Ta Hannun Matiyu
3 A kwanakin, Yohanna Mai Baftisma ya fito yana waꞌazi a dajin Yahudiya, 2 yana cewa: “Ku tuba, domin Mulkin sama ya yi kusa.” 3 Wannan shi ne wanda annabi Ishaya ya yi magana a kansa cewa: “Wata murya tana kira a daji tana cewa: ‘Ku shirya hanyar Jehobah!* Ku sa hanyoyinsa su miƙe.’” 4 Yohanna ya sa tufafin da aka yi da gashin raƙumi kuma ya yi ɗamara da fata. Abincinsa fāra ne da ruwan zuma. 5 Sai mutanen Urushalima, da dukan Yahudiya, da dukan yankunan da ke kusa da Kogin Jodan suna ta zuwa wurinsa, 6 kuma ya yi musu baftisma* a Kogin Jodan, yayin da suke faɗan zunubansu a gaban mutane.
7 Saꞌad da ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa wurin da yake baftisma, sai ya ce musu: “Ku ꞌyaꞌyan macizai masu dafi, wa ya gargaɗe ku ku guje wa hukuncin nan da ke zuwa? 8 Saboda haka, ku yi abin da zai nuna cewa kun tuba. 9 Kada ku yi taƙama kuna cewa, ‘Ibrahim babanmu ne.’ Domin ina gaya muku cewa Allah zai iya ta da wa Ibrahim ꞌyaꞌya daga duwatsun nan. 10 An riga an ajiye gatari a ƙarƙashin itatuwan. Saboda haka, duk wani itace da ba ya ba da ꞌyaꞌya masu kyau, za a sare shi, a jefa a cikin wuta. 11 Ni dai da ruwa nake yi muku baftisma don kun tuba. Amma wanda yake zuwa a bayana, ya fi ni ƙarfi. Wanda ko takalmarsa ma ban isa in cire ba. Shi ne wanda zai yi muku baftisma da ruhu mai tsarki da kuma wuta. 12 Matankaɗensa yana hannunsa, zai share wurin buga hatsinsa da kyau. Kuma zai tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙona dusar da wutar da ba za a iya kashewa ba.”
13 Sai Yesu ya zo wurin Yohanna daga Galili, domin Yohanna ya yi masa baftisma a Kogin Jodan. 14 Amma Yohanna ya yi ƙoƙarin hana shi, kuma ya ce wa Yesu: “Ni ne ya kamata ka yi wa baftisma, yaya kake zuwa wurina?” 15 Yesu ya amsa masa ya ce: “Kada ka hana ni, domin ta haka ne za mu iya yin nufin Allah.” Sai Yohanna ya yarda. 16 Bayan da aka yi wa Yesu baftisma, nan da nan ya fito daga ruwan. Sai sama ya buɗu, kuma ya ga ruhun Allah a kamannin kurciya yana saukowa a kansa. 17 Sai wata murya daga sama ta ce: “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna. Na amince da shi.”