Agusta
Jumma’a, 1 ga Agusta
Mai adalci yakan sami wahaloli da yawa, amma Yahweh yakan kuɓutar da shi daga cikinsu duka.—Zab. 34:19.
Ku yi laꞌakari da abubuwa guda biyu daga nassin da ke sama. (1) Masu adalci suna fuskantar matsaloli. (2) Jehobah yana kuɓutar da su daga matsalolin. Ta yaya Jehobah yake kuɓutar da mu? Hanya ɗaya da yake yin hakan ita ce ta wajen taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace game da rayuwa a wannan kwanakin ƙarshe. Ko da yake Jehobah ya yi mana alkawari cewa za mu yi farin ciki yayin da muke bauta masa, bai yi mana alkawari cewa za mu yi rayuwa ba tare da matsaloli ba. (Isha. 66:14) Yana dai so mu mai da hankali ga rayuwar da za mu more har abada a nan gaba. (2 Kor. 4:16-18) Kafin lokacin, yana taimaka mana mu ci gaba da jimrewa a kullum. (Mak. 3:22-24) Me za mu iya koya daga bayin Allah a zamanin dā da kuma a zamaninmu? Za mu iya fuskantar matsaloli ba zato. Amma idan muka dogara ga Jehobah, ba zai daina taimaka mana ba.—Zab. 55:22. w23.04 14-15 sakin layi na 3-4
Asabar, 2 ga Agusta
Kowa ya yi biyayya ga shugabannin gwamnati.—Rom. 13:1.
Za mu iya koyan darasi daga gun Yusufu da Maryamu, domin sun yi biyayya ga hukumomin gwamnati duk da cewa hakan bai yi musu sauƙi ba. (Luk. 2:1-6) Saꞌad da Maryamu ta yi wata tara da juna biyu, gwamnati ta umurce su su yi wani abu mai wuya sosai. A lokacin, Augustus ne yake mulkin Daular Roma kuma ya ba da umurni cewa a ƙirga mutanen da ke Daular. Don haka, ya zama dole Yusufu da Maryamu su je Baiꞌtalami, kuma tafiyar ta kai kilomita 150. Ban da haka, za su yi ta hawa a kan tuddai da yawa. Hakika, tafiyar za ta yi musu wuya sosai, musamman ma Maryamu. Wataƙila sun damu da yadda tafiyar za ta shafi lafiyar Maryamu da kuma ɗanta. Me zai faru idan ta soma nakuɗa a hanya? Jaririn da ke cikinta shi ne Almasihu da aka yi alkawarin sa. Shin dalilan nan sun sa sun ƙi yin biyayya ga shugabannin gwamnati ne? Yusufu da Maryamu ba su bar dalilan nan su hana su bin umurnin ba. Jehobah ya yi musu albarka don sun yi biyayya. Maryamu ta isa Baiꞌtalami cikin ƙoshin lafiya kuma babu abin da ya samu ɗan da ta haifa!—Mik. 5:2. w23.10 8 sakin layi na 9; 9 sakin layi na 11-12
Lahadi, 3 ga Agusta
Mu dinga ƙarfafa juna.—Ibran. 10:25.
Me za ka yi idan kana jin tsoron yin kalami? Wani abu da zai taimaka shi yin shiri sosai. (K. Mag. 21:5) Idan ka fahimci abin da za a tattauna sosai, hakan zai sa ya yi maka sauƙi ka yi kalami. Ban da haka, ka yi gajeren kalami. (K. Mag. 15:23; 17:27) Idan kalaminka gajere ne, ba za ka ji tsoro sosai ba. Idan ka yi gajeren kalami kuma ka faɗe shi daga zuciyarka, hakan zai nuna cewa ka yi shiri da kyau kuma ka fahimci abin da ake tattaunawa. Idan ka gwada yin duka abubuwan nan amma har ila kana jin tsoron yin kalami fiye da sau ɗaya fa? Kar ka damu. Ka tuna cewa Jehobah yana farin ciki don iya ƙoƙarin da kake yi. (Luk. 21:1-4) Yin iya ƙoƙarinka ba ya nufin ka yi abin da ya fi ƙarfinka. (Filib. 4:5) Ka dai san abin da kake so ka yi, kuma ka ƙafa maƙasudin yin sa, saꞌan nan ka roƙi Jehobah ya ba ka ƙarfin zuciya. Wasu daga cikinmu mukan fara ne da maƙasudin yin gajeren kalami. w23.04 21 sakin layi na 6-8
Litinin, 4 ga Agusta
Mu sa rigar ƙarfe . . . da kuma hular kwano.—1 Tas. 5:8.
Manzo Bulus ya kwatanta mu da sojojin da suke a shirye don yaƙi. Ana bukatar soja ya kasance a shirye a kowane lokaci idan yaƙi ya taso. Haka ma yake da mu. Muna zama da shiri ta wajen saka rigar ƙarfe ta bangaskiya da ƙauna, da kuma hular kwano ta sa zuciya ga samun ceto. Rigar ƙarfe tana kāre zuciyar soja. Haka ma, bangaskiya da ƙauna suna kāre zuciyarmu. Za su taimaka mana mu ci gaba da bauta wa Jehobah da kuma bin misalin Yesu. Bangaskiya tana sa mu kasance da tabbacin cewa Jehobah zai ba mu lada don muna bauta masa da dukan zuciyarmu. (Ibran. 11:6) Za ta sa mu riƙe aminci ga Shugabanmu Yesu ko da muna fuskantar matsaloli. Akwai mutane a zamaninmu da suka riƙe aminci duk da tsanantawa da talauci. Idan muna yin tunani a kan labaransu, hakan zai taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu kuma mu iya jimre matsalolinmu. Ƙari ga haka, za mu iya guje wa son kuɗi da kuma abin duniya idan muna yin koyi da waɗanda suka sauƙaƙa rayuwarsu domin su sa alꞌamuran Mulkin Allah farko. w23.06 10 sakin layi na 8-9
Talata, 5 ga Agusta
Duk wanda yake jiran iska, ba zai yi shuka ba.—M. Wa. 11:4.
Kamun kai yana nufin hana kanmu yin abin da bai dace ba. Muna bukatar kamun kai don mu iya cim ma maƙasudinmu, musamman idan yana da wuya ko kuma idan ba ma marmarin yin sa. Ka tuna cewa kamun kai yana ɗaya daga cikin halayen da ruhu mai tsarki yake taimaka mana mu kasance da su. Don haka, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka da ruhunsa mai tsarki don ka iya ƙara kasancewa da wannan halin. (Luk. 11:13; Gal. 5:22, 23) Kada ka jira sai kome ya yi sumul. A wannan duniyar, ba za mu iya samun lokacin da babu abin da zai iya hana mu cim ma maƙasudinmu ba. Idan mun jira lokacin, ba za mu taɓa iya cim ma maƙasudinmu ba. Idan maƙasudinmu yana da wuyar cim mawa, ba za mu kasance da niyyar cika shi ba. Idan haka yanayinka yake, za ka iya somawa da ƙananan maƙasudai. Idan kana so ka kasance da wani hali, za ka iya soma nuna halin kaɗan da kaɗan. Idan kana so ka karanta Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya, za ka iya somawa da karanta shi kaɗan da kaɗan. w23.05 29 sakin layi na 11-13
Laraba, 6 ga Agusta
Hanyar masu adalci kamar ɓullowar hasken rana take, hasken da yakan yi ta ƙaruwa har ya haskaka cikakke iri na tsakar rana.—K. Mag. 4:18.
A wannan kwanakin ƙarshe, Jehobah yana amfani da ƙungiyarsa don ya tanada mana abubuwan da za su taimaka mana mu ci-gaba da yin tafiya a “Hanyar Tsarki.” (Isha. 35:8; 48:17; 60:17) Za mu iya ce a duk lokacin da mutum ya yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi, ya sami damar yin tafiya a “Hanyar Tsarki” ke nan. Wasu idan suka soma tafiya a hanyar, sai su daina daga baya. Wasu kuma sun ƙudiri niyyar yin tafiya a hanyar har sai sun kai inda za su. Ina ne za su? Ga shafaffu, hanyar za ta kai su ga yin rayuwa a cikin aljannar Allah a sama. (R. Yar. 2:7) Waɗanda za su yi rayuwa har abada a duniya kuma, hanyar za ta kai su ga zama kamilai bayan Sarautar Yesu na Shekara 1000. Idan kana tafiya a wannan hanyar a yau, kada ka juya baya, kuma kada ka bar hanyar har sai ka kai inda za ka, wato sabuwar duniya! w23.05 17 sakin layi na 15; 19 sakin layi na 16-18
Alhamis, 7 ga Agusta
Muna ƙauna gama Allah ne ya fara ƙaunace mu.—1 Yoh. 4:19.
Idan ka yi tunanin yawan alherin da Jehobah ya yi maka, za ka so ka yi masa godiya kuma ka yi alkawarin bauta masa. (Zab. 116:12-14) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa, “kowace baiwa mai kyau, da kowace cikakkiyar kyauta” daga wurin Jehobah suke. (Yak. 1:17) Kuma kyauta mafi girma da Allah ya ba mu ita ce hadayar Ɗansa. Wannan ba ƙaramin alheri ba ne! Fansar Yesu ce ta buɗe maka hanyar zama aminin Jehobah. Ban da haka, Jehobah ya ba ka damar yin rayuwa har abada. (1 Yoh. 4:9, 10) Don haka, wata babbar hanyar da za ka nuna godiyarka ga Jehobah don fansar da sauran albarkun da Jehobah ya yi maka ita ce, ta wurin yin alkawarin bauta masa.—M. Sha. 16:17; 2 Kor. 5:15. w24.03 5 sakin layi na 8
Jumma’a, 8 ga Agusta
Mai yin tafiyarsa cikin gaskiya, mai tsoron Yahweh ne.—K. Mag. 14:2.
Idan muka ga halaye marasa kyau da mutane suke da su a yau, yana sa mu ji kamar yadda Lutu ya ji. Lutu “ya damu ƙwarai game da irin mugayen ayyuka na mutanen Sodom marasa bin doka,” domin ya san cewa Ubanmu na sama ya tsani mugayen halaye. (2 Bit. 2:7, 8) Da yake Lutu yana tsoron Allah kuma yana ƙaunar sa sosai, ya tsani halayen mugayen mutane a zamaninsa. Mu ma a yau, muna rayuwa ne tare da mutanen da ba sa daraja ƙaꞌidodin Allah game da ɗabiꞌa. Duk da haka, za mu iya kasancewa da halaye masu kyau idan muka ci gaba da ƙaunar Allah kuma muna jin tsoron sa. Saboda haka, Jehobah ya ba mu abin da zai taimaka mana ta wurin shawarwarin da ke littafin Karin Magana. Dukan Kiristoci, maza da mata, manya da ƙanana, za su amfana sosai idan suka bi shawarwari masu kyau da ke cikin littafin Karin Magana. Idan muna tsoron Jehobah da gaske, za mu kiyayi yin abokantaka da waɗanda ba su da hali mai kyau. w23.06 20 sakin layi na 1-2; 21 sakin layi na 5
Asabar, 9 ga Agusta
Duk mai so ya bi ni, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki [“gungumen azabarsa,” NWT] kowace rana, ya bi ni.—Luk. 9:23.
Mai yiwuwa ka fuskanci tsanantawa daga wurin ꞌyan iyalinku ko kuma ka sadaukar da dukiya ko wani abu don ka fi mai da hankali a kan hidimarka ga Jehobah. (Mat. 6:33) Idan haka ne, ka kasance da tabbacin cewa Jehobah yana lura da dukan abubuwan da kake yi dominsa. (Ibran. 6:10) Yesu ya ce: “Gaskiya ina gaya muku, wanda ya bar gidansa, ko ꞌyanꞌuwansa, ko mamarsa, ko babansa, ko ꞌyaꞌyansa, ko gonakinsa, saboda ni da kuma saboda labari mai daɗi, abin da zai samu a zamanin nan ma, zai fi sau ɗari, na gidaje, da ꞌyanꞌuwa, da iyaye, da ꞌyaꞌya, da gonaki, amma tare da tsanani. Saꞌan nan a zamani mai zuwa, sai rai na har abada.” (Mar. 10:29, 30) Mai yiwuwa ka ga yadda waɗannan kalaman Yesu suka cika a rayuwarka. Hakika, albarkun da ka samu sun ma fi duk wata sadaukarwa da ka yi.—Zab. 37:4. w24.03 9 sakin layi na 5
Lahadi, 10 ga Agusta
A koyaushe aboki yana nuna ƙauna, an haifi ɗanꞌuwa kuwa domin taimako a kwanakin masifa.—K. Mag. 17:17.
A lokacin da aka yi babbar yunwa a Yahudiya, ꞌyanꞌuwa a ikilisiyar Antakiya sun “yanke shawara cewa su aika wa ꞌyanꞌuwan da suke cikin yankin Yahudiya taimako, kowa daidai ƙarfinsa.” (A. M. 11:27-30) Duk da cewa inda ꞌyanꞌuwa da yunwar ta shafa suke yana nesa da Antakiya, ꞌyanꞌuwan nan sun ce sai sun taimaka musu. (1 Yoh. 3:17, 18) Mu ma za mu nuna cewa mu masu tausayi ne idan muka ji cewa balaꞌi ya sami ꞌyanꞌuwanmu. Za mu yi hakan ta wurin ɗaukan mataki nan da nan. Za mu iya tambayar dattawanmu ko akwai aikin da za mu yi don mu taimaka. Mu yi gudummawa don aikinmu na faɗin duniya, ko kuma mu sa ꞌyanꞌuwa da balaꞌin ya shafa a cikin adduꞌa. Hakan zai iya sa ꞌyanꞌuwanmu su ra abubuwan biyan bukata. Idan Sarkinmu, wato Yesu Kristi ya zo yin hukunci, bari ya same mu muna nuna wa ꞌyanꞌuwanmu halin tausayi kuma ya ce mana mu zo mu gāji mulkin.—Mat. 25:34-40. w23.07 4 sakin layi na 9-10; 6 sakin layi na 12
Litinin, 11 ga Agusta
Bari ku kasance da halin haƙuri cikin dangantakarmu da kowa.—Filib. 4:5.
Yesu ma ya nuna sanin yakamata kamar Jehobah. An aiko shi zuwa duniya don ya yi waꞌazi ga “tumakin Israꞌila waɗanda suka ɓata.” Amma ya nuna sanin yakamata saꞌad da yake yin aikin nan da aka ba shi. Akwai lokacin da wata mata da ba Ba-israꞌiliya ba ce ta roƙe shi ya warkar da ꞌyarta domin ‘wani aljani yana wahalar da ꞌyarta.’ Yesu ya tausaya wa matar kuma ya warkar da ꞌyarta. (Mat. 15:21-28) Ga wani misali kuma. Saꞌad da Yesu ya soma waꞌazi, ya ce: “Duk wanda ya yi musun sanina . . . , ni ma zan yi musun saninsa.” (Mat. 10:33) Amma da Bitrus ya yi musun sanin Yesu har ma sau uku, Yesu ya yi musun sanin Bitrus ne? Aꞌa. Yesu ya san cewa Bitrus ya tuba da gaske kuma shi mai bangaskiya ne. Bayan an ta da Yesu daga mutuwa, ya bayyana ga Bitrus. Da alama ya yi hakan ne don ya tabbatar wa Bitrus cewa ya yafe masa kuma yana ƙaunar sa. (Luk. 24:33, 34) Mun koyi cewa Jehobah da Yesu masu sanin yakamata ne. Mu kuma fa? Jehobah yana so mu zama masu sanin yakamata. w23.07 21 sakin layi na 6-7
Talata, 12 ga Agusta
Babu sauran mutuwa.—R. Yar. 21:4.
Me za mu iya gaya wa mutanen da suke shakkar cewa aljanna za ta zo kamar yadda Allah ya yi alkawari? Na ɗaya, Jehobah da kansa ne ya yi alkawarin. Littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna ya ce: “Shi kuma wanda ke zaune bisa kursiyin ya ce, ‘Duba, sabonta dukan abu ni ke yi.’” Jehobah yana da hikima, da iko, da kuma niyyar cika wannan alkawarin. Na biyu, Jehobah ya san cewa tabbas abin da ya faɗa zai faru, don haka a gunsa, kamar ya riga ya faru ne. Shi ya sa ya ce: “Waɗannan zantattuka masu-aminci ne masu-gaskiya. . . . Sun tabbata.” Na uku, idan Jehobah ya soma yin abu, ba abin da ya isa ya hana shi kammalawa. Shi ya sa ya ce, “Ni ne Alpha da Omega.” (R. Yar. 21:6, TSH) Jehobah zai nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne da bai isa ya hana shi cika nufinsa ba. Don haka, idan wani ya ce, “Anya! Wannan abin zai faru kuwa?” Ka karanta masa Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:5, 6. Ka bayyana masa abin da ke wurin. Ka nuna masa yadda Jehobah ya sa hannu don ya tabbatar mana cewa zai cika alkawarinsa.—Isha. 65:16. w23.11 7 sakin layi na 18-19
Laraba, 13 ga Agusta
Zan sa ka zama babbar alꞌumma.—Far. 12:2.
Saꞌad da Ibrahim ya kai shekara 75 kuma ba shi da yaro ne Jehobah ya yi masa wannan alkawarin. Shin Ibrahim yana raye saꞌad da annabcin nan ya cika? E, amma ba dukansu ba. Bayan ya tsallake Kogin Yufiretis, kuma ya ƙara yin shekaru 25 yana jira, Ibrahim ya ga yadda aka haifi ɗansa na farko, wato Ishaku a hanya mai ban mamaki. Bayan shekaru 60 kuma, ya ga yadda aka haifi jikokinsa guda biyu wato Isuwa da Yakubu. (Ibran. 6:15) Amma Ibrahim bai ga yadda zuriyarsa ta zama babbar alꞌumma kuma ta gāji Ƙasar Alkawari ba. Duk da haka, ya kasance da dangantaka mai kyau da Mahaliccinsa. (Yak. 2:23) Kuma bayan an tashi Ibrahim daga matuwa, zai yi farin cikin sanin cewa bangaskiyarsa da kuma haƙurinsa sun sa mutane daga dukan alꞌummai su sami albarka! (Far. 22:18) Wane darasi ne muka koya? Mai yiwuwa ba za mu iya shaida yadda dukan alkawuran Jehobah za su cika ba. Amma idan muka yi haƙuri kamar Ibrahim, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai yi mana albarka a yanzu, kuma zai yi mana albarku fiye da hakan a sabuwar duniya.—Mar. 10:29, 30. w23.08 24 sakin layi na 14
Alhamis, 14 ga Agusta
Muddin sarki yana bin Yahweh, Yahweh ya sa ya yalwata.—2 Tar. 26:5.
Saꞌad da Sarki Uzziya yake ƙarami, ya nuna sauƙin kai. Ya koyi jin “tsoron Allah.” Ya yi rayuwa na shekaru 68 kuma Jehobah ya albarkace shi a yawancin shekarun. (2 Tar. 26:1-4) Uzziya ya ci yawancin maƙiyan ƙasarsa da yaƙi, kuma ya kāre birnin Urushalima sosai. (2 Tar. 26:6-15) Babu shakka, Uzziya ya ji daɗi sosai don abubuwan da Jehobah ya taimaka masa ya yi. (M. Wa. 3:12, 13) Sarki Uzziya ya saba ba wa mutane umurni kuma su bi. Mai yiwuwa hakan ya sa yana ganin zai iya yin duk abin da yake so. Wata rana, Uzziya ya shiga haikalin Jehobah, kuma ya so ya kona turare a kan bagaden Jehobah, duk da cewa sarakuna ba su da izinin yin hakan. (2 Tar. 26:16-18) Babban Firist mai suna Azariya ya gargaɗe shi, amma hakan ya sa Uzziya fushi sosai. Uzziya bai riƙe amincinsa ga Jehobah ba, kuma hakan abin baƙin ciki ne. Saboda rashin amincinsa, Jehobah ya sa ya kamu da cutar kuturta. (2 Tar. 26:19-21) Da a ce ya ci-gaba da nuna sauƙin kai, da ba haka rayuwarsa ta ƙare ba! w23.09 10 sakin layi na 9-10
Jumma’a, 15 ga Agusta
Ya ware kansa . . . domin yana tsoron waɗanda suke so a yi wa waɗanda ba Yahudawa ba kaciya.—Gal. 2:12.
Har bayan ya zama shafaffen Kirista, manzo Bitrus ya ci-gaba da fama da kasawarsa. A shekara ta 36 bayan haifuwar Yesu, Allah ya aiki Bitrus zuwa wurin Karniliyus kuma a wurin Allah ya ba wa Karniliyus ruhu mai tsarki. Hakan ya nuna cewa “Allah ba ya nuna bambanci” kuma waɗanda ba Yahudawa ba za su iya zama Kiristoci. (A. M. 10:34, 44, 45) Bayan haka, Bitrus ya soma cin abinci da waɗanda ba Yahudawa ba. Hakan abu ne da ba ya yi a dā. Amma wasu Kiristoci da Yahudawa ne suna ganin bai kamata Kiristoci Yahudawa su ci abinci da waɗanda ba Yahudawa ba. Saꞌad da wasu Kiristoci Yahudawa da suke da irin wannan raꞌayin suka zo Antakiya, Bitrus ya daina cin abinci da ꞌyanꞌuwansa da ba Yahudawa ba. Da alama ya yi hakan ne domin ba ya so ya ɓata wa Kiristoci Yahudawa rai. Manzo Bulus ya ga abin da Bitrus ya yi, kuma ya yi masa gyara a gaban sauran ꞌyanꞌuwan. (Gal. 2:13, 14) Duk da wannan kuskuren da Bitrus ya yi, ya ci gaba da yin ƙoƙari. w23.09 22 sakin layi na 8
Asabar, 16 ga Agusta
Zai kuma ƙarfafa ku.—1 Bit. 5:10.
Idan ka bincika kanka kuma ka ga cewa kana bukatar gyara, kada ka yi sanyin gwiwa. Ubangijinmu Yesu mai alheri ne, kuma zai taimake ka. (1 Bit. 2:3) Manzo Bitrus ya tabbatar mana da cewa: Allah “shi da kansa zai mai da ku cikakku, zai kafa ku.” Da farko, Bitrus ya ɗauka cewa bai cancanci ya kasance tare da Ɗan Allah ba. (Luk. 5:8) Amma da taimakon Jehobah da Yesu, Bitrus ya ci gaba da ƙoƙarin bin Yesu. Don haka, Jehobah ya amince da Bitrus ya “shiga cikin madawwamin mulki na Ubangijinmu Yesu Almasihu Mai Cetonmu.” (2 Bit. 1:11) Wannan ba ƙaramin lāda ba ne! Idan ka ci gaba da yin ƙoƙari kamar Bitrus, kuma ka bar Jehobah ya koyar da kai, kai ma za ka samu ladar rai na har abada. Za ka samu ‘ceton ranka wanda shi ne manufar bangaskiyarka.’—1 Bit. 1:9. w23.09 31 sakin layi na 16-17
Lahadi, 17 ga Agusta
Ku yi masa sujada, shi wanda ya yi sama, da duniya.—R. Yar. 14:7.
Mazaunin yana da fili ko kuma farfajiya guda ɗaya. Filin babba ne kewaye da katanga, kuma a wurin ne firistoci suke hidimarsu. A wurin ne aka ajiye bagaden ƙona hadaya tare da daron jan ƙarfe wanda firistocin suke amfani da shi don su tsabtace kansu kafin su soma hidima. (Fitowa 30:17-20; 40:6-8) A yau, Kiristoci shafaffu suna yin hidimarsu da dukan zuciya a nan duniya, wato a farfajiya ko fili na ciki a haikalin. Daron jan ƙarfe da ke cikin mazaunin da na cikin haikalin da aka gina daga baya yana tuna wa shafaffu da dukan Kiristoci cewa yana da muhimmanci su kasance da tsabta a kowane fannin rayuwarsu. To a ina ne taro mai girma ko babban taro suke yin tasu hidimar? Manzo Yohanna ya gan su “suna tsaye a gaban kujerar mulkin . . . suna yi [ma Allah] hidima dare da rana a cikin haikalinsa.” Taro mai girman suna yin hidima a nan duniya, wato fili na waje na haikali na alama. (R. Yar. 7:9, 13-15) Muna godiya sosai don damar da Jehobah ya ba mu mu bauta masa a haikalinsa. w23.10 28 sakin layi na 15-16
Litinin, 18 ga Agusta
Bai yi shakkar alkawarin Allah . . . ba, amma ya ƙara ƙarfi cikin bangaskiyarsa.—Rom. 4:20.
Wata hanya kuma da Jehobah yake ba mu ƙarfi ita ce ta wurin dattawa. (Isha. 32:1, 2) Don haka, in kana cikin damuwa, ka gaya wa dattawa. Kuma idan suna so su taimaka, ka amince. Jehobah zai iya amfani da su don ya ba ka ƙarfi. Begenmu na yin rayuwa har abada ko a aljanna a duniya ko kuma a sama zai iya ƙarfafa mu sosai. (Rom. 4:3, 18, 19) Wannan begen yana ba mu ƙarfin jimre matsaloli da yin waꞌazi da yin ayyuka dabam-dabam a ikilisiya. (1 Tas. 1:3) Kuma wannan begen ne ya ba wa manzo Bulus ƙarfin jimrewa. An ba shi “wahala ta kowace hanya,” ya yi “shakka,” an “tsananta” masa kuma an ‘buga shi har ƙasa.’ Akwai lokutan da ma ya kusan rasa ransa. (2 Kor. 4:8-10) Manzo Bulus ya mai da hankali ga ladan da yake begen samuwa kuma hakan ya ba shi ƙarfin jimrewa. (2 Kor. 4:16-18) Bulus ya mai da hankali a kan begensa na yin rayuwa har abada a sama. Ya yi ta tunani mai zurfi a kan wannan begen kuma hakan ya sa ya ji kamar ana ‘mai da ruhunsa sabo kullum.’ w23.10 15-16 sakin layi na 14-17
Talata, 19 ga Agusta
Ubangiji za ya ba da ƙarfi ga mutanensa; Ubangiji za ya albarkaci mutanensa da salama.—Zab. 29:11, TSH.
Idan ka yi adduꞌa, ka tambayi kanka, ‘Shin wannan ne lokacin da ya dace Jehobah ya amsa adduꞌata?’ Muna iya ganin cewa ya kamata a amsa adduꞌarmu nan-da-nan. Amma gaskiyar ita ce, Jehobah ne ya san ainihin lokacin da ya dace ya amsa adduꞌarmu. (Ibran. 4:16) Idan ba mu sami abin da muka roƙa nan-da-nan ba, za mu ga kamar Jehobah ba ya so ya amsa roƙonmu. Amma ƙila abin da Jehobah yake gaya mana shi ne, ‘Lokaci bai yi ba tukuna.’ Alal misali, ka yi tunanin ɗanꞌuwa matashi da ya roƙi Jehobah ya warkar da shi daga cutarsa, amma bai sami sauƙi ba. Da Jehobah ya warkar da shi, da Shaiɗan ya gaya wa Jehobah cewa ɗanꞌuwan ya ci-gaba da bauta masa ne don ya warkar da shi. (Ayu. 1:9-11; 2:4) Ƙari ga haka, Jehobah ya riga ya shirya lokacin da zai warkar da mu daga dukan cututtuka. (Isha. 33:24; R. Yar. 21:3, 4) Kafin wannan lokacin, ba zai dace mu sa rai cewa Jehobah zai warkar da mu daga cututtukanmu ta hanyar muꞌujiza ba. Don haka, ɗanꞌuwan zai iya roƙon Jehobah ya ba shi ƙarfi da kwanciyar hankali, don ya iya jimre matsalarsa kuma ya ci-gaba da bauta masa da aminci. w23.11 24 sakin layi na 13
Laraba, 20 ga Agusta
Bai yi da mu bisa ga zunubanmu ba, bai kuwa sāka mana bisa ga laifofinmu ba.—Zab. 103:10.
Ba ƙaramin kuskure ne Samson ya yi ba, duk da haka, bai fid da rai ba. Ya nemi yadda zai cim ma aikin da Jehobah ya ba shi na yaƙar Filistiyawa. (Alƙa. 16:28-30) Samson ya roƙi Jehobah ya taimake shi ya “rama a kan Filistiyawa.” Jehobah ya ji adduꞌarsa kuma ya sake ba shi ƙarfi. Hakan ya sa Samson ya yi babban nasara a kan Filistiyawa, fiye ma da waɗanda ya yi a baya. Duk da cewa Samson ya yi fama da sakamakon kuskuren da ya yi, bai daina ƙoƙarin yin nufin Jehobah ba. Mu ma ko da mun yi kuskure kuma an yi mana gyara, ko mun rasa hidimar da muke yi, kada mu fid da rai. Mu tuna cewa Jehobah yana so ya yi mana gafara, komen kuskuren da muka yi. (Zab. 103:8, 9) Jehobah zai iya amfani da mu mu yi nufinsa kamar yadda ya yi da Samson. w23.09 6 sakin layi na 15-16
Alhamis, 21 ga Agusta
Jimrewa takan jawo halin kirki, halin kirki kuma yakan jawo sa zuciya.—Rom. 5:4.
Idan kana jimrewa, Jehobah zai yarda da kai. Amma hakan ba ya nufin cewa Jehobah yana jin daɗin ganin ka kana shan wahala. Yadda kake jimrewa da aminci ne yake sa Jehobah farin ciki. Jimrewarka za ta sa Jehobah ya yarda da kai. Hakan abin ban ƙarfafa ne sosai, ko ba haka ba? (Zab. 5:12) Ka tuna cewa Ibrahim shi ma ya jimre matsalolin da ya fuskanta kuma hakan ya sa Jehobah ya yarda da shi. Jehobah ya ce shi abokinsa ne kuma ya ɗauke shi a matsayin mai adalci. (Far. 15:6; Rom. 4:13, 22) Mu ma hakan zai iya faruwa da mu. Ba yawan ayyukan da muke yi ko inda muke hidima ne yake sa Jehobah ya yarda da mu ba. Yadda muke jimre matsaloli da aminci ne zai sa Jehobah ya yarda da mu. Kuma ko da a wane yanayi muke, komen shekarunmu ko baiwarmu, kowannenmu zai iya jimrewa. Akwai matsalar da kake jimrewa a yanzu da aminci? Idan haka ne, ka san cewa kana faranta ran Jehobah kuma ya yarda da kai. Idan muka san cewa Jehobah ya yarda da mu, hakan zai sa mu ƙara sa zuciya a kan ladan da ya ce zai ba mu. w23.12 11 sakin layi na 13-14
Jumma’a, 22 ga Agusta
Ka nuna kanka namiji ne.—1 Sar. 2:2.
ꞌYanꞌuwa maza suna bukatar su iya tattaunawa da mutane. Wanda ya iya tattaunawa da mutane yana sauraran su, kuma yana fahimtar yadda suke ji. (K. Mag. 20:5) Zai iya sanin yadda mutum yake ji ta muryarsa ko yanayin fuskarsa ko kuma motsin jikinsa. Amma ba za ka iya yin abubuwan nan ba idan ba ka kasancewa tare da mutane. Idan ta waya ko saƙo ne kake yawan tattaunawa da mutane, hakan zai sa ya ƙara yi maka wuya ka iya yin magana da mutane fuska-da-fuska da kyau. Don haka, ka yi iya ƙoƙarinka ka riƙa yin magana da mutane fuska-da-fuska. (2 Yoh. 12) Wajibi ne Kiristan da ya manyanta ya kuma iya kula da kansa da kuma iyalinsa. (1 Tim. 5:8) Zai dace ka koyi wani abu da zai taimaka maka ka sami aiki. (A. M. 18:2, 3; 20:34; Afis. 4:28) Ka sa a san da kai a matsayin wanda yake yin aiki da ƙwazo kuma yake yin ƙoƙarinsa ya gama aikin da aka ba shi. Idan ka yi hakan, mutane za su so su ɗauke ka aiki kuma ba za su so su rasa ka ba. w23.12 27 sakin layi na 12-13
Asabar, 23 ga Agusta
Ranar Ubangiji za ta zo kamar zuwan ɓarawo da dare.—1 Tas. 5:2.
A duk lokacin da Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da “ranar Ubangiji,” yana magana ne game da lokacin da Jehobah zai hukunta maƙiyansa kuma ya ceci mutanensa. A zamanin dā, Jehobah ya hukunta wasu alꞌummai. (Isha. 13:1, 6; Ezek. 13:5; Zaf. 1:8) A zamaninmu, “ranar Ubangiji” za ta soma saꞌad da za a kai wa Babila Babba hari, saꞌan nan ta ƙare a yaƙin Armageddon. Don mu tsira a wannan “ranar,” muna bukatar mu soma shiri tun yanzu. Yesu ya koya mana cewa ba yin shiri kawai za mu yi ba, amma mu ‘zauna da shiri’ don “azaba mai zafi” ko kuma ƙunci mai girma. (Mat. 24:21; Luk. 12:40) A wasiƙa ta farko da manzo Bulus ya rubuta wa Tasalonikawa, ya yi amfani da kwatanci dabam-dabam, don ya taimaka wa Kiristocin su zauna da shiri saboda ranar da Jehobah zai yi hukunci. Bulus ya san cewa ranar Jehobah ba za ta zo a lokacin ba. (2 Tas. 2:1-3) Duk da haka, ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwan su zauna da shiri kamar washegari ne za ta zo. Mu ma za mu iya bin gargaɗinsa. w23.06 8 sakin layi na 1-2
Lahadi, 24 ga Agusta
ꞌYanꞌuwana waɗanda nake ƙauna, ku tsaya daram, ku kafu.—1 Kor. 15:58.
A shekara ta 1978, an yi wani gini mai tsawo da ya kai hawa 60 a birnin Tokyo da ke Jafan. Mutane sun yi mamaki da suka ga ginin don akan yi girgizar ƙasa sosai a birnin. Suna ganin ginin ba zai kai labari ba. Me ya taimaka wa ginin? Maginan sun gina shi yadda zai yi ƙarfi sosai, kuma sun yi shi da ɗan danƙo. Zai iya tanƙwarewa kaɗan saꞌan nan ya miƙe, amma ba zai rushe ba. Kiristoci kamar wannan gini mai tsayi suke. Me ya sa muka ce haka? Kamar yadda ginin yake da ƙarfi, haka ma ya kamata Kirista ya tsaya daram. Bai kamata ya bar kome ya hana shi bin dokokin Jehobah da kuma ƙaꞌidodinsa ba. Amma kuma, kamar yadda ginin yake iya tanƙwarewa, haka ma ya kamata Kirista ya zama mai sanin yakamata. Ya zama mai “sauƙin kai,” wato mai saurin yin biyayya a koyaushe. Amma har ila, zai dace ya zama mai “hankali,” wato mai sanin yakamata, idan zai yiwu ko kuma idan da bukata. (Yak. 3:17) Idan Kirista ya iya daidaita tunaninsa tsakanin abubuwa biyun nan, ba zai zama mai nacewa a kan raꞌayinsa kawai ba, kuma ba zai zama mai halin ko-in-kula ba. w23.07 14 sakin layi na 1-2
Litinin, 25 ga Agusta
Ba ku taɓa ganin Yesu Almasihu ba, amma duk da haka kuna ƙaunarsa.—1 Bit. 1:8.
Sai da Yesu ya dage sosai don Shaiɗan ya yi ta ƙoƙarin sa shi ya yi zunubi. Shaiɗan ya takura ma Yesu, har ya ce ma Yesu ya yi masa sujada. (Mat. 4:1-11) Burinsa shi ne ya sa Yesu ya yi zunubi don ya kasa biyan fansar. A lokacin da Yesu yake hidimarsa a duniya, ya kuma yi fama da wasu matsaloli. An tsananta masa kuma sau da yawa an yi ƙoƙarin kashe shi. (Luk. 4:28, 29; 13:31) Mabiyansa ma sun yi ta yin abubuwa da ba su dace ba amma ya yi haƙuri da su. (Mar. 9:33, 34) A lokacin da ake yi masa shariꞌa, an zalunce shi kuma an yi masa baꞌa. Bayan haka, an zarge shi da aikata laifi kuma an rataye shi har ya mutu. (Ibran. 12:1-3) Ƙari ga haka, saꞌad da yake kan gungumen azaba ya sha wahala sosai shi kaɗai, Jehobah bai kāre shi ba. (Mat. 27:46) Ba shakka Yesu ya sha wahala sosai yayin da yake ba da wannan fansar. Tunanin irin sadaukarwar da Yesu ya yi saboda mu, yana sa mu ƙaunace shi sosai. w24.01 10-11 sakin layi na 7-9
Talata, 26 ga Agusta
Duk mai yin abu da gaggawa lallai ba zai sami biyan bukata ba.—K. Mag. 21:5.
Haƙuri yana sa mu kasance da dangantaka mai kyau da mutane. Yana taimaka mana mu saurari mutane da kyau yayin da suke magana. (Yak. 1:19) Yana kuma sa mu zauna lafiya da mutane. Ko da mun gaji sosai, haƙuri zai taimaka mana kada mu mai da martani cikin hanzari ko mu yi wa ꞌyanꞌuwanmu baƙar magana. Ƙari ga haka, idan muna da haƙuri, ba za mu yi saurin fushi ba don wani ya yi mana baƙar magana. Maimakon mu rama abin da aka yi mana, mu ci-gaba da yin haƙuri da juna da kuma gafarta wa juna da dukan zuciyarmu. (Kol. 3:12, 13) Haƙuri zai iya taimaka mana mu yanke shawarar da ta dace. Maimakon mu yi saurin yanke shawara, haƙuri zai taimaka mana mu yi bincike don mu san ko wace shawara ce ta fi dacewa. Alal misali, idan muna neman aiki, zai yi mana sauƙi mu karɓi aiki na farko da muka samu. Amma idan muna da haƙuri, za mu yi tunani ko hakan zai sa mu yi nisa da iyalinmu ko kuma ya shafi dangantakarmu da Jehobah. Idan muna da haƙuri, za mu guji yanke shawarar da ba ta dace ba. w23.08 22 sakin layi na 8-9
Laraba, 27 ga Agusta
A cikin gaɓoɓina ina ganin wata ƙaꞌida dabam wadda take yaƙi da ƙaꞌidar da hankalina ya ɗauka. Wannan kuwa ta ɗaure ni ga ƙaꞌidar nan ta zunubi wadda take zama a cikin gaɓoɓina.—Rom. 7:23.
Hakika, guje wa abin da zai sa ka yi zunubi bai da sauƙi. Hakan yana iya sa ka karaya. Amma idan ka tuna da alkawarin da ka yi ma Jehobah, hakan zai taimaka maka ka ci-gaba da guje wa shaꞌawoyin nan. Ta yaya? Idan ka yi alkawarin bauta wa Jehobah, ka ƙi kanka ke nan. Hakan yana nufin za ka ƙi duk wani abu ko wata shaꞌawa da za ta ɓata wa Jehobah rai. (Mat. 16:24) Don haka, idan ka fuskanci wata jarraba, ba za ka ɓata lokaci kana tunanin abin da ya kamata ka yi ba, domin ka riga ka yanke shawara cewa za ka riƙe amincinka ga Jehobah. Ba za ka ja da baya ba amma za ka zama kamar Ayuba. Duk da cewa ya fuskanci matsaloli masu wuyan gaske, ya ce: “Har in mutu, ba zan rabu da amincina ba.”—Ayu. 27:5, NWT. w24.03 9 sakin layi na 6-7
Alhamis, 28 ga Agusta
Yahweh yana kurkusa ga masu kira gare shi, ga waɗanda suke kira gare shi cikin gaskiya.—Zab. 145:18.
Jehobah “Allah mai ƙauna” yana tare da mu. (2 Kor. 13:11) Ya damu da kowannenmu. Muna da tabbacin cewa ƙaunarsa marar canjawa ta “kewaye” mu. (Zab. 32:10) Idan muka ƙara yin tunani mai zurfi a kan yadda Jehobah ya nuna mana ƙauna, za mu ƙara ganin tabbaci cewa ya damu da mu sosai, kuma hakan zai sa mu ƙara kusantar sa. Za mu iya yin adduꞌa hankalinmu a kwance kuma mu roƙi Jehobah ya ci-gaba da nuna mana ƙaunarsa. Za mu iya gaya masa dukan abubuwan da ke damun mu don mun san cewa zai fahimce mu kuma yana so ya taimaka mana. (Zab. 145:19) Kamar yadda wuta take sa mu ji ɗumi idan ana sanyi, haka ma ƙaunar Jehobah tana ƙarfafa mu saꞌad da muke fuskantar matsaloli. Don haka, ka yi farin ciki sosai domin ƙaunar Jehobah za ta iya ƙarfafa ka kuma ta ba ka salama. Ka nuna cewa kai ma kana ƙaunar Jehobah kuma ka ce: “Ina ƙaunar [Jehobah].”—Zab. 116:1. w24.01 31 sakin layi na 19-20
Jumma’a, 29 ga Agusta
Na kuma sanar musu da sunanka.—Yoh. 17:26, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
Ba sunan Jehobah ne kawai Yesu ya gaya wa mutane ba. Yahudawan da Yesu ya koyar da su, sun riga sun san sunan Allah. Amma Yesu ne “wanda . . . ya bayyana mana shi” fiye da kowa. (Yoh. 1:17, 18) Alal misali, Nassosin Ibrananci sun nuna mana cewa Jehobah yana da jin ƙai da kuma tausayi. (Fit. 34:5-7) Amma Yesu ya taimaka mana mu ƙara fahimtar yadda Jehobah yake nuna halayen nan ta wurin kwatancin da ya yi game da ɗa mubazzari da kuma babansa. A duk lokacin da muka karanta yadda babansa ya gan sa “tun yana daga nesa,” da yadda ya gudu ya same shi, ya rungume shi, da yadda ya yafe masa da dukan zuciyarsa, hakan yana ƙara taimaka mana mu fahimci cewa Jehobah mai jin ƙai ne da kuma tausayi. (Luk. 15:11-32) Yesu ya taimaka wa mutane su fahimci ainihin halayen Jehobah. w24.02 10 sakin layi na 8-9
Asabar, 30 ga Agusta
Mu yi wa waɗansu taꞌaziyya . . . da wannan taꞌaziyyar da muka samu daga wurin Allah.—2 Kor. 1:4.
Jehobah yana sa waɗanda suke cikin damuwa su samu ƙarfafa da kuma wartsakewa. Ta yaya mu ma za mu yi koyi da Jehobah wajen jin tausayin mutane da kuma ƙarfafa su? Wani abin da zai taimaka mana shi ne, koyan halayen da za su motsa mu mu riƙa jin tausayin mutane kuma mu ƙarfafa su. Waɗanne halaye ke nan? Me zai taimaka mana mu ci-gaba da ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu don mu yi ta “ƙarfafa juna” a koyaushe? (1 Tas. 4:18) Muna bukatar mu koyi halin jin tausayin juna da yin alheri, kuma mu ɗauki ꞌyanꞌuwa a ikilisiya kamar ꞌyan iyalinmu. (Kol. 3:12; 1 Bit. 3:8) Ta yaya halayen nan za su taimaka mana? Idan muna tausaya wa ꞌyanꞌuwanmu kuma mun damu da su da gaske, da zarar mun ga suna cikin damuwa, za mu ƙarfafa su. Yesu ya kuma ce, “Abin da yake cikin zuciya, shi yake fitowa a baki. Mutumin kirki, daga ajiyarsa na kirki, yakan fitar da abin kirki.” (Mat. 12:34, 35) Ba shakka, ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu saꞌad da suke cikin damuwa hanya ce ta musamman na nuna musu cewa muna ƙaunar su da gaske. w23.11 10 sakin layi na 10-11
Lahadi, 31 ga Agusta
Waɗanda suke da hikima za su gane.—Dan. 12:10.
Don mu iya fahimtar annabcin Littafi Mai Tsarki, muna bukatar taimakon Jehobah. Ka yi laꞌakari da misalin nan. A ce za ka je wani wuri da ba ka taɓa zuwa ba, amma abokin tafiyarka ya san wurin sosai. Ya san inda kake, kuma ya san inda kowace hanya ta nufa. Hankalinka zai kwanta ko ba haka ba? Jehobah yana kama da abokin tafiyar nan. Ya san abubuwan da za su faru da mu dalla-dalla. Don haka, idan muna so mu fahimci maꞌanar annabcin Littafi Mai Tsarki, dole ne mu nemi taimakon Jehobah. (Dan. 2:28; 2 Bit. 1:19, 20) Iyayen kirki sukan so yaransu su ji daɗin rayuwa a nan gaba. Abin da Jehobah yake so mu ma mu samu ke nan. (Irm. 29:11) Sai dai iyaye ba za su iya gaya wa yaransu abin da zai faru da su a nan gaba ba. Amma Jehobah zai iya yin hakan babu kuskure. Ya sa an rubuta annabce-annbace a Kalmarsa don ya sanar da mu muhimman abubuwan da za su faru a nan gaba.—Isha. 46:10. w23.08 8 sakin layi na 3-4