Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w22 Yuli pp. 26-30
  • Na Bar Jehobah Ya Yi Mini Ja-goranci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Na Bar Jehobah Ya Yi Mini Ja-goranci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • DAGA INGILA ZUWA AFIRKA
  • YIN HIDIMA A MUWAYACIN LOKACI A MALAWI
  • MUN SOMA HIDIMA A MALAWI DAGA ZIMBABUWE
  • MUN KOMA ƘASAR MALAWI
  • JEHOBAH YA BA DA CI GABA
  • NA GAMSU DA ZAƁIN DA NA YI
  • Albarka a Lokacin Zaman Lafiya da Lokacin Wahala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
w22 Yuli pp. 26-30

TARIHI

Na Bar Jehobah Ya Yi Mini Ja-goranci

KEITH EATON NE YA BA DA LABARIN

Keith Eaton a lokacin da yake matashi.

A lokacin da nake matashi, na zaɓi aikin da na ji daɗin sa sosai. Amma Jehobah ya gayyace ni in yi wani aiki dabam, kuma ya yi min alkawari cewa: “Zan koya maka in kuma nuna maka hanyar da za ka bi.” (Zab. 32:⁠8) Domin na yarda Jehobah ya yi min ja-goranci, na sami damar yin abubuwa da yawa a ƙungiyarsa. Hakan ya ƙunshi yin hidima na tsawon shekaru 52 a Afirka, kuma Jehobah ya yi min albarka sosai.

DAGA INGILA ZUWA AFIRKA

An haife ni a 1935 a Darlaston da ke yankin Black Country, a ƙasar Ingila. Ana kiran wurin Black Country ne domin hayaƙin da ke tashiwa daga kamfanonin da ke yankin. A lokacin da nake shekara huɗu, iyayena sun soma nazari da Shaidun Jehobah. Na amince da abin da nake koya sa’ad da nake wajen shekara 14, kuma na yi baftisma a 1952, a lokacin shekarana 16.

A daidai wannan lokacin, na soma koyan aikin sakatare a wani babban kamfani da ke ƙera kayan aikin hannu da kuma sassan motoci, kuma na so aikin sosai.

Na bukaci in yanke wata shawara mai muhimmanci a lokacin da wani mai kula mai ziyara ya ce min in soma gudanar da nazari a Rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya a Willenhall. Amma yanke shawarar bai yi mini sauƙi ba. A lokacin ina halartan taro a ikilisiyoyi biyu. A mako ina halartan taro a ikilisiyar da ke kusa da wurin aikina a Bromsgrove, mai nisan wajen kilomita 32 (mil 20) daga gidanmu. A ƙarshen mako kuma sa’ad da na koma gida, ina halartan taro da iyayena a ikilisiyar Willenhall.

Da yake ina so in taimaka wa ƙungiyar Jehobah, sai na amince da tayin da mai kula da da’irar ya yi min ko da yake hakan yana nufin cewa zan daina koyan aikin da nake so sosai. Ban taɓa yin da-na-sanin barin Jehobah ya yi min ja-goranci ba domin hakan ya sa na ji daɗin rayuwa sosai.

A ikilisiyar Bromsgrove, na haɗu da wata ’yar’uwa mai kyaun gaske, kuma mai dangantaka mai kyau da Jehobah. Sunanta Anne. Mun yi aure a shekara ta 1957, kuma tare mun sami gatan yin hidimar majagaba na kullum, da hidimar majagaba na musamman da hidimar mai kula mai ziyara da kuma hidima a Bethel. Anne ta sa ni farin ciki a dukan rayuwata.

A shekara ta 1966, mun yi farin ciki sosai da aka gayyace mu aji na 42 na makarantar Gilead. An tura mu ƙasar Malawi, ƙasar da aka san ta da karɓan baƙi. Amma ba mu san cewa ba za a bar mu mu daɗe a wurin ba.

YIN HIDIMA A MUWAYACIN LOKACI A MALAWI

Motar da muka yi amfani da ita don yin hidima a Malawi

Mun isa Malawi a ranar 1 ga Fabrairu, 1967. Bayan mun yi wata ɗaya muna koyan yaren, sai muka fara hidimar mai kula mai ziyara. Mun yi amfani da wata mota da wasu ke ganin za ta iya yin tafiya a ko’ina, har da cikin ruwa. Amma hakan ba gaskiya ba ne, cikin ƙaramin ruwa kawai muke iya shiga da motar. A wasu lokuta, muna zama a gidan taɓo da aka yi rufin da zana, kuma mukan bukaci tampol a lokacin damina. Yadda muka soma yin hidima a wata ƙasa ke nan, amma mun ji daɗin yin hakan!

