Ta Hannun Matiyu
11 Saꞌad da Yesu ya gama ba almajiransa goma sha biyun umurnai, sai ya tashi daga wurin ya soma waꞌazi da kuma koyarwa a garuruwa da ke yankin.
2 A lokacin, Yohanna yana cikin kurkuku, saꞌad da ya ji abubuwan da Kristi yake yi, sai ya aiki almajiransa 3 su tambayi Yesu cewa: “Kai ne Wanda Zai Zo, ko kuma mu jira wani dabam?” 4 Yesu ya amsa musu cewa: “Ku koma ku faɗa wa Yohanna abin da kuke ji da abin da kuke gani: 5 Yanzu makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da kutare, kurame suna ji, ana ta da waɗanda suka mutu, ana kuma gaya wa talakawa labari mai daɗi. 6 Wanda bai yi tuntuɓe* saboda ni ba zai yi farin ciki.”
7 Da almajiran Yohanna suka tafi, sai Yesu ya soma yi wa jamaꞌar magana game da Yohanna cewa: “Mene ne kuka fito ku gani a daji? Kun fito ganin dogayen ciyayi da iska take kaɗawa ne? 8 To, mene ne kuka fito ku gani? Mutumin da ke sanye da riguna masu kyau ne? Ai, ꞌyan gidan sarakuna ne suke saka riguna masu kyau. 9 To, wai mene ne ainihi kuka fito ku gani? Don ku ga annabi ne? E, ina gaya muku, shi annabi ne, har ma ya fi annabi sosai. 10 Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa: ‘Ga shi! Ina aika manzona ya riga ka, wanda zai shirya maka hanya kafin ka zo!’ 11 A gaskiya ina gaya muku, a cikin dukan ꞌyanꞌadam, babu wanda ya fi Yohanna Mai Baftisma daraja, amma mai matsayi mafi ƙanƙanta a Mulkin sama ya fi shi daraja. 12 Tun daga zamanin Yohanna Mai Baftisma zuwa yanzu Mulkin sama ne mutane suke iya ƙoƙarinsu su shiga, kuma waɗanda suka ci-gaba da yin iya ƙoƙarinsu suna shiga. 13 Kafin Yohanna ya zo, an annabta abin da zai faru a nan gaba a Dokar Musa da kuma littattafan da annabawa suka rubuta. 14 Ko kun yarda ko ba ku yarda ba, Yohanna shi ne ‘Iliya da ake cewa zai zo.’ 15 Bari mai kunne ya kasa kunne ya ji.
16 “Da wane ne zan kwatanta mutanen wannan zamanin? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa suna magana da abokan wasansu, 17 suna cewa: ‘Mun busa muku sarewa amma kun ƙi ku yi rawa, mun yi kuka sosai, amma ba ku yi abin da ya nuna cewa kuna baƙin ciki ba.’ 18 Haka nan ma, Yohanna ya zo, bai ci ba bai sha ba, amma mutane suka ce, ‘Yana da aljani.’ 19 Ɗan mutum ya zo yana ci yana sha, amma mutane sun ce, ‘Ga mai yawan ci da sha, abokin masu karɓan haraji da masu zunubi.’ Duk da haka, ana gane mai hikima ta wurin ayyuka masu kyau da yake yi.”*
20 Sai ya fara tsawata wa garuruwa da ya yi yawancin ayyukansa na ban mamaki don ba su tuba ba yana cewa: 21 “Kaiton ki, Korazin! Kaiton ki, Betsaida! domin da a ce ayyukan ban mamaki da aka yi a cikinku ne aka yi a Birnin Taya da Sidon, da sun tuba da daɗewa sun sa tsumma da toka a jikinsu. 22 Ina gaya muku, a Ranar Shariꞌa zai yi wa Taya da Sidon sauƙi su jimre fiye da ku. 23 Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za a ɗaukaka ki zuwa sama ne? A ina! Ƙasƙantar da ke za a yi zuwa kabari;* don da a Sodom ne aka yi ayyukan ban mamaki da aka yi a cikinki, da tana nan har zuwa yau. 24 Ina gaya muku, a Ranar Shariꞌa zai yi wa ƙasar Sodom sauƙi ta jimre fiye da ku.”
25 A wannan lokacin, Yesu ya ce: “Ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, ina yabon ka a gaban kowa, saboda ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da ilimi, ka kuma bayyana wa ƙananan yara. 26 Hakika, Ya Uba, wannan ne abin da kake so. 27 Ubana ya ba ni dukan abu, ba wanda ya san Ɗan sosai sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban sosai sai Ɗan, da kuma duk wanda Ɗan yake so ya bayyana masa Uban. 28 Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuma kuna fama da kaya masu nauyi, zan ba ku hutawa. 29 Ku zama almajiraina,* domin ni marar zafin rai ne, mai sauƙin kai, kuma za ku sami hutawa a ranku. 30 Zama almajiraina bai da wuya kuma umurnaina ba su da nauyi.”