Ta Hannun Yohanna
10 “A gaskiya ina gaya muku, duk wanda bai shiga ta ƙofa zuwa inda ake ajiye tumaki ba, amma ya hau ta wani gefe dabam, ɓarawo ne shi da kuma ɗan fashi. 2 Amma wanda ya bi ta ƙofa ya shiga, shi ne makiyayin tumakin. 3 Mai gadin ƙofar yakan buɗe masa ƙofa, kuma tumakin sukan ji muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna kuma ya kai su waje. 4 Bayan ya fitar da dukan tumakinsa waje, sai ya sha gabansu, su kuma sai su bi shi, domin sun san muryarsa. 5 Ba za su taɓa bin wanda ba su sani ba, amma za su guje masa, domin ba su san muryar baƙi ba.” 6 Yesu ya yi musu wannan kwatanci, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba.
7 Sai Yesu ya sake cewa: “A gaskiya ina gaya muku, ni ne ƙofar da tumakin suke bi. 8 Dukan waɗanda suka zo suka ce wai su ne ni, su ɓarayi ne da kuma ꞌyan fashi; amma tumakin ba su saurare su ba. 9 Ni ne ƙofar; duk wanda ya shigo ta wurina zai sami ceto, zai shiga da fita kuma zai sami ciyayi masu kyau. 10 Ɓarawo yana zuwa ne domin ya yi sata da kisa da kuma hallakarwa. Na zo ne domin su sami rai kuma su same shi a yalwace. 11 Ni ne makiyayi mai kyau, makiyayi mai kyau shi ne wanda yake ba da ransa a madadin tumakin. 12 Mutumin da aka yi hayar sa don kiwo, wanda ba makiyayi ba ne kuma tumakin ba nasa ba ne, zai gudu ya bar tumakin idan ya ga ƙyarkeci* yana zuwa, ƙyarkecin zai kama tumakin kuma ya watsar da su, 13 domin shi mutum ne da aka yi hayar sa kuma ba abin da ya dame shi da tumakin. 14 Ni ne makiyayi mai kyau. Na san tumakina kuma tumakina sun san ni. 15 Kamar yadda Uban ya san ni, kuma ni ma na san Uban; na ba da raina a madadin tumakin.
16 “Ina da waɗansu tumaki kuma da ba sa cikin wannan garken; su ma dole in kawo su ciki. Za su saurari muryata, kuma za su zama garke ɗaya, makiyayi ɗaya. 17 Shi ya sa Ubana yake ƙauna ta, gama na ba da raina domin in sake samun sa. 18 Ba mutumin da ya isa ya ƙwace shi daga wurina, amma da son raina ne na ba da shi. Ina da ikon ba da shi kuma ina da ikon sake karɓan sa. Wannan umurni ne da na karɓa daga wurin Ubana.”
19 Kan Yahudawan ya sake rabuwa saboda abin da ya faɗa. 20 Da yawa daga cikinsu suna cewa: “Yana da aljani kuma ba ya cikin hankalinsa. Me ya sa kuke sauraron sa?” 21 Wasu kuma suka ce: “Waɗannan ba abin da mutum mai aljani yake faɗa ba ne. Mutum mai aljani zai iya buɗe idanun makaho ne?”
22 A lokacin ana Bikin Keɓewa a Urushalima. Lokacin sanyi ne, 23 kuma Yesu yana tafiya a cikin haikali, a Rumfar Sulemanu. 24 Sai Yahudawa suka kewaye shi kuma suka soma gaya masa cewa: “Har yaushe za ka bar mu cikin shakka? Idan kai ne Kristi, ka gaya mana a fili.” 25 Yesu ya amsa musu ya ce: “Na gaya muku, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba. Ayyukan da nake yi cikin sunan Ubana suna ba da shaida game da ni. 26 Amma ba ku gaskata da ni ba domin ku ba tumakina ba ne. 27 Tumakina sukan saurari muryata, na san su kuma suna bi na. 28 Na ba su rai na har abada kuma ba abin da zai sa a hallaka su. Ƙari ga haka, babu wanda zai ƙwace su daga hannuna. 29 Abin da Ubana ya ba ni yana da girma fiye da sauran abubuwa, kuma babu wanda zai ƙwace su daga hannun Uban. 30 Ni da Ubana ɗaya ne.”*
31 Sai Yahudawan suka sake ɗebo duwatsu don su jejjefe shi. 32 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Na yi muku ayyuka masu kyau da Ubana ya aiko ni in yi. A kan wanne cikin ayyukan nan za ku jejjefe ni?” 33 Yahudawan suka amsa masa suka ce: “Ba domin aiki mai kyau da ka yi ne za mu jejjefe ka ba, amma domin ka yi saɓo; gama ko da yake kai mutum ne, ka mai da kanka allah.” 34 Sai Yesu ya amsa musu ya ce: “Ba an rubuta a cikin Dokarku* cewa, ‘Ina gaya muku: “Ku alloli* ne”’ ba? 35 Idan Allah ya kira waɗanda kalmarsa ta ce sun yi laifi ‘alloli,’ kuma duk da hakan nassi ba ya ƙarya, 36 me ya sa za ku ce ma ni wanda Uban ya tsarkake kuma ya aiko cikin duniya, ‘Kana saɓo,’ domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne’? 37 Idan ba na yin ayyukan Ubana, kada ku ba da gaskiya gare ni. 38 Amma idan ina yin ayyukansa, ko da yake ba ku ba da gaskiya gare ni ba, ku ba da gaskiya ga ayyukan, don ku sani kuma ku ci-gaba da sanin cewa Uban yana da haɗin kai da ni, kuma ni ma ina da haɗin kai da Uban.” 39 Sai suka sake ƙoƙarin kama shi, amma ya kuɓuce musu.
40 Sai ya sake ƙetare Kogin Jodan zuwa inda Yohanna yake baftisma a dā, kuma ya zauna a wurin. 41 Sai mutane da yawa suka zo wurinsa kuma suka soma cewa: “Yohanna bai yi wani abin ban mamaki ba, amma dukan abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.” 42 Kuma mutane da yawa sun ba da gaskiya gare shi.