Ta Hannun Matiyu
7 “Ku daina shariꞌanta mutane don kada ku ma a shariꞌanta ku; 2 don da irin shariꞌar da kuke yi wa mutane ne ku ma za a yi muku shariꞌa, kuma da mudun da kuke auna wa mutane, da shi za a auna muku. 3 Don me kake ganin ɗan tsinken da ke idon ɗanꞌuwanka amma ba ka lura da gungumen da ke cikin idonka ba? 4 Ko kuma me ya sa za ka ce wa ɗanꞌuwanka, ‘Bari in cire ɗan tsinken da ke idonka,’ amma kuma ga gungume a naka idon? 5 Munafuki! Ka soma da cire gungumen da ke naka idon tukuna, domin ka iya gani da kyau yadda za ka iya cire ɗan tsinken da ke idon ɗanꞌuwanka.
6 “Kada ku ba wa karnuka abu mai tsarki, ko kuma ku jefa wa aladu luꞌuluꞌanku,* don kada su tattaka su da ƙafafunsu kuma su juyo su ji muku rauni.
7 “Ku ci-gaba da roƙo, za a ba ku; ku ci-gaba da nema, za ku samu; ku ci-gaba da ƙwanƙwasawa, za a buɗe muku. 8 Duk wanda yake roƙo, za a ba shi, duk wanda yake nema, zai samu, kuma duk wanda yake ƙwanƙwasawa, za a buɗe masa. 9 Gama wane ne a cikinku, wanda idan ɗansa ya roƙe shi burodi, zai ba shi dutse? 10 Ko kuma idan ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji? 11 Don haka, idan ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba wa yaranku abubuwa masu kyau, ba kwa ganin Ubanku da ke sama zai fi ba ma waɗanda suke roƙon sa abubuwa masu kyau ba?
12 “Duk abubuwan da kuke so mutane su yi muku, dole ne ku ma ku yi musu hakan, domin wannan ne abin da Doka* da abubuwan da annabawa suka rubuta suke nufi.
13 “Ku shiga ta ƙaramar ƙofa, domin ƙofar zuwa hallaka na da girma kuma hanyarta na da fāɗi, mutane da yawa ne suke bin ta; 14 amma ƙofar zuwa rai ƙarama ce kuma hanyarta matsatsiya ce, mutane kaɗan ne suke samun ta.
15 “Ku yi hankali da annabawan ƙarya, waɗanda suke zuwa wurinku a kamannin tumaki, amma a ciki, su ƙyarketai* ne masu tsananin yunwa. 16 Za ku gane su ta wurin ayyukansu.* Shin mutane suna samun ꞌyaꞌyan inabi daga ƙaya ne, ko kuma ɓaure daga ciyayi? 17 Haka ma, kowane itace mai kyau yakan ba da ꞌyaꞌya masu kyau. Amma kowane itace marar kyau yakan ba da ꞌyaꞌya marasa kyau. 18 Itace mai kyau ba zai iya ba da ꞌyaꞌya marasa kyau ba, kuma itace marar kyau ba zai iya ba da ꞌyaꞌya masu kyau ba. 19 Kowane itace da ba ya ba da ꞌyaꞌya masu kyau, za a sare shi kuma a jefa cikin wuta. 20 Hakika, ta ayyukan mutanen nan ne za ku gane su.
21 “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji’ ne zai shiga Mulkin sama ba, amma sai wanda yake yin nufin Ubana da ke cikin sama ne zai shiga. 22 Mutane da yawa za su ce mini a ranar: ‘Ubangiji, Ubangiji, ba mun yi annabci a cikin sunanka ba? Ba mun fitar da aljanu a cikin sunanka ba? Kuma ba mun yi ayyuka da yawa masu ban mamaki a cikin sunanka ba?’ 23 Saꞌan nan zan ce musu: ‘Ni ban taɓa sanin ku ba! Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’
24 “Don haka, duk wanda ya ji abubuwan nan da na faɗa kuma ya yi su, zai zama kamar mai hikima da ya gina gidansa a kan dutse. 25 Da aka yi ruwan sama da ambaliya, kuma iska ta bugi gidan, bai rushe ba, don an gina shi a kan dutse. 26 Ƙari ga haka, duk wanda yake jin abubuwan nan da na faɗa amma ya ƙi ya yi su, zai zama kamar wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27 Da aka yi ruwan sama da ambaliya kuma iska ta bugi gidan, sai ya rushe, kuma ya hallaka gabaki-ɗaya.”
28 Da Yesu ya gama faɗan waɗannan abubuwan, sai jamaꞌar suka yi mamaki sosai don yadda yake koyarwa, 29 domin ya koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar marubutansu ba.