Ayyukan Manzanni
1 Ya Tiyofilus, a littafi na farko da na rubuta maka, na rubuta game da dukan abubuwan da Yesu ya yi da kuma abubuwan da ya koyar 2 har zuwa ranar da aka ɗauke shi zuwa sama, bayan da ya ba wa manzannin da ya zaɓa umurnai ta wurin ruhu mai tsarki. 3 Bayan ya sha wahala, ya bayyana a gare su sau da yawa, don ya tabbatar musu cewa yana da rai. Almajiransa sun gan shi har kwanaki arbaꞌin kuma ya yi ta magana game da Mulkin Allah. 4 Saꞌad da ya haɗu da su, ya umurce su cewa: “Kada ku bar Urushalima, amma ku ci-gaba da jiran abin da Uban ya yi alkawarin sa, wanda kuka ji daga bakina. 5 Hakika, Yohanna ya yi wa mutane baftisma da ruwa, amma nan da ꞌyan kwanaki, za a yi muku baftisma da ruhu mai tsarki.”
6 Saꞌad da almajiransa suka taru, sai suka tambaye shi cewa: “Ubangiji, yanzu ne za ka mayar wa Israꞌila mulkin?” 7 Yesu ya ce musu: “Ba ku da izinin sanin lokatai da zamanai waɗanda Uba ne kaɗai yake da ikon shiryawa. 8 Amma za ku sami iko saꞌad da ruhu mai tsarki ya sauko a kanku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da dukan Yahudiya da Samariya, har zuwa iyakar duniya.” 9 Bayan da ya faɗi abubuwan nan, yayin da suke kallo, sai aka ɗauke shi zuwa sama kuma gajimare ya rufe shi, ba su ƙara ganin sa ba. 10 Yayin da suke kallon sama saꞌad da yake komawa, nan take sai mazaje biyu sanye da fararen riguna suka tsaya kusa da su, 11 kuma suka ce: “Ku mutanen Galili, me ya sa kuke tsaye kuna kallon sama? Yesun nan da aka ɗauke daga wurinku zuwa sama, zai sake dawowa daidai yadda kuka ga yake tafiya zuwa sama.”
12 Sai suka koma Urushalima daga tudun da ake kira Tudun Zaitun, wanda yake kusa da Urushalima. Daga tudun zuwa Urushalima wajen kilomita ɗaya* ne kawai. 13 Saꞌad da suka isa, sai suka haura ɗakin da ke sama inda suke zama. Mutanen da suke wajen, su ne Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da Andarawus, da Filibus, da Toma, da Bartalomi, da Matiyu, da Yaƙub ɗan Alfiyus, da Siman mai ƙwazo, da kuma Yahuda ɗan Yaƙub. 14 Dukansu tare da wasu mata da Maryamu mamar Yesu da ꞌyanꞌuwansa suna adduꞌa da nufi ɗaya.
15 A kwanakin nan, saꞌad da ꞌyanꞌuwa wajen ɗari da ashirin suka taru, sai Bitrus ya tashi a tsakanin ꞌyanꞌuwan kuma ya ce: 16 “ꞌYanꞌuwana, yana da muhimmanci abin da yake cikin nassi ya cika, wanda ruhu mai tsarki ya faɗa ta bakin Dauda, game da Yahuda wanda ya ja-goranci mutane su kama Yesu. 17 A dā shi ɗaya ne daga cikinmu, kuma mukan yi aiki tare da shi. 18 (Mutumin nan ya sayi fili da ladan ayyukansa na mugunta, kuma ya faɗo da kai, cikinsa ya fashe, sai dukan kayan cikinsa suka zuba. 19 Dukan mutanen Urushalima sun san abin nan da ya faru, don haka, a yarensu suna kiran filin Akaldama, wato, “Filin Jini.”) 20 Domin an rubuta a littafin Zabura cewa, ‘Bari wurin zamansa ya zama kufai, kada kowa ya zauna a ciki,’ an kuma ce, ‘Bari wani ya ɗauki matsayinsa.’* 21 Saboda haka, ya kamata a zaɓi wani daga cikin mutanen nan, wanda yake tare da mu a duk kwanakin da Ubangiji Yesu yake yin ayyukansa* a tsakaninmu, 22 tun daga lokacin da Yohanna ya yi ma Yesu baftisma, zuwa ranar da aka ɗauki Yesu zuwa sama, dole ɗaya daga cikin mutanen nan ya zama shaida tare da mu na tashiwarsa daga mutuwa.”
23 Sai suka kawo sunayen mutane biyu, wato Yusufu da ake kiran sa Barsabas wanda ake kuma kiran sa Justus, da kuma Matiyas. 24 Sai suka yi adduꞌa suka kuma ce: “Ya Jehobah,* kai da ka san zuciyar dukan mutane, ka nuna mana wanda ka zaɓa a cikin mutane biyun nan, 25 don ya ɗauki wannan hidimar da kuma matsayin manzo, wanda Yahuda ya bari ya tafi abin sa.” 26 Sai suka jefa ƙuriꞌa, kuma ƙuriꞌar ta faɗi a kan Matiyas, aka kuma sa* shi ya zama manzon Yesu tare da goma sha ɗayan nan.