Ka Kusaci Allah
“Ni Ubangiji Allahnku Mai-Tsarki Ne”
Levitikus Sura 19
“MAI-TSARKI, Mai-tsarki, Mai-tsarki, Ubangiji Allah.” (Ru’ya ta Yohanna 4:8) Da waɗannan kalaman, Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Jehobah Mai Tsarki ne, wanda ya nuna cewa tsarkakarsa da tsabtarsa ta fi gaban a bayyana. Jehobah keɓaɓɓe ne gabaki ɗaya daga zunubi; babu yadda zai iya yin zunubi a kowace hanya. Hakan na nufi ne cewa ’yan adam ba za su iya more dangantaka da Allah mafi tsarki ba? A’a! Bari mu tattauna kalamai da ke cike da bege da aka rubuta a Levitikus sura 19.
Jehobah ya gaya wa Musa: “Sai ka yi magana da dukan jama’ar ’ya’yan Isra’ila.” Kalaman da ya faɗa bayan haka sun shafi kowa a al’ummar. Menene Musa zai gaya musu? Allah ya ci gaba da cewa: “Ka ce masu, Sai ku zama masu-tsarki: gama ni Ubangiji Allahnku mai-tsarki ne.” (Aya ta 2) Kowane Ba’isra’ile yana bukatan ya kasance da tsarki. Kalaman nan “ku zama” sun nuna cewa wannan maganar ba shawara ba ce amma umurni ne. Allah yana bukatar abin da ya fi ƙarfin su ne?
Ka lura cewa Jehobah bai bayyana tsarkinsa don mu zama masu tsarki daidai kamar sa ba, amma ya yi haka ne a matsayin dalilin da ya sa ya kamata mu zama masu tsarki. Wato, Jehobah bai gaya wa Isra’ilawa ajizai da suke bauta masa su kasance da tsarki daidai kamar sa ba. Hakan ba zai yiwu ba. Jehobah, “Mai-tsarkin,” ya ɗara kowa a tsarki. (Misalai 30:3) Amma, domin Jehobah mai tsarki ne, yana so masu bauta masa su kasance da tsarki, wato, iya gwargwadon ’yan adam ajizai. A waɗanne hanyoyi ne za su iya kasancewa masu tsarki?
Bayan ya ba da umurnin su kasance da tsarki, Jehobah ta wurin Musa ya bayyana bukatun da suka shafi dukan fasalolin rayuwa ta yau da kullum. Kowane Ba’isra’ile yana bukatan ya yi biyayya ga irin waɗannan mizanan da ke gaba: yin biyayya ga iyaye da tsofaffi (ayoyi 3, 32); ya nuna sanin ya kamata ga kurame, da makafi, da sauran naƙasassu (ayoyi 9, 10, 14); ya nuna gaskiya da rashin son kai a sha’aninsa da mutane (ayoyi 11-13, 15, 35, 36); kuma ya so ’yan’uwansa masu bauta wa Allah kamar kansa. (Aya ta 18) Ta yin biyayya ga waɗannan da sauran mizanai, Ba’isra’ilan za ya “zama mai-tsarki ga Allahn[sa].”—Littafin Lissafi 15:40.
Umurnin da aka bayar game da tsarki ya ba mu ƙarin haske game da tunani da kuma hanyoyin Jehobah Allah. Hakika, mun koyi cewa idan muna son mu kasance da matsayi mai kyau da Allah, muna bukatan mu yi rayuwar da ta jitu da mizanansa na hali mai tsarki. (1 Bitrus 1:15, 16) Ta wajen bin waɗannan mizanan, za mu iya more hanyar rayuwa mafi kyau.—Ishaya 48:17.
Umurnin da Jehobah ya bayar na kasancewa da tsarki ya nuna cewa ya tabbata da masu bauta masa. Jehobah ba ya bukatan fiye da abin da za mu iya yi. (Zabura 103:13, 14) Ya san cewa mu ’yan adam da ya halitta cikin siffarsa, za mu iya kasancewa tsarkakku, amma ba gabaki ɗaya ba. (Farawa 1:26) Hakan ya motsa ka ka ƙara koya game da yadda za ka kusaci Allah mai tsarki, Jehobah kuwa?
[Hotunan da ke shafi na 9]
Muna da damar kasancewa da tsarki