Zuwa ga Romawa
3 To mene ne amfanin zama Bayahude, ko kuma amfanin yin kaciya? 2 Akwai amfani sosai a kowace hanya. Da farko dai, Yahudawa ne Allah ya ba wa kalmominsa masu tsarki. 3 To mene ne zai faru idan wasu ba su da bangaskiya? Shin rashin bangaskiyarsu zai nuna cewa Allah bai da aminci ne? 4 Ko kaɗan! Amma bari Allah ya zama mai gaskiya ko da dukan mutane maƙaryata ne, kamar yadda aka rubuta cewa: “Bari abubuwan da kake faɗa su nuna cewa kai mai adalci ne kuma ka yi nasara saꞌad da ake shariꞌanta ka.” 5 Amma idan rashin adalcinmu ya bayyana adalcin Allah fa, me za mu ce ke nan? Allah ba marar adalci ba ne idan ya nuna fushinsa, ko shi marar adalci ne? (Ina dai yin magana ne kamar ɗanꞌadam.) 6 Ko kaɗan! Idan Allah marar adalci ne, to, ta yaya zai shariꞌanta duniya?
7 Amma idan ƙaryata ta sa gaskiyar Allah ta fita a fili sosai kuma an ɗaukaka shi, to, me ya sa ni ma ake shariꞌanta ni a matsayin mai zunubi? 8 Idan haka ne, ai sai mu ce, “Bari mu yi abubuwa marasa kyau don abubuwa masu kyau su faru,” kamar yadda wasu sun yi ƙarya a kanmu cewa haka muke magana. A gaskiya, hukuncin da aka yi wa mutanen nan ya yi daidai.
9 To yaya ke nan? Ko mu Yahudawa mun fi sauran mutane ne? Ko kaɗan! Kamar yadda muka faɗa a baya, da Yahudawa da kuma mutanen Girka, dukansu masu zunubi ne; 10 kamar yadda yake a rubuce cewa: “Babu mai adalci, ko ɗaya; 11 babu wani mai ganewa; babu wanda yake neman Allah. 12 Dukan mutane sun juya baya, dukansu sun zama marasa amfani; babu wanda yake yin alheri, ko mutum ɗaya babu.” 13 “Maƙogwaronsu kamar kabarin da yake a buɗe ne; sun yi yaudara da harsunansu.” “Dafin macizai yana leɓunansu.” 14 “Bakinsu cike yake da ɗaci da kuma zage-zage.” 15 “Ƙafafunsu na saurin zuwa zub da jini.” 16 “Suna lalatar da kayan mutane kuma suna wahalar da su, 17 ba su kuma san yadda ake zaman lafiya ba.” 18 “Ba sa tsoron Allah ko kaɗan.”
19 Yanzu mun san cewa dukan abubuwa da aka faɗa a cikin Doka,* ga waɗanda aka ba wa Dokar ne domin a iya rufe kowane baki kuma dukan duniya su fuskanci hukuncin Allah daidai da ayyukansu. 20 Saboda haka, babu wanda za a ɗauke shi a matsayin mai adalci a gaban Allah domin yana bin doka, gama doka ce take sa mu fahimci zunubi.
21 Amma yanzu a bayyane yake cewa, mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah ba tare da bin doka ba, abin da aka faɗa ke nan a cikin Doka da kuma littattafan annabawa. 22 Hakika, Allah zai iya ɗaukan dukan masu ba da gaskiya ga Yesu Kristi a matsayin masu adalci domin ba ya nuna bambanci. 23 Gama kowa ya yi zunubi kuma ya kasa kai ga darajar Allah, 24 kuma kyauta ce Allah ya ba su saꞌad da ya ce su masu adalci ne. Ya ba su kyautar ce ta wurin ba da Kristi Yesu a matsayin fansa domin alherinsa. 25 Allah ya ba da Yesu a matsayin hadaya da za ta sasanta mu da Shi ta wajen ba da gaskiya ga jinin Yesu. Allah ya yi hakan ne domin ya nuna adalcinsa. Domin haƙurinsa, Allah ya yi ta gafarta zunuban da aka aikata a dā. 26 Hakan ya faru ne don ya nuna cewa shi mai adalci ne a wannan lokacin, domin Allah ya zama mai adalci saꞌad da ya ɗauki wanda ya ba da gaskiya ga Yesu a matsayin mai adalci.
27 To, me za mu yi taƙama a kai? Babu wani abin taƙama. Mutum zai yi taƙama saboda doka ne? Cewa yana yin abubuwan da doka ta ce? Aꞌa, amma ta wurin dokar da ta ce mutum ya kasance da bangaskiya ne. 28 Gama mun san cewa bangaskiyar mutum ce take sa Allah ya ce shi mai adalci ne, ba bin doka ba. 29 Ko shi Allah ne ga Yahudawa kawai? Shi ba Allah ba ne har ga mutanen alꞌummai? Hakika, shi Allah ne ga mutanen alꞌummai ma. 30 Da yake Allah ɗaya ne, zai kira masu kaciya masu adalci saboda bangaskiyarsu, kuma zai kira marasa kaciya masu adalci saboda bangaskiyarsu. 31 To, za mu kawar da doka domin bangaskiyarmu ne? Ko kaɗan! A maimakon haka, muna goyon bayan doka ne.