Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • es25 pp. 67-77
  • Yuli

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yuli
  • Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Talata, 1 ga Yuli
  • Laraba, 2 ga Yuli
  • Alhamis, 3 ga Yuli
  • Jumma’a, 4 ga Yuli
  • Asabar, 5 ga Yuli
  • Lahadi, 6 ga Yuli
  • Litinin, 7 ga Yuli
  • Talata, 8 ga Yuli
  • Laraba, 9 ga Yuli
  • Alhamis, 10 ga Yuli
  • Jumma’a, 11 ga Yuli
  • Asabar, 12 ga Yuli
  • Lahadi, 13 ga Yuli
  • Litinin, 14 ga Yuli
  • Talata, 15 ga Yuli
  • Laraba, 16 ga Yuli
  • Alhamis, 17 ga Yuli
  • Jumma’a, 18 ga Yuli
  • Asabar, 19 ga Yuli
  • Lahadi, 20 ga Yuli
  • Litinin, 21 ga Yuli
  • Talata, 22 ga Yuli
  • Laraba, 23 ga Yuli
  • Alhamis, 24 ga Yuli
  • Jumma’a, 25 ga Yuli
  • Asabar, 26 ga Yuli
  • Lahadi, 27 ga Yuli
  • Litinin, 28 ga Yuli
  • Talata, 29 ga Yuli
  • Laraba, 30 ga Yuli
  • Alhamis, 31 ga Yuli
Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025
es25 pp. 67-77

Yuli

Talata, 1 ga Yuli

Ya dinga zagayawa yana yin aikin alheri, yana warkar da [mutane].—A. M. 10:38.

Yesu ya yi koyi da halaye da tunanin Ubansa a cikin dukan abubuwan da ya yi da kuma abubuwan da ya ce, har ma a muꞌujizan da ya yi. (Yoh. 14:9) Me za mu iya koya daga muꞌujizan da Yesu ya yi? Yesu da Ubansa suna ƙaunar mu sosai. Saꞌad da Yesu yake duniya, ya nuna cewa yana ƙaunar mutane ta wajen yin amfani da ikonsa na yin muꞌujiza don ya taimaka wa waɗanda suke shan wahala. Akwai wani lokacin da wasu makafi guda biyu suka roƙi Yesu ya taimaka musu. (Mat. 20:​30-34) Ku lura cewa “saboda tausayi,” Yesu ya je ya warkar da su. Irin wannan tausayin ne ya motsa shi ya ciyar da mayunwata, kuma ya warkar da wani kuturu. (Mat. 15:32; Mar. 1:41) Muna da tabbacin cewa Jehobah Allahnmu mai “yawan jinƙai” da kuma Ɗansa suna ƙaunar mu sosai kuma suna baƙin ciki saboda wahalar da muke sha. (Luk. 1:78; 1 Bit. 5:7) Hakika, suna marmarin su cire matsalolin da ꞌyan Adam suke fuskanta. w23.04 3 sakin layi na 4-5

Laraba, 2 ga Yuli

Ku da kuke ƙaunar Yahweh, ku ƙi mugunta! Gama yana kiyaye rayukan masu ƙaunarsa, yana kuɓutar da su daga hannun mugaye.—Zab. 97:10.

Za mu iya ɗaukan matakan da za su taimaka mana mu guji kallo, ko kuma karanta abubuwa marasa kyau da suke a koꞌina a yau. Karanta Littafi Mai Tsarki da kuma nazarin sa zai sa mu cika zuciyarmu da abubuwa masu kyau. Wani abin da zai kāre zuciyarmu kuma shi ne zuwa taro da kuma yin waꞌazi. Idan muna hakan, Jehobah ya ce ba zai bari a gwada mu fiye da ƙarfinmu ba. (1 Kor. 10:​12, 13) Kowannenmu yana bukatar yin adduꞌa ga Jehobah sosai fiye da dā, don ya iya riƙe aminci ga Jehobah a wannan kwanaki na ƙarshe. Jehobah yana so mu ‘faɗa masa dukan zuciyarmu.’ (Zab. 62:8) Ka dinga yabon Jehobah kana gode masa don abubuwan da yake yi. Ka roƙe shi ya ba ka ƙarfin zuciya don ka iya yin waꞌazi. Ka roƙe shi ya taimake ka ka iya jimre matsalolin da kake fuskanta kuma ka ƙi faɗa wa jarabobi. Kada ka bar kome ya hana ka yin adduꞌa ga Jehobah a-kai-a-kai. w23.05 7 sakin layi na 17-18

Alhamis, 3 ga Yuli

Mu lura da juna . . . , mu dinga ƙarfafa juna.—Ibran. 10:​24, 25.

Me ya sa muke zuwa taron ikilisiya? Muna yin hakan ne musamman don mu yabi Jehobah. (Zab. 26:12; 111:1) Wani dalili kuma da ya sa muke zuwa taro shi ne, don mu ƙarfafa juna, don muna a lokaci mai wuya. (1 Tas. 5:11) Idan muka ɗaga hannu kuma muka yi kalami a taro, za mu cim ma abubuwa biyun nan. Amma akwai wasu abubuwa da za su iya sa ya yi mana wuya mu yi kalami. Wataƙila muna jin tsoron yin kalami, ko kuma muna son yin kalami amma wasu lokuta ba a kiran mu saꞌad da muka ɗaga hannu. Me zai taimaka mana idan muna irin waɗannan yanayoyin? Manzo Bulus ya ce mu mai da hankali ga “ƙarfafa juna.” Ko da gajeren kalami muka yi, zai ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu. Idan muka tuna hakan, ba za mu ji tsoron yin kalami ba. Idan ma wani lokaci ba a kira mu ba, za mu iya yin farin ciki domin hakan zai ba wasu zarafi su ma su yi kalami.—1 Bit. 3:8. w23.04 20 sakin layi na 1-3

Jumma’a, 4 ga Yuli

Bari ya koma Urushalima, . . . ya sake gina Gidan.—Ezra 1:3.

Sarki ya yi wata sanarwa! Yahudawa da suka yi shekaru 70 suna bauta a Babila sun sami ꞌyanci, kuma za su iya komawa ƙasarsu Israꞌila. (Ezra 1:​2-4) Jehobah ne kawai zai iya sa hakan ya faru. Domin Babiloniyawa ba sa ba wa bayinsu ꞌyanci. (Isha. 14:​4, 17) Amma an ci ƙasar Babila da yaƙi, kuma sabon sarkin ya gaya wa Yahudawan cewa za su iya barin ƙasar. Dukan Yahudawan musamman ma magidanta suna bukatar su yanke shawara ko za su ci-gaba da zama a Babila ko za su koma Israꞌila. Mai yiwuwa yanke shawarar nan bai yi musu sauƙi ba. Da yawa daga cikin Yahudawan ba za su iya komawa Israꞌila ba saboda tsufa. Kuma da yake an haifi yawancin Yahudawan a Babila, ba su taɓa yin rayuwa a wani wuri ba. A ganinsu, ƙasar Israꞌila ƙasar kakaninsu ce. Da alama wasu Yahudawa sun yi arziki sosai a Babila. Don haka, zai yi musu wuya su bar ƙasar Babila inda suke da arziki su koma ƙasar da ba su sani ba. w23.05 14 sakin layi na 1-2

Asabar, 5 ga Yuli

Ku zauna da shiri.—Mat. 24:44.

Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu ci-gaba da zama masu jimiri, da tausayi da kuma ƙauna. Luka 21:19 ta ce: “Idan kuka jimre, za ku tsira.” Kolosiyawa 3:12 ta ce: “Ku ɗauki hali na jin tausayin juna.” 1 Tasalonikawa 4:​9, 10 kuma sun ce: “Ku da kanku Allah ya koya muku cewa ku ƙaunaci juna. . . . Sai dai muna ƙarfafa ku, ꞌyanꞌuwa, ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske.” ꞌYanꞌuwa da aka ambata a waɗannan ayoyin sun riga sun nuna cewa su masu jimiri, da tausayi, da kuma ƙauna ne. Duk da haka, suna bukatar su ci-gaba da nuna waɗannan halayen. Abin da mu ma muke bukatar mu yi ke nan. Me zai taimaka maka? Ka bincika yadda Kiristoci a ƙarni na farko suka nuna kowanne cikin halayen nan. Saꞌan nan, ka ga yadda za ka bi halinsu. Yin hakan zai sa ka zauna da shiri don ƙunci mai girma. Za ka ga cewa kafin ƙunci mai girma, ka riga ka koyi halin jimiri, kuma za ka ƙudura cewa za ka ci-gaba da jimrewa. w23.07 3 sakin layi na 4, 8

Lahadi, 6 ga Yuli

Hanya mai kyau za ta kasance a wurin, . . . “Hanyar Tsarki.”—Isha. 35:8.

Ko da mu shafaffu ne ko “waɗansu tumaki” muna bukatar mu ci-gaba da bin “Hanyar Tsarki” domin za ta taimaka mana mu ci-gaba da bauta ma Jehobah a yanzu da kuma a nan gaba saꞌad da Mulkin Allah zai mai da duniya aljanna. (Yoh. 10:16) Tun daga 1919, miliyoyin maza da mata da yara sun bar Babila Babba wadda ita ce daular addinin ƙarya, kuma suka soma tafiya a “Hanyar Tsarki.” Saꞌad da Yahudawan suke barin Babila, Jehobah ya cire duk wani abin da zai hana su tafiya. (Isha. 57:14) Waɗanda suke tafiya a “Hanyar Tsarki” a yau kuma fa? Ɗarurruwan shekaru kafin 1919, Jehobah ya sa waɗanda suke ƙaunar sa su kyautata hanyar don mutane su iya barin Babila Babba. (Ka kuma duba Ishaya 40:3.) Sun yi gyare-gyare da ake bukata a hanyar domin mutane masu zukatan kirki su iya barin bautar ƙarya, kuma su soma bauta ma Jehobah tare da bayinsa. w23.05 15-16 sakin layi na 8-9

Litinin, 7 ga Yuli

Ku yi wa Yahweh hidima da murna! Ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki!—Zab. 100:2.

Jehobah yana so mu bauta masa da farin ciki da kuma yardar rai. (2 Kor. 9:7) Amma zai dace mu ci gaba da yin ƙoƙarin cika maƙasudinmu ko da ba mu da niyya? Ka yi laꞌakari da misalin manzo Bulus. Ya ce: “Ina horon jikina, na mai da shi bawana.” (1 Kor. 9:​25-27) Ko a lokacin da manzo Bulus bai da niyyar yin abin da Jehobah yake so ya yi, ya tilasta wa kansa ya yi hakan. Jehobah ya amince da hidimar Bulus? Ƙwarai kuwa! Kuma Jehobah ya yi masa albarka domin ƙoƙarinsa. (2 Tim. 4:​7, 8) Jehobah yana farin cikin ganin ƙoƙarin da muke yi don mu cim ma maƙasudinmu ko da ba mu da niyyar yin hakan. Yana farin ciki domin ya san cewa muna ƙoƙari ne don muna ƙaunarsa ba don muna jin daɗin yin abin a koyaushe ba. Kamar yadda Jehobah ya albarkaci Bulus, Zai albarkace mu don ƙoƙarin da muke yi. (Zab. 126:5) Kuma idan muna ganin yadda yake mana albarka, hakan zai sa mu soma kasancewa da niyya. w23.05 29 sakin layi na 9-10

Talata, 8 ga Yuli

Ranar Ubangiji za ta zo.—1 Tas. 5:2.

Manzo Bulus ya ce waɗanda ba za su tsira a ranar Jehobah ba suna kama da masu barci. Waɗanda suke barci ba sa sanin abin da yake faruwa, kuma ba za su san yadda lokaci yake wucewa ba. Don haka, ba za su san lokacin da wani abu mai muhimmanci yake faruwa ba, balle ma su ɗau mataki. Yawancin mutane a yau suna kama da mutanen da suke barci. (Rom. 11:8) Ba su gaskata da alamun da suke nuna cewa muna “kwanakin ƙarshe” ba, kuma cewa ƙunci mai girma zai zo nan ba daɗewa ba. (2 Bit. 3:​3, 4) Amma a kowace rana, mun san cewa ranar tana ƙara matsowa, kuma yana da muhimmanci mu ƙara zama da shiri. (1 Tas. 5:6) Don haka, bukatar mu natsu kuma mu mai da hankali. Me ya sa? Don kada mu soma saka hannu a harkokin siyasa ko rikice-rikice da bambamce-bambamce na mutanen duniya. Yayin da ranar Jehobah take gabatowa, za a ƙara matsa mana mu goyi bayan wani ɓangare. Amma ba ma bukatar mu damu game da abin da za mu ce a yanayin nan. Ruhu mai tsarki zai taimaka mana mu natsu kuma mu yi tunani sosai don mu yi abin da ya dace.—Luk. 12:​11, 12. w23.06 10 sakin layi na 6-7

Laraba, 9 ga Yuli

Ya Ubangiji Yahweh, bari ka tuna da ni! Ina roƙonka, ya Allah, ka sāke ba ni ƙarfi.—Alƙa. 16:28.

Idan ka ji sunan nan Samson, wane tunani ne yake zuwa zuciyarka? Ba mamaki, za ka tuna cewa shi wani mutum ne mai ƙarfi sosai. Hakan gaskiya ne. Amma akwai wani zaɓi marar kyau da Samson ya yi da ya sa ya sha wahala sosai. Duk da haka, Allah ya mai da hankali ga amincinsa ne kuma ya sa an rubuta labarin wannan bawan Allah a Littafi Mai Tsarki don amfanin mu. Jehobah ya yi abubuwan ban mamaki ta wurin Samson don ya ceci mutanensa Israꞌilawa. Ɗarurruwan shekaru bayan mutuwar Samson, Jehobah ya sa manzo Bulus ya rubuta sunansa a cikin mutane masu bangaskiya sosai. (Ibran. 11:​32-34) Abubuwan da Samson ya yi za su iya ƙarfafa mu don ya dogara ga Jehobah har a yanayi mai wuya. Za mu ga abin da za mu koya daga wurin Samson, da kuma yadda labarinsa zai ƙarfafa mu. w23.09 2 sakin layi na 1-2

Alhamis, 10 ga Yuli

Ku faɗa wa Allah . . . roƙo [nku].—Filib. 4:6.

Wani abu kuma da zai sa mu ƙara zama masu jimiri shi ne, idan muna adduꞌa kullum muna gaya wa Jehobah abubuwa da muke fuskanta. (1 Tas. 5:17) Wataƙila ba ka fuskantar wata babbar matsala yanzu, amma idan wani abu ya ɓata maka rai, ko ka riƙice, ko abubuwa sun yi maka yawa, kana roƙon Jehobah ya taimaka maka? Idan ka saba roƙon Jehobah ya taimake ka da ƙananan matsalolin da kake fuskanta yanzu, za ka yi saurin neman taimakonsa idan babbar matsala ta same ka a nan gaba. Idan kana hakan, ba za ka yi shakkar cewa Jehobah ya san lokaci, da kuma hanyar da ta fi dacewa ya taimaka maka ba. (Zab. 27:​1, 3) Idan muna jimre matsalolin da muke fuskanta a yau, za mu iya jimre waɗanda za mu fuskanta a lokacin ƙunci mai girma. (Rom. 5:3) Me ya sa? Domin ꞌyanꞌuwa da yawa sun ce duk lokacin da suka jimre wata matsala, yana ba su ƙarfin jimre wadda za ta taso a gaba. Yadda Jehobah ya taimaka musu suka iya jimrewa yana ƙara sa su gaskanta cewa Jehobah yana tare da su kuma yana so ya taimake su. Wannan bangaskiyar ce ta taimaka musu suka jimre matsalar da ta sake taso musu.—Yak. 1:​2-4. w23.07 3 sakin layi na 7-8

Jumma’a, 11 ga Yuli

Na yarda maka.—Far. 19:21.

Da yake Jehobah mai sauƙin kai ne da kuma tausayi, yana nuna sanin yakamata. Alal misali, Jehobah ya nuna sauƙin kai saꞌad da yake so ya halaka birnin Saduma ko kuma Sodom. Ko da yake malaꞌikunsa sun gaya wa Lot, wato Lutu cewa ya gudu zuwa yankunan tuddai, Lutu ya ji tsoron zuwa wurin. Don haka, ya roƙa cewa a bar shi da iyalinsa su gudu zuwa wani ƙaramin gari mai suna Zowar, ko da yake Jehobah yana so ya halaka garin. Jehobah zai iya nace cewa Lutu ya yi daidai abin da ya gaya masa. Amma ya amince da roƙon da Lutu ya yi kuma ya fasa halaka garin Zowar. (Far. 19:​18-22) Ɗarurruwan shekaru bayan hakan, Jehobah ya tausaya wa mutanen Nineba. Ya aiki annabi Yona, wato Yunana, ya sanar cewa za a halaka birnin da kuma mugayen mutanen da ke cikinsa. Amma da mutanen Nineba suka tuba, Jehobah ya tausaya musu kuma ya fasa halaka birnin.—Yona 3:​1, 10; 4:​10, 11. w23.07 21 sakin layi na 5

Asabar, 12 ga Yuli

Suka kashe [Yowash] . . . , amma ba a binne shi inda ake binne sarakuna ba.—2 Tar. 24:25.

