Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ll kashi 3 pp. 8-9
  • Yaya Rayuwa Take a Lambun Adnin?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yaya Rayuwa Take a Lambun Adnin?
  • Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
  • Makamantan Littattafai
  • Wasu Sun Fi Mu Matsayi
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Abin Da Ya Sa Suka Yi Rashin Gidansu
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Sun Saurari Shaiɗan—Mene Ne Sakamakon?
    Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
  • Sashe na 3
    Ka Saurari Allah
Dubi Ƙari
Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
ll kashi 3 pp. 8-9

SASHE NA 3

Yaya Rayuwa Take a Lambun Adnin?

Jehobah ya ba Adamu da Hauwa’u abubuwa da yawa masu kyau. Farawa 1:28

Bayan da Jehobah ya gama halittar Hawa’u, sai ya mika ta ma Adamu

Jehobah ya halicci mace ta farko, Hauwa’u, kuma ya miƙa ta ga Adamu don ta zama matarsa.—Farawa 2:21, 22.

Jehobah ya halicce su da kamiltaccen jiki da hankali; ba tare da wani aibi ba.

Adamu da Hawa’u suna kallon abubuwan da Jehobah ya halitta a adnin

Lambun Adnin ne gidansu, kuma wuri ne kyakkyawa mai koguna da ’ya’yan itatuwa da dabbobi.

Jehobah ya yi magana da su; kuma ya koyar da su. Idan suka saurare shi, za su rayu har abada a cikin Aljanna a duniya.

Allah ya ce kada su ci ɗaya daga cikin itatuwan. Farawa 2:16, 17

’Ya’yan itacen da Allah ya ce wa Adamu Hawa’u kada su ci a gonar Adnin

Jehobah ya nuna wa Adamu da Hauwa’u wani itace mai ’ya’ya a cikin lambun kuma ya gaya musu cewa idan suka ci ’ya’yansa, za su mutu.

Mugun malai’ika, wato Satan Iblis, ya yi amfani da maciji don ya yi magana a Hawa’u

Ɗaya daga cikin mala’ikun ya yi wa Allah tawaye. Wannan mugun mala’ikan shi ne Shaiɗan Iblis.

Shaiɗan ba ya son Adamu da Hauwa’u su yi biyayya ga Jehobah. Saboda haka, ya yi amfani da maciji ya gaya wa Hauwa’u cewa idan ta ci daga ’ya’yan itacen, ba za ta mutu ba, amma za ta zama kamar Allah. Hakika, wannan ƙarya ce.—Farawa 3:1-5.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba