Ta Hannun Matiyu
4 Saꞌan nan ruhu ya kai Yesu cikin daji, kuma a wurin ne Ibilis ya gwada shi. 2 Bayan Yesu ya yi azumi na kwana arbaꞌin dare da rana, sai yunwa ta kama shi. 3 Sai Shaiɗan ya zo kuma ya ce masa: “Idan kai ɗan Allah ne, ka gaya wa duwatsun nan su zama burodi.” 4 Amma Yesu ya ce masa: “A rubuce yake cewa: ‘Ba da burodi kaɗai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace kalma da take fitowa daga wurin Jehobah.’”*
5 Sai Ibilis ya kai shi birni mai tsarki, kuma ya sa shi ya tsaya a wurin da ya fi tsawo a haikalin, 6 sai ya ce masa: “Idan kai ɗan Allah ne, ka yi tsalle zuwa ƙasa, domin a rubuce yake cewa: ‘Zai umurci malaꞌikunsa su taimake ka,’ kuma, ‘Za su ɗauke ka a hannunsu don kada ka buga ƙafafunka a kan dutse.’” 7 Sai Yesu ya ce masa: “A rubuce kuma yake cewa: ‘Kada ka gwada Jehobah* Allahnka.’”
8 Sai Shaiɗan ya sake kai shi kan wani tudu mai tsawo sosai, kuma ya nuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu. 9 Sai ya ce masa: “Zan ba ka dukan abubuwan nan idan ka durƙusa a gabana kuma ka yi mini sujada.”* 10 Sai Yesu ya ce masa: “Tafi daga nan Shaiɗan! Domin a rubuce yake cewa: ‘Jehobah* Allahnka ne za ka yi wa sujada, kuma shi kaɗai ne za ka bauta wa.’”* 11 Saꞌan nan Shaiɗan ya bar shi. Sai malaꞌiku suka zo suka soma yi masa hidima.
12 Da Yesu ya ji cewa an kama Yohanna, sai ya tashi ya tafi Galili. 13 Ƙari ga haka, bayan da ya bar Nazaret, sai ya soma zama a Kafarnahum, wadda take gefen teku a yankunan Zebulun da Naftali, 14 domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya, wanda ya ce: 15 “Ya ku mutanen da ke ƙasar Zebulun, da ƙasar Naftali, da ke hanyar da ake bi zuwa teku, a tsallaken Kogin Jodan, wanda shi ne Galili na waɗanda ba Yahudawa ba. 16 Mutanen da suke zama a cikin duhu sun ga haske, masu zama a yankin inuwar mutuwa kuma, haske ya ɓullo a kansu.” 17 Daga wannan lokacin, Yesu ya soma yin waꞌazi, yana cewa: “Ku tuba, domin Mulkin sama ya yi kusa.”
18 Da yake tafiya a gefen Tekun Galili, sai ya ga Siman wanda ake kira Bitrus, da ɗanꞌuwansa Andarawus, suna jefa raga a cikin teku, domin su masu kamun kifi ne. 19 Sai ya ce musu: “Ku bi ni, zan mai da ku masu jawo mutane kamar yadda ake kama kifi.” 20 Nan da nan suka bar ragarsu suka bi shi. 21 Da ya yi gaba kaɗan, sai ya ga wasu maza guda biyu da su ꞌyanꞌuwa ne, wato Yaƙub ɗan Zabadi, da ɗanꞌuwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da babansu Zabadi, suna gyaran ragarsu, sai ya kira su. 22 Nan da nan suka bar jirgin ruwan da kuma babansu, sai suka bi shi.
23 Sai Yesu ya zagaya dukan yankin Galili, yana koyarwa a majamiꞌunsu da yin waꞌazin labari mai daɗi na Mulkin Allah. Yana kuma warkar da kowane irin ciwo da kowane irin rashin lafiya da mutanen suke fama da su. 24 Sai labarinsa ya yaɗu a dukan Siriya, kuma suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da masu shan wuya, da masu aljanu, da masu farfaɗiya, da waɗanda jikinsu ya shanye, kuma ya warkar da su. 25 Saboda haka, mutane da yawa daga Galili, da Dikafolis,* da Urushalima, da Yahudiya, har ma daga ƙetaren Kogin Jodan suka bi shi.