Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb23 Satumba p. 16
  • Ku Yi Amfani da Shafin Farko na JW.ORG Yayin da Kuke Waꞌazi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Yi Amfani da Shafin Farko na JW.ORG Yayin da Kuke Waꞌazi
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Makamantan Littattafai
  • Shawara A Kan Dandalinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Shawara A Kan Yin Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Kana Yin Amfani da Katin JW.ORG Yadda Ya Dace Kuwa?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Yadda Za Mu Yi Amfani da JW.ORG
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
mwb23 Satumba p. 16
Hoton shafin farko na jw.org da ke nuna talifofi a harsuna dabam-dabam.

RAYUWAR KIRISTA

Ku Yi Amfani da Shafin Farko na JW.ORG Yayin da Kuke Waꞌazi

A shafin farko na dandalinmu, akwai talifofi da bidiyoyi da aka tsara su da niyyar jan hankalin mutanen da suke son gaskiya. (A. M 13:48) Ana yawan saka batutuwan da aka samo daga labaran duniya ko abin da mutane suke tunani ko magana a kai.

Ta yaya za ku iya amfani da shafin farko na jw.org/ha yayin da kuke waꞌazi?

  • Ku riƙa duba dandalin a kai a kai. Ku riƙa laꞌakari da batun da ake magana a kai a shafin kuma ku yi tunanin yadda za ku yi amfani da batun yayin da kuke tattaunawa da wanda yake son saƙon Littafi Mai Tsarki. (Don samun wasu talifofin da ake sakawa a shafin farkon, ku danna “Ƙarin Abubuwa.”) Idan kuna duba dandalin a kai a kai, za ku sami batutuwa dabam-dabam da za ka iya amfani da su ku yi wa mutane waꞌazi.

  • Ku yi amfani da talifofi da bidiyoyi da ke shafin farko wajen tattaunawa da mutane. Talifofi da bidiyoyin za su taimaka mana mu san abubuwan da ke zuciyar mutanen yankinmu.

  • Ku nuna wa mutane shafin farko. Ku nuna musu wasu batutuwa a dandanlin saꞌan nan ku koya musu yadda za su dinga samun bayanai a dandalin da kansu.

  • Ku tura musu mahaɗi. Wasu ba sa so mu yi musu waꞌazi ido da ido, amma za su so su shiga dandalinmu. Don haka, kada ku bata lokaci wajen tura musu mahaɗi zuwa shafin farko ko kuma zuwa wani talifi ko bidiyo a shafin.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba