Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 12/1 pp. 20-24
  • Abin Da Ake Nufi Da Mu Ƙaunaci Makwabcinmu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Abin Da Ake Nufi Da Mu Ƙaunaci Makwabcinmu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Wanene Maƙwabcinmu?
  • Abin da Ƙaunarmu ga Maƙwabci Take Nufi
  • Nuna Ƙauna ga ’Yan’uwanmu Kiristoci
  • Nuna Ƙauna ga Mutane
  • Ta Yaya Za Mu Ƙaunaci Maƙwabtanmu Kamar Kanmu?
  • Ka ‘Ƙaunaci Maƙwabcinka Kamar Ranka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • A Ina Ƙaunarka Ta Tsaya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Kana “Kaunar Makwabcinka Kamar Ranka” Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 12/1 pp. 20-24

Abin Da Ake Nufi Da Mu Ƙaunaci Makwabcinmu

“Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.”—MATTA 22:39.

1. Ta yaya muke nuna cewa muna ƙaunar Allah?

MENENE Jehobah yake bukata daga waɗanda suke bauta masa? Yesu ya ba da amsar a cikin ’yan kalmomi masu sauƙi kuma masu muhimmanci. Ya ce, doka da ta fi girma, ita ce mu ƙaunaci Jehobah da dukan zuciyarmu, ranmu da kuma ƙarfinmu. (Matta 22:37; Markus 12:30) Kamar yadda muka gani a talifin da ya gabata, ƙaunar Allah ta ƙunshi yi masa biyayya da kuma bin dokokinsa domin ƙaunar da ya nuna mana. Ga waɗanda suke ƙaunar Allah, yin nufinsa ba abu ba ne mai wuya domin yana kawo farin ciki.—Zabura 40:8; 1 Yohanna 5:2, 3.

2, 3. Me ya sa za mu mai da hankali ga doka da ta ce mu ƙaunaci maƙwabcinmu, waɗanne tambayoyi ne wannan ya ta da?

2 Yesu ya ce, doka ta biyu da ta fi girma tana da nasaba da ta farko: “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Matta 22:39) Wannan dokar ce yanzu za mu mai da wa hankali don dalili mai kyau. Lokacin da muke ciki na cike da ƙauna ta son kai. A kwatancinsa na “kwanaki na ƙarshe,” manzo Bulus ya rubuta cewa mutane ba za su ƙaunaci juna ba, amma za su ƙaunaci kansu, za su ƙaunaci kuɗi da kuma nishaɗi. Mutane da yawa za su zama “marasa-ƙauna irin na tabi’a,” ko kuma yadda wani juyin Littafi Mai Tsarki ya fassara, za su zama “marasa ƙaunar iyalansu.” (2 Timothawus 3:1-4) Yesu Kristi ya annabta: “Mutane dayawa . . . za su bada juna, za su ƙi juna kuma . . . ƙaunar yawancin mutane za ta yi sanyi.”—Matta 24:10, 12.

3 Amma, ka lura cewa Yesu bai ce ƙaunar kowa za ta yi sanyi ba. Da akwai waɗanda suke nuna irin ƙaunar da Jehobah yake bukata kuma ya cancanta. Waɗanda suke ƙaunar Jehobah da gaske za su yi ƙoƙari su ɗauki mutane yadda yake ɗaukansu. To, wanene maƙwabcinmu da dole ne mu ƙaunace shi? Ta yaya ya kamata mu ƙaunaci maƙwabcinmu? Nassosi zai taimake mu mu amsa waɗannan tambayoyi masu muhimmanci.

Wanene Maƙwabcinmu?

4. Bisa ga Leviticus sura ta 19 su wanene Yahudawa za su ƙaunaci?

4 Sa’ad da yake gaya wa Bafarisin cewa doka ta biyu da ta fi girma ita ce mutum ya ƙaunaci maƙwabcinsa kamar kansa, Yesu yana maganar wata doka ta musamman da aka ba Isra’ilawa. Tana rubuce a Leviticus 19:18. A wannan surar, an gaya wa Yahudawa su ɗauki wasu mutane a matsayin maƙwabtansu ba Isra’ilawa ’yan’uwansu ba kawai. Aya ta 34 ta ce: “Baƙon da ke sauke a wurinku za ya zama maku kamar ɗan da aka haifa a wurinku, za ka ƙaunace shi kamar kanka: gama ku dā baƙi ne cikin ƙasar Masar.” Da haka, za su ƙaunaci waɗanda ma ba Yahudawa ba ne, musamman shigaggu.

5. Ta yaya Yahudawa suka fahimci dokar da ta ce a ƙaunaci maƙwabci?

5 Amma, shugabannin Yahudawa na zamanin Yesu suna da wani ra’ayi dabam. Wasu sun ce kalmar nan “aboki” da “maƙwabci” na nuni ga Yahudawa ne kawai. Za a tsane waɗanda ba Yahudawa ba. Irin waɗannan malaman sun ce masu ibada dole su rena marasa ibada. Wata majiya ta ce: “Irin wannan yanayi na ƙarfafa ƙiyayya.”

6. Waɗanne darussa biyu ne Yesu ya furta sa’ad da yake magana game da ƙaunar maƙwabci?

6 A Hudubarsa bisa Dutse, Yesu ya tattauna wannan batun, kuma ya ƙara ba da haske a kan wanda ya kamata mu nuna wa ƙauna. Ya ce: “Kun ji aka faɗi, Ka yi ƙaunar maƙwabcinka, ka ƙi magabcinka: amma ni ina ce muku, Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a; Domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin sama: gama ya kan sa ranatasa ta fito ma miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu-adalci da marasa-adalci.” (Matta 5:43-45) A nan Yesu ya faɗi darussa biyu. Na farko, Jehobah yana wa nagarin mutane da miyagu alheri. Na biyu, ya kamata mu bi misalinsa.

7. Wane darassi ne muka koya daga almarar maƙwabci Basamariye?

7 A wani lokaci, wani Bayahude masanin Doka ya tambayi Yesu: “Wanene maƙwabcina?” Yesu ya amsa ta wajen ba da misalin da ta kwatanta wani Basamariye da ya ga wani mutum Bayahude da ’yan fashi suka yi masa mugun dūka suka ƙwace masa dukiyarsa. Ko da yake Yahudawa sun ƙi jinin Samariyawa, Basamariyen ya ɗaɗɗaure wa mutumin raunukansa kuma ya kai shi inda za a yi jinyarsa har ya samu sauƙi. Menene darassin? Ya kamata mu ƙaunaci waɗanda ba ƙabilunmu ba ne, waɗanda ba ƙasarmu ɗaya ba, kuma ba addininmu ɗaya ba.—Luka 10:25, 29, 30, 33-37.

Abin da Ƙaunarmu ga Maƙwabci Take Nufi

8. Menene Leviticus sura 19 ta ce game da yadda za a nuna ƙauna?

8 Ƙaunar maƙwabci, kamar ƙaunarmu ga Allah, ba kawai yadda muke ji ba ne, amma za mu yi ayyuka da suka nuna muna ƙaunar maƙwabcinmu. Zai yi kyau mu ƙara bincika umurnin da ke rubuce a Leviticus sura 19 da ya gargaɗi mutanen Allah su ƙaunaci maƙwabcinsu kamar kansu. Wajen ya ce an umurci Isra’ilawa su ƙyale matalauta da baƙi su yi girbi. Ba za a yi sata ba, cuci, ko kuma ƙarya. Isra’ilawa ba za su yi son kai ba a batun shari’a. Ko da za su ba da horo idan bukata ta kama, an gaya musu: “Ba za ka ƙi ɗan’uwanka cikin zuciyarka ba.” Waɗannan da dokoki da yawa ne aka taƙaita cewa: “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.”—Leviticus 19:9-11, 15, 17, 18.

9. Me ya sa Jehobah ya umurci Isra’ilawa su ware kansu daga sauran al’ummai?

9 Ko da Isra’ilawa za su yi ƙaunar wasu, za su ware kansu daga waɗanda suke bauta wa allolin ƙarya. Jehobah ya yi kashedi game da haɗari da sakamakon cuɗanya da miyagu. Alal misali, game da al’ummai da aka gaya wa Isra’ilawa kada su yi sha’ani da su, Jehobah ya ba da umurni: “Ba za ka yi surukuta da su ba; ɗiyarka ba za ka ba ɗansa ba, ba kuwa za ka ɗauka ma ɗanka ɗiyatasa ba. Gama za shi juyadda ɗanka ga barin bina, domin su bauta ma waɗansu alloli: hakanan fushin Ubangiji za ya yi ƙuna a kanku.”—Kubawar Shari’a 7:3, 4.

10. A kan menene muke bukatar mu mai da hankali?

10 Hakanan ma, Kiristoci za su kauce wa yin dangantaka da waɗanda za su raunanar da bangaskiyarsu. (1 Korinthiyawa 15:33) An yi mana gargaɗi: “Kada ku yi karkiya marar-dacewa tare da marasa-bangaskiya,” waɗanda ba sa cikin ikilisiyar Kirista. (2 Korinthiyawa 6:14) Ƙari ga haka, an gargaɗi Kiristoci su yi aure “sai dai cikin Ubangiji.” (1 Korinthiyawa 7:39) Duk da haka, ba za mu rena waɗanda ba sa imani da Jehobah kamar yadda muke yi ba. Kristi ya mutu don masu zunubi, da waɗanda dā sun yi mugun abubuwa amma sun canja hanyoyinsu kuma suka sulhunta da Allah.—Romawa 5:8; 1 Korinthiyawa 6:9-11.

11. Wace hanya ce ta fi kyau da za a ƙaunaci waɗanda ba sa bauta wa Jehobah, kuma me ya sa?

11 Idan muna son mu yi ƙaunar waɗanda ba sa bauta wa Allah, hanya da ta fi kyau da za mu yi haka ita ce ta yin koyi da Jehobah kansa. Ko da Allah ya tsane mugunta, yana nuna alheri ga duka mutane ta wajen ba su zarafi su bar hanyoyinsu na mugunta kuma su sami rai madawwami. (Ezekiel 18:23) Jehobah yana son “duka su kai ga tuba.” (2 Bitrus 3:9) Nufinsa ne “dukan [ire-iren] mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Timothawus 2:4) Shi ya sa Yesu ya ba mabiyansa aiki su yi wa’azi kuma su koyar da mutane su “almajirtadda dukan al’ummai.” (Matta 28:19, 20) Ta wajen sa hannu a wannan aikin, muna ƙaunar Allah da kuma maƙwabcinmu, hakika, har da magabtanmu!

Nuna Ƙauna ga ’Yan’uwanmu Kiristoci

12. Menene manzo Yohanna ya rubuta game da ƙaunar ɗan’uwanmu?

12 Manzo Bulus ya rubuta: “Bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda su ke cikin iyalin imani.” (Galatiyawa 6:10) Da yake mu Kiristoci ne, wajibi ne mu ƙaunaci waɗanda suke cikin iyalinmu na imani, wato, ’yan’uwanmu na ruhaniya. Menene muhimmancin wannan ƙauna? Da yake magana a kan wannan, manzo Yohanna ya rubuta: “Dukan wanda ya ƙi ɗan’uwansa mai-kisankai ne . . . Idan wani ya ce, Ina ƙaunar Allah, shi kuwa yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne shi: domin wanda ba ya yi ƙaunar ɗan’uwansa ba wanda ya gani, ba shi iya ƙaunar Allah wanda ba ya gani ba.” (1 Yohanna 3:15; 4:20) Waɗannan kalmomi suna da iko. Yesu Kristi ya yi amfani da kalmomi “mai-kisan kai” da “maƙaryaci” da yake maganar Shaiɗan Iblis. (Yohanna 8:44) Ba za mu so a kira mu da waɗannan kalmomi ba!

13. A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna wa ’yan’uwa ƙauna?

13 Kiristoci na gaskiya ‘koyayyu ne na Allah su ƙaunaci junansu.’ (1 Tassalunikawa 4:9) Ba za mu yi ƙauna “da baki ko kuwa da harshe; amma da aiki da gaskiya kuma.” (1 Yohanna 3:18) Ba za mu yi ƙauna “tare da riya ba.” (Romawa 12:9) Ƙauna na motsa mu mu zama masu kirki, mu yi juyayi, mu riƙa gafartawa, mu yi tsawon jimrewa, ba za mu yi kishi ba, fahariya, taurin kai, ko kuma son kai. (1 Korinthiyawa 13:4, 5; Afisawa 4:32) Ƙauna na motsa mu mu “zama masu-bauta ma juna.” (Galatiyawa 5:13) Yesu ya gaya wa almajiransa su yi ƙaunar juna kamar yadda ya ƙaunace su. (Yohanna 13:34) Saboda haka ya kamata Kirista ya kasance a shirye ya ba da ransa domin ’yan’uwa masu bi idan bukata ta kama.

14. Ta yaya za mu nuna ƙauna cikin iyali?

14 Ya kamata a nuna ƙauna cikin iyalin Kirista musamman tsakanin mata da miji. Gami na aure dangantaka ne na kud da kud da ya sa Bulus ya ce: “Ya kamata mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu.” Ya daɗa: “Wanda ya ke ƙaunar matatasa kansa ya ke ƙauna.” (Afisawa 5:28) Bulus ya maimaita wannan gargaɗin bayan ayoyi biyar. Mijin da ke ƙaunar matarsa ba zai yi koyi da Isra’ilawa na zamanin Malakai da suka ci amanar matansu ba. (Malachi 2:14) Zai daraja ta. Zai ƙaunace ta yadda Kristi ya ƙaunaci ikilisiya. Hakanan ma ƙauna za ta motsa mata ta yi wa mijinta ladabi.—Afisawa 5:25, 29-33.

15. Menene ganin yadda aka nuna ƙauna ga ’yan’uwa ya motsa wasu su faɗa kuma su yi?

15 Hakika, ta irin wannan ƙaunar ce ake sanin Kiristoci na gaskiya. Yesu ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:35) Ƙaunar juna na jawo mutane kusa da Allahn da muke ƙauna kuma muke wakilta. Alal misali, ga wannan labari daga ƙasar Mazambik game da wata iyalin Kirista. “Ba mu taɓa ganin irin wannan abin ba. Da rana aka soma mugun iska da ruwan sama da ƙanƙara. Iskar ta halaka gidanmu, kuma ta ɗauki rufin kwanon. Sa’ad da ’yan’uwanmu daga ikilisiyoyi na kusa suka zo, suka taimake mu sake gina gidanmu, maƙwabtanmu suka yi mamaki suka ce: ‘Addininku yana da kyau. Ba mu taɓa samun irin wannan taimako daga cocinmu ba.’ Mun buɗe Littafi Mai Tsarki muka nuna musu Yohanna 13:34, 35. Maƙwabtanmu da yawa yanzu suna nazarin Littafi Mai Tsarki.”

Nuna Ƙauna ga Mutane

16. Menene bambancin ƙaunar mutane a rukuni da ƙaunar mutane ɗaɗɗaya?

16 Ba shi da wuya mu ƙaunaci maƙwabtanmu gabaki ɗaya. Amma, ƙaunar mutane ɗaɗɗaya zai iya kasance da wuya. Alal misali, wasu mutane suna nuna ƙauna ga maƙwabtansu kawai ta wurin ba da kuɗi ga ƙungiyar ba da sadaka. Hakika, ya fi sauƙi mu ce muna ƙaunar maƙwabtanmu fiye da ƙaunar abokin aikinmu da kamar ba ya ƙaunarmu, ko kuma wanda ke zama kusa da mu da ba ma ƙaunarsa, ko kuwa abokin da ya ci amanarmu.

17, 18. Ta yaya Yesu yake nuna ƙauna ga mutane, da wane nufi ya yi hakan?

17 Muna iya koya daga wurin Yesu, wanda ya nuna halayen Allah sosai, a wannan batun ƙaunar mutane ɗaɗɗaya. Ko da ya zo duniya don ya ɗauke zunubin duniya, ya nuna ƙauna ga mutane ɗaɗɗaya kamar mata mai ciwo, kuturu, da kuma wani yaro. (Matta 9:20-22; Markus 1:40-42; 7:26, 29, 30; Yohanna 1:29) Hakanan ma, muna ƙaunar maƙwabcinmu ta yadda muke bi da mutane da muke saduwa da su kowace rana.

18 Amma, kada mu manta cewa ƙaunar maƙwabci yana nuna muna ƙaunar Allah. Ko da Yesu ya taimaki matalauta, ya warkar da masu ciwo, ya ciyar da mayunwata, nufinsa wajen yin dukan waɗannan abubuwa da kuma koya wa jama’a shi ne domin ya taimaki mutane su sulhunta da Jehobah. (2 Korinthiyawa 5:19) Yesu ya yi dukan abubuwa saboda ɗaukakar Allah, ba ya manta cewa yana wakiltar da kuma nuna halayen Allahn da yake ƙauna. (1 Korinthiyawa 10:31) Ta wajen yin koyi da misalin Yesu, mu ma za mu nuna tabbataciyar ƙauna ga maƙwabci kuma mu kasance mu ba na muguwar duniya na ’yan adam ba ne.

Ta Yaya Za Mu Ƙaunaci Maƙwabtanmu Kamar Kanmu?

19, 20. Menene ake nufi da mu ƙaunaci maƙwabtanmu kamar kanmu?

19 Yesu ya ce: “Ka ƙaunaci maƙwabtanka kamar kanka.” Ya dace mu kula da kanmu kuma mu kasance da darajar kanmu. Idan ba haka ba, dokar ba za ta kasance da wani amfani ba. Ba za a rikita wannan ƙaunar kanmu da ƙauna ta son kai da manzo Bulus ya ambata a 2 Timothawus 3:2 ba. Maimakon haka, darajar kai ne da ya dace. Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya kwatanta cewa “ƙauna ce inda mutum ba ya nuna ya fi wasu ko kuwa mutumin ya nuna ya yi ƙasa ainun.”

20 Mu ƙaunaci wasu kamar kanmu yana nufin mu ɗauki wasu yadda muke son wasu su ɗauke mu kuma mu bi da su yadda za mu so su bi da mu. Yesu ya ce: “Dukan abu fa iyakar abin da ku ke so mutane su yi maku, ku yi musu hakanan kuma.” (Matta 7:12) Yesu bai ce mu riƙa tunanin abin da wasu suka yi mana a dā kuma mu saka musu hakanan ba. Maimakon haka, za mu yi tunanin yadda za mu so mutane su bi da mu kuma mu aikata hakanan. Ka lura kuma cewa Yesu bai ce mu riƙa yin haka ga abokanmu da ’yan’uwanmu kawai ba. Ya yi amfani da kalmar “mutane” wataƙila don ya nuna ya kamata mu aikata hakanan ga duka mutanen da muka sadu da su.

21. Ta wajen ƙaunar mutane, menene muke nunawa?

21 Ƙaunar maƙwabtanmu za ta kāre mu daga yin mugunta. Manzo Bulus ya rubuta: “Ba za ka yi zina ba, Ba za ka yi kisankai ba, Ba za ka yi sata ba, Ba za ka yi ƙyashi ba, kuma idan da wata doka, an tarke ta cikin wannan magana, cewa, Sai ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka. Ƙauna ba ta aika mugunta ga maƙwabcinta ba.” (Romawa 13:9, 10) Ƙauna za ta motsa mu mu nemi hanyoyin da za mu yi wa mutane alheri. Ta wajen ƙaunar ’yan’uwanmu ’yan adam, muna nuna cewa muna ƙaunar Jehobah Allah wanda ya halicci mutum cikin surarsa.—Farawa 1:26.

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Wanene ya kamata mu nuna wa ƙauna, kuma me ya sa?

• Ta yaya za mu ƙaunaci waɗanda ba sa bauta wa Jehobah?

• Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta ƙauna da za mu nuna wa ’yan’uwanmu?

• Menene yake nufi mu ƙaunaci maƙwabtanmu kamar kanmu?

[Hoto a shafi na 21]

“Wanene maƙwabcina da gaske?”

[Hoto a shafi na 24]

Yesu ya nuna wa mutane ƙauna

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba