BABI NA 27
“Allah Mai Nagarta Ne da Babu Kamarsa!”
1, 2. Yaya yawar nagartar Allah, kuma wane nanaci Littafi Mai Tsarki ya yi game da wannan halin?
MANOMI ya dubi gonarsa ya yi murmushi domin hadari ya haɗu kuma ruwan fari yana saukowa a kan irinsa da suke da bukatar ruwa. A wata ƙasa kuma, tsofaffin abokanai, suna ci suna taɗi suna dariya da magariba yayin da suke sha’awar yadda rana take faɗuwa. A wani wurin kuma, mata da miji suna matuƙar farin ciki yayin da suke ganin ɗansu yana yin tetensa na farko.
2 Ko sun sani ko ba su sani ba, dukan waɗannan mutane suna amfana ne daga abu ɗaya—nagartar Jehobah Allah. Wasu masu addini sau da yawa suna cewa “Allah mai nagarta.” Littafi Mai Tsarki ya fi ma nanata hakan. Ya ce: “Allah mai nagarta ne da babu kamarsa!” (Zakariya 9:17, New World Translation) Amma kamar dai mutane kalilan ne ainihi suka fahimci abin da waɗannan kalmomi suke nufi. Mece ce nagartar Jehobah Allah ainihi ta ƙunsa, kuma yaya wannan halin Allah ya shafi kowannenmu?
Fitaccen Ɓangare na Ƙaunar Allah
3, 4. Mece ce nagarta, kuma me ya sa ya fi a kwatanta nagartar Jehobah da cewa nuna ƙauna ce ta Allah?
3 A cikin harsuna da yawa na zamani, “nagarta” kalma ce da ta zama ta kullum. Amma, kamar yadda aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki, nagarta ta wuce abu na kullum. Ainihi, tana nufin kirki da kuma tarbiyya mai kyau. Wato, za mu iya cewa Jehobah yana da alheri ƙwarai. Dukan halayensa—haɗe da iko, shari’a, da kuma hikima—suna da kyau ƙwarai da gaske. Har wa yau, nagarta za a kwatanta ta da kyau idan aka ce nuna ƙauna ce na Jehobah. Me ya sa?
4 Nagarta hali ne da ake yi, ana yi wa wasu. Manzo Bulus ya nuna cewa a wajen mutane ta fi adalci ma ban sha’awa. (Romawa 5:7) Za a iya tabbata cewa mutum mai adalci zai bi abin da doka take bukata daidai, amma nagarin mutum zai yi fiye ma da haka. Zai ɗauki zarafi, yana neman hanyoyin da zai amfani wasu. Kamar yadda za mu gani, Jehobah babu shakka nagari ne a wannan hanyar. Alhali ma, irin wannan nagartar ta taso ne daga ƙaunar Jehobah marar iyaka.
5-7. Me ya sa Yesu ya ƙi a kira shi “Malam managarci,” kuma wace gaskiya ce mai zurfi wannan ya tabbatar?
5 Jehobah farda ne wajen nagartarsa. Ba da daɗewa ba kafin Yesu ya mutu, wani mutum ya dumfare shi, ya yi tambaya, ya kira shi da “Malam managarci.” Yesu ya ce: “Don me ka ke ce da ni managarci? Babu wani managarci sai ɗaya, Allah.” (Markus 10:17, 18, NWT) Wannan amsar za ta ba ka mamaki. Me ya sa Yesu ya yi wa mutumin gyara? Shin Yesu, hakikanin gaskiya, ba “Malam managarci” ba ne?
6 A bayyane yake cewa mutumin ya yi amfani da kalmomin “Malam managarci” laƙabi ne na ɗaukaka. Yesu cikin filako ya ba da wannan ɗaukaka ga Ubansa na samaniya, wanda shi ne ƙarshen nagarta. (Karin Magana 11:2) Yesu yana kuma tabbatar da gaskiya ce mai zurfi. Jehobah ne kaɗai mizani na abin da yake da kyau. Shi ne kawai yake da cikakken iko ya kafa abin da yake da kyau da abin da ba shi da kyau. Adamu da Hauwa’u, ta wajen cin itacen sanin nagarta da mugunta cikin tawaye, sun nemi su ɗauki wannan matsayin ga kansu. Ba kamar su ba, Yesu cikin tawali’u ya bar kafa mizanin a hannun Ubansa.
7 Bugu da ƙari, Yesu ya sani cewa Jehobah shi ne tushen dukan abin da yake da kyau da gaske. Shi ne mai ba da “kowace baiwa mai kyau, da kowace cikakkiyar kyauta.” (Yakub 1:17) Bari mu bincika yadda nagartar Jehobah ta bayyana cikin karimancinsa.
Tabbaci na Yawar Nagartar Jehobah
8. Ta yaya Jehobah ya yi nagarta ga dukan mutane?
8 Duk wanda ya taɓa rayuwa ya amfana daga nagartar Jehobah. Zabura 145:9 ta ce: “Ubangiji mai alheri ne ga kowa.” Mene ne misalin wasu nagartarsa da take ga dukan mutane? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bai taɓa barin kansa babu shaida ba, saboda yana yin alherin ba ku ruwan sama da damina mai albarka. Yana ƙosar da ku da abinci a daidai lokaci, yana kuma sa ku yi farin ciki.” (Ayyukan Manzanni 14:17) Ka taba farin ciki sa’ad da kake cin abinci mai ɗanɗano? Idan ba don Jehobah cikin nagartarsa ya zana tsarin kewaya na ruwa na wannan duniya ba, da kuma “damina mai albarka” ta ba da yalwar abinci ba, da babu jibi. Jehobah yana yin nagartarsa ba kawai ga waɗanda suke ƙaunarsa ba amma ga kowa. Yesu ya ce: “Wanda yake sa rana ta yi haske a kan masu kirki da marasa kirki ma, ya kuma aiko ruwan sama a kan masu adalci da marasa adalci.”—Matiyu 5:45.
9. Ta yaya gawasa ta kwatanta nagartar Jehobah?
9 Mutane da yawa suna wasa da karimanci da aka tara bisa mutane domin aiki mai ci gaba na rana, ruwan sama, da kuma damina mai albarka. Alal misali, ka yi la’akari da ’ya’yan gawasa. A dukan wajaje masu sanyi na duniya itace ne gama gari. Duk da haka, yana da kyan gani, yana da zaƙi, kuma yana cike da ruwa mai wartsakarwa da kuma abubuwa na gina jiki. Ka sani cewa da akwai gawasa iri-iri har 7,500, da suke da launi daga ja zuwa mai ruwan zinariya zuwa mai ruwan ɗorawa zuwa kore kuma girmansu daga wadda ta fi ’ya’yan magarya kaɗan zuwa girman manyan lemo? Idan ka riƙe ƙwayar iri na gawasa a hannunka, kamar ba shi da wani muhimmanci. Amma daga shi ɗaya ake samun itatuwa masu kyan gani. (Waƙar Waƙoƙi 2:3) Kowacce bazara itacen gawasa yakan cika da dami dami na furanni; kowacce kaka sai ta yi ’ya’ya. Kowacce shekara—har zuwa shekara 75—matsakaicin itacen gawasa zai yi ’ya’ya isashe da zai cika kwali 20 da kowanne zai kai nauyin kilogiram 19!
Jehobah yana “ba ku ruwan sama da damina mai albarka”
Daga wannan ƙwayar ’yar mitsitsi irin itace yake girma ya ciyar kuma ya faranta wa mutane rai na shekaru da yawa
10, 11. Ta yaya ƙofofin hankali suke nuna nagartar Allah?
10 Cikin nagartarsa marar iyaka, Jehobah ya ba mu jiki da ‘ƙirarsa abin al’ajabi’ ne, da ƙofofin hankali da za su taimake mu mu ga ayyukansu kuma mu yi farin ciki. (Zabura 139:14) Ka yi tunanin yanayi da aka kwatanta a farkon wannan sura. Mene ne da ake gani ke kawo farin ciki a irin waɗannan lokatai? Yaro mai farin ciki domin ƙoshin lafiya. Yadda ruwa ke zubowa bisa gonaki. Launi ja, ruwan zinariya, da kuma ruɗa kuyangi. An tsara idon ɗan Adam ya bambance launuka dabam dabam dubbai, wataƙila ma miliyoyi! Kuma ƙofar hankalinmu ta ji tana bambance ƙarfin sauti a murya da muke ƙauna ƙwarai, raɗa ta iska a kunnen itatuwa, dariyar farin ciki ta jariri. Me ya sa muke iya ji da kuma gani? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kunne domin ji, ido kuma domin gani, Yahweh ne ya yi su duka.” (Karin Magana 20:12) Amma waɗannan ƙofofi ne biyu kawai na hankali.
11 Ƙofar hankali ta jin ƙamshi wata tabbaci ce ta nagartar Jehobah. Hancin ɗan Adam zai iya ya bambance ƙamshi da wari da yawa dabam dabam, wajen dubbai zuwa tiriliyon ɗaya. Ka yi tunanin ’yan kaɗan kawai: ƙamshin abinci da ka fi so, furanni, na ganye, warin hayaƙin wuta. Ƙofar hankali ta ji a jiki tana sa ka ji iska tana shafar fuskarka, runguma ta tabbaci ta wadda kake ƙauna, da kuma santsin ’ya’yan itace a cikin tafin hannunka. Idan ka kafa masa haƙori, ƙofar hankali ta ɗanɗano ta samu aiki. Sai ka ji ɗanɗano daga ruwan ’ya’yan itacen, kana jin daɗin abin da ke ƙunshe cikin ’ya’yan itacen. Hakika, muna da dalilai na cewa game da Jehobah: “Ina misalin yawan alherinka, alherin da ka shirya wa masu tsoronka!” (Zabura 31:19) Ta yaya Jehobah ya “shirya” alheri ga waɗanda suke da tsoron Allah?
Nagarta Mai Madawwamiyar Fa’ida
12. Waɗanne tanadi ne na Jehobah suka fi muhimmanci, kuma me ya sa?
12 Yesu ya ce: “An rubuta a cikin Rubutacciyar Maganar Allah cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga wurin Allah.’ ” (Matiyu 4:4) Hakika, tanadin Jehobah na ruhaniya za su amfane mu fiye ma da na zahiri, domin za su kai zuwa rai madawwami. A Babi na 8 na wannan littafin, mun lura cewa Jehobah ya yi amfani da ikonsa na maidowa a lokatan nan na zamanin ƙarshe ya kawo aljanna ta ruhaniya. Muhimmiyar aba ta wannan aljannar ita ce abinci mai yawa na ruhaniya.
13, 14. (a) Mene ne annabi Ezekiyel ya gani a wahayi, da wace ma’ana a gare mu a yau? (b) Wane tanadi ne na ruhaniya Jehobah ya yi wa bayinsa masu aminci?
13 A cikin annabce-annabce masu girma na Littafi Mai Tsarki, an ba wa annabi Ezekiyel wahayi na haikali mai girma da aka maido da shi. Daga cikin haikalin ruwa ya malalo, yana daɗa faɗi kuma yana zurfi yayin da yake tafiya har sai da ya zama kogi. Duk inda ya bi, kogin zai kawo albarka. A bakin kogin da akwai itatuwa masu ba da ’ya’ya don abinci da kuma warkarwa. Kogin har ma ya ba da rai da kuma amfani ga kogi marar rai, mai gishiri, Mataccen Kogi! (Ezekiyel 47:1-12) Mene ne wannan duka yake nufi?
14 Wahayin haikalin yana nufin cewa Jehobah zai maido da tsarin bautarsa ta gaskiya. Zai jitu da ƙaꞌidodinsa na adalci. Kamar wannan kogin na wahayi, tanadin Allah na rayuwa zai malalo a yalwace ƙwarai ga mutanensa. Tun da aka maido da bauta ta gaskiya a shekara ta 1919, Jehobah ya albarkaci mutanensa da tanadi mai ba da rai. Ta yaya? Littafi Mai Tsarki, littattafai na Littafi Mai Tsarki, taro, da kuma taron gunduma dukansu suna kawo muhimmiyar gaskiya ga miliyoyi. Ta wannan hanyar Jehobah ya koya wa mutanensa game da tanadi mafi muhimmanci don rai—hadayar fansa ta Kristi, wadda take kawo matsayi mai tsabta a gaban Jehobah da kuma begen rai madawwami ga dukan waɗanda suke ƙaunar kuma ke tsoron Allah da gaske.a Saboda haka, a cikin dukan wannan kwanaki na ƙarshe, yayin da duniya tana fama da ƙarancin abinci na ruhaniya, mutanen Jehobah suna more dina na ruhaniya.—Ishaya 65:13.
15. A wace hanya ce nagartar Jehobah za ta malalo zuwa ga mutane masu aminci a lokacin Sarautar Kristi ta Alif?
15 Amma kogin wahayi na Ezekiyel bai daina malalowa ba sa’anda wannan tsohon zamani ya zo ƙarshensa. Akasarin haka, zai malalo ma fiye da haka a lokacin Sarautar Kristi ta Alif. Sai ta wajen Mulkin Almasihu, Jehobah zai yi amfani cikakke da tamanin hadayar Yesu, a hankali a ɗaukaka mutane masu aminci zuwa kamilci. Lallai sa’an nan za mu ɗaukaka nagartar Jehobah!
Ƙarin Ɓangarori na Nagartar Jehobah
16. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa nagartar Jehobah ta haɗa da wasu halaye, kuma waɗanne ne wasu a cikinsu?
16 Nagartar Jehobah ta ƙunshi fiye da karimanci. Allah ya gaya wa Musa: “Zan sa dukan darajar alherina ta wuce a gabanka, zan kuma yi shelar Sunan nan Yahweh a gabanka.” Labarin ya ci gaba da cewa: “Yahweh kuwa ya wuce a gaban Musa ya ce, ‘Ni ne Yahweh, ni ne Yahweh! Allah mai jinƙai ne, mai alheri, marar saurin fushi, mai yawan ƙauna marar canjawa, cike da aminci kuma.’ ” (Fitowa 33:19; 34:6) Saboda haka nagartar Jehobah ta haɗa da wasu halaye masu kyau. Bari mu bincika biyu kawai cikinsu.
17. Mene ne alheri, kuma yaya Jehobah ya nuna ta ga mutane turɓaya, ajizai?
17 “Mai-alheri.” Kalmar nan da aka fassara alheri tana iya kuma nufin “tausayi.” Wannan halin ya gaya mana game da yadda Jehobah yake bi da halittunsa. Maimakon ya kasance babu taushi, marar tausayi ko kuma azzalumi, kamar yadda yake sau da yawa da masu iko, Jehobah yana da kamewa da kuma kirki. Alal misali, Jehobah ya gaya wa Abram: “[Ina roƙonka ka] ɗaga inda kake tsaye, ɗaga idanunka ka duba ta arewa, da ta kudu, da ta gabas, da ta yamma.” (Farawa 13:14) Fassara da yawa sun cire kalmar nan na nuna ‘roƙo.’ Amma manazartan Littafi Mai Tsarki sun lura cewa kalmomin asali na Ibranancin sun haɗa da kalma da ta canja furucin daga umurni zuwa roƙo. Da akwai wasu yanayi masu kama da haka. (Farawa 31:12; Ezekiyel 8:5) Ka yi tunani, Mamallakin dukan halitta ya ce ‘ina roƙo’ ga mutum turɓaya! A duniyar da mugunta, baƙar magana, da rashin hankali suka zama ruwan dare, ba ya wartsakarwa ne mu yi bimbinin alherin Allahnmu, Jehobah?
18. A wace hanya ce Jehobah “mai-yalwar . . . gaskiya,” kuma me ya sa waɗannan kalmomin suke ba da tabbaci?
18 “Mai-yalwar . . . gaskiya.” Rashin gaskiya ya zama hanyar rayuwa a duniya ta yau. Amma Littafi Mai Tsarki ya tuna mana cewa: “Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya!” (Littafin Ƙidaya 23:19) Alhali ma, Titus 1:2 ta ce: “Allah, . . . ba ya ƙarya.” Nagartarsa ba za ta ƙyale shi ba ya yi ƙarya. Saboda haka, alkawuran Jehobah tabbatattu ne ƙwarai; maganarsa, kullum a tabbace take, za ta cika. An kira Jehobah ma “Allah na gaskiya.” (Zabura 31:5, New World Translation) Ba kawai ba ya ƙarya ba amma kuma yana ba da gaskiya mai yawa. Ba a rufe yake ba, ko kuma ya ɓoye saƙo, ko kuma asirce; maimakon haka, yana faɗakar da bayinsa masu aminci daga ma’ajin hikimarsa marar iyaka.b Har yana koya musu yadda za su rayu cikin gaskiya da yake bayarwa saboda su je su ci gaba da “bin gaskiya.” (3 Yohanna 3) Galibi, yaya ya kamata nagartar Jehobah ta shafe kowannenmu?
Ka “Yi Haske Saboda Nagartar Jehobah”
19, 20. (a) Ta yaya Shaiɗan ya nemi ya yi wa dogarar Hauwa’u ga nagartar Jehobah zangon ƙasa, kuma mene ne sakamakon haka? (b) Yaya nagartar Jehobah ya kamata ta shafe mu, kuma me ya sa?
19 Sa’ad da Shaiɗan ya jarabci Hauwa’u a lambun Adnin, ya fara a hankali wajen yi wa dogararta ga nagartar Jehobah zangon ƙasa. Jehobah ya gaya wa Adamu: “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace na gonar.” A dukan dubban itatuwa da wataƙila suke lambun, ɗaya ne kurum Jehobah ya saka wa mutum taƙunƙumi a kai. Duk da haka, ka lura da yadda Shaiɗan ya yi tambayarsa: “Ko Allah ya ce, lallai ba za ku ci daga kowane itacen da yake a gonar ba?” (Farawa 2:9, 16; 3:1) Shaiɗan ya murɗe kalmomin Allah ya sa Hauwa’u ta yi tunanin cewa Jehobah yana hana su wani abu mai kyau. Abin baƙin ciki, kissar ta yi nasara? Hauwa’u, kamar mutane da yawa maza da mata daga bayan ta, ta fara shakkar nagartar Allah, wanda ya ba ta dukan abin da take da su.
20 Mun san zurfin baƙin ciki da azaba da wannan shakkar ta jawo. Saboda haka bari mu riƙe a zuciyarmu kalmomin Irmiya 31:12: “Za su haske saboda nagartar Jehobah, NWT.” Ya kamata nagartar Jehobah ta samu farin ciki da annuri. Bai kamata mu yi shakkar Allahnmu ba, wanda yake cike da nagarta. Za mu iya dogara gare shi ƙwarai, domin dukan abin da yake nema nagari ne ga waɗanda suke ƙaunarsa.
21, 22. (a) Waɗanne hanyoyi ne za mu so mu yi na’am ga nagartar Jehobah? (b) Wane hali ne za a tattauna a babi na gaba, kuma ta yaya ya bambanta da nagarta?
21 Ƙari ga haka, sa’ad da muka samu zarafi mu yi magana da wasu game da nagartar Allah, mu yi farin ciki a yin haka. Game da mutanen Jehobah, Zabura 145:7 ta ce: “Za su ɓarke da shelar yawan alherinka.” Kowacce rana da muke raye, muna amfana a wata hanya daga nagartar Jehobah. Me ya sa ba za ka yi ƙoƙari ka riƙa yi wa Jehobah godiya kowacce rana domin nagartarsa, ka faɗi takamammun abubuwa? Ka yi tunanin wannan halin, ka riƙa godiya ga Jehobah kowacce rana, kuma ka gaya wa wasu game da ita za ta taimake mu mu yi koyi da Allahnmu nagari. Yayin da muke neman hanyoyin da za mu yi nagarta, kamar yadda Jehobah yake yi, mu kusace shi sosai. Tsoho manzo Yohanna ya rubuta: “Ya abokina wanda nake ƙauna, kada ka bi mugun gurbi, a maimakon haka, ka bi gurbin kirki. Duk mai aikin kirki na Allah ne.”—3 Yohanna 11.
22 Nagartar Jehobah an danganta ta da wasu halaye. Alal misali, Allah “mai yawan ƙauna marar canjawa” ne, ko kuma ƙauna ta aminci. (Fitowa 34:6) Wannan halin ba kamar nagarta ba, takamaimai ne, domin Jehobah yana nuna shi musamman ga bayinsa masu aminci. A babi na gaba za mu koyi yadda yake yin haka.
a Babu wani misali na nagartar Jehobah mafi girma fiye da na fansa. Dukan yawan miliyoyin halittu na ruhu da zai zaɓa daga ciki, Jehobah ya zaɓi Ɗansa makaɗaici wanda yake ƙauna, ya mutu dominmu.
b Ya dace da Littafi Mai Tsarki ya danganta haske da gaskiya. Ka “aiko da haskenka da gaskiyarka,” yadda mai Zabura ya rera ke nan. (Zabura 43:3) Jehobah yana ba da haske na ruhaniya mai yawa ga waɗanda suke a shirye a koyar da su, ko kuma ya faɗakar da su.—2 Korintiyawa 4:6; 1 Yohanna 1:5.