Zuwa ga Romawa
7 ꞌYanꞌuwana, ba ku san cewa Doka* tana da iko a kan mutum muddin yana da rai ba? (Ina magana ne da waɗanda suka san doka). 2 Alal misali, bisa ga doka, mace mai aure za ta kasance da mijinta muddin yana da rai; amma idan mijinta ya mutu, ta sami ꞌyanci daga dokar mijinta. 3 Saboda haka, idan ta auri wani saꞌad da mijinta yake da rai, za ta zama mai zina. Amma idan mijinta ya mutu, ta sami ꞌyanci daga dokarsa kuma ba za ta zama mai zina ba idan ta auri wani.
4 Don haka ꞌyanꞌuwana, saboda jikin Kristi, ku ma kun sami ꞌyanci daga Dokar domin ku zama na wani, wato na wanda aka ta da daga mutuwa, domin mu ba da amfani ga Allah. 5 Saꞌad da muke yin rayuwa yadda jikinmu yake so, Dokar ta sa mun san abubuwa marasa kyau da jikinmu yake so da suke kai wa ga zunubi kuma zunubin yana jawo mutuwa. 6 Amma yanzu mun sami ꞌyanci daga Dokar, gama mun mutu mun bar abubuwan da suke riƙe da mu, domin mu iya zama bayin Allah da yake ruhu yana yi mana ja-goranci, ba domin doka tana yi mana ja-goranci ba.
7 To, me za mu ce ke nan? Dokar zunubi ne? Aꞌa, ko kaɗan! Da ba don Dokar ba, da ban san zunubi ba. Alal misali, da Dokar ba ta ce: “Kada ka yi kwaɗayin abin wani” ba, da ban san mene ne yin kwaɗayin abin wani yake nufi ba. 8 Amma saboda dokar, zunubi ya sami dama don ya sa in riƙa yin kowane irin kwaɗayi, gama saꞌad da babu doka, zunubi ba shi da iko.* 9 A gaskiya, ina da rai saꞌad da babu doka. Amma saꞌad da aka kafa doka, ya kasance a bayyane cewa ni mai zunubi ne, kuma ba ni da begen yin rayuwa. 10 Ya kamata dokar da aka kafa ta kawo rai, amma na fahimci cewa ta jawo mutuwa. 11 Gama da zunubi ya sami dama daga dokar, sai ya yaudare ni kuma ya kashe ni ta wurinta. 12 Saboda haka, Dokar da kanta tana da tsarki, abin da aka faɗa a ciki ma yana da tsarki, da adalci, da kuma kyau.
13 Don haka, abu mai kyau zai kashe ni ne? Aꞌa, ko kaɗan! Amma zunubi ya jawo mini mutuwa domin a nuna abin da zunubi yake nufi ta wurin abu mai kyau. Domin ta wurin dokar an gane cewa zunubi yana da muni sosai. 14 Gama mun sani cewa Dokar daga wurin Allah ne, amma ni jiki ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi. 15 Gama ban gane abin da nake yi ba. Ba na yin abin da nake so, sai dai abin da ba na so nake yi. 16 Amma idan na yi abin da ba na so, na yarda cewa Dokar tana da kyau. 17 Amma yanzu ba ni nake yin sa ba, zunubin da ke jikina ne. 18 Gama na sani cewa, babu wani abin kirki da ke zama a jikina; domin ina shaꞌawar yin abu mai kyau amma ba na iya yin sa. 19 Gama ba na yin abu mai kyau da nake so, amma abu marar kyau da ba na so shi nake yi. 20 To, idan ina yin abin da ba na so, ba ni ne nake yin sa ba, amma zunubin da ke zama a jikina ne.
21 Saboda haka, na gano wata doka da ke zama a jikina: Wato saꞌad da nake so in yi abu mai kyau, sai in soma marmarin yin abu marar kyau. 22 A cikin zuciyata ina son dokar Allah sosai, 23 amma a cikin jikina* akwai wata doka da take yaƙi da dokar da take iko da hankalina kuma tana kai ni bauta ga dokar zunubi da ke jikina.* 24 Kaito na! Wane ne zai cece ni daga jikin nan da yake mutuwa? 25 Godiya ga Allah, ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu! Saboda haka, a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a cikin jikina, ni bawa ne ga dokar zunubi.