tabon wannan zunubin ba a duk rayuwarmu?
10 Ka taɓa ƙoƙarin cire datti daga farar riga? Wataƙila duk da ƙoƙarinka dattin ya kasance ana gani. Ka lura yadda Jehobah ya kwatanta yawan yadda yake gafartawa: “Ko da kun yi ja wur da zunubi, za ku yi fari fat kamar [dusar ƙanƙara]. Ko da laifofinku sun sa kun yi ja kamar jini, za ku koma fari kamar farin ulu.” (Ishaya 1:18) Ba za mu taɓa iya cire tabon zunubi ba ta wajen ƙoƙarinmu. Amma Jehobah zai iya ɗaukar zunuban da suka yi ja da waɗanda suka yi ja kamar garura ya mai da su fari fat kamar dusar ƙanƙara ko ulu da ba a rine ba. Sa’ad da Jehobah ya gafarta mana zunubanmu, ba ma bukatar jin cewa muna ɗauke da tabon wannan zunubi a duk rayuwarmu.
11. A wace hanya ce Jehobah yake yar da zunubi a bayansa?
11 A waƙar godiya da Hezekiah ya yi bayan an ceci ransa daga ciwon ajali, ya ce wa Jehobah: “Ka kawar da dukan zunubaina daga gabanka.” (Ishaya 38:17) A nan an nuna cewa Jehobah yana ɗaukan zunuban masu laifi da suka tuba ya yar da su a bayansa inda ba zai gansu ba ko kuma ya lura da su. In ji wata majiya, za a iya furta abin da ake nufi haka: “Ka mayar da [zunubai na] kamar ba su taɓa faruwa ba.” Wannan ba yana da ban ƙarfafa ba?
12. Yaya annabi Mikah ya nuna cewa sa’ad da Jehobah ya gafarta, Ya ɗauke zunubanmu dindindin?
12 A cikin alkawarin maidowa, annabi Mikah ya furta tabbacinsa cewa Jehobah zai gafarta wa mutanensa da suka tuba: “Babu wani Allah kamarka, . . . mai kawar da zunubi na ragowar jama’arka ta gādo. . . . Za ka jefar da dukan zunubanmu a cikin zurfafan teku.” (Mika 7:18, 19) Ka yi tunanin abin da kalmomin nan suke nufi ga waɗanda suke a zamanin Littafi Mai Tsarki. Zai yiwu ne a maido da abin da aka riga aka jefa “cikin zurfin teku”? Saboda haka, kalmomin Mikah sun nuna cewa sa’ad da Jehobah ya gafarta, ya ɗauke zunubanmu dindindin.
13. Mene ne ma’anar kalmomin Yesu “Ka gafarta mana [basusukanmu]”?
13 Yesu ya yi amfani da dangantaka da ke tsakanin mai ba da bashi da mai cin bashi ya kwatanta gafartawa ta Jehobah. Yesu ya aririce mu mu yi addu’a: “Ka gafarta mana [basusukanmu].” (Matiyu 6:12) Saboda haka Yesu ya kwatanta zunubi da bashi. (Luka 11:4) Sa’ad da muka yi zunubi mun zama “mabarta” ga Jehobah. Game da kalmar Helenanci da aka fassara “gafarta,” wani littafin neman bayani ya ce: “A ƙyale, a bar bashi, ta wajen ƙin neman a biya bashin.” Wato, sa’ad da Jehobah ya yi gafara, ya yafe bashin da yake binmu ne. Saboda haka masu zunubi da suka tuba sai su ƙarfafa. Jehobah ba zai taɓa neman a biya bashin da ya yafe ba!—Zabura 32:1, 2.
14. Furucin “domin a wanke zunubanku” yana sa mutane su yi tunanin me?
14 Gafartawar Jehobah an ƙara kwatanta ta a Ayyukan Manzanni 3:19: “Ku tuba, ku juyo ga Allah domin a wanke zunubanku.” Wannan kalmar ta kusa da ta ƙarshen ta fassara aikatau na Helenanci da yake nufin “Wanke, . . . kashe ko kuma halaka.” In ji wasu manazarta, ma’anar furucin na wanke rubutun hannu ne. Ta yaya wannan zai yiwu? Tawadar da ake yin amfani da ita a zamanin dā ana yin ta ne da gawayi, ƙaro, da kuma ruwa. Ba da daɗewa ba bayan rubutu da wannan tawadar, mutum zai iya ɗaukan jiƙaƙƙen tsumma ya wanke rubutun. A cikin wannan akwai kwatanci na jinƙan Jehobah. Idan ya gafarta mana zunubanmu, kamar ya ɗauki tsumma ne ya wanke su.
15. Mene ne Jehobah yake so mu sani game da shi?
15 Idan muka yi waswasi bisa waɗannan kwatanci dabam dabam, ba a bayyane yake ba cewa Jehobah yana son mu sani cewa da gaske yana shirye ya gafarta mana zunubi tun da ya ga mun tuba da gaske? Ba ma bukatar mu ji tsoro cewa zai riƙe mu domin waɗannan zunuban a nan gaba. Wannan ya bayyana a wani abu da Littafi Mai Tsarki ya bayyana game da jinƙai mai girma na Jehobah: Sa’ad da ya gafarta, ya manta.
Jehobah yana so mu sani cewa shi “mai yin gafara” ne
“Ba Kuwa Zan Sāke Tunawa da Zunubansu Ba”
16, 17. Idan Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ya manta da zunubanmu, mene ne yake nufi, kuma me ya sa ka ba da wannan amsar?
16 Jehobah ya yi alkawari game da waɗanda suke cikin sabon alkawari: “Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan sāke tunawa da zunubansu ba.” (Irmiya 31:34) Wannan yana nufi ne cewa idan Jehobah ya gafarta ba zai iya tuna da zunubai ba kuma? Da ƙyar ya zama haka. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da zunubai na mutane da yawa da Jehobah ya gafarta, har da Dauda. (2 Sama’ila 11:1-17; 12:13) A bayyane yake cewa Jehobah har yanzu yana sane da zunubi da suka yi. Tarihin zunubansu, da kuma tuba da gafarar Allah, duka an adana domin amfaninmu. (Romawa 15:4) To, mene ne Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ce Jehobah ba ya “tuna” zunuban waɗanda ya gafarta musu?
17 Aikatau na Ibrananci da aka fassara “zan tuna” yana nufi fiye da kawai tuna abin da ya wuce. Theological Wordbook of the Old Testament ya lura cewa ya haɗa da “ɗaukan mataki da ya dace.” Saboda haka, a nan, “tuna” zunubi ya haɗa da ɗaukan matakin gāba da masu zunubin. (Hosiya 9:9) Amma da Allah ya ce “ba kuwa zan sāke tunawa da zunubansu ba,” yana tabbatar musu ne cewa da zarar ya gafarta wa masu zunubi da suka tuba, ba zai ɗauki mataki ba gāba da su domin wannan zunubin. (Ezekiyel 18:21, 22) Mantuwa da Jehobah yake yi ita ce wato ba zai sake ta da batun ba domin ya tuhume mu ko ya yi mana horo dominsa sau da yawa. Ba abin ƙarfafa ba ne mu sani cewa Allahnmu yana gafartawa kuma ya manta?
To Yaya Batun Hakkin Zunubin?
18. Me ya sa gafartawa ba ya nufin cewa mai zunubi da ya tuba ya wanku daga hakkin zunubinsa?
18 Kasancewar Jehobah a shirye ya gafarta tana nufi ne cewa mai zunubi da ya tuba ya wanku daga dukan hakkin tafarkinsa na saɓo? A’a. Ba za mu yi zunubi ba kuma mu yi tunanin ba abin da zai same mu. Bulus ya rubuta: “Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.” (Galatiyawa 6:7) Za mu fuskanci wasu hakkin halayenmu. Wannan ba ya nufin cewa bayan ya gafarta mana Jehobah zai sa bala’i ya faɗo mana. Sa’ad da masifa ta faɗo, kada Kirista ya yi tsammanin cewa, ‘Wataƙila Jehobah ne yake yi masa horo domin zunubinsa na dā.’ (Yakub 1:13) A wani ɓangare kuma, Jehobah ba ya kāre mu daga sakamakon munanan ayyukanmu. Kashe aure, cikin shege, cututtuka daga jima’i, da kuma rashin yarda ko kuma daraja—dukan waɗannan abin baƙin cikin da za su iya kasancewa sakamakon da ba makawa ne na zunubi. Ka tuna cewa bayan ma ya gafarta wa Dauda zunubinsa game da Bath-sheba matar Uriah, Jehobah bai kāre Dauda daga sakamako na bala’i da ya biyo baya ba.—2 Sama’ila 12:9-12.
19-21. (a) Ta yaya doka da take rubuce a Littafin Firistoci 6:1-7 ta amfani wanda aka cuta da wanda ya yi cuta? (b) Idan zunubinmu ya ɓata wa wasu rai, Jehobah zai yi farin ciki idan muka ɗauki wane mataki?
19 Zunubanmu za su kasance da ƙarin hakki, musamman ma idan abin da muka yi ya ɓata wa wasu rai. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ke Littafin Firistoci sura 6. A nan Dokar Musa ta yi magana ne bisa yanayi da mutum ya yi zunubi mai tsanani ta wajen ƙwace kayan ɗan’uwansa Ba’isra’ile ko ta wajen fashi, zamba ko damfara. Kuma mai zunubi ya musanta laifinsa, har ya kai ga rantsuwar ƙarya. Inda kalmar mutum ɗaya ta saɓa ne da ta ɗayan. Amma, daga baya sai mai zunubin lamirinsa ya dame shi ya yi ikirarin zunubinsa. Domin ya samu gafarar Allah, yana bukatar ya yi abubuwa uku: ya maida abin da ya ɗauka, ya biya wanda ya ɗauki abin sa diyyar kashi 20 na abin da ya sata, kuma ya ba da rago domin hadaya ta zunubi. Sai dokar ta ce: “Firist zai ɗauki alhakin zunubi domin mutumin a gaban Yahweh, za a kuwa gafarta masa.”—Littafin Firistoci 6:1-7.
20 Dokar tanadi ne jinƙai daga Allah. Tana amfanar wanda aka cuta, wanda aka mai da masa da kayansa kuma babu shakka zai samu sauƙi sa’ad da mai laifin ya yarda da laifinsa. Har ila kuma, dokar ta amfani wanda lamirinsa a ƙarshe ya motsa shi ya yarda da laifinsa kuma ya gyara halinsa. Idan ya ƙi ya yi haka, to babu wata gafara dominsa daga wajen Allah.
21 Ko da yake ba ma ƙarƙashin Dokar Musa, Dokar ta ba mu fahimi cikin azancin Jehobah, haɗe da tunaninsa game da gafara. (Kolosiyawa 2:13, 14) Idan zunubinmu ya ɓata wa wasu rai, Allah zai yi farin ciki idan muka yi iyakar ƙoƙarinmu domin gyara halinmu. (Matiyu 5:23, 24) Wannan zai haɗa da fahimtar zunubinmu, yarda da shi, da kuma ba wa wanda ya cutu haƙuri. Sa’an nan za mu yi addu’a ga Jehobah bisa hadayar Yesu kuma mu samu tabbacin cewa ya gafarta mana.—Ibraniyawa 10:21, 22.
22. Mene ne zai biyo bayan gafarar Jehobah?
22 Kamar uba mai ƙauna, Jehobah yana yin gafara tare da ɗan horo. (Karin Magana 3:11, 12) Kirista da ya tuba zai bukaci ya tuɓe matsayinsa na dattijo, bawa mai hidima, ko kuma mai wa’azi na cikakken lokaci. Zai kasance da zafi a gare shi ya yi rashin gata da yake so ƙwarai. Amma irin wannan horo, ba ya nufin cewa Jehobah ya hana gafara. Dole ne mu tuna cewa horo daga Jehobah tabbaci ne na ƙaunarsa. Karɓa da kuma yin amfani da shi domin amfaninmu ne.—Ibraniyawa 12:5-11.
23. Me ya sa bai kamata mu kammala ba cewa ba mu kai Jehobah ya yi mana jinƙai ba, kuma me ya sa ya kamata mu yi koyi da gafararsa?
23 Lalle yana da wartsakewa mu sani cewa Allah “mai yin gafara” ne! Duk da kuskure da muka riga muka yi, kada mu kammala da cewa ba mu kai Jehobah ya yi mana jinƙai ba. Idan mun tuba da gaske, mun ɗauki matakai mu gyara halayenmu, kuma muka yi addu’a domin gafara bisa jinin da Yesu ya zubar, to za mu tabbata cewa Jehobah zai gafarta mana. (1 Yohanna 1:9) Bari mu bincika gafararsa a sha’aninmu da juna. Domin ma, idan Jehobah wanda ba ya zunubi, ya gafarta mana cikin ƙauna, bai kamata mu mutane masu zunubi mu gafarta wa juna ba?