TALIFIN NAZARI NA 25
WAƘA TA 96 Kalmar Allah Tana da Daraja
Darussan da Za Mu Iya Koya Daga Annabcin Yakubu—Kashi na 2
“Ya sa wa kowannensu albarkar da ta dace da shi.”—FAR. 49:28.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga abin da za mu koya daga annabcin da Yakubu ya yi game da sauran ꞌyaꞌyansa takwas kafin ya mutu.
1. Me za mu tattauna a wannan talifin?
ꞌYAꞌYAN Yakubu sun zagaya shi, suna sauraran abin da zai gaya wa kowannensu. A talifin da ya wuce, mun ga cewa Yakubu ya gaya wa Ruben da Simeyon da Lawi da kuma Yahuda abubuwan da ba su yi tsammani ba. Saboda haka, dukansu za su riƙa tunani a kan abin da zai faɗa game da sauran ꞌyaꞌyansa takwas. Bari mu ga abin da za mu iya koya daga abin da ya faɗa game da Zebulun da Issakar, da Dan, da Gad, da Asher, da Naftali, da Yusuf, da kuma Benyamin.a
ZEBULUN
2. Mene ne Yakubu ya faɗa game da Zebulun, kuma ta yaya hakan ya cika? (Farawa 49:13) (Ka kuma duba akwatin.)
2 Karanta Farawa 49:13. Yakubu ya ce, zuriyar Zebulun za ta zauna kusa da teku, wato yankinsu zai kasance a arewacin Ƙasar Alkawari. Hakan ya faru fiye da shekaru 200 bayan da ya faɗi hakan. A lokacin, zuriyar Zebulun sun sami gādonsu tsakanin tekun Galili da na Bahar Rum. Ƙari ga haka, Musa ya yi annabci cewa: “Ka yi murna, ya Zebulun, cikin fitarka.” (M. Sha. 33:18) Mai yiwuwa hakan yana nufin cewa zai yi wa zuriyar Zebulun sauƙi su saya, su kuma sayar da wasu abubuwa ga mutane daga wurare dabam-dabam, da yake suna zama kusa da bakin teku. Amma ko da mene ne annabcin nan da Musa ya yi yake nufi, zuriyar Zebulun tana da dalilin yin farin ciki.
3. Me zai taimaka mana mu ci gaba da farin ciki?
3 Mene ne za mu iya koya? Ko da a ina muke zama, ko kuma muna cikin wani irin yanayi, akwai abubuwan da za su iya sa mu farin ciki. Idan muka yi tunani a kan abubuwa masu kyau da muke da su, hakan zai sa mu farin ciki. (Zab. 16:6; 24:5) A wasu lokuta, yakan yi mana sauƙi mu mai da hankali a kan abubuwan da ba mu da su, maimakon abubuwa masu kyau da muke morewa. Saboda haka, yana da kyau mu kasance da raꞌayin da ya dace game da kowane yanayin da muka tsinci kamu.—Gal. 6:4.
ISSAKAR
4. Mene ne Yakubu ya faɗa game da Issakar, kuma ta yaya hakan ya cika? (Farawa 49:14, 15) (Ka kuma duba akwatin.)
4 Karanta Farawa 49:14, 15. Yakubu ya yaba wa Issakar don yadda yake aiki tuƙuru. Ya ce Issakar na kama da jaki mai ƙarfi da ke kwance da kwandunan kaya. Yakubu ya kuma ce, Issakar zai sami yanki mai kyau sosai. Kuma abin da ya faru ke nan. An ba wa zuriyar Issakar wani wurin da ake samun amfanin gona sosai kusa da Kogin Urdun. (Yosh. 19:22) Babu shakka, zuriyar Issakar sun yi iya ƙoƙarinsu wajen kula da yankin da aka ba su. Kuma sun yi ƙoƙari wajen taimaka ma wasu. (1 Sar. 4:7, 17) Alal misali, a lokacin da Barak da annabiya Deborah suka roƙi ꞌyanꞌuwansu Israꞌilawa su zo su taya su yaƙan Sisera, ɗaya daga cikin zuriyoyin da suka taimaka shi ne na Issakar. Ƙari ga haka, akwai lokutan da suka kasance a shirye su taimaka wa ꞌyanꞌuwansu su yaƙi magabtansu.—Alƙa. 5:15
5. Me ya sa ya kamata mu yi aiki tuƙuru?
5 Mene ne za mu iya koya? Idan muka yi iya ƙoƙarinmu a hidimarmu ga Jehobah, Jehobah zai albarkace mu kamar yadda ya yi wa zuriyar Issakar. (M. Wa. 2:24) Alal misali, ka yi laꞌakari da yadda ꞌyanꞌuwan da suke kula da ikilisiya suke aiki tuƙuru. (1 Tim. 3:1) Ko da yake ba sa zuwa yaƙi a zahiri, suna aiki tuƙuru don su kāre ꞌyanꞌuwan da ke ikilisiya daga duk wani abin da zai ɓata dangantakarsu da Jehobah. (1 Kor. 5:1, 5; Yahu. 17-23) Kuma suna aiki tuƙuru don su shirya kuma su ba da jawaban da za su ƙarfafa ꞌyanꞌuwa a ikilisiya.—1 Tim. 5:17.
DAN
6. Wane aiki ne aka ba wa zuriyar Dan? (Farawa 49:17, 18) (Ka kuma duba akwatin.)
6 Karanta Farawa 49:17, 18. Yakubu ya ce Dan na kama da maciji da ke saran manyan dabbobi, kamar dokin da ake yaƙi da shi. Kuma haka yake, domin zuriyar Dan suna da ƙarfin zuciya, kuma suna a shirye su yaƙi magabtan Israꞌilawa. Saꞌad da Israꞌilawa suke zuwa Ƙasar Alkawari, zuriyar Dan sun kasance a ‘bayan dukan sauran zuriyoyin,’ ta hakan suka kāre su. (L. Ƙid. 10:25) Ko da yake sauran kabilun ba za su iya ganin kome da komen da zuriyar Dan suke yi musu ba, sun ci gaba da yin wannan aiki mai muhimmanci.
7. Me ya kamata mu tuna game da kowane aikin da aka ba mu a ƙungiyar Jehobah?
7 Mene ne za mu iya koya? Ka taɓa yin wani aikin da kake ganin ba wanda ya sani? Mai yiwuwa ka taimaka wajen kula ko share Majamiꞌar Mulkinku, ko ka yi aiki a taron daꞌira ko taron yanki, ko kuma wasu ayyuka dabam. Idan haka ne, ka kyauta! Ka tuna cewa Jehobah yana gani kuma yana jin daɗin kome da kake yi. Yana jin daɗi sosai idan kana bauta masa da dukan zuciyarka don kana ƙaunar sa, ba don a yaba maka ba.—Mat. 6:1-4.
GAD
8. Me ya sa ya kasance da sauƙi magabtan Israꞌila su kai wa zuriyar Gad hari? (Farawa 49:19) (Ka kuma duba akwatin.)
8 Karanta Farawa 49:19. Yakubu ya annabta cewa masu hari za su kai wa Gad hari. Wajen shekaru 200 bayan hakan, zuriyar Gad ta gaji ƙasar da ke gabashin Kogin Urdun. Wurin na da iyaka da ƙasashen magabtansu. Don haka, yana da sauƙi magabtansu su kawo musu hari. Duk da haka, zuriyar Gad sun so wannan wurin sosai domin akwai wurare masu kyau da za su iya yin kiwon dabbobinsu. (L. Ƙid. 32:1, 5) Babu shakka, zuriyar Gad masu ƙarfin zuciya ne. Kuma sun dogara ga Jehobah ya taimaka musu su yaƙi duk wani maƙiyansu da ya kawo musu hari. Ƙari ga haka, sun tura sojojinsu don su taimaka wa sauran kabilun su yi nasara a kan magabtansu a ɗayan bangaren Ƙogin Urdun. (L. Ƙid. 32:16-19) Suna da tabbaci cewa Jehobah zai kāre matansu da yaransu saꞌad da mazajen suka tafi yaƙi. Jehobah ya albarkace su don ƙarfin zuciyarsu, da yadda suka kasance a shirye su taimaka ma wasu, duk da cewa hakan bai da sauƙi.—Yosh. 22:1-4.
9. Waɗanne zaɓi ne za mu iya yi idan mun dogara ga Jehobah?
9 Mene ne za mu iya koya? Wajibi ne mu ci gaba da dogara ga Jehobah yayin da muke bauta masa a wannan mawuyacin lokaci. (Zab. 37:3) ꞌYanꞌuwa da yawa a yau suna nuna cewa sun dogara ga Jehobah ta wajen yin sadaukarwa don su iya yin gine-gine na ƙungiyarmu, da yin waꞌazi a inda ake bukatar masu shela, da kuma yin ayyuka dabam-dabam a ƙungiyar Jehobah. Suna yin hakan da tabbacin cewa Jehobah zai ci gaba da tanada musu abin da suke bukata.—Zab. 23:1.
ASHER
10. Mene ne ya kamata zuriyar Asher su yi da ba su yi ba? (Farawa 49:20) (Ka kuma duba akwatin.)
10 Karanta Farawa 49:20. Yakubu ya annabta cewa zuriyar Asher za su yi arziki, kuma abin da ya faru ke nan. Zuriyar Asher sun gaji yankin da ke ba da amfanin gona sosai. (M. Sha. 33:24) Yankinsu na kusa da tekun Bahar Rum da kuma babban tashar jirgin ruwa na Sidon. Amma zuriyar Asher ba su iya sun kori Kanꞌaniyawan da suke yankinsu ba. (Alƙa. 1:31, 32) Da yake suna da arziki sosai kuma suna zama da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah, wataƙila hakan ya sa zuriyar Asher sun soma kasancewa da rashin ƙwazo ga yin nufin Jehobah. Alal misali, da Barak ya roƙi alꞌummar Israꞌila su zo su taimaka masa wajen yaƙan Kanꞌaniyawa, zuriyar Asher ba su taimaka ba. Hakan ya sa ba su ga abubuwan ban mamakin da Jehobah ya yi ba, saꞌad da ya sa Israꞌilawa suka yi nasara a “rafin Megiddo.” (Alƙa. 5:19-21) Mai yiwuwa, zuriyar Asher sun ji kunya sosai saꞌad da Barak da Deborah suka rera waƙa kuma suka ce: “Zuriyar Asher ta zauna a bakin teku.”—Alƙa. 5:17.
11. Me ya sa za mu guji sa kuɗi ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu?
11 Mene ne za mu iya koya? Zai dace mu bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu. Don mu iya yin hakan, ya kamata mu guji ɗaukan cewa kuɗi da tara dukiyoyi ne suka fi muhimmanci a rayuwa kamar yadda mutane a duniya suke yi. (K. Mag. 18:11) Ko da yake muna bukatar kuɗi don biyan bukatunmu na yau da kullum, bautarmu ga Jehobah ta fi tara kuɗi muhimmanci. (M. Wa. 7:12; Ibran. 13:5) Ba ma barin neman kuɗi ya sa mu ja da baya a bautarmu ga Jehobah. A maimakon haka, muna yin duk abin da za mu iya yi a bautarmu ga Jehobah. Mun san cewa, idan muka riƙe aminci, Jehobah zai albarkace mu kuma za mu yi rayuwa a sabuwar duniya.—Zab. 4:8.
NAFTALI
12. Ta yaya mai yiwuwa abin da Yakubu ya faɗa game da Naftali ya cika? (Farawa 49:21) (Ka kuma duba akwatin.)
12 Karanta Farawa 49:21, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.b Yakubu ya ce Naftali zai yi “nagargarun zantattuka.” Mai yiwuwa yadda Yesu yake magana saꞌad da yake duniya ne ya cika wannan annabcin. Yesu yana yawan zama a birnin Kafarnahum da ke yankin zuriyar Naftali. Shi ya sa ake cewa a garin ne ya yi girma. (Mat. 4:13; 9:1; Yoh. 7:46) Ƙari ga haka, Ishaya ya annabta cewa Yesu zai zama kamar “babban haske” ga mutanen Zebulun da Naftali. (Isha. 9:1, 2) Kuma ta wurin koyarwarsa, Yesu ya zama “haske na gaskiya wanda yake ba da haske ga dukan mutane”.—Yoh. 1:9.
13. Ta yaya za mu riƙa yin maganar da za ta faranta wa Jehobah rai?
13 Mene ne za mu iya koya? Jehobah yana lura da abubuwan da muke faɗa da kuma yadda muke faɗan su. Ta yaya za mu yi “nagargarun zantattukan” da za su faranta wa Allah rai? Hanya ɗaya da za mu iya yin hakan ita ce ta wurin faɗin gaskiya. (Zab. 15:1, 2) Za mu kuma ƙarfafa ꞌyanꞌuwa idan muna saurin yaba musu, maimakon mu kushe su ko kuma mu yi gunaguni a kan abin da suke yi. (Afis. 4:29) Ban da haka, za mu iya koyan hanyoyi dabam-dabam da za mu iya tattaunawa da mutane da zai sa mu sami damar yi musu waꞌazi.
YUSUF
14. Ta yaya annabcin da aka yi game da Yusuf ya cika? (Farawa 49:22, 26) (Ka kuma duba akwatin.)
14 Karanta Farawa 49:22, 26. Yakubu ya yi alfahari da Yusuf, kuma Jehobah ya ‘keɓe shi daga ꞌyanꞌuwansa’ don ya yi wasu abubuwa na musamman. Yakubu ya ce Yusuf reshe “ne mai ba da ꞌyaꞌya”. Yakubu da kansa ne bishiyar, Yusuf kuma reshe daga jikinsa. Yusuf ne ɗan farin Rahila, matan da Yakubu ya fi ƙauna. Yakubu ya annabta cewa Yusuf ne zai sami gādon ɗan fari maimakon Ruben wanda shi ne ɗan farin Laiꞌatu. (Far. 48:5, 6; 1 Tar. 5:1, 2) Annabcin da Yakubu ya yi ya cika a lokacin da ꞌyaꞌyan Yusuf guda biyu, Ifrayim da Manasse, suka sami gādon yankuna dabam-dabam.—Far. 49:25; Yosh. 14:4.
15. Mene ne Yusuf ya yi saꞌad da aka wulakanta shi?
15 Yakubu kuma ya ce masu harbi sun kai wa Yusuf hari, suka harbe shi kuma suka tsananta masa. (Far. 49:23) Yakubu yana magana ne game da ꞌyanꞌuwan Yusuf da suka yi kishinsa a dā, kuma suka sa ya sha wahala sosai. Amma abin da suka yi, bai sa Yusuf ya tsane su ba kuma bai ɗaura wa Jehobah laifin abin da ya same shi ba. A maimakon haka, Yakubu ya ce, bakan Yusuf ‘ya tsaya daram, hannuwansa sun sami ƙarfi.’ (Far. 49:24) Hakan ya nuna cewa Yusuf yana da ikon da zai rama mugunta da ꞌyanꞌuwansa suka yi masa, amma bai yi hakan ba. Yusuf ya dogara ga Jehobah a lokacin da yake fama da matsaloli. Ya gafarta wa ꞌyanꞌuwansa kuma ya yi musu alheri. (Far. 47:11, 12) Matsalolin da Yusuf ya fuskanta sun taimaka masa ya zama mutumin kirki. (Zab. 105:17-19) Hakan ya sa Jehobah ya yi amfani da shi a hanyoyi dabam-dabam masu muhimmanci.
16. Idan muna fama da matsaloli, ta yaya labarin Yusuf zai taimaka mana?
16 Mene ne za mu iya koya? Kada mu yarda ƙaunarmu ga Jehobah da kuma ꞌyanꞌuwanmu ta yi sanyi. Mu tuna cewa Jehobah zai iya ƙyale mu a lokacin da muke fuskantar matsaloli don mu koyi wani darassi mai kyau. (Ibran. 12:7) Hakan zai iya taimaka mana mu koyi wasu halayensa kamar jinƙai da gafartawa. (Ibran. 12:11) Idan muka jimre, Jehobah zai albarkace mu kamar yadda ya yi wa Yusuf.
BENYAMIN
17. Ta yaya annabcin da aka yi game da Benyamin ya cika? (Farawa 49:27) (Ka kuma duba akwatin.)
17 Karanta Farawa 49:27. Yakubu ya annabta cewa zuriyar Benyamin za su zama da ƙarfin yaƙi kamar kyarkeci. (Alƙa. 20:15, 16; 1 Tar. 12:2) Sarkin Israꞌila na farko, wato Shawulu, ya fito daga zuriyar Benyamin ne. Shi gwarzo ne a fagen yaƙi kuma ya yaƙi Filistiyawa. (1 Sam. 9:15-17, 21) Shekaru da yawa bayan haka ma, Sarauniya Esta da Mordekai da suka fito daga zuriyar Benyamin sun ceci Israꞌilawa daga kisan kāre dangi da aka so a yi musu.—Esta 2:5-7; 8:3; 10:3.
18. Ta yaya za mu yi koyi da irin amincin da zuriyar Benyamin suka nuna?
18 Mene ne za mu iya koya? Babu shakka, mutanen Benyamin sun yi farin ciki sosai da suka ga wani daga zuriyarsu, wato Shawulu, ya zama sarki. Amma daga baya, Jehobah ya naɗa Dauda daga zuriyar Yahuda ya zama sarki. Duk da haka, zuriyar Benyamin sun ci gaba da ba shi goyon baya. (2 Sam. 3:17-19) Kuma shekaru da yawa bayan hakan, lokacin da kabilu goma suka yi wa sarki tawaye, zuriyar Benyamin sun ci gaba da kasancewa da aminci ga sarkin da Jehobah ya zaɓa da kuma zuriyar Yahuda. (1 Sar. 11:31, 32; 12:19, 21) Kamar yadda zuriyar Benyamin suka yi, bari mu ma mu ci gaba da goyon bayan waɗanda Jehobah ya zaɓa su yi mana ja-goranci.—1 Tas. 5:12.
19. Ta yaya annabce-annabcen da Yakubu ya yi kafin ya mutu za su amfane mu?
19 Abubuwan da Yakubu ya faɗa kafin ya mutu za su amfane mu sosai. Annabce-annabcen da Yakubu ya yi da kuma yadda suka cika da muka tattauna sun tabbatar mana cewa, sauran annabce-annabcen da Jehobah ya yi a cikin Kalmarsa za su cika. Kuma idan muka yi laꞌakari da yadda Yakubu ya albarkaci ꞌyaꞌyansa, hakan zai taimaka mana mu fahimci yadda za mu riƙa faranta wa Jehobah rai.
WAƘA TA 128 Mu Jimre Har Ƙarshe
a Saꞌad da Yakubu yake sa wa Ruben, da Simeyon, da Lawi, da Yahuda albarka, ya yi haka ne daga babba zuwa ƙarami, amma saꞌad da yake sa wa sauran ꞌyaꞌyansa takwas albarka, bai yi hakan ba.
b Farawa 49:21: “Naftali ɗan barewa ne sakakke: Yana ba da nagargarun zantattuka.”