Zuwa ga Romawa
10 ꞌYanꞌuwana, abin da na fi so a zuciyata kuma ina roƙon Allah shi ne Israꞌilawa su sami ceto. 2 Na dai shaida cewa suna da ƙwazon bauta wa Allah, amma ba bisa cikakken sani ba. 3 Da yake ba su san adalcin Allah ba, amma suna neman su kafa nasu, ba su miƙa kansu ga adalcin Allah ba. 4 Ta wurin Kristi ne aka kawo ƙarshen Doka,* domin duk wanda yake ba da gaskiya gare shi ya zama mai adalci.
5 Musa ya rubuta game da yadda mutum zai zama mai adalci ta wurin Doka cewa: “Mutumin da yake yin abubuwan nan zai rayu saboda su.” 6 Game da adalcin da ake samu daga bangaskiya, an rubuta cewa: “Kada ka ce a cikin zuciyarka, ‘Wane ne zai hau sama?’ wato, don ya sauko da Kristi, 7 ko kuma, ‘Wane ne zai shiga cikin rami mai zurfi?’* wato, don ya ta da Kristi daga mutuwa.” 8 Mene ne kalmar Allah ta ce? “Kalmar tana kusa da kai, a cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka”; wato, “kalmar” bangaskiya da muke waꞌazin ta. 9 Idan ka yi shela da bakinka cewa Yesu shi ne Ubangiji, kuma ka ba da gaskiya a zuciyarka cewa Allah ya ta da shi daga mutuwa, za ka sami ceto. 10 Gama da zuciya ce mutum yake ba da gaskiya don adalci, amma da baki ne mutum yake shelar samun ceto.
11 Domin nassi ya ce: “Babu wanda ya ba da gaskiya a gare shi da zai sha kunya.” 12 Gama babu bambanci tsakanin Bayahude da mutumin Girka. Ubangiji ɗaya ne dukansu suke da shi, kuma yana bayarwa a yalwace ga dukan waɗanda suke kira a gare shi. 13 Domin “duk wanda ya kira ga sunan Jehobah* zai sami ceto.” 14 Amma ta yaya za su kira ga wanda ba su ba da gaskiya gare shi ba? Kuma ta yaya za su ba da gaskiya gare shi idan ba su taɓa ji game da shi ba? Ta yaya kuma za su ji game da shi idan wani bai yi waꞌazi ba? 15 To, ta yaya za su yi waꞌazi idan ba a aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa: “Ƙafafun masu shelar labarin abubuwa masu daɗi suna da kyau sosai!”
16 Duk da haka, ba dukansu ne suka yi biyayya ga labari mai daɗin ba. Domin Ishaya ya rubuta cewa: “Jehobah,* wa ya ba da gaskiya ga abin da ya ji daga wurinmu?” 17 Saboda haka, mutum yana ba da gaskiya ne bayan ya ji saƙo, kuma akan ji saƙon ne ta wurin waꞌazi game da Kristi. 18 Amma ina tambaya cewa, Wai gaskiya ne ba su ji ba? Ai sun ji mana, a gaskiya kalmar Allah ta ce “mutane a koꞌina a duniya sun ji saƙon har ma da waɗanda suke zama a wurare masu nisa.” 19 Ina tambaya, hakan yana nufin cewa Israꞌilawa ba su sani ba ne? Da farko Musa ya ce: “Zan yi amfani da mutanen da ba Israꞌilawa ba don in sa ku kishi; zan yi amfani da wata alꞌumma marar wayo don in sa ku fushi sosai.” 20 Amma Ishaya ya yi ƙarfin hali kuma ya ce: “Waɗanda ba sa nema na ne suka same ni; waɗanda ba sa tambaya game da ni, su ne suka san ni.” 21 Amma ya ce game da Israꞌilawa: “Dukan yini na miƙa hannayena ga mutane marasa biyayya da masu taurin kai.”