BABI NA 3
“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki ne” Jehobah
1, 2. Wane wahayi ne annabi Ishaya ya gani, kuma mene ne yake koya mana game da Jehobah?
ISHAYA ya cika da mamaki, da ɗaukaka, da tsoron Allah domin abin da ya gani a gabansa, wato wahayi daga Allah. Kamar a zahiri! Daga baya, Ishaya ya rubuta cewa ya “ga Ubangiji” zaune a kan kursiyi. Sitirar Jehobah ta cika haikali na Urushalima.—Ishaya 6:1, 2.
2 Ishaya kuma ya cika da tsoro domin abin da ya ji, wato waƙa mai ƙarfi ta cika haikali har sai da tushen ya girgiza. Waƙar tana fitowa ne daga mala’iku masu babban matsayi, halittu na ruhu. Muryoyinsu ya furta kalmomin ɗaukaka: “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Yahweh Mai Runduna! Dukan duniya tana cike da ɗaukakarsa!” (Ishaya 6:3, 4) Rera “mai tsarki” sau uku ya ba ta nanaci na musamman da ya dace, domin tsarkaka ta Jehobah ta fi gaban a bayyana. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:8) An nanata tsarkakar Jehobah a dukan cikin Littafi Mai Tsarki. Ɗarurruwan ayoyi sun haɗa sunansa da kalmar nan “tsarki” da kuma “tsarkaka.”
3. Ta yaya kuskure game da tsarkakar Jehobah take sa mutane su guji Allah maimakon su yi kusa da shi?
3 Don haka, ɗaya daga cikin abubuwa na farko da Jehobah yake so mu fahimta shi ne cewa shi mai tsarki ne. Duk da haka, da yawa a yau wannan yana koransu. Wasu mutane cikin kuskure suna haɗa tsarkaka da adalcin kai ko kuma tsarkaka ta ƙarya. Mutane da suke kokawa da jin ba su da daraja, tsarkakar Allah za ta riƙa tsoratar da su maimakon rinjayarsu. Za su tsorata cewa ba za su taɓa cancanta su kusaci wannan Allah mai-tsarki ba. Saboda haka, da yawa suna guje wa Allah domin tsarkakarsa. Wannan abin baƙin ciki ne, domin tsarkakar Allah da gaske ita ce dalilin matsowa kusa da shi. Me ya sa? Kafin mu amsa wannan tambayar, bari mu tattauna abin da tsarkaka ta gaskiya take nufi.
Mecece Tsarkaka?
4, 5. (a) Mece ce “tsarkaka” take nufi, kuma mecece ba ta nufa ba? (b) A waɗanne hanyoyi biyu ne masu muhimmanci Jehobah ya kasance “keɓaɓɓe”?
4 Domin Allah mai tsarki ne ba ya nufin cewa ya gamsu da kansa kawai, mai fahariya ne, ko kuma mai ba’a ne ga wasu. Maimakon haka, yana ƙyamar waɗannan halaye. (Karin Magana 16:5; Yakub 4:6) To, mene ne ainihi kalmar nan “tsarki” take nufi? A Ibrananci na Littafi Mai Tsarki, kalmar an samo ta ne daga furci da take nufin “keɓaɓɓe.” A bauta, “tsarki” yana nufin abin da aka keɓe daga amfani na yau da kullum, ko kuma da aka riƙe don bauta. Tsarkaka kuma na ba da ma’ana sosai ta tsabta. Ta yaya wannan kalmar take ga Jehobah? Tana nufi ne cewa “keɓaɓɓe” ne da nesa daga gare mu ajizai?
5 Ba haka ba ne. “Mai Tsarki na Isra’ila,” Jehobah ya kwatanta kansa cewa yana tare da mutanensa, ko da yake masu zunubi ne su. (Ishaya 12:6; Hosiya 11:9) Saboda haka, tsarkakarsa ba ta sa ya yi nisa ba. To, ta yaya ne yake “keɓaɓɓe”? A hanyoyi biyu masu muhimmanci. Na ɗaya, keɓaɓɓe ne daga dukan halittu saboda shi kaɗai ne Maɗaukaki Duka. Tsabtarsa cikakkiya ce ba ta da iyaka. (Zabura 40:5; 83:18) Na biyu, Jehobah keɓaɓɓe ne gabaki ɗaya daga zunubi, kuma wannan abin ƙarfafa ne. Me ya sa?
6. Me ya sa za mu sami ƙarfafa daga keɓewar Jehobah gabaki ɗaya daga zunubi?
6 Muna rayuwa ne a duniya da ake rashin tsarki na gaske. Kome na jama’a da suke a ware daga Allah, ya gurɓata a wata hanya, zunubi ya lalata shi da kuma ajizanci. Dukanmu muna bukatar mu yaƙi zunubi da ke cikinmu. Kuma dukanmu muna cikin haɗarin da zunubi zai iya nasara a kanmu idan muka sake. (Romawa 7:15-25; 1 Korintiyawa 10:12) Jehobah ba ya cikin irin wannan haɗarin. Tun da keɓaɓɓe ne daga zunubi, ɗigon zunubi ba zai taɓa taɓa shi ba. Wannan ya sake tabbatar mana cewa Jehobah Uba ne nagari, domin yana nufin cewa matabbaci ne ƙwarai. Ba kamar ubanni ba na mutane masu zunubi, Jehobah ba zai taɓa zama marar gaskiya ba, marar kamewa, ko kuma azzalumi. Tsarkakarsa ta sa irin wannan abin ba zai taɓa yiwuwa ba. A wasu lokatai Jehobah ya yi rantsuwa da tsarkakarsa, wannan ya sa rantsuwar abin dogara. (Amos 4:2) Wannan ba tabbaci ba ne?
7. Me ya sa za a iya cewa tsarkaka yanayi ne na Jehobah?
7 Tsarkaka yanayin Jehobah ne. Me wannan yake nufi? Alal misali: Ka lura da kalmomin nan “ɗan Adam” da kuma “ajizi.” Ba za ka iya kwatanta na farkon ba, ba tare da amfani da na biyun ba. Ajizanci ya cika mu kuma yana rinjayar dukan abin da muke yi. Yanzu ka lura da wannan kalmomi biyun masu bambanci, wato “Jehobah” da “tsarki.” Tsarkaka ta cika Jehobah. Kome game da shi mai tsabta ne, mai kyau, kuma nagari. Ba za mu zo ga ainihin sanin Jehobah ba idan ba tare da fahimtar wannan muhimmiyar kalmar ba, wato “tsarki.”
“An Keɓe da Tsarki ga” Jehobah
8, 9. Mene ne ya nuna cewa Jehobah yana taimakon mutane ajizai su zama masu tsarki a ƙaramar hanya?
8 Tun da Jehobah yana riƙe da halin tsarki, za a iya cewa shi ne tushen tsarkaka. Bai ɓoye wannan halin ba cikin son kai; ya ba wa wasu, kuma ya yi hakan hannu sake. Sa’ad da Allah ya yi magana da Musa ta wajen mala’ika a kurmi mai ci da wuta, har ƙasar wajen ta tsarkaka domin nasabarta da Jehobah!—Fitowa 3:5.
9 Mutane ajizai za su iya zama masu tsarki da taimakon Jehobah? Hakika, a ƙaramar hanya. Allah ya ba mutanensa Isra’ila damar zama “al’ummar da aka keɓe da tsarki.” (Fitowa 19:6) Ya albarkaci wannan al’ummar da tsarin bauta mai tsarki, mai tsabta, kuma mai kyau. Tsarki ne jigon da ya bayyana sau da yawa cikin Dokar Musa. Hakika, babban firist yana sanye da allo na sahihiyar zinariya a gaban rawaninsa, inda ko waye zai ga walƙiyarta. Kuma an zana rubutu irin ta hatimi a kansa: “An keɓe da tsarki ga Yahweh.” (Fitowa 28:36) Saboda haka mizani mai girma na tsabta zai bambance bautarsu, hakika, hanyar rayuwarsu. Jehobah ya gaya musu: “Ku zama masu tsarki, gama ni Yahweh Allahnku ni mai tsarki ne.” (Littafin Firistoci 19:2) Muddin Isra’ilawa suna raye bisa gargaɗin Allah iyakar abin da zai yiwu ga mutane ajizai, masu tsarki ne a ƙaramar hanya.
10. Idan ya zo ga tsarkaka, wane bambanci ne yake tsakanin Isra’ila ta dā da kuma al’ummai da suka kewaye su?
10 Wannan nanaci a kan tsarkaka bambanci ne ƙwarai da bautar wasu al’ummai da suka kewaye Isra’ila. Waɗannan al’umman arna suna bauta wa alloli waɗanda wanzuwarsu ma ƙarya ce da ruɗu, alloli da aka kwatanta su masu nuna ƙarfi ne, ’yan haɗama, kuma karuwai. Ba su da tsarki ta kowacce hanya. Bautar irin waɗannan alloli tana sa mutane su zama marasa tsarki. Saboda haka, Jehobah ya yi wa mutanensa kashedi su ware kansu daga bautar arna da kuma ayyukan addinansu marasa tsabta.—Littafin Firistoci 18:24-28; 1 Sarakuna 11:1, 2.
11. Ta yaya tsarkakar sashen ƙungiyar Jehobah da ke sama ta bayyana (a) a mala’iku? (b) a mala’iku seraf? (c) a Yesu?
11 Duk da ƙoƙarin da al’ummar Isra’ila ta yi, tsarkakarta ba ta zo kusa da na sashen ƙungiyar Allah da ke sama ba. Miliyoyin ruhohi waɗanda suke bauta wa Allah da aminci an kira su “mala’ikunsa masu tsarki.” (Yahuda 14) Suna nuna hasken, kyakkyawar tsarkakar Allah. Ka tuna kuma da mala’iku seraf da Ishaya ya gani a wahayi. Abin da suke faɗa a waƙarsu ta nuna cewa waɗannan halittu na ruhu masu girma suna muhimmin aiki wajen sanar da tsarkakar Jehobah a dukan sararin sama. Wani halittar ruhu, da ya fi dukan waɗannan shi ne makaɗaici Ɗan Allah. Yesu shi ne mafi girma wajen nuna tsarkakar Jehobah. Shi ya sa an san shi da “Mai Tsarkin nan na Allah.”—Yohanna 6:68, 69.
Suna Mai Tsarki, Ruhu Mai Tsarki
12, 13. (a) Me ya sa aka kwatanta sunan Allah da tsarki? (b) Me ya sa dole ne a tsarkake sunan Allah?
12 To, sunan Allah fa? Kamar yadda muka gani a Babi na 1, sunan ba laƙabi ba ne ko kuma lamba. Yana wakiltan Jehobah Allah, ya ƙunshi dukan halayensa. Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “Sunansa Mai Tsarki ne.” (Ishaya 57:15) A Dokar Musa babban zunubi ne a saɓa wa sunan Allah. (Littafin Firistoci 24:16) Ka lura da abin da Yesu ya sa farko a cikin addu’a: “Ubanmu wanda yake cikin sama, a kiyaye sunanka da tsarki.” (Matiyu 6:9) A tsarkake abu yana nufin a keɓe shi domin ibada, a riƙa ɗaukarsa da tsarki. Amma me ya sa abin da yanayinsa ma mai tsabta ne kamar sunan Allah zai bukaci a tsarkake shi?
13 An tuhumi sunan Allah mai tsarki, an lalata sunan da ƙarya da tsegumi. A Adnin, Shaiɗan ya yi ƙarya game da Jehobah wanda ya nuna cewa Jehobah ba Mamallaki ba ne mai gaskiya. (Farawa 3:1-5) Tun daga lokacin, Shaiɗan mai mulkin wannan duniyar, marar tsarki, ya tabbata cewa wannan ƙarya game da Allah ta yaɗu. (Yohanna 8:44; 12:31; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:9) Addinai suna kwatanta Allah cewa mugun sarki ne, yana nesa, kuma azzalumi ne. Suna da’awar suna da goyon bayansa cikin zubar da jini a yaƙe-yaƙensu. Sau da yawa ana bai wa ra’i na bayyanau darajar ayyukan halitta da Allah ya yi. Hakika, an ɓata sunan Allah ƙwarai da gaske. Dole ne a tsarkake shi; dole ne a mai da masa da darajarsa. Muna sa ran ganin ranar da Jehobah zai wanke sunansa daga zargi har abada. Zai yi amfani da Mulkin da Yesu ne sarkinsa wajen cim ma hakan. Muna farin cikin yin duk abin da ya kamata don hakan ya faru.
14. Me ya sa ake kiran ruhun Allah mai tsarki, kuma me ya sa saɓo ga ruhu mai tsarki yana da haɗari?
14 Da akwai abin da yake da nasaba sosai da Jehobah da akan iya kira mai tsarki, wato ruhunsa, ko kuma ikon aiki. (Farawa 1:2) Jehobah ya yi amfani da ƙarfinsa da ya fi kome ya kammala nufe-nufensa. Dukan abin da Allah ya yi, yana yi ne a hanya mai tsarki, mai kyau, mai tsabta, daidai ne aka kira ikon aikinsa ruhu mai tsarki ko kuma ruhun tsarkaka. (Luka 11:13; Romawa 1:4) Yi wa ruhu mai tsarki saɓo, wanda ya ƙunshi saɓa wa nufin Jehobah da gangan, yana nufin zunubi da ba a gafartawa.—Markus 3:29.
Abin da Ya Sa Tsarkakar Jehobah Take Jawo Mu Gare Shi
15. Yaya ya kamata mu ji game da Jehobah da yake shi mai tsarki ne?
15 Ba shi da wuya a fahimci dalilin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce mu ji tsoron Allah domin shi mai tsarki ne. Alal misali, Zabura 99:3 ta ce: “Bari su yabi Sunansa mai girma mai ban tsoro! Mai tsarki ne shi!” Hakan yana nufin cewa mu daraja shi da kuma sunansa sosai. Daidai ne mu ji hakan, tun da tsarkakar Jehobah ta fi nesa da mu. Tsabtacce mai haskaka, mai ɗaukaka. Duk da haka, bai kamata mu guje shi ba. Maimakon haka, ɗaukaka tsarkakar Allah yadda ta dace za ta jawo mu kusa da shi. Me ya sa?
16. (a) Ta yaya tsarkaka take da alaƙa da kyau? Ka ba da misali. (b) Ta yaya kwatanci na wahayi na Jehobah ya nanata tsabta, kyau da kuma haske?
16 Abu ɗaya shi ne, Littafi Mai Tsarki ya dangana tsarkaka da kyau. A Zabura 96:6, mun karanta game da wuri mai tsarki na Allah, “ƙarfi da jamali suna cikin tsatsarkan wurinsa.” Jamali yana rinjaya. Alal misali, dubi hoto da yake shafi na 33. Wannan yanayin bai rinjaye ka ba? Me ya sa yake da ban sha’awa? Ka lura da yadda ruwan yake da kyau. Har iskar ma dole ne ta kasance da tsabta, kuma gajimare yana da kyau kuma haske yana haskakawa. A yanzu, idan aka lalata wannan yanayi, wato tabkin ya cika da juji, itatuwa da duwatsu an ɓata su da rubuce-rubuce, iskar kuma ta cika da hayaƙi, ba zai rinjaye mu ba kuma; za mu guje shi. Muna danganta kyau da tsabta da kuma haske. Waɗannan kalmomin za a iya amfani da su wajen kwatanta tsarkakar Jehobah. Ba mamaki da kwatancin Jehobah na wahayi yake rinjayarmu! Yana haskakawa, yana walƙiya kamar duwatsu masu daraja, yana haske kamar wuta ko kuma ƙarafa masu tamani, haka kyan Allah mai tsarki yake.—Ezekiyel 1:25-28; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 4:2, 3.
Kyau yana rinjayarmu, haka ma ya kamata tsarkaka ta yi
17, 18. (a) Ta yaya wahayin Ishaya ya taɓa shi da farko? (b) Yaya Jehobah ya yi amfani da mala’ika seraf ya ƙarfafa Ishaya, kuma mene ne muhimmancin abin da mala’ikan ya yi?
17 Amma, ya kamata tsarkaka ta Allah ta sa mu ji muna kasa da shi ne? Hakika, amsar E, ce. Tun da, muna kasa da Jehobah, wannan ma rage magana ce ƙwarai. Sanin wannan ya kamata ne ya ware mu daga gare shi? Ka dubi yadda Ishaya ya ji, da jin seraf suka sanar da tsarkakar Jehobah. “Sai na ce, “Kaitona! Tawa ta ƙare! Gama kowace maganar bakina zunubi ce, ina kuma zama tare da mutanen da kowace maganar bakinsu zunubi ce. Amma duk da haka, idanuna sun ga Sarki, sun ga Yahweh Mai Runduna!” (Ishaya 6:5) Hakika, tsarkakar Jehobah da ba ta da iyaka ta nuna wa Ishaya yadda yake mai zunubi kuma ajizi. Da farko, wannan amintaccen mutumin ya razana. Amma Jehobah bai ƙyale shi a wannan yanayin ba.
18 Mala’ika seraf ya ƙarfafa annabin. Ta yaya? Wannan ruhu mai ɗaukaka ya yi firiya zuwa bagadi, ya ɗauko garwashi, kuma ya taɓa leɓunan Ishaya da shi. Wannan za ka ji yana da zafi maimakon ƙarfafawa. Amma, ka tuna cewa wannan wahayi ne, da yake cike da ma’ana ta alama. Ishaya, Bayahude mai aminci ya san cewa ana yin hadaya kowacce rana a bagadi na haikali domin a nemi gafarar zunubi. Kuma mala’ikan ya tunasar da annabin cewa ko da yake shi ajizi ne, “mai-leɓuna marasa-tsarki,” zai iya kasancewa da tsarki a gaban Allah.a Jehobah yana shirye ya ɗauki ajizi, mutum mai zunubi da tsarki, aƙalla a ƙaramar hanya.—Ishaya 6:6, 7.
19. Ta yaya za mu iya zama masu tsarki a ƙaramar hanya, ko da yake muna ajizai?
19 Haka yake a yau. Dukan waɗancan hadayu da aka miƙa a kan bagadi na Urushalima hoto ne na abu babba da ke zuwa, wato hadaya ɗaya kamiltacciya, da Yesu Kristi ya miƙa a shekara ta 33 A. Z. (Ibraniyawa 9:11-14) Idan da gaske mun tuba daga zunubanmu, mun gyara hanyarmu da ba ta dace ba, kuma muka ba da gaskiya a wannan hadayar, an gafarta mana. (1 Yohanna 2:2) Mu ma za mu iya kasancewa da tsabta a gaban Allah. Saboda haka, manzo Bitrus ya tunasar da mu: “A rubuce yake cewa, ‘Sai ku zama da tsarki, gama ni mai tsarki ne.’ ” (1 Bitrus 1:16) Ka lura da cewa Jehobah bai ce dole mu zama masu tsarki kamarsa ba. Bai taɓa bukatar abin da ba zai yiwu ba a gare mu. (Zabura 103:13, 14) Maimako, Jehobah ya ce mana mu zama masu tsarki domin shi ma mai tsarki ne. Tun da yake mu “ ’ya’ya waɗanda Allah yake ƙauna” ne, muna ƙoƙarin mu yi koyi da shi iyakar gwargwadon iyawarmu mu mutane ajizai. (Afisawa 5:1) Saboda haka, iya zama tsarkaka aba ce da za a ci gaba da yi. Yayin da muke girma a ruhaniya, muna ƙoƙarin “zama da cikakken tsarki” a kowacce rana.—2 Korintiyawa 7:1.
20. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu fahimci cewa za mu iya kasancewa da tsabta a idanun Allahnmu mai tsarki? (b) Yaya ya taɓa Ishaya da ya fahimci cewa an gafarta masa zunubansa?
20 Jehobah, Allah mai tsarki, yana ƙaunar abin da yake nagari kuma mai tsabta. Yana ƙyamar zunubi. (Habakkuk 1:13) Amma ba ya ƙyamarmu. Idan muka ɗauki zunubi kamar yadda ya ɗauke shi, wato muna ƙin abin da ke munana, muna ƙaunar abin da ke mai kyau kuma mu yi ƙoƙari mu bi kamiltaccen sawun Kristi Yesu, Jehobah zai gafarta mana zunubanmu. (Amos 5:15; 1 Bitrus 2:21) Sa’ad da muka fahimci cewa za mu iya kasancewa da tsabta a idanun Allahnmu mai tsarki, zai iya taɓa mu ƙwarai. Ka tuna cewa, tsarkakar Jehobah da farko ta tunasar da Ishaya rashin tsarkinsa. Ya yi kuka: “Kaitona!” Amma da ya fahimci cewa an gafarta masa zunubansa, ra’ayinsa ya canja. Da Jehobah ya nemi wanda zai ba da kai ya aika, Ishaya ya amsa ba tare da ɓata lokaci ba, ko da yake bai san abin da zai ƙunsa ba. Ya ɗaga murya: “Ga ni nan, ka aike ni!”—Ishaya 6:5-8.
21. Mene ne tushen tabbacinmu cewa za mu iya gina halaye na tsarkaka?
21 An halicce mu a kamanin Allah mai tsarki, an ba mu ɗabi’a da kuma fahimtar abubuwa na ruhaniya. (Farawa 1:26) Dukanmu muna da iyawa na zama tsarkaku. Yayin da muke ƙoƙari mu koyi tsarkaka, Jehobah zai yi farin ciki ya taimaka mana. A wannan hanyar za mu kusaci Allahnmu mai tsarki. Bugu da ƙari, yayin da muka bincika halayen Jehobah a babobi da suke gaba, za mu ga cewa da akwai dalilai masu ƙarfi da yawa na kusantarsa!
a Furucin nan “maganar bakinsa zunubi ce,” wato (leɓuna marasa tsarki) ya dace, domin leɓuna sau da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki a hanya ta alama na nufin magana ko kuma yare. A dukan ajizancin mutane, yawancin zunubanmu za a iya samunsu a yadda muke amfani da furuci ne.—Misalai 10:19; Yakub 3:2, 6.