Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 5/15 pp. 26-28
  • Ka Biɗi “Tsarki Cikin Tsoron Allah”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Biɗi “Tsarki Cikin Tsoron Allah”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Za a Sami Hanya Mai Tsarki’
  • “Marasa-Tsarki Ba Za Su Bi Kanta Ba”
  • ‘Zaki Ba Zai Kasance A Wurin Ba’
  • Biɗar “Tsarki Cikin Tsoron Allah” na Kawo Albarka!
  • “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki ne” Jehobah
    Ka Kusaci Jehobah
  • “Ni Ubangiji Allahnku Mai-Tsarki Ne”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka Ci Gaba da Yin Tafiya a “Hanyar Tsarki”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • “Ku Zama da Tsarki”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 5/15 pp. 26-28

Ka Biɗi “Tsarki Cikin Tsoron Allah”

TA WAJEN nuna cewa Jehobah Allah mai tsarki ne wanda babu kamarsa, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai-tsarki, Mai-tsarki, Mai-tsarki ne, Ubangiji.” (Isha. 6:3; R. Yoh. 4:8) Kalmomin Ibraniyanci da Helenanci na “tsarki” suna nufin tsabta ta addini wanda ke keɓe mutum daga ƙazanta. Tsarkin Allah yana nuni ne ga ɗabi’a mai kyau wanda dole ne a gare shi.

Jehobah Allah mai tsarki, yana son waɗanda suke bauta masa su kasance masu tsarki, wato, su kasance da tsarki a jiki, a ɗabi’a da kuma a ruhaniya. Ko ba haka ba? Jehobah ya bayyana dalla-dalla a cikin Littafi Mai Tsarki cewa yana son mutanensa su kasance masu tsarki. Mun karanta hakan a cikin 1 Bitrus 1:16: “Ku za ku zama masu-tsarki; gama ni mai-tsarki ne.” Mutane ajizai za su iya yin koyi da tsarkin Jehobah? Ƙwarai kuwa, amma ba za su iya zama kamar Jehobah ba. Allah yana iya ɗaukanmu masu tsarki idan muna bauta masa da zuciya mai tsarki da kuma sa’ad da muke da dangantaka na kud da kud da shi.

To, ta yaya za mu kasance masu tsarki a duniya marar tsarki? Waɗanne halaye ne za mu guje wa? Waɗanne canje-canje ne wataƙila za mu yi a furcinmu da kuma halinmu? Bari mu ga abin da za mu koya game da wannan daga abin da Allah yake bukata daga Yahudawan da suke komawa ƙasarsu daga Babila a shekara ta 537 K.Z.

‘Za a Sami Hanya Mai Tsarki’

Jehobah ya annabta cewa mutanensa da suke zaman bauta a ƙasar Babila za su koma ƙasarsu. Annabcin maidowar ya ƙunshi wannan tabbacin: “A wurin kuwa za a tarasda karabka da hanya kuma; za a ce da ita Hanyar tsarki.” (Isha. 35:8a) Waɗannan kalaman sun nuna cewa Jehobah ya buɗe wa Yahudawa hanyar komawa gida kuma ya tabbatar da su cewa zai kāre su a kan hanya.

Ga bayinsa na wannan zamanin da suke duniya, Jehobah ya buɗe ‘Hanya mai tsarki’ wadda ta fitar da su daga Babila Babba, daular duniya ta addinin ƙarya. A shekara ta 1919 ya ’yanta shafaffun Kiristoci daga yin tarayya da addinin ƙarya, kuma sun tsabtace bautarsa daga dukan wata koyarwa ta ƙarya. A matsayinmu na masu bauta wa Jehobah a yau, muna more mahalli na ruhaniya mai tsabta a inda muke bauta wa Jehobah kuma muna da dangantaka mai kyau da shi da kuma mutane.

“Ƙaramin garke” na shafaffun Kiristoci da kuma “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki” sun zaɓi su bi hanya mai tsarki kuma suna gayyatar wasu. (Luka 12:32; R. Yoh. 7:9; Yoh. 10:16) ‘Hanya mai tsarki’ tana buɗe ga dukan waɗanda suke son su “miƙa jikunan[su] hadaya mai-rai mai-tsarki, abin karɓa ga Allah.”—Rom. 12:1.

“Marasa-Tsarki Ba Za Su Bi Kanta Ba”

A shekara ta 537 K.Z., Yahudawan da za su koma ƙasarsu suna bukatar su cika wata bukata mai muhimmanci. Game da waɗanda suka cancanci su bi ‘Hanya mai tsarki,’ Ishaya 35:8b ta ce: “Marasa-tsarki ba za su bi kanta ba; amma za ta kasance domin waɗannan; masu-tafiya, i, har marasa-wayo, ba za su ɓata a ciki ba.” Tun da yake dalilin da ya sa Yahudawa za su koma Urushalima shi ne don su sake kafa bauta ta gaskiya, mutane masu son kai, waɗanda ba sa daraja abubuwa masu tsarki, ko kuwa waɗanda suke yin abin da bai da kyau ba za su kasance a wurin ba. Waɗanda za su koma ɗin suna bukatar su riƙe mizanan Jehobah na ɗabi’a sosai. Waɗanda suke son su sami tagomashin Jehobah a yau suna bukatar su cika waɗannan mizanan. Dole ne su biɗi “tsarki cikin tsoron Allah.” (2 Kor. 7:1) Waɗanne ayyuka marasa tsabta ne muke bukatar mu guje ma wa?

Manzo Bulus ya rubuta cewa: “Ayyukan jiki fa a bayyane su ke, fasikanci ke nan, ƙazanta, lalata.” (Gal. 5:19) Fasikanci ya ƙunshi duk wani sashe na jima’i wanda ya haɗa da yin amfani da al’aura a tsakanin waɗanda ba su auri juna ba. Lalata ya ƙunshi “fajirci; iskanci; rashin kunya, da batsa.” Fasikanci da lalata sun saɓa wa tsarkin da Jehobah yake da shi. Saboda haka, dukan waɗanda suka ci gaba da yin su ba za a ƙyale su su zama sashen ikilisiyar Kirista ba ko kuma a yi musu yankan zumunci. Hakan ya shafi dukan waɗanda suke aikata mugun ƙazanta, wato, “dukan ƙazanta tare da kwaɗayi.”—Afis. 4:19.

“Ƙazanta” kalma ce da ta ƙunshi zunubai masu yawa. Kalmar ta Helenanci tana nufin duk wani rashin tsarki a ɗabi’a, a magana, da kuma dangantaka ta ruhaniya. Ta haɗa da yin wasu abubuwa marar tsarki da wataƙila ba zai sa a hukunta mutum ba.a Amma waɗanda suke aikata waɗannan abubuwa marar tsarki suna biɗar tafarki mai tsarki ne?

A ce wani Kirista ya soma kallon hotunan batsa a ɓoye. A hankali a hankali, sa’ad da ya soma tunanin abubuwa marar tsarki, sai hakan ya soma yi wa ƙudurinsa na kasance mai tsarki a gaban Jehobah zagon ƙasa. Wataƙila halinsa bai lalace ba har ya kai ga zama mugun ƙazanta, amma ya daina yin la’akari da ‘abin da ke da tsabta, abin da ke da kyakkyawan ambato; abin kirki, da yabo.’ (Filib. 4:8) Kallon hotunan tsirarun mutane ƙazanta ce kuma yana lalata dangantakar mutum da Allah. Bai kamata a ambata ƙazanta kowane iri a tsakaninmu ba.—Afis. 5:3.

Yi la’akari da wani misali. A ce wani Kirista yana yin tsaranci, wato, yin wasa da al’aura har ya biya bukatarsa na jima’i, wataƙila yana yin hakan da hotunan tsirarun mutane ko a’a. Ko da yake kalmar nan “tsaranci” ba ta cikin Littafi Mai Tsarki, ya kamata a yi shakka ne cewa hakan yana ɓata tunani da motsin rai na mutum? Idan mutum ya ci gaba da yin wannan ƙazantar hakan ba zai ɓata dangantakarsa sosai ba ne da Jehobah kuma ya zama marar tsarki a gaban Allah? Bari mu ci gaba da bin umurnin da manzo Bulus ya ba mu na “tsarkake kanmu daga dukan ƙazamtar jiki da ta ruhu” kuma mu ‘matar da gaɓaɓuwanmu fa waɗanda ke a duniya; fasikanci, ƙazanta, kwaɗayi, mugun guri, da sha’awa.’—2 Kor. 7:1; Kol. 3:5.

Wannan duniyar da ke ƙarƙashin sarautar Shaiɗan ta amince da halayen banza, kuma tana ƙarfafa yin su. Guje wa jarrabar yin abin da bai da tsarki yana iya zama ƙalubale. Dole ne Kiristoci na gaskiya su guje wa yin “irin tafiya da Al’ummai su ke yi kuma, cikin holoƙon azancinsu.” (Afis. 4:17) Sa’ad da muka guje wa halaye marar kyau a ɓoye ko a fili ne kawai Jehobah zai ƙyale mu mu ci gaba da bin ‘Hanya Mai Tsarki.’

‘Zaki Ba Zai Kasance A Wurin Ba’

More tagomashin Allah mai Tsarki, Jehobah, zai bukaci wasu su yi canje-canje a halinsu da furcinsu. Ishaya 35:9 ta ce: “Ba za a tarasda zaki a wurin ba, ba kuwa naman jeji mai-zafin rai da za ya hau ta kanta ba,” wato, “Hanyar tsarki.” A alamance, ana kwatanta mugayen mutane waɗanda suke yin maganganun banza da dabbobi. Irin su ba za su kasance a cikin sabuwar duniya ta Allah ba. (Isha. 11:6; 65:25) Saboda haka, waɗanda suke son su sami amincewar Allah suna bukatar su ƙyale waɗannan halaye na dabbobi kuma su biɗi tafarkin adalci.

Nassosi ya aririce mu: “Bari dukan ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage, su kawu daga gareku, tare da dukan ƙeta.” (Afis. 4:31) A Kolossiyawa 3:8 mun karanta cewa: “Ku kawasda dukan waɗannan; fushi, hasala, ƙeta, tsegumi, alfasha daga cikin bakinku.” Kalmar nan “zage-zage” wadda aka yi amfani da ita a Afisawa 4:31 tana nufin maganganun da ke ɓata wa mutum suna, masu ɓata rai ko kuwa masu ƙasƙantarwa.

A yau, maganganun banza masu ɓata rai, har da batsa, sun zama gama gari har ma a cikin gida. Ma’aurata suna gaya wa kansu ko yaransu maganganu masu ɓata rai ko kuwa masu ƙasƙantarwa. Bai kamata ana yin irin waɗannan maganganun a gidajen Kirista ba.—1 Kor. 5:11.

Biɗar “Tsarki Cikin Tsoron Allah” na Kawo Albarka!

Gata ne mu bauta wa Jehobah Allah mai tsarki! (Josh. 24:19) Aljanna ta ruhaniya wadda Jehobah ya saka mu a ciki abu ne mai tamani. Kasancewa da hali mai kyau a gaban Jehobah shi ne hanyar rayuwa mafi kyau.

Nan ba da daɗewa ba, aljanna ta duniya wadda Allah ya yi alkawarinta za ta zo. (Isha. 35:1, 2, 5-7) Waɗanda suke ɗokin ta kuma suka ci gaba da bin tafarki mai tsarki ne za su kasance a cikinta. (Isha. 65:17, 21) Ko ta yaya, bari mu ci gaba da bauta wa Allah da zuciya mai tsarki kuma mu ci gaba da kasancewa da dangantaka mai kyau da shi.

[Hasiya]

a Domin ganin bambancin “ƙazanta . . . da kwaɗayi” da “rashin tsabta,” ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2006, shafuffuka ta 29-31 na Turanci.

[Hoto a shafi na 26]

Menene ake bukata daga Yahudawa idan suna son su bi ‘Hanya mai Tsarki’?

[Hoto a shafi na 27]

Kallon hotunan tsirarun mutane yana ɓata dangantakar mutum da Jehobah

[Hoto a shafi na 28]

“Bari dukan . . . hargowa, da zage-zage, su kawu daga gareku”

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba