Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w22 Yuli pp. 20-25
  • Kada Ka Yi Wasa da Gatan da Kake da Shi na Yin Addu’a

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ka Yi Wasa da Gatan da Kake da Shi na Yin Addu’a
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “SAI KU YI ADDU’A KAMAR HAKA”
  • KA GODE WA JEHOBAH DOMIN ƊANSA
  • KA YI ADDU’A A MADADIN ’YAN’UWA
  • SA’AD DA AKA BA MU DAMAR YIN ADDU’A A MADADIN WASU
  • KA SA ADDU’A TA ZAMA ABU MAI MUHIMMANCI SOSAI A RAYUWARKA
  • Ka Rika Yin Addu’a don Ka Kusaci Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Gatan da Muke da Shi Na Yin Addu’a
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Jawowa Kurkusa da Allah Cikin Addu’a
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
w22 Yuli pp. 20-25

TALIFIN NAZARI NA 31

Kada Ka Yi Wasa da Gatan da Kake da Shi na Yin Addu’a

“Karɓi addu’ata kamar turaren ƙonawa.”​—ZAB. 141:2.

WAƘA TA 47 Mu Riƙa Addu’a ga Jehobah Koyaushe

ABIN DA ZA A TATTAUNAa

1. Yaya ya kamata mu ɗauki gatan da Jehobah ya ba mu na yin addu’a?

MAHALICCIN sama da ƙasa ya ba mu babban gata, wato damar yin addu’a. Ka yi tunanin wannan: Za mu iya gaya masa kome da muke so a duk lokacin da muke so kuma a duk yaren da muke so, ba sai mun nemi izinin yin hakan ba. Za mu iya yin addu’a ga Allah ko da muna asibiti ne ko kurkuku, kuma mu kasance da tabbaci cewa Ubanmu mai ƙauna zai saurare mu. Ba ma wasa da wannan damar da muke da ita.

2. Ta yaya Sarki Dauda ya nuna godiya don gatan da yake da shi na yin addu’a?

2 Sarki Dauda ya nuna godiya sosai don gatan da Jehobah ya ba shi na yin addu’a. Ga abin da ya faɗa a cikin waƙa ga Jehobah, ya ce: “Karɓi addu’ata kamar turaren ƙonawa.” (Zab. 141:​1, 2) A zamanin Dauda, firistocin da suke shirya turare mai tsarki suna mai da hankali sosai yayin da suke hakan. (Fit. 30:​34, 35) Dauda ya nuna cewa yana so ya mai da hankali sosai ga abin da zai faɗa yayin da yake addu’a kamar yadda firistocin nan ma suke mai da hankali yayin da suke shirya turare. Mu ma abin da muke so mu yi ke nan domin muna so addu’o’inmu su faranta wa Jehobah rai.

3. Me ya kamata mu yi yayin da muke addu’a ga Jehobah, kuma me ya sa?

3 Ya kamata mu girmama Jehobah yayin da muke addu’a. Ku yi tunanin wahayoyi masu ban al’ajabi da Ishaya da Ezekiyel da Daniyel, da kuma Yohanna suka gani. Ko da yake wahayoyin sun bambanta, akwai alaƙa tsakaninsu. Dukansu sun nuna cewa Jehobah Sarki mai girma ne sosai. Ishaya ya ga Jehobah “yana zaune a can sama a kan kujerar mulki mai girma.” (Isha. 6:​1-3) Ezekiyel ya ga Jehobah zaune a kan karusarsa a sama kuma walƙiya kamar bakan gizo ta kewaye shi. (Ezek. 1:​26-28) Daniyel ya ga “Wanda Yake Tun Dā,” sanye da tufafi fari fat kuma harshen wuta mai ci yana fitowa daga kursiyinsa. (Dan. 7:​9, 10) Kuma Yohanna ya ga Jehobah zaune a kan kursiyinsa da bakan gizo mai ƙyalli kewaye da shi. (R. Yar. 4:​2-4) Yayin da muke tunanin irin ɗaukakar da Jehobah yake da shi, ya kamata mu riƙa tuna cewa babban gata ne muke da shi na yin addu’a kuma mu yi hakan cikin ban girma. Amma me ya kamata mu yi addu’a a kai?

“SAI KU YI ADDU’A KAMAR HAKA”

4. Mene ne za mu iya koya game da yin addu’a daga yadda Yesu ya fara yin addu’a a Matiyu 6:​9, 10?

4 Karanta Matiyu 6:​9, 10. A Huɗubar da Yesu Ya Yi a kan Dutse, Yesu ya koya wa almajiransa yadda za su yi addu’a a hanyar da za ta faranta wa Allah rai. Bayan da Yesu ya ce “sai ku yi addu’a kamar haka,” sai ya fara da ambata abubuwa masu muhimmanci a addu’arsa. Ya roƙa a tsarkake sunan Allah, Mulkin Allah ya zo domin ya hallaka dukan maƙiyan Allah kuma ya sa nufin Allah wa duniya da kuma ’yan Adam ya cika. Idan mun ambata abubuwan nan yayin da muke addu’a, za mu nuna cewa nufin Allah yana da muhimmanci a gare mu.

5. Shin ya dace mu yi addu’a game da abubuwa da suka shafe mu?

5 Bayan haka, addu’ar Yesu ya nuna cewa za mu iya roƙan Jehobah abubuwan da suka shafe mu. Za mu iya roƙan Jehobah ya ba mu abincinmu na yau da kullum, ya kāre mu daga jarraba, ya gafarta mana zunubanmu kuma ya tsare mu daga mugun nan. (Mat. 6:​11-13) Idan muna roƙan Jehobah saboda abubuwan nan, za mu nuna cewa muna bukatar taimakonsa kuma muna so mu faranta masa rai.

Wani mutum da matarsa suna yin addu’a. Hotuna: 1. ’Yarsu tana zaune a cikin aji. 2. Wani tsoho yana kwance a gado. 3. Matarsa tana nazari da wata mata.

Mene ne maigida zai iya yin addu’a a kai tare da matarsa? (Ka duba sakin layi na 6)b

6. Shin abubuwan da aka ambata a addu’ar misalin ne kaɗai za mu riƙa yin addu’a a kai? Ka bayyana.

6 Yesu bai ce mabiyansa su riƙa maimaita addu’ar misalin nan daidai yadda yake ba. A wasu addu’o’in da Yesu ya yi, ya ambata abubuwa dabam-dabam da suke damun sa a lokacin. (Mat. 26:​39, 42; Yoh. 17:​1-26) Haka ma za mu iya yin addu’a game da kome da ke damunmu. Idan muna so mu yanke shawara, za mu iya roƙan Jehobah ya ba mu hikima da kuma fahimta. (Zab. 119:​33, 34) Idan aka ba mu wani aiki mai wuya mu yi, za mu iya roƙan Jehobah ya taimaka mana mu san yadda za mu yi aikin. (K. Mag. 2:6) Iyaye za su iya yin addu’a a madadin yaransu, yara kuma a madadin iyayensu. Ya kamata dukanmu mu riƙa yin addu’a a madadin ɗalibanmu da kuma waɗanda muke musu wa’azi. Amma ba roƙo ne kaɗai za mu yi ta yi a addu’armu ba.

Wani dan’uwa yana addu’a. Hotuna: 1. Yesu a kan gungumen azaba. 2. Wani kogi mai kyau da tuddai suka kewaye shi. 3. Kayan lambu da ganyaye dabam-dabam.

A kan me za mu iya yabon Jehobah kuma mu yi masa godiya? (Ka duba sakin layi na 7-9)c

7. Me ya sa ya kamata mu yabi Jehobah a addu’armu?

7 Ya kamata mu riƙa yabon Jehobah a addu’armu. Ba wanda ya cancanci yabo kamar Allah. Shi “mai alheri ne kuma mai yin gafara.” Ƙari ga haka, shi “mai jinƙai mai alheri kuma, marar saurin fushi, mai yawan ƙauna marar canjawa mai aminci ne.” (Zab. 86:​5, 15) Hakika muna da dalilai da yawa na yabon Jehobah domin halinsa da kuma ayyukansa.

8. Waɗanne abubuwa ne za mu iya yin godiya saboda su? (Zabura 104:​12-15, 24)

8 Ƙari ga yabon Jehobah a cikin addu’o’inmu, muna masa godiya don abubuwa masu kyau da yake tanada mana. Alal misali, za mu iya masa godiya don furanni masu kyau da muke gani, abinci masu daɗi iri-iri da muke da su, da kuma farin ciki da muke samu daga cuɗanya da abokan kirki. Ubanmu mai ƙauna ya ba mu abubuwan nan ne da kuma wasu don ya sa mu farin ciki. (Karanta Zabura 104:​12-15, 24.) Amma abubuwa guda biyu masu muhimmanci da ya kamata mu yi addu’a game da su su ne, koyarwa da Jehobah yake mana don ya ƙarfafa bangaskiyarmu da kuma begen da ya ba mu na yin rayuwa har abada.

9. Me zai taimaka mana mu riƙa tunawa mu gode wa Jehobah? (1 Tasalonikawa 5:​17, 18)

9 Yana da sauƙi mutum ya manta ya yi godiya ga Jehobah don dukan abubuwan da yake masa. Me zai taimake ka kada ka manta? Za ka iya rubuta abubuwa dabam-dabam da ka roƙe Jehobah ya yi maka, sa’an nan ka riƙa duba abubuwan a kai a kai don ka ga yadda Jehobah ya amsa addu’o’inka. Sai ka yi addu’a ka gode masa don taimakonsa. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:​17, 18.) Ka yi tunanin wannan: Muna farin ciki sosai idan mutane suka gode mana. Haka ma, idan muka gode wa Jehobah don ya amsa addu’armu, yana yin farin ciki. (Kol. 3:15) Amma akwai wani dalili mai muhimmanci kuma da ya kamata mu gode wa Allah.

KA GODE WA JEHOBAH DOMIN ƊANSA

10. Bisa ga abin da ke 1 Bitrus 2:​21, me ya sa kamata mu gode wa Jehobah don ya turo Yesu?

10 Karanta 1 Bitrus 2:21. Ya kamata mu riƙa gode wa Jehobah don ya turo Ɗansa da yake ƙauna sosai ya zo ya koyar da mu. Idan muka yi nazari game da Yesu, za mu koyi abubuwa da yawa game da Jehobah da yadda za mu sa shi farin ciki. Idan muka ba da gaskiya ga hadayar Kristi, za mu sami dangantaka mai kyau da Jehobah kuma za mu mori salama.​—Rom. 5:1.

11. Me ya sa muke addu’a a cikin sunan Yesu?

11 Muna godiya ga Jehobah cewa za mu iya yin addu’a ta wurin Ɗansa. Ta wurin Yesu ne Jehobah yake ba mu abubuwa da muke roƙa. Jehobah yana sauraron addu’o’in da muke yi a cikin sunan Yesu. Yesu ya bayyana cewa: “Duk dai abin da kuka roƙa cikin sunana zan yi, domin Uban ya sami ɗaukaka ta wurin Ɗan.”​—Yoh. 14:​13, 14.

12. Wane dalili ne kuma ya kamata ya sa mu gode wa Jehobah don Ɗansa?

12 Jehobah yana gafarta mana zunubanmu domin hadayar Yesu. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Yesu a matsayin “Babban Firist wanda yake zaune a hannun daman kujerar mulkin Maɗaukaki a can sama.” (Ibran. 8:1) Yesu shi ne “mai tsaya mana a gaban Uba.” (1 Yoh. 2:1) Muna godiya ga Jehobah don ya ba mu Babban Firist wanda ya san kasawarmu kuma “yana roƙon Allah a madadinmu”! (Rom. 8:34; Ibran. 4:15) Mu ajizai ne, saboda haka, da ba don hadayar Yesu ba, da ba za mu iya yin addu’a ga Jehobah ba. Hakika, ba ƙaramin godiya ba ne ya kamata mu yi wa Jehobah don wannan kyauta mai daraja da ya ba mu, wato, Ɗansa da yake ƙauna!

KA YI ADDU’A A MADADIN ’YAN’UWA

13. A dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, yaya ya nuna cewa yana ƙaunar almajiransa?

13 A darensa na ƙarshe kafin ya mutu, Yesu ya ɗauki lokaci mai tsawo yana addu’a a madadin almajiransa, yana roƙan Ubansa ya “tsare su daga Mugun nan.” (Yoh. 17:15) Hakan ya nuna cewa Yesu yana ƙaunar su sosai. Ya san cewa yana dab da fuskantar azaba, amma duk da haka, ya damu da almajiransa.

Wata ’yar’uwa tana addu’a. Hotuna: 1. Wani memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidunmu yana ba da jawabi a Tashar JW. 2. Wani dan’uwa da matarsa suna barin gidansu da guguwa ta rusa. 3. Dennis Christensen, a hannun ’yan sandan Rasha da ankwa a hannunsa.

Me za mu iya yin addu’a a kai a madadin ’yan’uwanmu? (Ka duba sakin layi na 14-16)d

14. Ta yaya za mu iya nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu?

14 Bin misalin Yesu yana sa mu yi tunanin wasu maimakon kanmu kawai. Muna yin addu’a a madadin ’yan’uwanmu a kowane lokaci. Yin hakan zai nuna cewa muna bin dokar da Yesu ya ba mu cewa mu ƙaunace juna, kuma za mu nuna wa Jehobah yadda muke ƙaunar ’yan’uwanmu. (Yoh. 13:34) Yin addu’a a madadin ’yan’uwanmu zai taimaka musu. Kalmar Allah ta gaya mana cewa “addu’ar mai adalci tana da ƙarfin aiki da iko sosai.”​—Yak. 5:16.

15. Me ya sa ’yan’uwanmu masu bi suke bukatar addu’o’inmu?

15 ’Yan’uwanmu masu bi suna bukatar addu’o’inmu don suna jimre jarrabobi da yawa. Za mu iya roƙan Jehobah ya taimaka musu don su jimre rashin lafiya, da bala’o’i da yaƙe-yaƙen basasa da tsanantawa da dai wasu matsaloli. Za mu kuma iya yin addu’a a madadin ’yan’uwanmu da suke sadaukar da kansu don su taimaka ma waɗanda bala’i ya shafa. Mai yiwuwa ma ka san wasu da suke fama da matsalolin nan. Za ka iya ambata su a cikin addu’arka ga Jehobah. Za mu nuna cewa muna ƙaunar su ta wajen roƙan Jehobah ya taimaka musu su jimre.

16. Me ya sa ya kamata mu riƙa addu’a a madadin waɗanda suke ja-goranci a ikilisiyoyinmu?

16 ’Yan’uwan da suke ja-goranci a cikin ikilisiya ma suna godiya sosai don yadda muke addu’a a madadinsu, kuma addu’o’in nan suna taimaka musu. Manzo Bulus ya san cewa yana bukatar ’yan’uwa su yi addu’a a madadinsa. Ya ce: “Ni ma ku yi mini addu’a, in sami baiwar yin magana ba tsoro, in sanar da asirin labari mai daɗi ga mutane.” (Afis. 6:19) A yau ma muna da ’yan’uwa masu ƙwazo sosai da suke ja-goranci a tsakanin mu. Za mu nuna cewa muna ƙaunar su idan muna roƙan Jehobah ya albarkaci aikinsu.

SA’AD DA AKA BA MU DAMAR YIN ADDU’A A MADADIN WASU

17-18. A waɗanne lokuta ne za a iya ce mu yi addu’a a madadin wasu, kuma me ya kamata mu yi idan aka gaya mana hakan?

17 A wasu lokuta, za a iya ba mu damar yin addu’a a madadin wasu. Alal misali, ’yar’uwar da take so ta yi nazari da ɗalibarta za ta iya gaya wa ’yar’uwa da suke wa’azi tare ta yi musu addu’a. Da yake ’yar’uwar ba ta san ɗalibar sosai ba, zai fi dacewa a gaya mata ta yi addu’a a ƙarshen nazarin. Da haka, za ta san abin da ya kamata ta faɗa game da ɗalibar yayin da take addu’ar.

18 Za a iya gaya wa ɗan’uwa ya yi addu’a a taron fita wa’azi ko taron ikilisiya. Ya kamata waɗanda za su yi addu’ar nan su yi tunanin dalilin da ya sa ake taron. Bai kamata su yi amfani da addu’ar su gargaɗi ’yan’uwa ko su yi sanarwa ba. A yawancin lokuta, ana ba da minti biyar ne kawai don waƙa da addu’a a taron ikilisiya, don haka bai kamata ɗan’uwan da zai yi addu’a ya yi “dogon surutu” ba, musamman ma addu’ar buɗewa.​—Mat. 6:7.

KA SA ADDU’A TA ZAMA ABU MAI MUHIMMANCI SOSAI A RAYUWARKA

19. Me zai taimaka mana mu kasance a shirye don ranar hukuncin Jehobah?

19 Ya kamata mu daɗa mai da hankali sosai ga yin addu’a yayin da ranar hukuncin Jehobah take kusatowa. Saboda haka, Yesu ya ce: “Ku zauna a shirye fa, kuna addu’a kullum don ku sami ƙarfin kuɓuce wa dukan waɗannan abubuwan da za su faru.” (Luk. 21:36) Hakika, idan muna yin addu’a a kai a kai, bangaskiyarmu za ta yi ƙarfi kuma za mu kasance a shirye a lokacin da ranar hukuncin Jehobah ya zo.

20. A wace hanya ce addu’o’inmu za su iya zama kamar turare mai ƙanshi?

20 Me muka tattauna a wannan talifin? Muna ɗaukan yin addu’a a matsayin babban gata. Abubuwa mafi muhimmanci da ya kamata mu yi addu’a a kai su ne abubuwa da suka shafi nufin Jehobah. Muna kuma yin godiya don Ɗan Allah, da Mulkinsa, kuma muna yi wa ’yan’uwanmu addu’a. Ƙari ga haka, Jehobah yana so mu yi addu’a don abubuwa da muke bukata yau da kullum da kuma abubuwa da za su ƙarfafa bangaskiyarmu. Idan muna tunani sosai kafin mu yi addu’a, za mu nuna cewa muna godiya sosai don wannan gatan. Furucinmu zai zama kamar turare mai ƙanshi kuma Jehobah zai ‘ji daɗin addu’ar.’​—K. Mag. 15:8.

MECE CE AMSARKA?

  • Waɗanne abubuwa ne za mu iya yin addu’a a kai?

  • Me ya sa ya kamata mu yi addu’a a madadin ’yan’uwanmu masu bi?

  • Me ya kamata mu riƙa tunawa idan aka ce mu yi addu’a a madadin wasu?

WAƘA TA 45 Abubuwan da Nake Tunani a Kai

a Muna godiya ga Jehobah don yadda yake ba mu damar yin addu’a. Muna so addu’o’inmu su zama kamar turare mai ƙanshi da za su faranta masa rai. A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa da za mu iya yin addu’a a kai. Ƙari ga haka, za mu tattauna wasu abubuwa da ya kamata mu tuna idan aka kira mu mu yi addu’a a madadin wasu.

b BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa da matarsa suna yin addu’a Jehobah ya kāre ’yarsu, ya taimaka wa babansu da ke rashin lafiya, kuma ya taimaka wa ɗalibarsu ta sami ci gaba.

c BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa matashi yana godiya ga Jehobah domin hadayar Yesu, da duniya mai kyau da Jehobah ya tsara mana, da kuma abinci mai gina jiki.

d BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ’yar’uwa tana yin addu’a Jehobah ya ba wa Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ruhunsa, kuma ya taimaki waɗanda bala’i ya shafa da waɗanda ake tsananta musu.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba