Zuwa ga Romawa
15 Ya kamata mu da bangaskiyarmu take da ƙarfi, mu taimaka wa marasa ƙarfi, ba yin abin da mu kaɗai za mu amfana ba. 2 Bari kowannenmu ya riƙa yin abin da zai faranta wa maƙwabcinsa rai, da kuma yi masa kirki don mu ƙarfafa* shi. 3 Gama ko Kristi ma bai faranta ransa ba, amma kamar yadda aka rubuta cewa: “Zage-zage da waɗansu suka yi maka duk sun faɗo a kaina.” 4 Dukan abubuwa da aka rubuta tun dā, an rubuta su ne don a koyar da mu, domin ta wurin jimrewarmu da kuma ƙarfafa da muke samu daga Nassosi, za mu iya samun bege. 5 Yanzu bari Allah da ke sa mu jimre da kuma ƙarfafa mu ya taimaka muku ku kasance da tunani irin wanda Kristi Yesu ya yi, 6 don ku kasance da haɗin kai kuma da murya* ɗaya ku ɗaukaka Allah da Uban Ubangijinmu Yesu Kristi.
7 Don haka, ku marabci* juna yadda Kristi ya marabce ku don ku sa a ɗaukaka Allah. 8 Ina gaya muku cewa, Kristi ya zama mai hidima ga waɗanda aka yi wa kaciya, don ya nuna cewa Allah mai gaskiya ne, kuma a tabbatar da alkawura da Allah ya yi wa kakanninsu, 9 don alꞌummai su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa, kamar yadda yake a rubuce cewa: “Shi ya sa zan yabe ka a cikin alꞌummai kuma zan rera yabo ga sunanka.” 10 Ya kuma ƙara da cewa: “Ku yi farin ciki ku alꞌummai tare da mutanensa.” 11 Ƙari ga haka: “Ku yabi Jehobah,* ya dukanku alꞌummai, kuma bari dukan mutane su yabe shi.” 12 Kuma Ishaya ya sake cewa: “Akwai wani tushen Jessi da zai taso ya yi mulkin alꞌummai, a gare shi ne alꞌummai za su yi bege.” 13 Bari Allah wanda yake ba da bege ya sa ku cika da farin ciki sosai da salama, da yake kuna dogara gare shi. Hakan zai sa ku kasance da bege sosai ta wurin ruhu mai tsarki.
14 ꞌYanꞌuwana, ni da kaina na tabbata cewa ku da kanku kuna yin abubuwa masu kyau sosai. Kuna cike da ilimi kuma kuna iya ba wa juna shawara.* 15 Amma na rubuta muku don in bayyana muku wasu abubuwa dalla-dalla, kuma in tuna muku su saboda alherin da Allah ya yi mini 16 don in zama mai hidimar Kristi Yesu ga alꞌummai. Ina yin aiki mai tsarki don in yaɗa labari mai daɗi na Allah, domin alꞌumman nan su zama hadaya da Allah zai karɓa, da aka tsarkake ta wurin ruhu mai tsarki.
17 Ina da dalilin yin taƙama cikin Kristi Yesu game da hidimata ga Allah. 18 Ba zan faɗi kome da na yi da kaina ba, sai dai abin da Kristi ya yi ta wurina, domin alꞌummai su riƙa yin biyayya ta wurin kalmomina da ayyukana, 19 da ikon alamu da ayyukan ban mamaki, da kuma ikon ruhun Allah. Ta hakan ne na zagaya daga Urushalima har zuwa Ilirikum, ina shela da kyau game da labari mai daɗi na Kristi. 20 Hakika, ta wannan hanya, na ƙuduri niyyar cewa ba zan yi shelar labari mai daɗi a wurin da an riga an yi shelar sunan Kristi ba. Domin kada ya zama ina yin gini a kan tushen da wani ya kafa, 21 amma kamar yadda aka rubuta cewa: “Waɗanda ba su taɓa ji game da shi ba, za su gan shi, kuma waɗanda ba su taɓa ji ba, za su fahimta.”
22 Wannan yana cikin dalilai da suka sa sau da yawa an hana ni zuwa ganin ku. 23 Amma a yanzu, ba wurin da ban taɓa zuwa ba a waɗannan yankunan, kuma na yi shekaru da yawa* ina marmarin zuwa wurinku. 24 Saboda haka, saꞌad da nake tafiya zuwa Sifen, ina fatan zan gan ku, kuma za ku ɗan raka ni zuwa wurin da zan je bayan na ji daɗin kasancewa da ku na ɗan lokaci. 25 Amma a yanzu, na kusa in tafi Urushalima don in taimaka* wa tsarkaka. 26 Gama ꞌyanꞌuwa da suke Makidoniya da Akaya suna farin cikin ba da gudummawar abubuwan da suke da su ga talakawa da suke cikin tsarkaka a Urushalima. 27 Hakika sun ji daɗin yin hakan, kuma a gaskiya wannan hakki ne a kansu, gama idan mutanen alꞌummai suka samu rabo daga abin da tsarkaka suka samu daga Allah, ya kamata su ma su taimaka wa tsarkaka da dukiyarsu. 28 Don haka, bayan na gama wannan aikin, kuma na tabbata cewa na miƙa musu wannan gudummawar, zan ziyarce ku saꞌad da nake hanya zuwa Sifen. 29 Ƙari ga haka, na san cewa saꞌad da zan zo wurinku, zan kawo muku cikakkiyar albarka daga wurin Kristi.
30 Ina roƙon ku ꞌyanꞌuwa, ta wurin Ubangijinmu Yesu Kristi da ƙaunar da ruhun Allah yake sa ku nuna, cewa ku taya ni yin adduꞌa da dukan zuciyarku ga Allah, 31 don in sami tsira daga marasa bi a Yahudiya, kuma taimakon da zan yi a Urushalima ya zama abin karɓa ga tsarkaka da ke wurin, 32 ta hakan kuwa, idan nufin Allah ne, zan zo wurinku da farin ciki kuma in huta tare da ku. 33 Bari Allah da ke ba da salama ya kasance da dukanku. Amin.