Ayyukan Manzanni
15 Ana nan, sai wasu mutane suka zo daga Yahudiya kuma suka soma koyar da ꞌyanꞌuwan cewa: “Idan ba a yi muku kaciya bisa ga Dokar Musa ba, ba za ku sami ceto ba.” 2 Amma bayan Bulus da Barnabas suka ƙi yarda, kuma sun ɗau lokaci suna ta gardama da mutanen, sai aka shirya Bulus da Barnabas da wasu daga cikin mutanen, su kai wannan batun gaban manzanni, da dattawa da ke Urushalima.
3 Bayan ikilisiyar ta ɗan raka su, Bulus, da Barnabas, da abokan tafiyarsu sun ci-gaba da tafiya suka bi ta Finikiya da Samariya suna ba da labarin yadda mutanen alꞌummai suka juyo ga Allah kuma hakan ya sa dukan ꞌyanꞌuwan farin ciki sosai. 4 Da suka isa Urushalima, sai ikilisiyar da manzannin da dattawa sun karɓe su hannu bibbiyu, kuma sun ba da labarin abubuwa da yawa da Allah ya yi ta wurinsu. 5 Amma wasu daga ƙungiyar Farisiyawa da suka zama masu bi, sun tashi daga inda suke zama kuma suka ce: “Ya kamata a yi musu kaciya kuma a umurce su su bi Dokar Musa.”
6 Sai manzannin da dattawan suka taru domin su tattauna wannan batun. 7 Bayan da sun tattauna batun sosai,* sai Bitrus ya tashi ya ce musu: “ꞌYanꞌuwa, kun san cewa tun da farko, Allah ya zaɓe ni a tsakaninku cewa ta bakina ne mutanen alꞌummai za su ji kalmar labari mai daɗi kuma su ba da gaskiya. 8 Kuma Allah wanda ya san abin da ke zuciyar mutum ya ba da shaida ta wurin ba su ruhu mai tsarki, kamar yadda mu ma ya ba mu. 9 Kuma bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, amma ya tsabtace zukatansu ta wurin bangaskiya. 10 To, me ya sa kuke gwada Allah ta wajen ɗaura ma almajiran kaya mai nauyi wanda kakanninmu da mu ma ba za mu iya ɗaukawa ba? 11 Amma mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto kamar yadda su ma suka samu.”
12 Da jin haka, sai dukan jamaꞌar da ke rukunin suka yi shuru kuma suka soma sauraran yadda Barnabas da Bulus suke ba da labarin alamu da abubuwa masu ban mamaki da yawa da Allah ya yi wa alꞌummai ta wurinsu. 13 Bayan da suka gama magana, sai Yaƙub ya amsa ya ce: “ꞌYanꞌuwa, ku saurare ni. 14 Simeyon ya ba da labari dalla-dalla yadda Allah a karo na farko, ya mai da hankalinsa ga mutanen alꞌummai don ya zaɓa daga cikinsu mutane don sunansa. 15 Hakan ya jitu da abubuwan da annabawa suka faɗa, kamar yadda aka rubuta cewa: 16 ‘Bayan abubuwan nan, zan sake dawowa; don in ta da tentin* Dauda da ya faɗi, zan sake gina shi kuma in sabonta shi, 17 domin waɗanda suka rage su nemi Jehobah* da dukan zuciyarsu, tare da mutane daga dukan alꞌummai, mutanen da ake kira da sunana, in ji Jehobah,* wanda yake yin dukan abubuwan nan, 18 wanda tun zamanin dā ya riga ya san cewa za su faru.’ 19 Don haka, shawarata ita ce* kada a matsa wa mutanen alꞌummai da suke juyowa ga Allah, 20 amma a rubuta musu su guji abubuwan da suke da alaƙa da gumaka, da lalata,* da naman dabbar da aka murɗe wuyarta,* da kuma jini. 21 Gama tun zamanin dā mutane sukan yi waꞌazin littattafan da Musa ya rubuta daga birni zuwa birni, domin akan karanta wa jamaꞌa a majamiꞌu kowace Ranar Assabaci.”
22 Sai manzannin da dattawan da kuma dukan ikilisiyar suka yanke shawarar zaɓa daga cikinsu waɗanda za su aika zuwa Antakiya tare da Bulus da Barnabas; sai suka aiki Yahuda wanda ake kira Barsabas da kuma Sailas, maza da ke ayyuka sosai a tsakanin ꞌyanꞌuwansu. 23 Sun rubuta wasiƙar nan, kuma sun aika wasiƙar ta wurin ꞌyanꞌuwan, suna cewa:
“Daga ꞌyanꞌuwanku, manzanni da dattawa, zuwa ga ꞌyanꞌuwan da ke Antakiya, da Siriya, da Kilikiya waɗanda ꞌyan alꞌummai ne: Muna gaisuwa! 24 Da yake mun ji cewa wasu daga cikinmu sun zo wurinku, kuma sun tayar muku da hankali da abin da suka faɗa, sun yi ƙoƙari su yaudare ku, duk da cewa ba mu umurce su su yi hakan ba, 25 don haka, mun yanke shawarar aika muku maza daga wurinmu tare da ƙaunatattunmu Barnabas da Bulus, 26 mazan da suka sadaukar da rayukansu saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kristi. 27 Muna kuma aika muku Yahuda da Sailas don su tabbatar muku da abubuwan da ke cikin wasiƙar nan da bakinsu. 28 Ruhu mai tsarki ya taimaka mana mu ga cewa, bai dace mu ƙara muku wani nauyi fiye da waɗannan abubuwan da suka zama dole ba, wato: 29 ku ci-gaba da guje wa abubuwan da aka miƙa wa gumaka, da jini, da naman dabbar da aka murɗe wuyarta,* da lalata.* Idan kuka ci-gaba da guje wa abubuwan nan, za ku yi nasara. Ku huta lafiya!”*
30 Saꞌad da aka sallami mutanen nan, sai suka tafi Antakiya, kuma suka tara rukunin gabaki-ɗaya suka ba su wasiƙar. 31 Bayan sun karanta wasiƙar, sun yi farin ciki don ƙarfafa da aka yi musu. 32 Da yake Yahuda da Sailas ma annabawa ne, sun ƙarfafa ꞌyanꞌuwan da jawabai kuma sun sa bangaskiyarsu ta yi ƙarfi. 33 Bayan da suka zauna a wurin na ɗan lokaci, sai ꞌyanꞌuwan suka sallame su cikin salama zuwa ga waɗanda suka aiko su. 34* —— 35 Amma Bulus da Barnabas sun ci-gaba da zama a Antakiya, kuma tare da wasu ꞌyanꞌuwa da yawa suna koyarwa da yin shelar labari mai daɗi na kalmar Jehobah.*
36 Bayan ꞌyan kwanaki, sai Bulus ya ce wa Barnabas: “Bari* mu koma mu ziyarci ꞌyanꞌuwa da ke kowane birni da muka yi musu shelar kalmar Jehobah,* don mu ga yadda suke.” 37 Barnabas ya nace cewa zai tafi tare da Yohanna, wanda ake kiran sa Markus. 38 Amma Bulus ba ya so Yohanna ya bi su domin a dā ya bar su a Famfiliya kuma bai bi su yin aikin ba. 39 Hakan ya sa suka yi fushi da juna, kuma suka yi gardama sosai, har suka rabu da juna. Barnabas ya ɗauki Markus, kuma suka shiga jirgin ruwa suka tafi Saifrus. 40 Bayan da masu bi suka roƙi Jehobah* ya yi wa Bulus alheri, sai Bulus ya zaɓi Sailas suka tafi. 41 Ya bi ta Siriya da Kilikiya, yana ƙarfafa ikilisiyoyin.