TALIFIN NAZARI NA 19
WAƘA TA 6 Sammai Suna Nuna Ɗaukakar Jehobah
Ku Yi Koyi da Malaꞌikun Jehobah
“Yabi Yahweh, ya ku malaꞌikunsa.”—ZAB. 103:20.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga darussan da za mu koya daga wurin malaꞌiku.
1-2. (a) Wane bambanci ne ke tsakaninmu da malaꞌiku? (b) A waɗanne hanyoyi ne muka yi kama da malaꞌiku?
SAꞌAD DA muka soma bauta wa Jehobah, mun shiga cikin iyalin da ke bauta masa. A cikin iyalin nan, akwai ꞌyanꞌuwanmu maza da mata da kuma miliyoyin malaꞌiku. (Dan. 7:9, 10) Mun san cewa akwai bambanci sosai tsakaninmu da malaꞌiku. Alal misali, malaꞌiku sun daɗe suna rayuwa, an halicce su kafin ma a halicci Adamu. (Ayu. 38:4, 7) Ƙari ga haka, sun fi mu ƙarfi. Suna da tsarki fiye da mu, kuma sun fi mu yin adalci domin mu masu zunubi ne.—Luk. 9:26.
2 Duk da haka, muna kama da malaꞌiku a wasu hanyoyi. Alal misali, malaꞌiku suna iya nuna halaye masu kyau irin na Jehobah, kuma mu ma za mu iya yin haka. Muna da ꞌyancin zaɓan abin da za mu yi kamar yadda su ma suke da shi. Kowane malaꞌika yana da sunansa, da irin halinsa da kuma aikin da aka ba shi. Mu ma muna da abubuwan nan. Ƙari ga haka, muna son bauta wa Mahaliccinmu kamar yadda suke so.—1 Bit. 1:12.
3. Mene ne za mu iya koya daga wurin malaꞌiku?
3 Da yake muna kama da malaꞌiku a hanyoyi da yawa, yin bincike a kansu zai ƙarfafa mu, kuma zai sa mu koyi darussa da yawa masu muhimmanci. A wannan talifin, za mu ga yadda za mu yi koyi da sauƙin kan malaꞌiku, da yadda suke ƙaunar mutane, da jimirinsu, da kuma aikin da suke yi don su sa ikilisiya ta kasance da tsabta.
MALAꞌIKU SUNA DA SAUƘIN KAI
4. (a) Ta yaya malaꞌiku suke nuna sauƙin kai? (b) Me ya sa malaꞌiku suke da sauƙin kai haka? (Zabura 89:7)
4 Malaꞌiku suna da sauƙin kai. Ko da yake sun san abubuwa da yawa, kuma suna da iko sosai da kuma hikima, suna bin abin da Jehobah ya ce. (Zab. 103:20) Ko da me suka yi, ba sa taƙama, kuma ba sa yin amfani da ikonsu su yi abu don kawai a ɗaukaka su. Suna yin duk abin da Jehobah ya ce su yi da farin ciki, ko da ba a san sunansu ba.a (Far. 32:24, 29; 2 Sar. 19:35) Kuma ba sa yarda a ɗaukaka su maimakon Jehobah. Me ya sa malaꞌiku suke da sauƙin kai haka? Domin suna ƙaunar Jehobah kuma suna girmama shi sosai.—Karanta Zabura 89:7.
5. Ta yaya wani malaꞌika ya nuna sauƙin kai lokacin da yake yi wa Yohanna gyara? (Ka kuma duba hoton.)
5 Ga wani labari da ya nuna cewa malaꞌiku suna da sauƙin kai. A wajen shekara ta 96 bayan haihuwar Yesu, wani malaꞌika da ba a ambata sunansa ba, ya nuna wa Yohanna abubuwa masu ban mamaki a wahayi. (R. Yar. 1:1) Mene ne Yohanna ya yi da ya ga abubuwan nan? Ya so ya yi wa malaꞌikan sujada. Amma sai malaꞌikan ya yi sauri ya hana shi, kuma ya ce: “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bautarku ne, kai da ꞌyanꞌuwanka . . . Yi wa Allah sujada!” (R. Yar. 19:10) Ba shakka, wannan malaꞌikan mai sauƙin kai ne sosai! Bai so a girmama shi ba. A maimakon haka, ya gaya wa Yohanna ya yi wa Allah sujada. Kuma malaꞌikan bai rena Yohanna ba. Ko da yake ya daɗe yana bauta ma Jehobah kuma ya fi Yohanna iko sosai, ya ƙasƙantar da kansa, kuma ya ce shi ma bawan Allah ne kamar Yohanna. Ƙari ga haka, da yake yi wa Yohanna gyara, ya daraja shi. Ba mamaki ya san cewa abin da Yohanna ya gani ne ya sa ya so ya yi masa sujada.
Da malaꞌikan yake magana da Yohanna, malaꞌikan ya nuna sauƙin kai (Ka duba sakin layi na 5)
6. Ta yaya za mu yi koyi da sauƙin kan malaꞌiku?
6 Ta yaya za mu yi koyi da sauƙin kan malaꞌiku? Idan muka yi wani aiki a ƙungiyar Jehobah, ba zai dace mu yi taƙama ko mu yi ƙoƙarin sa a yaba mana ba. (1 Kor. 4:7) Ƙari ga haka, kada mu ɗauka cewa mun fi wasu ꞌyanꞌuwa don mun daɗe muna bauta ma Jehobah, ko muna yin wasu ayyuka na musamman. Idan muna yin ayyuka da dama a ƙungiyar Jehobah, mu ne ya kamata mu fi kasancewa da sauƙin kai. (Luk. 9:48) Kamar malaꞌiku, abin da ya kamata mu sa a gaba shi ne yi wa mutane hidima, ba ɗaukaka kanmu ba.
7. Ta yaya za mu nuna sauƙin kai idan za mu yi wa mutum gyara?
7 Zai kuma dace mu nuna sauƙin kai idan za mu yi ma wani a ikilisiya ko yaranmu gyara. Wani lokaci, zai dace mu gaya wa mutum gaskiya ba ɓoye-ɓoye. Amma kamar malaꞌikan da muka ambata ɗazu, ko da za mu gaya wa mutum gaskiya, bai kamata mu yi hakan a hanyar da zai sa mutumin ya yi sanyin gwiwa ba. Idan ba ma tunanin cewa mun fi wasu, zai yi mana sauƙi mu yi musu gyara cikin ƙauna da ban girma.—Kol. 4:6.
MALAꞌIKU SUNA ƘAUNAR MUTANE
8. (a) Bisa ga Luka 15:10, me ya nuna cewa malaꞌiku suna ƙaunar mutane? (b) Ta yaya malaꞌiku suke taimaka mana saꞌad da muke waꞌazi? (Ka kuma duba hoton.)
8 Malaꞌiku sun damu da abin da yake faruwa da mu domin suna ƙaunar mu. Shi ya sa suke farin ciki saꞌad da mai zunubi ya tuba, ko wanda ya daina bauta ma Jehobah ya komo gare shi. Kuma suna farin ciki saꞌad da mutum ya koya game da Jehobah, ya canja halinsa kuma ya soma bauta masa. (Karanta Luka 15:10) Ƙari ga haka, malaꞌiku suna taimaka mana a waꞌazin da muke yi. (R. Yar. 14:6) Ba sa yi wa mutane magana kai tsaye, amma za su iya taimaka mana mu haɗu da wanda yake so ya san Jehobah. Ban da malaꞌiku, Jehobah zai iya yin amfani da ruhu mai tsarki don ya yi wa mutanensa ja-goranci. Saboda haka, ba za mu iya faɗa da tabbaci cewa malaꞌika ne ya sa muka je gun wani ko wata saꞌad da muke waꞌazi ba. (A. M. 16:6, 7) Duk da haka, Jehobah yana amfani da malaꞌiku sosai. Don haka idan muna waꞌazi, kada mu yi shakkar cewa malaꞌiku suna tare da mu.—Ka duba akwatin da ya ce, “An Amsa Adduꞌoꞌinsu.”b
Wani ɗanꞌuwa da matarsa sun kammala yin waꞌazi da amalanke suna komawa gida. Da suke kan tafiya, sai ꞌyarꞌuwar ta ga wata mata tana cikin damuwa. ꞌYarꞌuwar ta san cewa malaꞌiku za su iya sa mu haɗu da waɗanda suke so su san Jehobah. Don haka, ta tausaya wa matar kuma ta ƙarfafa ta (Ka duba sakin layi na 8)
9. Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar mutane kamar malaꞌiku?
9 Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar mutane kamar malaꞌiku? Idan muka ji cewa an dawo da wani da aka cire daga ikilisiya, mu yi farin ciki kamar yadda malaꞌiku suke yi. Mu yi ƙoƙari mu marabci mutumin, kuma mu nuna masa cewa muna ƙaunar sa. (Luk. 15:4-7; 2 Kor. 2:6-8) Za mu kuma iya yin koyi da malaꞌiku ta wurin yin waꞌazi iya gwargwadon ƙarfinmu. (M. Wa. 11:6) Kuma zai dace mu nemi yadda za mu taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu a hidimarsu, kamar yadda malaꞌiku suke taimaka mana. Alal misali, za mu iya shirya yadda za mu yi waꞌazi tare da mai shela da bai ƙware kamar mu ba. Za mu kuma iya taimaka ma tsofaffi da marasa lafiya su iya yin waꞌazi.
10. Me muka koya daga labarin ꞌYarꞌuwa Sara?
10 Idan yanayinmu yana hana mu yin wasu abubuwa kuma fa? Kada mu damu, malaꞌiku za su taimaka mana mu yi nasara a duk wata hanyar da muke yin waꞌazi. Ga abin da ya faru da wata ꞌyarꞌuwa mai suna Sarac a ƙasar Indiya. Ta yi shekaru 20 tana hidimar majagaba. Amma sai ta soma rashin lafiya da ya kwantar da ita, kuma ba ta iya sauka daga kan gadonta. Abin ya sa ta baƙin ciki sosai. Amma taimakon da ꞌyanꞌuwa suka yi mata, da karatun Littafi Mai Tsarki da take yi babu fashi, sun sa ta daina baƙin ciki. Tun da ba za ta iya fita ba, dole ta koma yin waꞌazi ta wasu hanyoyi dabam. Ko zama ba ta iya yi, balle ta rubuta wasiƙa. Don haka, ta waya ne kaɗai take iya yin waꞌazi. Da ta kira waɗanda take yin nazari da su, sai suka gaya mata cewa akwai wasu da za su so a yi nazari da su. A sakamakon haka, cikin ꞌyan watanni, ꞌYarꞌuwa Sara ta soma nazari da mutane 70! Ita kaɗai ba za ta iya ci gaba da yin nazari da dukansu ba. Don haka, ta ba ma ꞌyanꞌuwa a ikilisiya wasu ɗalibanta. Yanzu ɗalibanta da yawa suna zuwa taro. Ba shakka, malaꞌiku suna jin daɗin taimaka ma ꞌyanꞌuwa kamar Sara, da suke yin waꞌazi iya gwargwadon ƙarfinsu!
MALAꞌIKU SUNA DA JIMIRI
11. Ta yaya malaꞌiku suka nuna halin jimiri?
11 Malaꞌiku sun nuna halin jimiri sosai. Sun yi dubban shekaru suna haƙuri da mugunta da rashin adalci da suke gani. Alal misali, sun ga yadda Shaiɗan da wasu malaꞌiku da yawa suka yi wa Jehobah tawaye. (Far. 3:1; 6:1, 2; Yahu. 6) Littafi Mai Tsarki ya kuma ba mu labarin yadda wani malaꞌika ya yi kwanaki da yawa yana faɗa da wani aljani. (Dan. 10:13) Ƙari ga haka, malaꞌiku sun ga cewa tun daga zamanin Adamu da Hauwaꞌu, mutane kaɗan ne suka zaɓi su bauta wa Allah. Duk da haka, waɗannan malaꞌikun sun ci gaba da bauta wa Jehobah da ƙwazo da kuma farin ciki. Sun san cewa Allah zai kawar da rashin adalci a daidai lokacin da ya dace.
12. Me zai taimaka mana mu jimre?
12 Ta yaya za mu nuna halin jimiri kamar malaꞌiku? Mu ma muna ganin rashin adalci, kuma akan tsananta mana. Amma kamar malaꞌiku, mun san cewa Allah zai kawar da dukan mugunta a daidai lokacin da ya dace. Saboda haka, mu ma kada mu “gaji da yin abin da yake da kyau.” (Gal. 6:9) Allah ya ce zai taimaka mana mu jimre. (1 Kor. 10:13) Za mu iya roƙon sa ya ba mu ruhunsa da ke sa mu kasance da haƙuri da kuma farin ciki. (Gal. 5:22; Kol. 1:11) Idan kuma ana tsananta maka, ka dogara ga Jehobah da dukan zuciyarka kuma kada ka ji tsoro. A ko yaushe, Jehobah zai taimake ka kuma zai ƙarfafa ka.—Ibran. 13:6.
MALAꞌIKU SUNA SA IKILISIYA TA KASANCE DA TSABTA
13. Wane aiki na musamman ne Jehobah ya ba wa malaꞌiku a waɗannan kwanaki na ƙarshe? (Matiyu 13:47-49)
13 A waɗannan kwanaki na ƙarshe, Jehobah ya ba wa malaꞌiku wani aiki na musamman. (Karanta Matiyu 13:47-49.) Akwai miliyoyin mutane a duniya da suke so su ji waꞌazinmu. Wasu suna canja halinsu kuma su ɗauki matakin bauta ma Jehobah, amma wasu ba sa haka. Allah ya ba wa malaꞌiku aikin “cire mugaye daga masu adalci.” Hakan na nufin cewa za su taimaka wajen sa ikilisiya ta kasance da tsabta. Amma wannan ba ya nufin cewa idan mutum ya daina nazari da kuma zuwa taro, ko ya daina bauta ma Jehobah, ba zai iya dawowa cikin ikilisiya ba. Kuma hakan ba zai sa a daina samun matsala a ikilisiya ba. Duk da haka, muna da tabbaci cewa malaꞌiku suna aiki sosai don su sa ikilisiyoyinmu su kasance da tsabta.
14-15. Kamar malaꞌiku, ta yaya za mu nuna cewa muna so ikilisiyarmu ta kasance da tsabta? (Ka kuma duba hotunan.)
14 Kamar malaꞌiku, ta yaya za mu nuna cewa muna so ikilisiyarmu ta kasance da tsabta? Mu yi duk abin da ya kamata mu yi don mu sa ikilisiyarmu ta kasance da tsabta. Za mu iya yin hakan idan muna abokantaka da waɗanda suke ƙaunar Jehobah, kuma muna guje wa duk abin da zai ɓata abokantakarmu da shi. (Zab. 101:3) Zai kuma dace mu taimaka ma ꞌyanꞌuwanmu su bauta wa Jehobah da aminci. Alal misali, idan muka san cewa wani ɗanꞌuwa ko wata ꞌyarꞌuwa ta yi zunubi mai tsanani, me ya kamata mu yi? Mu gaya wa mutumin cewa ya je ya gaya wa dattawa. Idan ya ƙi, mu je mu gaya wa dattawa. Za mu yi hakan don muna ƙaunar wanda ya yi zunubin, kuma muna so ya sami taimako da wuri!—Yak. 5:14, 15.
15 Abin baƙin cikin shi ne, wasu da suka yi zunubi mai tsanani sukan ƙi tuba kuma a cire su daga ikilisiya. Saꞌad da hakan ya faru, mukan daina “haɗa kai” ko kuma yin tarayya da su.d (1 Kor. 5:9-13) Irin wannan horon yakan sa ikilisiya ta kasance da tsabta. Ƙari ga haka, idan ba ma tarayya da waɗanda aka cire daga ikilisiya, alheri ne muke musu, domin zai iya sa su sake tunani. Idan suka komo ga Jehobah, dukanmu da Jehobah da malaꞌikunsa, za mu yi farin ciki.—Luk. 15:7.
Idan muka san cewa wani ɗanꞌuwa ko wata ꞌyarꞌuwa ta yi zunubi mai tsanani, me ya kamata mu yi? (Ka duba sakin layi na 14)e
16. A waɗanne hanyoyi ne za ka so ka yi koyi da malaꞌiku?
16 Muna godiya sosai ga Jehobah, da ya ba mu dama mu san abubuwa game da malaꞌiku, kuma mu yi aiki tare da su! Bari mu yi koyi da sauƙin kansu, da yadda suke ƙaunar mutane, da jimirinsu, da kuma yadda suke sa ikilisiya ta kasance da tsabta. Idan muka yi koyi da malaꞌiku, mu ma za mu kasance cikin iyalin Jehobah har abada.
WAƘA TA 123 Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah
a Akwai miliyoyin malaꞌiku, amma guda biyu ne kawai Littafi Mai Tsarki ya gaya mana sunayensu, wato Mikaꞌilu da Jibraꞌilu.—Dan. 12:1; Luk. 1:19.
b Za ka iya samun wasu labarai irin waɗannan a Watch Tower Publications Index a ƙarƙashin jigon nan, “Angels,” sai ka duba “angelic direction (examples).”
c An canja sunan.
d Kamar yadda aka bayyana a 2024 Ƙarin Bayani na 2 Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu, idan wanda aka cire daga ikilisiya ya zo taro, kowane mai shela zai iya yanke shawara ko zai ɗan gai da shi kuma ya marabce shi, ko aꞌa. Kowa zai yi abin da ya gamshe shi bisa ga abin da ya sani daga Littafi Mai Tsarki.
e BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ꞌyarꞌuwa ta gaya wa abokiyarta ta je ta gaya wa dattawa abin da ta yi, kuma ta ba ta lokaci don ta yi hakan. Da ꞌyarꞌuwar ta ga cewa abokiyarta ba ta yi hakan ba, sai ta je da kanta ta gaya wa dattawa abin da abokiyarta ta yi.