DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ku Ci-gaba da Nuna Yadda Kuke Ƙaunar Jehobah
[Ku kalli bidiyon Gabatarwar Littafin Ayuba.]
Shaiɗan ya yi daꞌawa cewa Ayuba yana ƙauna da kuma bauta wa Jehobah don abin da yake samu ne (Ayu 1:8-11; w18.02 6 sakin layi na 16-17)
Shaiɗan yana daꞌawa cewa ba ma ƙaunar Allah da gaske (Ayu 2:4, 5; w19.02 5 sakin layi na 10)
Jehobah ya ba mu dama mu nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. (K. Ma 27:11) Za mu iya nuna yadda muke ƙaunar Jehobah ta wajen sa yin nufinsa farko a rayuwarmu ko a lokacin da muke jin daɗi ko aꞌa.