Ta Hannun Yohanna
19 Saꞌan nan Bilatus ya sa aka yi wa Yesu bulala. 2 Sai sojojin suka yi rawanin ƙaya suka saka masa a kai, suka saka masa jar riga, 3 kuma suka yi ta zuwa wurinsa suna ce masa: “Ranka ya daɗe,* Sarkin Yahudawa!” Kuma suna ta marin shi a fuska. 4 Sai Bilatus ya sake fitowa ya ce musu: “Ga shi fa, zan fito muku da shi waje domin ku ga cewa ban same shi da wani laifi ba.” 5 Sai Yesu ya fito waje, yana sanye da rawanin ƙaya da jar riga. Sai Bilatus ya ce musu: “Ga mutumin!” 6 Amma saꞌad da manyan firistocin da jamiꞌan suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce: “A rataye shi a kan gungume! A rataye shi a kan gungume!”* Sai Bilatus ya ce musu: “Ku ɗauke shi da kanku ku kashe shi,* domin ban same shi da wani laifi ba.” 7 Sai Yahudawan suka amsa masa suka ce: “Muna da doka, kuma bisa ga dokar dole ne ya mutu, domin ya mai da kansa ɗan Allah.”
8 Da Bilatus ya ji abin da suke faɗa, sai ya ƙara jin tsoro, 9 kuma ya sake shiga gidan gwamna, ya ce wa Yesu: “Daga ina ne ka fito?” Amma Yesu bai ba shi amsa ba. 10 Sai Bilatus ya ce masa: “Ka ƙi ka yi magana da ni ko? Ba ka san cewa ina da iko in sake ka, kuma ina da iko in kashe ka ba?” 11 Yesu ya amsa masa ya ce: “Ai, da a ce ba a ba ka iko daga sama ba, da ba ka da iko a kaina. Shi ya sa mutumin da ya miƙa ni a hannunka, ya fi ka zunubi.”
12 Saboda haka, Bilatus ya yi ta neman hanyar da zai sake shi, amma Yahudawa suka ɗaga murya suna cewa: “Idan ka saki mutumin nan, kai ba abokin Kaisar ba ne. Domin duk wanda yake mai da kansa sarki, yana yi wa Kaisar tawaye* ne.” 13 Bayan da Bilatus ya ji abubuwan nan da suka faɗa, sai ya fito da Yesu waje, kuma ya zauna a kujerar shariꞌa, a wurin da ake kira Daɓen Duwatsu, amma a Ibrananci, ana kiran wurin Gabbata. 14 Ranar, Ranar Shiri* ce na Bikin Ƙetarewa; kuma wajen ƙarfe sha biyu ne na rana.* Sai Bilatus ya ce wa Yahudawan: “Ku ga sarkinku!” 15 Amma suka ta da murya, suna cewa: “Ka tafi da shi! Ka tafi da shi! Ka rataye shi a kan gungume!”* Sai Bilatus ya ce musu: “Kuna so in kashe sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce: “Ba mu da wani sarki sai Kaisar.” 16 Sai Bilatus ya ɗauke shi ya ba su domin su kashe shi a kan gungume.
Kuma suka tafi da Yesu. 17 Yesu ya ɗauki gungumen azabar* da kansa, sai ya tafi wurin da ake kira, Wurin Ƙoƙon Kai, a Ibrananci kuma ake kira Golgota. 18 A wurin ne suka rataye Yesu a kan gungume, tare da wasu mutane biyu. Ɗaya a hagunsa, ɗayan kuma a damarsa, Yesu kuma yana tsakiya. 19 Bilatus ya yi wani rubutu, kuma ya manne shi a kan gungumen azabar.* Ya rubuta cewa: “Yesu mutumin Nazaret, Sarkin Yahudawa.” 20 Yahudawa da yawa sun karanta wannan rubutun, domin wurin da aka rataye Yesu a kan gungume yana kusa da birni ne, kuma an rubuta shi da Ibrananci, da Latin, da kuma Girkanci. 21 Amma manyan firistocin Yahudawa suka ce wa Bilatus: “Kada ka rubuta ‘Sarkin Yahudawa,’ ka rubuta, ya ce ‘Ni ne Sarkin Yahudawa.’” 22 Bilatus ya amsa ya ce: “Abin da na rubuta, na rubuta ke nan.”
23 Bayan da sojojin suka rataye Yesu a kan gungume, sai suka ɗauki mayafinsa kuma suka raba shi kashi huɗu, kowane soja ya ɗauki kashi ɗaya, sun kuma ɗauki rigar cikinsa. Amma rigar cikin ba a ɗinka ta ba, an saƙa ta ne daga sama zuwa ƙasa. 24 Sai suka ce wa juna: “Kada mu yaga rigar, amma bari mu jefa ƙuriꞌa a kanta don mu ga wanda zai ci.” Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce: “Suka rarraba rigunana a tsakaninsu, kuma sun jefa ƙuriꞌa a kan rigata.” Sojojin sun yi abubuwan nan da gaske.
25 Kuma mamar Yesu, da ꞌyarꞌuwarta, da Maryamu matar Kilobas, da kuma Maryamu Magdalin, suna tsaye kusa da gungumen azabar* Yesu. 26 Saꞌad da Yesu ya ga mamarsa da almajirin da yake ƙauna suna tsaye kusa, sai ya ce wa mamarsa: “Ga ɗanki!” 27 Sai ya ce wa almajirin: “Ga mamarka!” Tun daga lokacin, almajirin ya kai mamar Yesu gidansa.
28 Bayan wannan, da yake yanzu Yesu ya san cewa an gama kome, domin a cika abin da aka faɗa a cikin nassi, sai ya ce: “Ina jin ƙishin ruwa.” 29 Akwai wani gora cike da ruwan inabi mai tsami da ke wurin. Sai suka jiƙa soso da ruwan inabi mai tsamin, suka soka soson a sandar hissof,* sai suka ɗaga suka kai bakin Yesu. 30 Bayan da Yesu ya ɗanɗana ruwan inabi mai tsamin, sai ya ce: “An gama!” kuma ya sunkuyar da kansa, ya saki ransa.*
31 Sai Yahudawa suka roƙi Bilatus ya ba da izini a kakkarye ƙafafun mutanen da aka rataye, kuma a sauko da gawawwakinsu daga gungumen. Sun yi haka ne domin Ranar Shiri ce, kuma ba sa so gawawwakin mutanen su kasance a kan gungume a Ranar Assabaci (domin wannan Ranar Assabaci ce ta musamman). 32 Sai sojojin suka zo, suka kakkarya ƙafafun mutum na farko da na ɗayan mutumin da aka rataye su a gefen Yesu. 33 Amma da suka zo wurin Yesu, sai suka ga cewa ya riga ya mutu. Saboda haka, ba su karya ƙafafunsa ba. 34 Sai ɗaya daga cikin sojojin ya soki Yesu a gefen jikinsa da mashi, kuma nan da nan, jini da ruwa suka fito. 35 Wanda ya ga hakan, ya ba da shaidar nan, shaidarsa kuwa gaskiya ce, kuma ya san cewa abin da ya faɗa gaskiya ne, domin ku ma ku ba da gaskiya. 36 Hakika, waɗannan abubuwa sun faru don a cika abin da aka rubuta a nassi cewa: “Ba ko ƙashinsa ɗaya da za a karya.” 37 Wani nassi kuma ya ce: “Za su dubi wanda suka soki da mashi.”
38 Bayan abubuwan nan, Yusufu na Arimatiya, wanda almajirin Yesu ne amma a ɓoye, domin yana tsoron Yahudawa, ya roƙi Bilatus ya ba shi izini ya ɗauki gawar Yesu, kuma Bilatus ya ba shi izinin. Sai ya zo ya ɗauki gawar Yesu ya tafi da shi. 39 Nikodimus, mutumin da ya taɓa haɗuwa da Yesu da dare, shi ma ya zo, ya kawo kayan ƙamshi na mur da aloe da suka kai wajen kilo talatin. 40 Sai suka ɗauki gawar Yesu, suka nannaɗe gawar da yadin lilin haɗe da kayan ƙamshin nan, bisa ga yadda Yahudawa suke binne mutane. 41 A wurin da aka rataye Yesu,* akwai wani lambu, kuma a cikin lambun akwai wani sabon kabari da ba a taɓa binne kowa a ciki ba. 42 Da yake Ranar Shiri ce ta Yahudawa kuma kabarin yana nan kusa, sai suka kwantar da gawar Yesu a kabarin.