A watan Afrilu, na soma ganin alamu cewa gwamnatin ƙasar za ta soma tsananta mana. Na saurari jawabin da shugaban ƙasar Malawi Dr. Hastings Banda ya yi a rediyo. Ya ce Shaidun Jehobah ba sa biyan haraji kuma suna adawa da gwamnati. Hakika, wannan ba gaskiya ba ne. Mun san cewa matsalar ita ce domin ba ma saka hannu a harkokin siyasa kuma mun ƙi mu sayi katin jam’iyyar siyasa.

A watan Satumba, mun karanta a jarida cewa shugaban ƙasar ya zargi ’yan’uwanmu da tā da zaune tsaye. Ya yi sanarwa a taron jam’iyyarsa cewa gwamnatinsa za ta ɗauki mataki nan da nan ta saka wa Shaidun Jehobah takunkumi. An saka wannan takunkumin a ranar 20 ga Oktoba, 1967. Nan da nan bayan hakan, ’yan sanda da kuma hukumomin shige da fice suka zo ofishinmu don su kulle ofishin kuma suka kama ’yan’uwan da suka zo daga ƙasar waje.

An kama mu kuma aka kore mu daga ƙasar Malawi a 1967, tare da wasu ’yan’uwa da suke hidima a ƙasar waje, masu suna Jack da Linda Johansson

Bayan mun yi kwana uku a kurkuku, sai aka kai mu ƙasar da Birtaniya ce take mulki, wato Mauritius. Amma hukumomi a ƙasar Mauritius sun ƙi su bar mu mu zauna a wurin a matsayin masu wa’azi a ƙasar waje. Don haka, sai aka tura mu Rhodesia (wanda ake kira Zimbabuwe a yanzu). Da muka isa wurin, mun haɗu da wani jami’in hukumar da ke kula da shige da fice mai zafin rai sosai. Ya ƙi bari mu shiga ƙasar kuma ya ce: “An kore ku daga Malawi, an ƙi barin ku ku zauna a Mauritius, yanzu kun zo nan domin kun ga gidan sauƙi. Sai Anne ta soma kuka. Kamar dai kowa yana ƙin mu! A lokacin, na so in koma Ingila nan da nan. Amma daga baya, sun ce za su yarda mu kwana a ofishinmu da ke ƙasar, amma mu je hedkwatarsu washegari. Mun gaji sosai, amma mun ci gaba da dogara ga Jehobah. Washegari da rana, mun sami izinin zama a ƙasar Zimbabuwe a matsayin baƙi. Ba mu yi tsammanin hakan ba. Ba zan taɓa manta yadda na ji ranar ba. Na tabbata cewa Jehobah ne yake yi mana ja-goranci.

MUN SOMA HIDIMA A MALAWI DAGA ZIMBABUWE

Keith da Anne suna aiki tare a cikin ofishi.

Ni da Anne a Bethel a Zimbabuwe a 1968

A ofishinmu da ke Zimbabuwe, an ba ni aiki a Sashen Kula da Hidima, kuma na soma kula da hidimarmu a Malawi da Mozambik. A lokacin ana tsananta wa ’yan’uwan da ke Malawi sosai. Wasu cikin ayyukan da nake yi shi ne fassara rahotanni daga masu kula da da’ira na Malawi. Wata rana da na yi dare ina aiki, na yi kuka da na ga irin tsanantawa da ake yi wa ’yan’uwana a ƙasar.a Duk da haka, bangaskiyarsu da amincinsu da kuma yadda suke jimrewa ya ƙarfafa ni sosai.​—⁠2 Kor. 6:​4, 5.

Mun yi iya ƙoƙarinmu don mu tanada wa ’yan’uwan da suka rage a Malawi, da kuma waɗanda suka gudu zuwa Mozambik domin tsanantawa abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. An komar da mafassaran yare mafi girma a Malawi, wato yaren Chichewa zuwa Zimbabuwe, kuma sun zauna a babban gonar wani ɗan’uwa a ƙasar. Ya gina musu gida da ofisoshi, kuma suka ci gaba da yin wannan aikin fassara mai muhimmanci.

Mun yi shiri domin masu kula da da’ira a Malawi su riƙa halartan taron gunduma a yaren Chichewa a Zimbabuwe kowace shekara. Idan suka iso sai a ba su awutlayi na taron gundumar. Sa’ad da suka koma Malawi, idan suka haɗu da ’yan’uwa suna ƙarfafa su da abin da suka koya a taron. Wata shekara da suka ziyarci Zimbabuwe, mun yi ƙoƙari mun shirya Makarantar Hidima ta Mulki domin a ƙarfafa waɗannan masu kula da da’ira masu ƙarfin zuciya.

Ina ba da jawabi da yaren Chichewa a taron gundumar Chichewa da Shona a Zimbabuwe

A watan Fabrairu 1975, na yi tafiya don in ziyarci ’yan’uwan da suka gudu daga Malawi zuwa Mozambik kuma suke zama a sansani. ’Yan’uwan suna bin sabbin umurnan da ƙungiyarmu ta bayar, har da umurnin kafa rukunin dattawa. Dattawan sun tsara ayyukan ibada da dama, har da ba da jawabai, da tattauna nassin yini, da Hasumiyar Tsaro da kuma yin manyan taro. Sun tsara sansanin kamar yadda ake tsara wurin taron gunduma. Sun saka sashen shara da sashen abinci da kuma sashen tsaro. Waɗannan ’yan’uwa masu aminci sun cim ma abubuwa da yawa da taimakon Jehobah, kuma na sami ƙarfafa sosai bayan na ziyarce su.

A wajen 1979, ofishinmu da ke Zambiya ta soma kula da Malawi. Duk da haka, na ci gaba da yin tunani da kuma addu’a wa ’yan’uwan da ke Malawi, kamar yadda wasu ’yan’uwa ma suke yi. Sau da yawa sa’ad da nake yin hidima a matsayin memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu na Zimbabuwe, mukan yi taro da wakilan hedkwatarmu tare da wasu ’yan’uwa da ke ja-goranci daga Malawi da Afirka ta Kudu da kuma Zambiya. A duk lokacin da muka haɗu muna tattauna tambayar nan, “Mene ne za mu yi don mu daɗa taimaka wa ’yan’uwan da ke Malawi?”

A kwana a tashi, tsanantawar ta ragu. ’yan’uwan da suka gudu suka bar ƙasar Malawi sun fara komawa. Waɗanda ba su guda ba kuma sun soma samun sauƙi daga tsanantawar. Ƙasashen da ke kusa da Malawi sun soma barin Shaidun Jehobah su riƙa yin wa’azi da taro, kuma sun ɗage takunkumin da suka saka musu. A shekara ta 1991, ƙasar Mozambik ma ta yi hakan. Amma tambayar da muka yi ta yi a zuciyarmu ita ce, ‘Yaushe Shaidun Jehobah da ke Malawi za su sami ’yanci?’

MUN KOMA ƘASAR MALAWI

A kwana a tashi, tsarin siyasa a ƙasar Malawi ya canja, kuma a shekara ta 1993, gwamnati ta cire takunkumin da ta saka wa Shaidun Jehobah. Jim kaɗan bayan hakan, da nake tattaunawa da wani ɗan’uwa da ke hidima a ƙasar waje, sai ya tambaye ni, “Za ka koma ƙasar Malawi?” Shekarana 59 a lokacin, sai na ce masa, “Na tsufa, ba zan iya komawa ba!” Amma a ranar muka sami saƙo daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu. Sun tambaye mu ko za mu so mu koma ƙasar Malawi.

Muna jin daɗin hidimar da muke yi a Zimbabuwe kuma mun riga mun yi abokai da yawa, don haka, barin wurin ya yi mana wuya. Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta nuna mana alheri ta wajen cewa idan muna so, za mu iya ci gaba da yin hidimarmu a Zimbabuwe. Saboda haka, da mun so da mun zaɓa abin da zuciyarmu take so. Amma mun tuna yadda Ibrahim da Saratu suka yi wa Jehobah biyayya ta wurin barin gidansu duk da cewa sun tsufa.​—⁠Far. 12:​1-5.

Mun yanke shawarar yin abin da ƙungiyar Jehobah take so, kuma muka koma ƙasar Malawi a ranar 1 ga Fabrairu, 1995, wato bayan shekara 28 da muka zo ƙasar ke nan. An kafa Kwamitin da Ke Kula da Ayyukanmu a ƙasar, kuma ni da wasu ’yan’uwa biyu ne muke cikin kwamitin. Ba da daɗewa ba bayan haka, muka soma tsara ayyukan Shaidun Jehobah a ƙasar.

JEHOBAH YA BA DA CI GABA

Abin farin ciki ne ganin yadda Jehobah ya sa aikin ya sami ci gaba cikin ƙanƙanin lokaci! Adadin masu shela ya ƙaru daga 30,000 a 1993 zuwa fiye da 42,000 a 1998.b Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta amince a gina sabon ofishi domin masu shela suna ƙaruwa. Mun sayi fili mai girman hekta 12 a birnin Lilongwe, kuma an naɗa ni memban kwamitin da ke kula da aikin ginin.

Ɗan’uwa Guy Pierce, memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ya ba da jawabin keɓe ginin ga Jehobah a watan Mayu, 2001. Shaidu fiye da dubu biyu daga ƙasar ne suka halarci taron kuma yawancinsu sun yi fiye da shekaru 40 da yin baftisma. Waɗannan ’yan’uwa masu aminci sun yi shekaru da yawa suna fuskantar tsanantawa da ba za a iya kwatantawa ba. Su talakawa ne, amma suna da dangantaka mai kyau da Jehobah. Bayan an keɓe ginin, ’yan’uwan sun je zagaya a wurin kuma sun ji daɗin sa sosai. Duk inda suka shiga, suna rera waƙoƙinmu da kayan kiɗa na gargajiya. Ban taɓa halartan biki irin wannan ba. Wannan ya nuna cewa Jehobah yana yi wa masu aminci albarka.

Bayan an gama gina ofishinmu, sai aka soma gina Majami’un Mulki da yawa, kuma na yi farin ciki da aka soma ba ni damar yin jawaban keɓe Majami’un Mulkin ga Jehobah. ’Yan’uwanmu a Malawi sun amfana sosai daga tsarin ƙungiyarmu na gina Majami’un Mulki a cikin ƙanƙanin lokaci a ƙasashen da ba su da arziki. A dā, ’yan’uwan suna yin taro a cikin rumfar da suka yi da itace. Suna yin amfani da zana su yi rufin rumfar kuma suna yin bencuna da laka. Yanzu, ’yan’uwan suna yin aiki da ƙwazo sosai su yi bulo don su yi amfani da shi wajen gina Majami’un Mulki. Amma har ila ’yan’uwan sun fi son bencuna a Majami’ar Mulki maimakon kujeru domin zai iya ɗaukan mutane da yawa.

Na kuma yi farin cikin ganin yadda mutanen Jehobah suke ci gaba da manyanta. Matasa ne musamman suka fi burge ni domin a shirye suke su taimaka kuma sun koyi abubuwa da yawa da sauri daga koyarwa da ƙungiyarmu ta ba su. Hakan ya sa sun sami ƙarin ayyuka a Bethel da ikilisiyoyinsu. Ban da haka, ikilisiyoyin sun sami ƙarfafa daga sabbin masu kula da da’ira da aka naɗa. Da yawa daga cikin masu kula da da’irar suna da aure. Ko da yake iyalan ma’auratan da ma wasu mutane suna matsa musu su haifi ’ya’ya, ma’auratan sun zaɓa su yi hidima ta cikakken lokaci.

NA GAMSU DA ZAƁIN DA NA YI

Ni da Anne a Bethel a Birtaniya

Bayan na yi shekaru 52 a Afirka, na soma rashin lafiya. Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta amince da shawarar da Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu na Malawi ta bayar cewa a mayar da mu Birtaniya. Barin Malawi bai yi mana sauƙi ba domin muna son wurin sosai. Amma ’yan’uwa a ofishinmu na Birtaniya suna kula da mu sosai.

Na tabbata cewa barin Jehobah ya yi min ja-goranci a rayuwa shi ne shawara mafi muhimmanci da na yanke. Da a ce na bi abin da zuciyata take so, da a yanzu ban san inda nake ba. Jehobah ya san abin da nake bukata don in ‘daidaita hanyoyina.’ (K. Mag. 3:​5, 6) A lokacin da nake matashi, na yi farin cikin koyan yadda babban kamfani ke aiki. Amma ƙungiyar Jehobah ta ba ni rayuwa mafi gamsarwa. A gare ni, bauta ma Jehobah shi ne abu mafi gamsarwa a rayuwa!

a Za ka iya samun labarin Shaidun Jehobah a Malawi a littafin nan 1999 Yearbook of Jehovah’s Witnesses, shafuffuka na 148-223.

b A yanzu, akwai masu shela sama da 100,000 a Malawi.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba