15-21 GA SATUMBA
KARIN MAGANA 31
Waƙa ta 135 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Darussa da Muka Koya Daga Shawara da Wata Mahaifiya Ta Ba Ɗanta
(minti 10)
Ku koya wa yaranku raꞌayin Jehobah game da jimaꞌi da aure (K. Ma 31:3, 10; w11 4/1 19 sakin layi na 7-8)
Ku koya wa yaranku raꞌayin da ya dace game da giya (K. Ma 31:4-6; ijwhf talifi na 4 sakin layi na 11-13)
Ku koya wa yaranku yadda za su taimaka wa mutane kamar yadda Jehobah yake yi (K. Ma 31:8, 9; g17.6-E 9 sakin layi na 5)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
- K. Ma 31:26—Mene ne muka koya daga ayar nan? (w23.12 21 sakin layi na 12) 
- A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu? 
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) K. Ma 31:10-31 (th darasi na 10)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka soma tattaunawa da wani bayan ya yi maka wani abin alheri, ko ya gaya maka wani abu mai kyau. (lmd darasi na 5 batu na 3)
5. Fara Magana da Mutane
(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka tattauna da mutumin batu ɗaya da ke cikin “Gaskiyar da Muke Jin Daɗin Koya wa Mutane” ƙarin bayani na 1 na ƙasidar Ƙaunar Mutane Za Ta Sa Ka Almajirtar da Su. (lmd darasi na 1 batu na 4)
6. Komawa Ziyara
(minti 5) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka gayyaci wani da ka ba shi Hasumiyar Tsaro Na 1, 2025 zuwa jawabi na musamman da za a yi. (lmd darasi na 7 batu na 4)
Waƙa ta 121
7. Ku Taimaki Yaranku Su Dinga Yin Amfani da Naꞌura a Hanyar da Ta Dace
(minti 8) Tattaunawa.
Shin, ka taɓa ganin yadda ƙananan yara suke shiga wurare dabam-dabam a cikin waya? Yana musu sauƙi sosai! A yawancin lokuta ba sa bukata a koya musu, amma tabbas, suna bukata a koya musu yadda za su dinga amfani da waya a hanyar da ta dace. Idan kana da yara, ta yaya za koya musu yadda za su dinga amfani da waya a hanyar da ta dace?
Ku kalli BIDIYON Ka Yi Amfani da Lokaci Yadda Ya Dace. Sai ka tambayi masu sauraro:
- Me ya sa zai dace mu rage yadda muke amfani da naꞌurori? 
- Waɗanne abubuwa ne kuma muke bukata mu tsara lokacin yi? 
Idan za ku ba da doka a iyalinku, ku yi amfani da ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki maimakon ku yi abin da kun ga wasu iyaye suke yi kawai. (Ga 6:5) Alal misali, ka tambayi kanka:
- Shin, yarona ya nuna cewa zai iya amfani da wayata a hanyar da ta dace? Yana da kamun kai da zan iya saya masa nasa wayar?—1Ko 9:25 
- Zai dace in bar yarona ya yi amfani da waya idan yana nan shi kaɗai?—K. Ma 18:1 
- A ina da ina ne zan iya barin shi ya shiga a waya, waɗanne wurare ne kuma zan hana shi shiga?—Afi 5:3-5; Fib 4:8, 9 
- Awa nawa ne zan bar su su yi amfani da waya kowace rana don su sami lokacin yin wasu ayyuka masu muhimmanci?—M. Wa 3:1 
8. Bukatun Ikilisiya
(minti 7)
9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) lfb darasi na 18-19