ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE NUFI
Allah Ya Ƙyale Zunuban da Aka Yi a Dā
Fansar da Yesu ya bayar ta wurin jininsa ne kaɗai yake sa Allah ya yafe zunubanmu. (Afis. 1:7) Amma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Don a cika haƙurinsa [Allah] ya ƙyale zunuban da aka yi a dā,” wato tun kafin Yesu ya ba da fansar. (Rom. 3:25) Da yake a gun Allah, ana bukatar a ba da fansar kafin a yafe zunubi, kuma shi mai yin shariꞌar gaskiya ne, yaya aka yi ya yafe wa mutane tun ba a ba da fansar ba?
Dalilin shi ne, tun lokacin da Jehobah ya yi alkawarin wani ‘zuriya’ da zai ceci waɗanda suka ba da gaskiya gare shi, a gun Jehobah kamar hakan ya riga ya faru ne. (Far. 3:15; 22:18) Jehobah ya san cewa da zarar lokacinsa ya kai, Ɗansa makaɗaici zai ba da wannan fansar da son ransa. (Gal. 4:4; Ibran. 10:7-10) Lokacin da Yesu yake duniya shi ma Jehobah ya ba shi ikon yafe zunubai, tun kafin ya ba da fansar. Yesu ya iya yafe wa mutane zunubansu ne don ya san cewa hadayar ransa da zai bayar za ta iya goge zunubansu.—Mat. 9:2-6.