Wane darasi za mu koya daga labarin Yowash? Abin da Yowash ya yi ya nuna cewa shi kamar bishiya ne da jijiyoyinsa ba su riƙe ƙasa ba. Sanda da aka tokare bishiyar da ita ce take taimaka ma bishiyar ta tsaya a tsaye. Yehoyida shi ne kamar wannan sandan da Yowash ya dogara a kai. Da Yehoyida ya rasu kuma Yowash ya saurari ꞌyan ridda, ya faɗi kasa, wato ya daina bauta wa Jehobah. Wannan ya koya mana cewa, bai kamata mu dinga jin tsoron Allah don kawai mun ga ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci ko kuma ꞌyan gidanmu suna hakan ba. Idan muna so mu riƙe aminci ga Jehobah, dole mu ci-gaba da yin abubuwan da za su sa mu ƙaunace shi kuma mu girmama shi, wato mu dinga yin nazarin Littafi Mai Tsarki a-kai-a-kai, da yin tunani mai zurfi, da kuma yin adduꞌa. (Irm. 17:​7, 8; Kol. 2:​6, 7) Jehobah ba ya gaya mana mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. Littafin Mai-Waꞌazi 12:13 ta gaya mana abin da yake so daga gare mu. Ta ce: “Ka ji tsoron Allah, ka kiyaye umarnansa, gama wannan kaɗai shi ne aikin mutum.” Idan muna da tsoron Allah, za mu iya riƙe amincinmu ga Jehobah ko da me zai faru a nan gaba. Ba abin da zai ɓata dangantakarmu da Jehobah. w23.06 19 sakin layi na 17-19

Lahadi, 13 ga Yuli

Duba, sabonta dukan abu ni ke yi.—R. Yar. 21:​5, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

Aya ta biyar ta soma da cewa: “Shi kuma wanda ke zaune bisa kursiyin ya ce.” (R. Yar. 21:5a, TSH) Waɗannan kalaman suna da muhimmanci, domin a littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna, sau uku ne kaɗai Jehobah da kansa ya yi magana. Jehobah bai ba da wannan tabbacin ta bakin wani malaꞌika mai iko ko ta bakin Yesu ba, a maimako ya faɗe shi da kansa! Wannan babban dalili ne na gaskata kalmomin da ke Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21 ayoyi 5 da 6. Me ya sa? Domin Jehobah “ba ya ƙarya.” (Tit. 1:2) Ba shakka abin da ayoyin nan suka ce zai faru. Jehobah ya soma da cewa: “Duba.” Kuma an yi ta amfani da kalmar nan “duba” sau da yawa a littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna. Wani littafin bincike ya ce, “a Helenanci, ana amfani da kalmar nan ne don a jawo hankalin wanda yake karatu ya lura da abin da za a faɗa.” Mene ne Jehobah ya faɗa bayan haka? Ya ce: “Sabonta dukan abu ni ke yi.” Jehobah yana magana ne a kan abin da zai faru a nan gaba, amma ya san cewa ba abin da zai hana wannan abin faruwa. Shi ya sa a ayar nan, ya yi magana kamar ya riga ya soma yin su.—Isha. 46:10. w23.11 3-4 sakin layi na 7-8

Litinin, 14 ga Yuli

Ya fita waje ya yi kuka mai zafi.—Mat. 26:75.

Bitrus ya yi fama da kasawarsa. Bari mu ga wasu misalai. Da Yesu ya bayyana yadda zai sha wahala kuma ya mutu kamar yadda aka annabta, Bitrus ya gaya masa cewa hakan ba zai faru ba. (Mar. 8:​31-33) Bitrus da sauran manzannin sun yi ta gardama da juna a kan wane ne mafi girma. (Mar. 9:​33, 34) A dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, Bitrus ya kai ma wani mutum hari kuma ya yanke kunnensa. (Yoh. 18:10) A daren, tsoron mutane ya sa Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu har sau uku. (Mar. 14:​66-72) Bitrus ya yi kuka sosai saboda kuskuren da ya yi. Yesu bai yashe manzonsa da ya yi sanyin gwiwa ba. Bayan an tashi Yesu daga mutuwa, ya sake ba wa Bitrus dama don Bitrus ya nuna masa cewa yana ƙaunarsa. Yesu ya gaya wa Bitrus ya yi kiwon tumakinsa. (Yoh. 21:​15-17) Kuma Bitrus ya yarda. Yana Urushalima a ranar Fentakos kuma yana cikin mutane na farko da aka ba su ruhu mai tsarki. w23.09 22 sakin layi na 6-7

Talata, 15 ga Yuli

Ka yi kiwon tumakina.—Yoh. 21:16.

Manzo Bitrus ya gaya wa ꞌyanꞌuwansa dattawa cewa: “Ku yi kiwon garken Allah.” (1 Bit. 5:​1-4) Idan kai dattijo ne, mun san kana ƙaunar ꞌyanꞌuwa da ke ikilisiya, kuma kana so ka kula da su. Amma wani lokaci, kana iya ji kamar ba za ka iya yin hakan ba domin ka gaji sosai ko kuma ayyuka sun yi maka yawa. Me zai taimaka maka? Ka gaya wa Jehobah damuwarka da kuma yadda kake so ka taimaki ꞌyanꞌuwa. Bitrus ya rubuta cewa: “Duk wanda baiwarsa ta yin hidima ce, to, sai ya yi hidimar da ƙarfin da Allah ya bayar.” (1 Bit. 4:11) Wataƙila matsalolin da wasu ꞌyanꞌuwa suke fuskanta, ba za a iya magance su a wannan zamanin ba. Don haka, ka tuna cewa ‘Babban Makiyayi,’ wato Yesu Kristi zai iya taimakon su fiye da kai. Zai iya yin hakan a yau da kuma a sabuwar duniya. Abin da kawai Jehobah yake so dattawa su yi shi ne su ƙaunaci ꞌyanꞌuwansu, su kula da su kuma su ‘zama gurbi’ ga ꞌyanꞌuwansu. w23.09 29-30 sakin layi na 13-14

Laraba, 16 ga Yuli

Ubangiji ya san cewa tunanin masu hikima banza ne.—1 Kor. 3:20.

Dole mu yi niyyar kauce ma tunanin raꞌayin mutane. Idan muka bi raꞌayin mutane, hakan zai iya sa mu yi banza da umurnin Jehobah. (1 Kor. 3:19) A yawancin lokuta, “hikimar wannan duniya” takan zuga mutane su ƙi bin umurnin Jehobah. Wasu Kiristoci a ikilisiyar Birgamum da Tiyatira sun bi raꞌayin mutanen birninsu game da lalata da kuma bautar gumaka. Yesu ya ja musu kunne sosai don yadda suke ƙyale halin lalata a ikilisiyarsu. (R. Yar. 2:​14, 20) A yau ma, ana matsa mana mu bi raꞌayoyi marasa kyau. ꞌYan iyalinmu ko kuma abokanmu za su iya ce mana yadda muke bin dokokin Jehobah ya wuce gona da iri. Misali, za su iya cewa yin abin da zuciyarka take so ba laifi ba ne, kuma abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da lalata tsohon yayi ne. Wani lokaci za mu iya yin tunanin cewa, umurnin da Jehobah ya ba mu bai isa ba. Ƙila ma mu ji kamar gwamma mu “wuce abin da aka rubuta.”—1 Kor. 4:6. w23.07 16 sakin layi na 10-11

Alhamis, 17 ga Yuli

Aboki na ƙwarai yana nuna ƙauna a koyaushe, kuma shi ɗanꞌuwa ne da ke ba da taimako a lokacin damuwa.—K. Mag. 17:​17, New World Translation.

Mahaifiyar Yesu, wato Maryamu tana bukatar ƙarfafa. Ba ta yi aure ba amma malaꞌikan ya ce za ta yi ciki. Ba ta taɓa renon yaro na kanta ba, ga shi yanzu an ce ita ce za ta reni yaron da zai zama Almasihu. Kuma da yake ba ta taɓa kwana da namiji ba, me za ta gaya wa Yusufu wanda yake neman ta da aure? (Luk. 1:​26-33) Me Maryamu ta yi don ta samu ƙarfi? Ta nemi taimako. Alal misali, ta yi wa malaꞌikan tambayoyi don ya yi mata ƙarin bayani. (Luk. 1:34) Jim kaɗan bayan hakan, sai ta yi doguwar tafiya zuwa wani gari a “tuddan yankin Yahudiya” gun wata danginta mai suna Alisabatu. Kuma tafiyar ta ƙarfafa ta. Jehobah ya sa Alisabatu ta gaya wa Maryamu wani annabci game da ɗan da za ta haifa. (Luk. 1:​39-45) Maryamu ta ce Jehobah ya yi “manyan abubuwa” da hannunsa mai tsarki. (Luk. 1:​46-51) Jehobah ya ƙarfafa Maryamu ta wurin malaꞌikan nan Jibrailu da Alisabatu. w23.10 14-15 sakin layi na 10-12

Jumma’a, 18 ga Yuli

Ya mai da mu mu zama masu mulki da firistoci masu hidimar Allah Ubansa.—R. Yar. 1:6.

An shafe wasu mabiyan Yesu Kristi da ruhu mai tsarki, kuma suna da dangantaka ta musamman da Jehobah. Waɗannan shafaffu guda 144,000 za su yi hidima a matsayin firistoci tare da Yesu a sama. (R. Yar. 14:1) Wuri Mai Tsarki da ke cikin mazaunin yana wakiltar matsayinsu na ꞌyaꞌyan Allah ko da yake suna duniya. (Rom. 8:​15-17) Wuri Mafi Tsarki kuma yana wakiltar sama inda Jehobah yake. “Labulen” da ya raba tsakanin wuri Mai Tsarki da Mafi Tsarki yana wakiltar jikin Yesu. Saꞌad da yake duniya, da yake yana da jiki irin na ꞌyan Adam, ba zai iya zuwa sama don ya yi hidima a matsayin Babban Firist a haikalin Jehobah ba. Da ya mutu, ya ba da jikinsa a matsayin hadaya, kuma hakan ya buɗe wa shafaffu hanyar zuwa sama. Amma kafin su iya zuwa sama, wajibi ne su ma su rabu da jikinsu na ꞌyan Adam.—Ibran. 10:​19, 20; 1 Kor. 15:50. w23.10 28 sakin layi na 13

Asabar, 19 ga Yuli

Ba ni da zarafi in yi zance a kan Gideyon.—Ibran. 11:32.

Gideyon bai yi fushi ba da mutanen Ifrayim suka kushe shi. (Alƙa. 8:​1-3) Ya amsa musu a hankali. Yadda ya saurare su ya nuna cewa shi mai tawaliꞌu ne, kuma ya yi maganar da za ta kwantar musu da hankali. Dattawa masu hikima suna bin halin Gideyon. Sukan saurari mutum da kyau, kuma idan aka kushe su, sukan faɗi alheri. (Yak. 3:13) Ta yin hakan, suna ƙara sa ikilisiya ta zauna lafiya. Da aka yabi Gideyon don nasarar da ya yi a kan mutanen Midiyan, ya miƙa yabon ga Jehobah. (Alƙa. 8:​22, 23) Ta yaya dattawa za su bi halin Gideyon? Idan aka yabe su don wani abin da suka yi, zai dace su miƙa yabon ga Jehobah. (1 Kor. 4:​6, 7) Misali, idan aka yabi dattijo don yadda yake koyarwa, zai iya cewa abin da ya koyar daga Kalmar Allah ne, kuma koyawar da muke samu daga ƙungiyar Jehobah ce take taimaka wa dukanmu. Wani lokaci, zai dace dattawa su yi tunani ko suna yin abubuwa don su jawo hankalin mutane gare su. w23.06 4 sakin layi na 7-8

Lahadi, 20 ga Yuli

Tunanina ba kamar tunaninku ba ne.—Isha. 55:8.

Idan ba mu samu abin da muka roƙa ba, zai dace mu tambayi kanmu cewa, ‘Abin da nake adduꞌa a kai ya dace kuwa?’ A yawancin lokuta, mukan ɗauka cewa mun san abin da ya dace da mu. Amma mai yiwuwa abubuwan da muka roƙa ba su ne za su amfane mu ba. Idan muna fuskantar matsala, mai yiwuwa ba abin da muka roƙi Jehobah ya yi mana ne zai warware matsalar ba. Kuma ƙila wasu abubuwan da muka roƙa ba su jitu da nufin Jehobah ba. (1 Yoh. 5:14) Alal misali, a ce iyaye sun roƙi Jehobah ya sa yaronsu ya ci-gaba da bauta masa. Za mu iya ganin cewa roƙo mai kyau ne suka yi. Amma Jehobah ba ya tilasta mana mu bauta masa. Yana so dukanmu har da yaranmu mu bauta masa da son ranmu. (M. Sha. 10:​12, 13; 30:​19, 20) Don haka, abin da ya kamata iyayen su roƙa shi ne, Jehobah ya taimaka musu su iya ratsa zuciyar yaronsu don ya ƙaunace Shi kuma ya bauta masa.—K. Mag. 22:6; Afis. 6:4. w23.11 21 sakin layi na 5; 23 sakin layi na 12

Litinin, 21 ga Yuli

Ku ƙarfafa juna.—1 Tas. 4:18.

Bari mu bincika ɗaya daga cikin hanyoyin nan da za mu iya nuna wa juna ƙauna. Bulus ya ce: “Ku ƙarfafa juna.” Me ya sa ƙarfafa mutane ko yi musu taꞌaziyya, musamman zai nuna cewa muna ƙaunar su? Wani littafin binciken Littafi Mai Tsarki ya ce kalmar nan “ƙarfafa” da Bulus ya yi amfani da ita a nan, tana nufin “mutum ya tsaya a gefen wanda yake cikin damuwa sosai don ya taimake shi ya samu ƙarfin jimre yanayin.” Idan muka ƙarfafa ꞌyarꞌuwa ko ɗanꞌuwa da yake cikin damuwa, za mu taimaka masa ya ci-gaba da bauta ma Jehobah da aminci. A duk lokacin da muka nuna cewa mun damu da ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa, kuma muka ƙarfafa su, ƙauna ce muke nuna musu. (2 Kor. 7:​6, 7, 13) Tausayi da ƙarfafa ko taꞌaziya, tare suke tafiya. Me ya sa muka ce hakan? Domin idan har ka tausaya wa mutum, za ka so ka ƙarfafa shi kuma ka yi wani abu don ka taimaka masa. Wato jin tausayin mutane yana sa mu ƙarfafa su. Manzo Bulus ya nuna cewa tausayi yana sa Jehobah ya ƙarfafa mutane. Ya ce da Jehobah: “Uba mai yawan tausayi, Allah wanda yake yi mana kowace irin taꞌaziyya.”—2 Kor. 1:3. w23.11 9-10 sakin layi na 8-10

Talata, 22 ga Yuli

Muna farin ciki cikin wahalolinmu.—Rom. 5:3.

Dukan mabiyan Yesu za su sha wahala. Abin da ya faru da manzo Bulus ke nan. Ya gaya wa Kiristocin da ke Tasalonika cewa: “Saꞌad da muke tare da ku, mun gaya muku tun da wuri, cewa za mu sha azaba. Haka kuwa ya kasance.” (1 Tas. 3:4) Ya kuma gaya wa Korintiyawa cewa: “ꞌYanꞌuwa, ba ma so ku kasance da rashin sani game da irin wahalar da muka sha . . . har ba mu san za mu rayu ba.” (2 Kor. 1:8; 11:​23-27) Kiristoci a yau su ma sun san za su iya fuskantar matsaloli iri-iri. (2 Tim. 3:12) Da yake ka ba da gaskiya ga Yesu kuma kana bin sa, abokanka ko danginka za su iya cin zalinka. Ko kuma ƙila shugabanka ko abokan aikinka sun taɓa tsananta maka don kana faɗin gaskiya. (Ibran. 13:18) Hukuma ta taɓa tsananta maka don kana gaya wa mutane game da abubuwan da kake begen su? Ko da wane irin wahala ne za mu sha, Bulus ya ce mu yi farin ciki. w23.12 10-11 sakin layi na 9-10

Laraba, 23 ga Yuli

Kun jawo wahala a kaina.—Far. 34:30.

Yakubu ya fuskanci wasu matsaloli da yawa. Biyu daga cikin yaransa, wato Simeon da Lawi sun yi abin da ya ɓata sunan iyalin da kuma sunan Jehobah. Ƙari ga haka, matar Yakubu da yake ƙauna, wato Rahila ta mutu saꞌad da take haifan ɗansu na biyu. Kuma a lokacin da Yakubu ya tsufa, tsananin yunwa da aka yi ya sa shi da iyalinsa sun ƙaura zuwa ƙasar Masar. (Far. 35:​16-19; 37:28; 45:​9-11, 28) Duk da matsalolin da Yakubu ya fuskanta, ya ci gaba da gaskata da Jehobah da kuma alkawuran da Ya yi masa. Jehobah kuma ya nuna wa Yakubu cewa yana ƙaunar sa. Alal misali, Jehobah ya ba wa Yakubu dukiya mai yawa. Kuma ka yi tunanin irin farin cikin da Yakubu ya yi saꞌad da ya sake haɗuwa da ɗansa wanda ya ɗauka cewa ya mutu da daɗewa. Dangantaka mai kyau da Yakubu yake da ita da Jehobah, ita ce ta taimaka masa ya jimre matsalolin nan. (Far. 30:43; 32:​9, 10; 46:​28-30) Mu ma idan muna da dangantaka mai kyau da Jehobah, za mu iya jimre matsaloli da za su iya abko mana ba zato. w23.04 15 sakin layi na 6-7

Alhamis, 24 ga Yuli

Yahweh shi ne makiyayina, ba zan rasa kome ba.—Zab. 23:1.

Zabura sura 23, waƙa ce da ta nuna tabbacin da Dauda yake da shi cewa Jehobah yana ƙaunar sa kuma zai kula da shi. A wannan Zaburar, Dauda ya bayyana irin ƙaunar da ke tsakaninsa da Makiyayinsa, wato Jehobah. Dauda ya bar Jehobah ya yi masa ja-goranci, kuma ya dogara gare Shi da dukan zuciyarsa. Dauda ya san cewa ƙaunar Jehobah marar canjawa za ta yi ta bin shi dukan kwanakin rayuwarsa. Me ya ba shi wannan tabbacin? Dauda ya ce bai rasa kome ba domin a ko da yaushe Jehobah yana ba shi abin da yake bukata. Dauda ya kuma san cewa Jehobah abokinsa ne kuma ya yarda da shi. Shi ya sa ya kasance da tabbaci cewa ko da me zai faru, Jehobah zai biya masa dukan bukatunsa. Maimakon Dauda ya riƙa damuwa, ya riƙa farin ciki kuma ya gamsu, domin ya san cewa Jehobah yana ƙaunarsa kuma zai kula da shi.—Zab. 16:11. w24.01 29 sakin layi na 12-13

Jumma’a, 25 ga Yuli

Ina tare da ku kullum har ƙarshen zamani.—Mat. 28:20.

Tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu, Shaidun Jehobah sun yi waꞌazi a ƙasashe da yawa ba tare da taƙura ba. Mutane da yawa a faɗin duniya sun ji game da Jehobah kuma sun soma bauta masa. A yau, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta ci-gaba da neman ja-gorancin Yesu Kristi. Tana son umurnin da take ba wa ꞌyanꞌuwa ya yi daidai da raꞌayin Jehobah da na Kristi. Tana kuma ba da umurni ta wurin masu kula da daꞌira da kuma dattawa. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa dattawa suna ‘hannun daman’ Kristi. (R. Yar. 2:1) Hakika, dattawa ajizai ne, haka ma yake da Kiristoci shafaffu, kuma sukan yi kuskure. Musa da Joshua sun yi kurakurai, haka ma yake da manzanni a ƙarni na farko. (L. Ƙid. 20:12; Yosh. 9:​14, 15; Rom. 3:23) Har yanzu, Kristi yana yi wa bawan nan mai aminci mai hikima da dattawa ja-goranci, kuma zai ci-gaba da yin hakan. Don haka, muna da dalilai da yawa da ya kamata su sa mu gaskata umurnan da ꞌyanꞌuwan nan suke ba mu. w24.02 23-24 sakin layi na 13-14

Asabar, 26 ga Yuli

Tun da yake kun zama ꞌyaꞌya waɗanda Allah yake ƙauna, sai ku ɗauki misali daga wurin Allah a cikin zamanku.—Afis. 5:1.

A yau, za mu iya yabon Jehobah ta wajen gaya wa mutane abubuwa game da shi, wato abubuwan da za su nuna cewa muna ƙaunar sa kuma muna gode masa. Yayin da muke yin waꞌazi, zai dace mu tuna cewa burinmu shi ne mu taimaka wa mutane su yi kusa da Jehobah kuma su ɗauki Ubanmu mai ƙauna yadda muke ɗaukan sa. (Yak. 4:8) Muna farin cikin gaya wa mutane bayanin da Littafi Mai Tsarki ya yi game da Jehobah, wato cewa yana da ƙauna, da adalci, da hikima, da iko, da kuma wasu halaye masu kyau. Ban da haka, za mu yabi Jehobah kuma mu faranta masa rai idan muka yi koyi da shi. Idan mun yi hakan, mutane za su lura cewa mun yi dabam da mutanen muguwar duniyar nan, kuma za su so su san dalilin da ya sa. (Mat. 5:​14-16) Saꞌad da muke ayyukanmu na yau da kullum, za mu iya bayyana musu dalilin da ya sa muka yi dabam. Hakan zai sa mutane masu zuciyar kirki su yi kusa da Allah. Idan muka yabi Ubanmu na sama a wannan hanyar, za mu sa shi farin ciki.—1 Tim. 2:​3, 4. w24.02 10 sakin layi na 7

Lahadi, 27 ga Yuli

Ya ƙarfafa waɗansu . . . ya kuma iya ƙaryata kuskuren waɗanda suke gāba da koyarwar.—Tit. 1:9.

Kafin ka zama Kiristan da ya manyanta, kana bukatar ka koyi yin wasu abubuwa. Hakan zai taimaka maka ka iya yin ayyukan da aka ba ka a ikilisiya, ka sami aikin da zai taimaka maka ka kula da iyalinka, kuma ka kasance da dangantaka mai kyau da mutane. Alal misali, ka koyi yin karatu da rubutu da kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce mutumin da yake ɗaukan lokaci ya karanta Kalmar Allah zai yi farin ciki kuma ya yi nasara a rayuwa. (Zab. 1:​1-3) Idan kana karanta Littafi Mai Tsarki koyaushe, za ka san yadda Jehobah yake tunani, kuma hakan zai taimaka maka ka san yadda za ka bi ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarka. (K. Mag. 1:​3, 4) ꞌYanꞌuwanmu maza da mata sukan je wurin ꞌyanꞌuwa maza da suka manyanta don su nemi shawara daga Littafi Mai Tsarki. Idan ka iya karatu da rubutu da kyau, za ka iya yin jawabai da kalamai masu kayatarwa da kuma ban ƙarfafa. Ƙari ga haka, za ka iya rubuta darussan da za su ƙarfafa bangaskiyarka da na wasu. w23.12 26-27 sakin layi na 9-11

Litinin, 28 ga Yuli

Ruhun Allah da yake cikinku ya fi ruhun da yake cikin mutanen da suke na duniya.—1 Yoh. 4:4.

Idan kana jin tsoro, ka yi tunani a kan abin da Jehobah zai yi a nan gaba bayan an hallaka Shaiɗan. A wani gwaji da aka yi a taron yanki na 2014, wani mahaifi ya bayyana wa iyalinsa yadda kalaman da ke 2 Timoti 3:​1-5 za su kasance idan ana annabci ne game da Aljanna. Ya ce: ‘A sabuwar duniya, za a yi farin ciki sosai. Gama mutane za su zama masu son juna, masu son ibada, masu sanin kasawarsu, masu tawaliꞌu, masu yabon Allah, masu biyayya ga iyayensu, masu godiya, masu tsarki, masu ƙaunar iyalinsu sosai, masu gafartawa, masu yin maganganu masu kyau game da waɗansu. Masu kame kansu, masu tausayi, masu son nagarta, masu riƙon amana, masu hankali, masu sauƙin kai, masu son Allah fiye da jin daɗi, kuma suna da dangantaka mai kyau da Allah. Masu bauta wa Allah da gaske. Ka manne wa irin mutanen nan.’ Kana tattaunawa da iyalinka ko ꞌyanꞌuwa game da yadda rayuwa za ta kasance a sabuwar duniya? w24.01 6 sakin layi na 13-14

Talata, 29 ga Yuli

Ina jin daɗinka ƙwarai.—Luk. 3:22.

Sanin cewa Jehobah ya amince da bayinsa yana da ban ƙarfafa! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yahweh yakan ji daɗin mutanensa.” (Zab. 149:4) Amma a wasu lokuta, Kirista zai iya yin sanyin gwiwa kuma ya soma shakkar ko Jehobah ya amince da shi. Akwai bayin Allah masu aminci da yawa a Littafi Mai Tsarki da su ma sun yi fama da irin wannan tunani. (1 Sam. 1:​6-10; Ayu. 29:​2, 4; Zab. 51:11) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ꞌyan Adam ajizai za su iya samun amincewar Allah. Ta yaya? Ta wurin ba da gaskiya ga Yesu Kristi da kuma yin baftisma. (Yoh. 3:16) Ta yin hakan, za mu nuna wa mutane cewa mun tuba daga zunubanmu kuma mun yi alkawarin yin nufin Jehobah. (A. M. 2:38; 3:19) Jehobah zai yi farin ciki sosai idan muka ɗau matakan nan don mu zama abokansa. Idan muka ci-gaba da cika alkawarin da muka yi cewa za mu yi nufin Jehobah, Jehobah zai amince da mu kuma zai ɗauke mu a matsayin abokansa.—Zab. 25:14. w24.03 26 sakin layi na 1-2

Laraba, 30 ga Yuli

Ba za mu iya yin shiru a kan abin da muka ji, muka kuma gani ba.—A. M. 4:20.

Za mu iya yin koyi da almajiran Yesu ta wajen ci-gaba da yin waꞌazi ko da hukuma ta ce mu daina yin hakan. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana mu iya yin aikin da ya ba mu. Don haka mu roƙi Jehobah ya ba mu ƙarfin zuciya da hikima, kuma ya taimake mu mu iya jimre matsalolinmu. Yawancinmu muna fama da matsaloli dabam-dabam. Ko rashin lafiya, ko rasuwar wani da muke ƙauna, ko wata matsala a iyalinmu, ko tsanantawa da dai sauran su. Annoba da tashe-tashen hankula sun sa jimre wa matsalolin nan ya ƙara yin wuya. Idan kana cikin matsala, ka faɗa wa Jehobah duk abin da ke zuciyarka. Ka bayyana masa abin da ke faruwa da kai kamar yadda za ka gaya wa amininka. Tabbas, Jehobah zai taimake ka, “zai lura da kai.” (Zab. 37:​3, 5) Idan muka nace da yin adduꞌa, zai taimaka mana mu “yi haƙuri a cikin azaba.” (Rom. 12:12) Jehobah ya san matsalolin da bayinsa suke fuskanta. “Yakan kuma ji kukansu ya cece su.”—Zab. 145:​18, 19. w23.05 5-6 sakin layi na 12-15

Alhamis, 31 ga Yuli

Ku tabbata cewa kun koyi abin da zai gamshi Ubangiji.—Afis. 5:10.

Idan muna so mu tsai da shawara mai muhimmanci, muna bukatar mu fahimci mene ne “nufin Ubangiji,” kuma mu bi shi. (Afis. 5:17) Idan muna neman ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da suka dace da yanayin da muke ciki, muna neman sanin raꞌayin Jehobah game da batun ke nan. Kuma idan muka gano ƙaꞌidodin Jehobah kuma muka bi su, za mu iya yin zaɓi mai kyau. “Mugun nan,” wato maƙiyinmu Shaiɗan, zai so ya cika mu da ayyuka da yawa har ma mu rasa lokacin bauta ma Jehobah. (1 Yoh. 5:19) Kirista zai iya sa neman abin duniya, ko makaranta, ko kuma aikin da yake yi, ya zama farko a rayuwarsa, maimakon ya nemi hanyoyin da zai bauta ma Jehobah. Idan ya yi hakan, ya nuna cewa ya soma bin tunanin mutanen duniyar nan ke nan. Hakika, biɗan abubuwan nan ba laifi ba ne. Amma bai kamata a ce su ne muka sa a kan-gaba ba. w24.03 24 sakin layi na 16-17

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba